Kishi Rahama Ne Ko Azaba //17

    2) ZARGI: Yakan taso ne kuma ya yi tasiri ga zamantakewar da ke tsakanin mutum biyu a lokacin da dayansu yake ganin cewa abokin tafiyarsa na boye rashin gaskiya game da alaÆ™ar dake tsakaninsu ta aure ko Æ™auna kafin auren bisa wasu hujjoji marasa kan gado da ya riga ya tattara daga Æ™usurwoyi daban-daban. Daganan kuma mutum ya sami aikin yi ke nan ta yadda zai rabu da hidundumunsa masu mahimmanci ya koma bibiyan  abin da inda zai same shi hankalinsa sai ya fi na kowa tashi.

    Za ka ga mutum na maida hankalinsa kan  abin da masoyi ke cewa, ba don fahimta ko yarda ba, kuskurensa yake nema wanda zai kai shi ga  abin da yake zarginsa da shi. Ba maganarsa kadai yake bincika ba har da kai-komonsa bayan a jiya ba wanda ya fi yarda da shi kamarsa a duk fadin duniya. Ƙila a ce Æ™auna ta jawo haka, amma fa in ya samo  abin da yake nema to rabuwarsu kenan. Tunda kishi zai hana shi ganin alkhairan masoyinsa, ya dauko Æ™iyayya ya yi gilashi da ita. Wani ya yi duka, wata ta yi Æ™one-Æ™one ko kisa, wani ya saki.

    3) TUHUMA: Duka dai kishi ke sa sashi ya fara tuhumar sashi da cewa yana kallon wani, da a ce mace za ta ce "Yadda Daushe yake wasa a shirin Arewa24 na Gidan Badamasi yana burge ni don shi nake kallon shirin!" In ba a yi sa'a ba daga ranar an daina kallon shirin ke nan a gidan, maigidan zai fara tuhumarta da cewa tana son Daushe, wata ƙila kuma ko a hanya suka hadu ba dole ne ma ta gane shi ba. Ta yuwu a wannan wasan ne ma kawai inda yakan ce "A bi duniya a sannu, ga shi ba shi da gaskiya a cikin gidansa shi ma kansa ba ya bin duniyar a sannu". Miji ba zai kalli wannan ba, kawai tana son Daushe don haka an daina kallonsa sai dai wata tashar. Wannan kishi ne.

    Ita kuwa mace takan fara ne da zura wa mutum ido ta gani ko yana kallon wata, bare ya taimake ta, nan take za ta yi ƙoƙarin sanin dalilin da ya sa ya yi hakan, ko ta sanin ma dole dai komai ya tsaya daganan don kar ya kai inda ba a so, in kuwa a bayan idonta aka yi labari ya iske ta to zargi zai iya shigowa ciki, sai tuhuma ta fado "Me ya sa ka ba wance kaza? In don Allah ka yi ba mata ne a duk fadin duniyannan sai ita?" Tambayar wai ba matan aure ne mai ya sa sai maras miji? Na taba ganin wani mutumin da ya tausaya wa wata mata a cikin motar haya. Ya saya wa matansa Multina ne mai sanyi saboda a ganinsa zai dan sassauta musu tsananin zafin da suke ciki.

    Ganin matar na tare da matansa sai ya saya mata guda daya ya miƙa mata, nan take matarsa ta ƙwace ta galla masa harara, amma da ta je miƙa wa matar sai ta saki fuska tana yi mata murmushi. Tabbas ta fahimce ta amma ya za ta yi? Ta karba ta yi godiya, ko iya kallon mijin matar ba ta yi ba bare ta yi masa tasa godiyar, zargi ya riga ya kurdado tsakiya ba yadda za a yi, duka sun san juna, a yadda na san maza wannan kisar macijin mata ne, an kashe ba a sare kan ba, zai farfado ya ci gaba da tafiya sai yadda hali ha ya yi. Don wani lokaci daga irin haka ƙaunar ke shukuwa.

    4) RASHIN GANE MUTUM: Idan mace ta fara ganin wasu abubuwan da ba ta saba gani ba, ko kuma ta ga ana yinsu amma ba a lokacinsu ba. Misali, kwalliyar namiji da safe yake yinta lokacin da zai fita aiki, in ba haka ba to akwai wani abu na masamman kamar daurin aure ko wani sha'ani wanda zai halarta, in ta ga yana shan adaka da daddare tabbas za ta fara shan jinin jikinta, bare kuma ta ga yana fesa turare, ko yana zaben kaya da kansa bayan ita ke zaba masa, ko ya fara makarar dawowa gida ba tare da wata ƙaƙƙarfar hujja ba, ko kuma ya fara yi wa wata kyauta ba gaira ba dalili, masamman in ba ta da miji.

    Duk wadannan abubuwa ne da za su sanya mace cikin dimuwar cewa da walakin wato goro a miya. Akwai matar da mijinta ya sami halin da zai ƙara gini, tun da ya fara kawo bulo gidan aka fara samun dauki ba dadi, duka dai kishi ne wanda ya taso daga rashin gane halin da maigida ko saurayi yake ciki a dalilin wasu abubuwa da ya ƙirƙiri yinsu na ba gaira ba dalili. A irin wannan halin sai mace ta yi haƙuri don in ma yana shakkarta da zarar ta matsa masa zai fito sarari ya ce mata aure yake nema sai me? Kuma shikenan an gama.

    Koda yake akwai abubuwa da dama waɗanda suke saka mace kishi kamar kyau idan ta ga wace ta fi ta kuma ba ta da miji, ko wani matsayi na wurin aiki ko dai na al'umma gaba daya, ko ta fi ta karatu tana da kwali babba, ko tana aikin gwamnati ga albashi mai tsoka ita ba ta kai nan ba, ko ta gan ta da babbar mota ko waya ta hannu da dai sauransu duk za su iya saka ta kishi da ita, sai in ta san cewa ta ko'ina ba yadda za a yi mijinta ya yi sha'awarta. Kishin mace ga wata a matakin farko ba wai hassada ba ce, kar dai a ce wata alaƙa ce ta kurdado tsakaninta da maigidanta, ba ta damu ba in za ta auri kowa amma banda maigidanta.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.