Ticker

6/recent/ticker-posts

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //14

7) DAGA GIDAN AURE ZUWA FAGEN FAMA: Mummunan kishi kan canja ma'anar aure gaba daya, yadda za ka taras komai na gidan ya lalace, tunda akan kai yadda miji bai magana da matarsa ko ka taras matar ba ta magana da mijin kuma ma'aurata ne me kenan? Wani sa'in shakku ne ke sa mutum ya fara yin wasu abubuwan da za a zarge shi da su, wani sa'in kuma daga baƙin kishin ake farawa. In mijin ne ya dena takin iyalinsa saboda zargin tana yawo, in ta ga abin na neman wuce makadi da rawa sai ta fara neman mafita.

A 'yan shekarun baya ne wani ma'aikaci ya yi aure amma kamar yana shakkun cewa matar ba ta iya riƙe masa amana, shi kuma ya dena saduwa da ita kwata-kwata, amma bai sake ta ba.  abin da zai daure maka kai yaranta hudu a gidan, kuma mijinta sam bai saduwa da ita, kuma in ta haihu zai yi komai na sha'anin suna. A taƙaice shi yake biyan kudin makarantan yaran kuma ya riƙe su kamar 'ya'yansa. Sai dai a cikin yaran akwai wanda ya yi muguwar kama da maƙwabcinsa. Da aka bincika sai aka gano dansa ne, wani yaron ma Inyamuri ne ubansa.

Wa za a zarga kenan? Mijin za a ce baida kishi, ko matar da ta zama ballagaza a gidansa? Ya tabbatar da cewa bai kwanciya da ita, amma a gidansa take kuma yana ba su abinci daidai gwargwado, za a yi ciki a gidansa a haihu masa amma ba  abin da wani zai ji na hayaniya tsakaninsa da matar! Gaskiya duk inda rashin kishi ya kai wannan ya kai. Ita kuma matar tana sukarsa da cewa shi ma yana yi ne a waje ya sa ba ya kula ta, kishin hakan ya sa ita kuma ta bar hundonta a bude yadda za ta riƙa biyan buƙatarta. Wannan kam gida ya lalace gaba daya.

8) SAKI: Babban  abin da zai gama wargaza gida shi ne saki bayan an hayayyafa. Daya daga cikin  abin da yake ba ta gidan Hausa/Fulani kenan, saki ba komai ba ne a wurin malam Bahaushe, a ganinsa shi ne hanya mafi sauƙi da za a magance matsalolin aure. Su kuma Fulani sun fi kowa zuwa kotu kan matsalolin da suka shafi auren. ko da yake ana dan samun canje-canje a 'yan shekarunnan. Da zarar mutum ya ga  abin da ransa bai amince da shi ba sai ka ji ya miƙa takarda, shikenan ya yi saki. Na san mutumin da ya yi amarya 'yan kwanaki kadan ya sake ta, wai ya same ta ba cikakkiyar budurwa ba, to shi da ya sake ta ya mayar da ita bazawara a kwana daya fa?

Da ya take ta sai ya gano cewa ba cikakkiyar budurwar ba ce, shi kuma kishi ba zai bari ya amince wani ya riga shi ba. Burinsa a ce ya riga kowa. Akwai mazan da ba za su iya auren bazawara ba ko kadan, ba don tana da illa ba, kawai don wani ya taba aurenta. Kana sakin mace ai ka wargaza gidanka sai dai wani auren kuma. Na taba yin wata tambaya a kafar sadarwa cewa wata ta boye wa maigidan cewa ta taba aure kuma tana yara a wani gidan. Kusan kashi 8.8 sun nuna ba za su iya ci gaba da zama da ita ba sakinta za su yi.

Koda yake galibin hujjarsu ba don an sake ta ba ne ko don sun auro bazawara, gani suke kamar ta yi ƙarya. Sai dai akwai waɗanda za ka shinshini burbushin kishi a amsarsu. Ko ma ya aka yi dai, saki ba zai taba zama matakin farko na warware matsalar kishi ba. Domin akwai yaran da za a maishe su marayu ba gaira ba dalili su ci gaba da dandanar rayuwa kan laifukan da ba su ci ba ba su sha ba. A kawo musu wata matar ta fara gasa musu gyada a hannu da sunan kishi. Ko ta maishe 'yan Bora waɗanda ta haifa kuma na Mowa.

Tunda saki a wannan matattarar abu ne mai sauƙi har ma a kan 'yan ƙananan abubuwa me zai hana mata su yi wani tsari da zai taimake su da yaransu gaba daya? Na sha ganin mata a gidanjen uwayensu sun debo yaransu bayan ubansu na da rai sun tara su a gabansu. Yaran su hana su aure, su kuma sun kasa tunanin su maishe su ga uwayensu ko 'yan uwan maigidan. Kusan duk matar da mijinta ya mutu ko aka sako ta za ka ji ba za ta iya barin yaranta a hannun kishiya ba saboda tunanin kishin ba zai bar ta da imani a wurin mu'amalla da su ba.

To in ya kasance mutum mai auri saki ne ai sai ka ji yaransa guda kaza a gida kaza, guda kaza a wani gidan, duk an watsa su, gidan da ya kamata a ce ya yi ƙarfi gashinan an watsa shi, ba komai ya ba ta shi ba sai kishi da saki. Na san matar da ta kwaso yaranta guda hudu ta dawo gidan mahaifinta da su, wai ba za a iya riƙe su a can ba. Mu kuma maza ba dukammu ne muke da nazari ba, kwanaki wani ya saki matarsa bayan sun shafe sama da shekara 20 suna tare. Wani ma da ya kwashe sama da shekara 40 ya saki matar a dalilin kiyoshi, ta bar gidan amma 'ya'yanta na ba-ta-kashi da 'ya'yan kishiya a kullum. Me gidan ya koma kenan?

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments