5) TITSIYE: Na farko shi kansa mijin abin da zai sa ya titsiye matarsa ko masoyiyarsa ke nan kan abin da bai gama gamsuwa da shi ba, masamman dangane waya, wani kan saka mata tsarin nadar duk hirar da take yi da mutane, matar na gano abin da ya faru za ta ce "Don Allah in ba rashi yarda ba me zai kawo haka?" Me ya sa zai saka mata ido har a cikin waya? Me zai sa ya fara bibiyar lambobin da ta taskace a waya har ya tsare ta yana tambayar "Da wa kike magana? Ko "Wannan sunan waye?"
Haka ita macen
idan ta fara bibiyar wayar maigida tabbas akwai
abin da take ƙoƙarin gani a wayar, kwanakin baya wata ke cewa ta sami
wata baƙuwar lamba a wayar mijinta, da ta kira sai ta ga mace ce, kuma ta lura
suna yawan magana tare, da ta shiga WhatsApp dinsa sai ta ga har turo masa
hotuna take yi, ta ce "Wannan wani irin cin amana ne malam?" Malamin
ya tambaye ta ko mijin mazinaci ne, ta ce "A'a" ya tambaye ta yawan
matansa ta ce "3" ya ce "Ba ki ganin aurenta zai yi?"
Wannan bai dame ta ba, ita dai mijinta ya ci amanarta tunda yana magana da
wata.
Duka dai
dube-duben ne ya jawo wannan kishin, amma akwai abubuwan da tabbas za su iya
zama ƙofa na kishin namiji, kamar in yana tare da ita ya ga wani ƙato ya zo
suna gaisawa cikin fara'a da sakin fuska bayan shi bai taba ganinsa ba. Dole ya
tsare ta da tambaya ya ji inda suka hadu, in ya ji bai kwanta masa a rai ba ya
taka mata burki. Wannan ke nan to bare kuma a yi ta bugo mata waya ta kasa
dagawa, in ya ce ta daga ta ƙi, ya nemi ta ba shi wayar ta hana. An sami ƙofar
kishi wagegiya kuwa.
Ko kuma duk in
ana zaune wani ya bugo waya sai ta tashi ta tafi inda ba wanda zai ji me take
cewa, anan dole mijin ya titsiye ta "Wai ke wace waya kike yi wace ba wanda
zai ji abin da kike fada? To bare kuma a
ce duk lokacin da ya zo ya same ta tana waya sai ta katse, kuma ko yaushe tana
dab-dab da wayar ba ta son ya yi kusa da ita, duka dai alamu ne dake nuna akwai
nau'i na rashin gaskiya in mai gida ya ce zai titsiye ta a kan haka yana da
hujja. Me take boyewa? Meye ba ta so kowa ya ji?
Kai ma Alhaji
malam ba cewa nake ba ka da gaskiya ba me ya sa kake boye sunan masoyiyarka da
sunanka? Ko ka sa sunan wani ƙato, in shakku ya kama ta ta buga wayar ta sami
cewa mace ke maganar ba namiji kamar yadda aka rubuta ba dole ka amsa wasu
tambayoyi. Wasu matan kishinsu na gaskiya ne, dazu wani dattijo ya zo yake gaya
min cewa wata malama ta yi wa'azi kan mata su bari mazansu su riƙa ƙarin aure,
wannan ya sa wata daga cikin daliban ta saki jiki ta je don su gaisa har take
gaya mata cewa ai maigidanta ne zai aure ta.
A ƙarshe hawan
jini ya buge ta dalilin rasuwarta kenan. Wannan lamarin ya kawo tattaunawa wasu
ke ganin wautar yarinyar yadda ta bari abin boye ya fito sarari ta bakinta. Na
ce dan yau ko ta san za ta mutu za ta iya gaya mata albashi in ta nade
tabarmarta ita ta shimfida tata. Kishi ba
abin da bai haifarwa. Don haka duk wanda ya san zai motsa kishin dan
uwansa ya tabbatar da cewa in an titsiye shi yana da bakin da zai iya fitar da
kansa. Shekaran jiya na ga wata shari'a da miji ke zargin matarsa da bin maza,
har ta kai ga yana cewa dan da aka haifa ba nasa ba ne, amma ƙofar farko da ya
fara bi ita ce matar ta ƙi amsa wayarsa na tsawon lokaci kuma hakan kan faru
daga lokaci zuwa lokaci.
Da ya fara
bincike sai kuwa ya tarar da walakin goro a miya. Ba cewa muka yi maza su bar
wayoyinsu a bude ba, su kulle abinsu in suna tsoron bincike, domin an ba ka
dama ka yi mata hudu, ko daya ce da kai za ta iya tsayawa a gabanka cewa ba za ka
ƙara ba, in ta gano kana magana da wata matsala ne. Ke kuma ba abin da zai sa ki kulle waya don ke ba yadda
za a yi ki yi maza biyu to me za ki boye masa? Ki yi iya ƙoƙarinki wurin ganin
ba ki yi abin da zai sa ya tsare ki don
amsa wasu tambayoyi dake da alaƙa da zargi ba. Haƙƙinsa ne ya ba ki kariya ta
masamman, kuma shi yana da damar ƙara aure matuƙar ba za su wuce 4 ba, ke kuma
ba ki da wannan damar.
Maganar cewa
in mutum zai ƙara aure ya gaya wa matarsa tabbas wannan ba matsala ba ce a wani
wurin, amma wallahi wani wajen kamar ya ƙona kansa ne ya gama, don shi da samun
kwanciyar hankali sai an daura auren. Wata za ta ba ta tsakaninsa da 'ya'yansa
da maƙwabta da kowa ma don ya ce zai ƙara aure, akwai wace ta sa ma aka kore
shi a wurin aiki, don haka ga namiji in ya boye alaƙarsa da wace zai aura ba
wani titsiye da matar za ta masa, amma mace meye nata na boye-boye?
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.