Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba (20)

7) DALILIN YIN KISHI DA KAFAR SADARWA: In fa namiji zai yi kishi da wani abu to gaskiya kafar sadarwa ya kamata ya fara da ita, don kishin mace shi ne ka kare komai nata ya zama sai kai kadai. Kar a ga adonta, kar a ji muryarta, kar a yi hira da ita, kar wani ya dauke lokaci suna maganar soyayya suna dararraku na jin dadi. In dai tana kan kafar sadarwa ba  abin da ba za a yi ba, jikinta ne kawai ko shi za a iya isa gare shi tunda tana da ƙafar da za ta fita.

Kusan ma na ce duk wani  abin da ba zai yuwu a zahiri ba kafar sada zumunci za ta iya sauƙaƙe yadda za a yi. Nan ne matar aure in maigidanta bai samun damar zama a gida za ta fito maka a matsayin budurwa, shedan a sa wa alaƙar ta su albarka, don ta yi ƙarfi sosai, ƙila kafin namijin ya san tana da aure an kai matsayin da ba zai iya dawowa ba sai dai a dawo da shi. Nakan ce in ana ƙwacen mata irin wadannan sun fi kowa sauƙin ƙwace, don takan bayyana wa namiji inda take da rauni ita da maigidan, ta ba shi hanyar da zai a bullo mata ya kai ga biyan buƙatarsa.

In shedanin ya san abubuwan da take buƙata nan take zai fara binsu sannu a hankali, yana mata duk abubuwan da maigidanta bai iyawa, shikenan an gama, kamin ya farga an yi masa sakiyar da ba ruwa. Rana guda za ta fara tunanin mijin media a maimakon maigidanta na zahiri. Maigida na fita za ta dauko waya su fara maganganunsu, har ya zamanto ko maigidan ya makara ba ta damu ba, ta ma fi son ya yi ta zamansa a waje yadda za ta sami damar tattaunawa da wanda take so. A sarari ne kawai matarsa, an riga an ƙwace ta, ina da ya yi kishi tun farko!

Koda yake akwai mazan da sukan dauki hoto da matansu bayan sun ƙure adaka, sun sha lalle na gobe amarci, abin takaici ba ma matan ne ke saka hotunan a kafofin sadarwa ba mazan ne da kansu, sun manta cewa duk lokacin da matan suka yi irin wannan wankan sukan burge su to bare wanda bai san asalin halittarta ba kyawun kawai yake gani? Idan ma mutum bai da kishi a zuciyarsa ya kamata ya sani cewa duk da matarsa na tare da shi a cikin gida za a iya sace mata zuciya, shi yana tare da gangan jikin ne kawai, zuciyar na wurin mijin media, yanzu kodai ya dawo da ita akan lokaci, ko a dauke gangan jikin wata rana.

'Yan shekarun baya da wasu manyan matan suka ƙirƙiro da raye-raye da mazajensu na waƙoƙin Breaker suna dorawa a kafar sadarwa muka ji wata daga cikinsu tana cewa maigidanta ya sake ta, sakamakon ganin hotunan da ta dauka suna yawo. Ba wani abu ya kawo haka ba illa kishin iyalinsa. Irin wadannan abubuwa da wasu ke ganinsu a matsayin ƙanana, su ne abubuwan da rusa gidajemmu. Da kaina na sha gaya wa wasu matan cewa "In ba a kishinki ke bai dace ki yi kishin gidanki ba?" Akwai waɗanda suka tura matansu gida a dalilin samunsu da wasu mazan a kafofin sadarwa.

Su kuwa mata suna kishi da kafofin sadarwa don abu biyu ne, amma mafi girma a ciki shi ne lokacin da maigida zai rasa samun lokacin da zai yi hira da su, sukan ce zai jima a waje da ya dawo gida kuma a maimaikon ya bari su maida  abin da suka rasa na rashin ganinsa sai kuma ya dauko waya ya dora. Mafi yawan mata na kuka da haka, ke nan wayar ta zama kishiyarsu, in akwai  abin da suka ƙi jini a duniya bai wuce wayar ba, shi ya sa wasu a cikinsu in maigidan ya dauki wayar su ma sai su ce ya hada su da datarsu su ma su haye a yi ta yi, ga su a wuri guda amma zaman ƙuda ake yi.

Na biyu kuwa ba ta da yadda za ta yi a kai, domin in kyau take taƙama da shi a kan sami wace ta fita a kafar sadarwa, wuri ne na ka zo- na zo, duk wata kwamacala tana ciki, bare kuma wannan zamanin da mata suka zama hawainiya, kana rabuwa da yarinya na kwana biyu za ka ga ta zama fara fat, ba wuya wata ta ƙwace miki miji ko saurayi, abu ne da ya kamata a yi kishi a kai, ya dace a yi mata hanzari, amma mun sani ba ta da hurumin da za ta hana shi magana da wasu.

Sai mas'alar binciken asusun mace ko na maigidan a kafar sadarwa. Shin abu ne mai kyau ko a'a? To gaskiya malamai sun yi magana mai dama a kai, ba ni da sabuwar fahimta sama da tasu, illa dai tunda ana tsare mace a bayyane ya dace a tsare ta a boye, don wannan ne ma ya fi zama hatsari, sai dai a yi aiki da hikima yadda zargi ba zai shigo ba, a yi wa'azi, a sa tsoron Allah, sannan a hada da addu'a. Wayon mutum ba ya maganin matsala, hikima kan yi abubuwa da dama waɗanda kudi ko ƙarfi ko dabara ba za su iya yi ba.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments