6) KAFOFIN SADARWA: Wasu 'yammatan na kafa hujja da cewa kwalliyar da suke yi da dora hotuna na daya daga cikin hanyoyin da suke samun mazan aure, in hakan ta tabbata to matan aure da suke dora nasu hotunan bayan sun ƙure adaka mazan wasu suke nema ko me? Kun ga dai ƙofar kishi a bude take ga duk wani maigida, masamman yadda matarsa ke neman ta zama ta kowa a irin wadannan kafafen na sadarwa. Ban ga laifin wanda ya hana matarsa shiga wasu kafofin ba masamman waɗanda za su sada ta da duniya ko su koya mata fitsara.
Bare ma
maganar samun miji a kafafen sadarwa ba ta sami karbuwa a wurin mutane da dama
ba, daga malaman addinin har zuwa 'yammata masu kamun kai, sun tabbatar da cewa
yawancin matan da aka lalata su dalilin wadannan kafafen ne namu na sada
zumunta. Ko ba haka ba ma an sami mata da yawa da suka sami mazan aure ta kafar
sadarwar ba tare da sun nuna tsaraici ko sun yi tamfatsa ba, kamun kai din ne
ya kai su ga biyan buƙatunsu. Yana da kyau duk wata mace ta sani cewa kafar
sada zumunci wata duniya ce ta daban wace mutane ke yawo a ciki, ta daina ganin
cewa tana gida ne ko dakin mijinta a waje take, ya rage nata ta sa hijabi ko
tsaya haka.
Ko meye za ta
yi dole ta kula da kanta a matsayin matar aure, ba za ta yi magana ba sai inda
ya zama dole, kuma ta san da wa take magana kuma wace iriyar magana ake yi?
Cikin sauƙi za ta iya zama matar kowa maras kamun kai, domin tana hira da
kowani namiji a kowani irin yanayi. Shi ya sa ya zama dole a kan masu gida su
saka tsaro a wannan sashin ma kamar yadda suke sakawa a lokacin da mace take
gidanta, ba baƙin kishi ba ne. Tsaro a kafofin sada zumunci ya fi wahala sama
da yadda maigida yake ba iyalinsa lokacin da take gida, wannan ba fita za ta yi
ba bare a ce ga inda ta je, ba magana za ta yi ba a wasu lokutan bare a ce ga abin da ta ce.
Hanyoyin da
maigida zai ba iyalinsa kariya ta wannan bangaren suna da wahalar bi don in aka
bar shiri tun rani da wahala a sami abin
da ake so. Manufa ya zamanto in maigida ya ce wa matarsa bai amince da Tiktok,
Youtube, Fesbuk, Snapchat da wasu kafofin ba za ta ji maganarsa ta watsar da
su.
Na biyu ya riƙa
jawo hankalinta ta wurin nuna mata hatsarin dake tattare da wadannan kafofi da
dalilin da ya sa ba ya son ta shige su. Na uku samo mata wasu abubuwan da za ta
shagala da su waÉ—anda ba za su ba ta damar da za ta yi sha'awar shiga a dama da
ita a kafofin ba. Na hudu ya wadata ta da ilimin addini ko ya kai ta inda za ta
samu. Na biyar ya hada da addu'a sauran ya bar wa Allah, amma kafofin sadarwa
tabbas wurare ne da mutum zai yi kishi a kan iyalinsa, don duk wata lalacewa da
tamfatsa tananan sama da yadda ake ganinta a rayuwarmu ta zahiri.
To idan wasu
mazan suka hana matansu hawa kafar sadarwa kowace iri ce kuwa saboda kishi ai
ba su tsananta ba. Wata matar fa ba ta da sirri ko kadan, yadda take bi
gida-gida tana sakin magana ko a kafar sadarwar haka za ka iske ta, tana iya
rufe gidanta ba mai shiga, amma kafar sadarwa ƙofarta a bude ne har cikin
dakinta har kan gadonta tunda kowa na gani, da yawan mata akan san me suke
dafawa a rana, daga safiya har dare, hatta suturarsu da ta maigidan akan sani
bare ta 'ya'yansu. Wasu lokutan duk hotunan da za su yi a cikin dakunansu ne a
akan gadajensu.
Ba don
dauke-dauken mutane da ake yi yanzu ya taka wa wasu burki ba ko tafiya wata za
ta yi sai ta gaya wa mutane inda za ta, da motar da ta shiga da irin kwalliyar
da ta yi, shi yallaboi yana ganin ya tsare iyalinsa a gida ya hana ta fita
aiki, bai yadda ta yi wata sana'a ta wahalar da jiki ba, amma ya sayi waya mai
zafi ya bar ta da ita a gida yadda za ta sami cikakken lokacin da za ta riƙa
saduwa da wasu mazajen a fadin duniya. Kusan da ya bar ta ma ta fita ya fi masa
sauƙi wurin ba ta tsaron da ya kamata, in za ta fita dole dai ana ganin inda za
ta tafi da wanda za ta yi magana sabanin kafofin sadarwa.
Akwai fa matan
da suka rabu da mazajensu a dalilin irin wadannan kafafen, misali: Na ga hirar
wasu matan inda wata take cewa 'ya'yanta 8 da maigidanta amma a rayuwarta ba ta
taba sanin ya shimfida take ba. Sauran mata nata tofa albarcin bakinsu, irin
wannan in wani shedanin ya bi ta ta zauren tattaunawa ai barna ta auku, tunda a
bude suke maganar kowa na gani. Shi yallabai yana cewa ya bar matarsa a killace
a gida bai san ya bar ta a bude da wayar dake hannunta ba. Duk wani namijin ƙwarai
ya ga wannan ya san akwai matsala, ya kamata ya gyara ta kafin wani ya gyara
masa zama.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.