KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 29

    2) YARDA AKAN GASKIYA: Mukan saka yarda ba a mahallinta ba, hakan kuma kan jawo kishi, mun sani akwai yardar da ko ba a gaya wa mutum ba ya san a kan kuskure aka yi ta, wanda aka yi masa bai cancance ta ba, ka lura da kyau, galibin masu wasa da muggan dabbobi kamar macizai, zakoki da sauransu su ke zama ajalinsu, saboda sun amince wa wanda bai kamata su amince masa haka ba. Kowa ya san wadannan dabbobin ba mutane ne ba, kuma alaƙarsu da mutum kisa ce, amma mutum ya saki jiki da cewa ba za su taba yi masa komai ba, bayan ba haƙoransu aka cire ba ba bakunansu aka rufe ba.

    A taÆ™aice yadda aka san dabbobinnan da gaba tsakaninsu da duk  abin da suke gani abincinsu ne in suka sami dama kuma za su ci, haka Allah SW ya halicci namiji da son mace. Ko ya furta ba zai Æ™ara aure ba ba abin sakankancewa ne ba. Halittarsa ce in ya ga wata zai so, dan dalili Æ™arami zai canza magana, in ba haka ba ko ya yi Æ™oÆ™arin zama da mace daya kadai ba za ta ishe shi ba sai ya Æ™ara da wata a waje, kin ga kuwa da a yi haka gwara ya bi ta kyakkyawar hanya ya aure wace yake so. Na sha fadin cewa: Duk namijin da ya ce wa matarsa "Ke kadai ce tauraruwa a sararin samaniyata!" Kuma ta yarda ta yaudari kanta.

    Abinda ya sa na fadi haka ba a samun tauraruwa daya a sama, Æ™ila dai daya ce ido yake iya gani amma sauran nanan a boye. In dare ya yi dare gari ya yi duhu tsab za su fito sarari. Haka ba yadda za a yi mutum don jin dadi ya ce wa mace "Ke kadai ce fure a cikin lambuna" Ba a yin Æ™aton lambu kuma a saka fure Æ™wara daya tal, duk yadda namiji zai ce miki ba ya neman mata ba zan ce kar ki gasgata shi ba, Æ™ila Allah ya riga ya shirya shi, sai ki taimake shi ki yi masa duk  abin da zai hana ya nemi wata din.

    Na farko in kika masa  abin da zai sa hankalinsa ya dawo kanki ke kadai kin taimake shi a kan shiriya. Na biyu kin hana shi yi miki kishiya idan ya ga zamansa dake yana samun duk  abin da yake buÆ™ata ba sai ya Æ™aro aure ba. Tunda sai ya yi sha'awar wata zai neme ta, ke kuma kina yin  abin da ba zai iya sha'awar kowa ba. A taÆ™aice dai kin magance matsalarki. Mu a Hausa da maÆ™wabtanmu ko mutum bai da sha'awar Æ™ara aure akwai abubuwan da za su saka shi dole ya Æ™ara, koda kuwa ya ce miki daga ke sai ke ba wata.

    Misali akwai wata kwalliya da in mace ta yi za ta dauke hankali maigida, ke kuma gaskiya ba a tarbiyantar dake yinta ba lokacin da kike gida, kuma a addinance ba haramun ne yinta, dole ki koya in ba ki iya ba. In kuma kin iya me zai hana ki fara yi don ganin kin biya masa buƙata ke ma kin biya taki? Ƙarƙarinki dai kar idonsa ya je wurin wata? To in kika hana ai kin ci riba, In ba haka ba ko shakka babu labari zai canza.

    Mu dauki lalle a matsayin misali. Wasu mazan ba su damu da shi ba ko kadan, mace kan kashe kudinta ta ba ta lokaci wurin yinsa don ta burge maigida kawai, ta san kowa ya gani dole ya jinjina har mata bare maza, in ta ga ko kallonsa bai yi bare ya yaba, ashe shi ba kwalliyar da yake so ba kenan, an ajiye abu ba a mahallinsa ba. Wani kuwa ba  abin da yake so kamar lallen, sai kuma aka yi dace iyalin ta sa ba ta da lokacin yinsa, ko yanayin wayewarta bai ba ta damar yi, ko jikinta bai karbarsa, a irin wannan yanayin sai ta kwashe shekaru ba ta diga lalle a hannunta ba bare Æ™afa. Amma fa za ta kashe kudi a kan hoda da man-gashi, dilka da sauransu.

    To a irin wannan yanayi ko za ta kashe kudinta gaba daya a kansu ba zai yaba ba don ba  abin da yake so take yi masa ba. Idan ya Æ™yalla ido ya hango na wata yadda yake Æ™yalÆ™yalinnan yake daukar zuciya, take zai Æ™yasa, sai sha'awarta ta kama shi, nan zai fara son gani yana Æ™arawa in aka yi dace wani bai riga shi ba zai fara magana da ita, sai dai uwargida ta fara surutai da cewa ya saba alÆ™awarin da ya yi mata na cewa ba zai Æ™ara aure ba sai bayan shekara goma, ga shi ko biyu ba a hada ba ya fara saka ido a mata.

    Anan gaskiya ita ce ba ta taimaka masa ba wajen cika alkawarin da ya yi mata. Me ya hana ta yi masa adon da yake buÆ™ata? Duk mace ta san mijinta sama da duk yadda wani ya san shi. An kai matsayin da in ka yi wa mace wani irin kallo ba ita ba ko ta kusa da ita za ta gane. Wannan misali daya na kawo, amma irinsa ya shafi abinci: in mutum dan boko ne za ki ga yana son rayuwa da irin ciyeyennan na 'yan boko. In kuma dan Arabiyya ne yana son shayi da irin kayan da Larabawannan suke ci, ke ma canza ki zama irinsa, yi masa  abin da yake so sai a zauna lafiya.

    Akwai wata dali ata mace ce babba na ji ta tana lissafo manyan 'yan ƙwallonnan da ƙongiyoyinsu da abubuwan da suke yi. Na ga a shekarunta dai bai dace ta ba ta lokacinta wurin ƙwallo ba, yaranta maza ma sun yi aure bare matan, amma gatacan tana gardama da yara. Koda na tambaye ta dalilin haka sai ta ce min "To malam maigida baida abin yi sai kallon ƙwallo, na yi ƙoƙarin canja shi na ga abin zai kawo min damuwa, haka na bi shi muka zama daya don dai na sami kwanciyar hankali.

    Komai tsakar dare in dai za a buga Æ™wallonnan tare za mu kalla, team dinmu daya da shi, dukammu muna da rigarsu, in za su yi sai mu saka mu dauko hana salla mu kakara mu zauna cikin yara muna kallo muna gardama". Wannan bai yi min ba amma ina da darasin da na dauka a ciki. Ta iya Æ™irÆ™iro wa kanta jin dadi cikin  abin da ba ta so, ba ta saba masa ba bare ya nemo wace za ta yi daidai da shi ta zo tana zargin ta yarda da shi amma ya ha'ince ta ya yi mata kishiya.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.