KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 28

    KISHI A MATATTARARMU

    Akan sami bambancin yadda ake nuna kishi tsakanin ƙasa zuwa ƙasa, gwargwadon bambancin addini da wayewa. Akwai matattarun da in maigida ya dawo ya tarar da wani ƙato da matarsa a gidansa suna cin abinci suna hira, kawai za ta gabatar da baƙon ne da cewa abokinta ne ko abokin karatunta ne ko wani abu shi ke nan an wuce wurin, in maigidan ransa bai kwanta da shi ba sai ya wuce su ya shiga daki.

    In kuma ransa bai baci da shi ba sai ya zauna tare da su a ci gaba da hirar har baÆ™on ya kama gabansa. Wani lokacin ma maigidan kan fita ya samo musu kayan Æ™walan da maÆ™ulashe don faranta wa iyalinsa. Za ta ji dadi sosai don ya karrama ta. Wannan kenan, a al'adance kuwa 'yan shekarun baya na san wasu 'yan Æ™abilu da in suka yi baÆ™o maigidan kan karrama shi da duk  abin da yake da shi har da iyalinsa, zai bar musu dakin su kwana tare, cikakkiyar girmamawa kenan.

    Idan muka dawo addini kuwa, akwai wata aƙida da ake jingina ta da muslunci; wace in mutum zai tafi wani ƙauye inda iyalin abokinsa suke, sai a yi musayar matan, shi ya je wurin matar abokin, anan kuma abokin ya riƙa kwana da iyalinsa. Zahiri bai yi kama da muslunci ba amma tunda aƙida ce sai dai addu'ar Allah ya tsare mu da iyalinmu daga fadawa cikin wannan mummunar aƙidar. Matattarar muslunci na da tsari na kare mace a shigarta, maganganunta adonta da sauransu.

    Amma wadanda ba musulmai ba wannan ba ya damunsu, duk wata kwalliya a waje ake barinta duk wanda yake so ya kalla ga shinan, mazansu ba sa damuwa da duk shigar da mace za ta yi, ba wani kishi da mutum zai yi wurin ganin ya killace iyalinsa da yaransa. Saduwa ce kawai ba sa yarda a yi da matansu, amma yaran samari kan shigo har cikin gida su dauke su su tafi da su sai gobe su dawo. Wata ma za ta yi 'yan kwanaki kafin ta dawo, matuƙar uwayen sun san inda suke ko kwana nawa za su yi ba abin damuwa ba ne.

    A musluncin ma akwai wata ƙabila mai mai kwatanta irin wannan, wani sa'in ma in saurayi bai iya yi wa yarinya ciki ba to shakku kan shiga tsakanin iyayen bangarorin biyu, kowa zai ƙi yarda, ya dage kan cewa dansa lafiyarsa lau. Amma ilimin addini na ci gaba da gyaran kura-kuran da ake tafkawa. Dole duk wani maigida ya yi kishin matansa da 'ya'yansa ta wurin ba su tsaro, bisa wannan dalilin ne har wurin ibada sai da aka bambance.

    Wurin maza daban na mata daban. Suturar sallar daban, wata fahimtar ma ba ta bar matan su tafi wuraren sallan ba, in ma sun tafin ba a yarda a ji muryoyinsu ba bare a ga adonsu, in wani abu na ƙara a jikinsu wanda zai nuna cewa mace ce an hana ta motsa shi. Nigeria, masamman Hausa fulani, ana ƙoƙari a kan wannan. In wani ya saba to ya bi son zuciyarsa ne ba addinin ne ya ba shi damar yin hakan ba.

    Daga cikin abubuwan dake sanya Hausa/Fulani kishi akwai:-

    1) YARDA DA KAI: Rashin yarda da kai na daya daga cikin abubuwan da suke saka matanmu kishi, yadda mace za ta riƙa gaya wa kanta cewa wance ta fita, koda kuwa ba ta taba ganinta ba. In aka ce mijinta zai auri Bayarbiya ko Babarbariya sai ka ji sauran mata na cewa "Tab! Wallahi sai kin tsaya in ba haka ba tsab za ta kore ki!" Daganan su fara ambatar iya abinci, ko gyaran jiki, ko biyayya ga miji, ko haƙuri da kadan, ko taimakon miji a cefane, ko yi wa miji hidima da sauransu.

    Ba  abin da ba za ta iya ba a cikinsu, ba wani abu wanda wata mace ke da shi da wata ba ta da shi, mace gaba dayanta ado ce, in wata gabar ba ta kai yadda maigidan yake so ba akwai wata, da komai za ta iya kama maigidanta a hannu. Kamar Barebari da ake yaba musu Æ™amshi da lalle da iya ado da jimirin zaman aure da kame miji ba wani abu da yake halittacce ne a wadannan. ke nan za a iya koyon konnensu a iya. Ba  abin da za a ji tsoro a ciki. Hasali ma mace na da damar da za ta bi kishiyarta a hankali har ta koyi duk  abin da ba ta iya ba. Inda matanmu suke da rauni kenan, in mace ta zo ba ta iya girki ba har ta tsufa ba  abin da zai canza.

    Wace ta zo da wata kalar kwalliya daga gidansu ba za ta iya koyon wace mijin ke buƙata ta yi ba, ma'ana dai ta zama daskararriya ba canji, wannan ke sa dole ta yi kishi, in ba haka ba duk ababan halitta da amarya za ta shigo da su uwargidan na da su, kuma tana amfani da su wurin yi wa maigida hidima to meye na damuwa? Idan suna buƙatar gyara ta koyo yadda ake gyarawar ta gyara ta gani in komai bai canja ba, uwargida na da hanyoyi da dama wadanda ba duka ba zagi ba mummunan kallo za ta riƙe maigidanta a hannu. Kawai ta yarda da cewa amaryanta dinnan mace ce, ita ma haka, in akwai abubuwan da ta rasa ne sai ta yi azama ta samo su.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.