Shin Aljani Yana Auren Mace?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Wai Dagaskene Aljani Yana Auren Mace, Idan Ya Aureta Hakan Yana Nufin Ba Ita Ba Aure Har Mutuwa? Wadanne Alamomine Suke Tabbatar Da Aljani Ya Auri Mace?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Tabbas dalilai daka alƙur'ani da sunnah sun tabbatar da aljani yana shiga jikin Ɗan Adam mace kona miji, sannan kuma hakika akwai wani nau'in aljani dayake auren mace ko namiji ba tare da mutum yasani ba.

    Amma ba gaskiya bane cewa inya auri mace ba ita ba aure har mutuwa, na'am yana kawowa mace ko namiji matsala wajan yin aure akan kari, ko kuma rabuwa bayan anyi auren, yana shafar budurwa damai aure mace ko namiji.

    Dalilan Dasuke Saka Aljani Auren Mace Ko Namiji

    Shaikul Islam ibnu taimiyyah rahimahullah a cikin maj'mu'u fatawa ɗinsa ya ce:

    Daka cikin dalilan dasuke sa aljani ya auri mutum sune, so, ko sha'awa, ko tsoratar da mutu.

    Jinsin wannan aljani na jinsin mata suna shiga jikin mace cikin mutane tana cutar da ita da ta'addanci tana suranta mata cikin bacci kamar tana madigo da 'yar'uwarta mace, ko abokiyarta, kota dinga jin sha'awar 'yan'uwanta mata da haka hartaji tana san mace 'yar'uwarta so na sha'awa.

    Haka aljani na miji yanaiwa mutum irin wanann illar har mutum yatasirantu dahakan ya auka cikin liwadi,

     

     

    DALILAN DAKESA ALJANI YASAMU NASARAR SHIGA JIKIN MUTUM HARYA AURESHI.

    Daka cikinsu shi ne idan mutum yaburge aljani wannan zaisa aljani yaita bibiyar mutum wajan wasanni da guraren kazanta ko shiga banɗaki koyin fitsari a gidan tururuwa, ko wajan saduwa, ko mace tadunga shigar bayyana tsiraici kirjinta da guraren shawarta duk abayyane, har aljani yaga yasamu wata kofar shiga jikin mutum.

    - Kambun baka ko hassada, maikarfi, daka aljani ko mutum, suna sanya aljani yasamu damar shiga jikin mutum.

    -Yiwa mutum sihiri, wani yaiwa mutum sihiri, Musamman idan aljani da bokan yawakilta namijine jikin mace, ko mace ajikin namiji, wannan shi ne galibin abun da yafi faruwa. Wanann nau'in yakasu kashi kashi

    Akwai shirin alfasha aiwa mutum sihiri dan adunga alfasha dashi.

    ko Sihirin soyayya, shima kashi-kashi ne akwai wanda za a kashewa mutum sha'awa ko tada masa sha'awa.

    Wakilta mazinacin aljani gawanda akaiwa shihirin yadinga alfasha dashi dare da rana.

    -Wakilta aljani bayahude ko kirista ga wanda akaiwa sihirin, musulmi.

    - Aljanin yaiwa mutum sihiri danya dunga saduwa dashi.

    - Nisantar Allah, da wulaƙanta salloli koƙin yinsu, da dulmiya cikin abubuwan da aka haramta, wannan yakan yiwa aljani saukin shiga jikin mutum.

    - idan mutum da kansa yanemi mu'amala da aljani wato ya zama boka.

    -karanta litattafan bokanci da mu'amala dasu.

    Irin wannan aljani idan yashiga jikin mutum mai yakeyi

    Wannan nau'in aljani yana iya yin komai ajikin mutum, tadowa da mutum wutar sha'awa, kawatawa mutum alfasha dason zina, da kalle kallen maza, in macece da kalle kallen mata, inna mjine Hakan zaidunga faruwa ga mutum cikin kutse ba tare daya so hakan ba.

    harkisa aljanin yanayi yadanganta da yanayin aljanin kafiri ko musulmi, wani zakaga musulmine yanasa mutum aikin ɗa'a dabin Allah, aljanin yana taimaka masa wajan san aikin alkhairi, amma tare dahakan shi aljanin yana biyan bukatarsa ajikin wanda yashigeshin, yana iya kasancewa kuma kafiri yadinga yiwa mutum makirci, cikin ibadarsa, aljanin dayake jima'i damace yana iya yin komai wanda mutum zaiji alamun yana yare da Shaiɗanin aljani.

     

     

    ALAMOMIN DA'AKE GANE MUTUM YANA TARE DA NAU'IN WANANN ALJANI

    1- Yawan mafarki, amma mafarkin wanda yadanganci ganin namiji tsirara, ko ganin mace tsirara, ko jima'i da muharrami damakamantansu.

    2- Jin sha'awa ba tare da wani dalili ba, kojin sha'awar muharrami, basaida Mai aure ba kawai.

    3- Ƙin miji darashin sha'awarsa, in budurwace taji kwata kwata bata sha'awar namiji.

    4- Jin kamar ana jima'i damace ko ana mata wasa da farji kojin motsi afarjin, motsin maitada sha'awane ko kawai motsin takeji, ko jin motsin jima'i.

    6- jin kamar wani yana biye dakai abayanka inkana tafiya kojin kamar wanine abayanka kuke bacci tare dashi. Kojin kamar wanine kusa dake akan gado yake numfashi.

    7- Namiji yadunga jin mace tare dashi, ko cikin wandansa, koyajita cikin al'aurarsa.

    8- Wasu matan za su dunga ganin namji tsirara a nau'ika kala-kala, kuma yana saduwa da ita, a cikin barci ko ido abude.

    9- Miji yadinga gujewa matarsa yadunga bacci nesa da ita, gabansa yadunga faduwa idan takusanceshi, dasan zama shi kaɗai, sai ya shafe watanni masu yawa bai sadu da matarsa ba.

    10- Mata tadinga gudun mijinta kuma tana yawan fitar ruwa daka farjinta, da kiyayya dagadar da matsaloli da nauyin jiki, mace taji batasan ko shafa jikinta mijinta yayi, watama hatta 'ya'yanta bataso su tabata, dasan zama ita kaɗai, dakwanciya kamar tsirara tsirara, da dogon bacci nalokaci maitsawo.

    11-Rashi ko raunin gabobi ko saurin kawowa yayin jima'i, dajin ciwo karkashin cibiya, da yatsu kamar suka daciwo da budewar dubura, dajin wani abu a cikinta.

    12- Rashin bacci da daddare, dazama lokaci maitsawo a cikin banɗaki, ko tirken dabobi kozama wajan zub da shara.

    13- Jin kamshin turare a ɗaki ba tare da sanin daka ina kamshin yake tasowa ba.

    14- Yayin jima'i tadunga jin wanda yake jima'in nan da ita ba mijinta bane, ko bayan gama jima'i taji wani yana jima'i da ita wanda ba mijinta bane.

    15-Wasu yara za su dunga bijirowa mutum yafarka yaga kayansa antube masa, yadunga hakaito wani abu na jima'i wanda baisan ma'anarsa ba,

    16- Jin sha'awa mai tsanani dakarkatuwa zuwa luwadi ko madigo,.

    17- Budurwa tadunga kuka idan wani ya zo neman Aurenta, ko saurayi yaguji budurwa bayan sun yi yarjejeniyar aure, da wasu uzurori waɗanda ba karɓaɓɓu ba, ko kuma inyatafi ba zai sake dawowaba, tare dacewa mace tanada dukkan abun da ake son mace nakyawu da kamala.

    18- Mutum yai iya yinsa amma kememe matarsa taƙi yarda dashi, yai aure yasaki, ko taki yarda dashi saidai araba aurensu,

    19- Namiji yaji baya iya kallan mata, yakanji radadi ma idan yai magana da mace, ko gumi yadunga keto masa, wasu suna ɗaukar hakan kamar kunyace, na'am akwai nakunya akwai kuma na aljani, koya dunga jin motsi ajikinsa.

    19- jin ciwo al'aura da bayansa, dajin tafiyar wani abu kaman kiyashi ko da yaushe,

    20- Jin ciwo a azzakari ko makwallato, ko mahaifa, ko wajan bahaya.

    21- Daka cikin abubuwanda da'ake gane Aljanin dayake auren mutum shi ne karanta ayoyinda dasuke zargin zina ko alfasha su kaɗai, yayin yiwa mara lafiyar/mara lafiyan ruƙya, Suna tasiri akan aljanin, ko da aljanin yana cikin nau'in aljanu masu tashi kamar tsuntsaye zai bayyana.

    za mu dakata anan in Shã Allahu za mu karasa kawo cikwan bayanin, munkuma tsawaita dan kada mutakaita kuma adamemu da tambayoyi da suka shafi wannan janibin mukuma bashi ne aikin muba.

    🖊 Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄��𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.