4) GAZAWAR ABOKIN ZAMA: Daya daga cikin abubuwan dake daga kishin matammu ke nan na Hausa/Fulani, wani sa'in ka rasa wanda za ka ba wa laifi, don duk wanda ka daga da sauran kashi a duwawunsa. abin da na fi gani kawai muna aurar da yaranmu mata ba tare da sun san me za su je su yi ba, ba abu ne da za a gaya wa amarya na kwana daya ko biyu a ce ta iya ba. Tun tana ƙaramar yarinya ya kamata a ce ta fara koyo yadda za ta zauna da maigida, tun daga dafa abinci, har gyare-gyaren gida da tsabta, zuwa yadda za a yi magana da maigida.
Wasu ƙabilun sun nisa a wannan bangaren, shi ya sa in Bahaushe ya auro wata daga cikinsu sai ka ga duk wanda ya han su sai ya fara sha'awarsu. Ba yadda za a ce maigida ne zai koya wa mace yadda za ta so shi, kamata ya yi a ce da abinta ta zo. A ido dai tana ganin zamantakewar dake tsakanin mamanta da babanta, sannan ana saka ta tana yin wasu abubuwan, kuma ana gaya mata a baki cewa yadda za ta riƙa yi ke nan idan ta yi aure, duk dan kuskure in ta yi za a kambama shi cikin raha "Ke haka za ki riƙa yi in muka kai ki gidan mijin? Ai sai ya ce kaza da kaza!" Da haka har a gama koya mata komai.
To idan ta zo gidan aure ba wani sabon abu da za ta gani, ba ta da buƙatar a ce mata "Yi kaza" ta riga ta yi shi tun kafin a nema. Ta san yadda ake tarairayar namiji, a yi masa duk abubuwan da yake buƙata. Ta mai da shi wani sarki a cikin gidansa, zaki a gaban yaransa, in ya ba da abu kadan a yaba a yi godiya, in ya yi kuskure a yi dariya sannan a fada masa laifinsa ba tuhumarsa ake yi ba, in an dan yi kuskure a ba shi haƙuri kafin ya sani ya yi magana, shi da kansa bai da buƙatar wata mace in ta gida ta rufe duk barakar da yake fama da su. To matsalar uwaye mata ba sa maida hankali kan wadannan abubuwan masu mahimmanci.
Lokacin da za su yi wa mazansu hidima yaran ba sanan, kodai suna makaranta, ko suna kasuwa. Yaran masu hali kuma suna can bangarensu daban suna fama da waya ko fima-fiman soyayya wadanda suka bambanta da namu. Ba abin da suke koyo a wurin uwayen sai kishi na hauka saboda galibin abin da za a yi ko dai uwayen su gaya musu ko a yi a gabansu. abin da ya zama dole a kan uwayen ba su yi ba sun je suna fada a kan abin da ba su da haƙƙi. Duk kishin da mace za ta yi na banza ne. Ba za ta iya gyara komai ba sai ta yi abin da ake buƙata a wurinta.
To mu ma mazan fa ba wai mun san kan auren ne ba a lokacin da muke ƙoƙarin yi. Galibin samari kan fara tunanin aure ne idan dayan abu uku ya samu: Kodai an girma gabobin sha'awar mutum sun fara aiki. Ko kuma galibin abokansa sun yi mata shi kadai ne bai yi ba, har sun fara yi masa lalata. Ko ya sami abin hannunsa ya kamata a ce yana da iyali, zai iya kashe duk abin da ake buƙata don ganin ya yi auren. Amma akwai abin da ya fi wadannan mahimmanci abin takaici ba ma kallonsa.
Wato ya ake zama da mace? Dole a karance ta a dabi'arta; wani abu ne in ta yi tabbas da gangan ta yi, wani abu ne yake kuskure? Ya ya kamata a yi ma'amalla da mace a lokacin al'ada ko sa'in da take da ciki? Wasu abubuwa ne ya kamata a kau da kai, wani sa'i ya zama dole a yi magana? Me ya kamata a koya mata wani abu ne ya zama dole a yi haƙuri da shi? Me da me ya kamata ka kawo gida a matsayin wajibi mene ne kyautatawa? Da wace murya ya kamata ka riƙa magana da matar? Wasu abubuwa ne suka zama dole ka tsaya sai an canja don kauce wa gaba? Wasu abubuwa ne za ka yi kamar ba ka gansu ba? In za ka tsawata ya za ka yi, a ina za ka yi?
To in irin wadannan ba su samu ba tabbas matar ba za ta ji dadin zama da mijin ba, ita ma ƙila ta fara daukar mataki a ƙarshe sai a fara fito na fito tsakaninta da shi, sai maganar saki ko ƙara wani auren. Amma in aka dubi duka bangarorin guda biyu ba wanda bai da laifi. Gaskiya mu maza muna buƙatar sanin yadda za mu zauna da matan. A yi haƙuri muna wuce gona da iri a wasu abubuwan kuma mu ce dole mu muke da gaskiya. Alhali mu ma muna da namu kuskuren, muna hada abin da bai haduwa kuma mana so a zauna lafiya.
Mutum Allah ya hore masa halin da zai sanya kowace mace a gidanta ita kadai, amma ya hada mata a gida daya suna amfani da kicin daya, ƙila ma falo daya makewaya daya. Sannan in sun wuce gona da iri mu ce sun yi rashin hankali. Na taba yi wa wani mutum magana, mai arziƙi ne, kan raba su kowace mace gidanta daban. Sai ya ce "Kowace mace abincinta daban ke nan za ta yi?" Yana kallon kudin da zai kashe, bayan kullum cikin bala'in kishinsu yake.
Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.