9) ƘONA KAI: Wani kishin jefa kai ne a halin ƙaƙa-ni-kayi, da mace za ta tsaya ta karanci lamarin sosai ko ta dube shi da idon basira za ta gano cewa haƙuri da kishin shi ya fi. Misali: Na san namijin da mace daya ko biyu ba su isansa a shimfida sai ya faro daga dakin ta farko zuwa ta biyu ya ƙare a dakin mai girki duk dare. A ƙarshe dayansu ta ga ba za ta iya rayuwa da shi ba ta cika rigarta da iska, ganin haka ya nemo wata yarinya ƙarama wace take iya daidai da shi, tun daganan ya huda da biye-biye, a irin wannan me zai sa mace ta ce sam ba za a yi mata kishiya ba za ta jure duk wahala?
Akwai wata da
ke wa mijin wanki da guga ta wanke masa mota, ga hidundumun gida ga na yara, me
zai sa ta ce ta ji ta gani za ta iya komai? Da fa zai auro wata za ta huta sai
kuma ranarta ta sake juyowa, nau'i ne na ƙona kai ta ce ita fa lallai komai za
ta iya ba ta da matsala. Wata ma bayan duk wadannan hidundumun hatta fita
kasuwannan da kanta za ta yi. Wata takan ce gwara a dauko mata 'yar aiki ta
rage mata amma ba ta yarda da kishiya ba, ko da ta san mijin na dan leƙe-leƙe.
Wannan maganar
ba kowa ce mace za ta iya ganewa ba, bari na yi miki dalla-dalla: Lokacin da
nake makaranta wani ya kawo mana kukan wata mata mai bala'in kishi wace ba ta
yarda a ƙaro mata kishiya ba, kuma ba ta iya ririta mijin kamar yadda ya
kamata. Ranar da ya gaya mata gazawarta da dalilin da ya sa dole sai ya yi mata
kishiya ranar ta tayar da ƙayar baya, har ta ce ga shinan da yara in ita ba ta
ishe shi ba, amma ba zai kawo mata wata cikin gida ba. ko da yake ba Bahaushiya
ba ce amma musulma ce. Wannan wani irin kishi ne? A ganinki ba za ta iya kisar
kai a dalilinsa ba?
Wata tunda ta
ga maigidan zai ƙara aure ta tayar da hankalinta, rigimar yau daban ta gobe
daban, ta ba ta da duk waÉ—anda bai dace ta sami matsala da su ba, kuma ta nuna
cewa za ta iya ƙasƙantar da kanta a komai amma kar mijin ya ƙaro mata wata
matar. Shi kuma ya ce haƙurin da ya yi a baya ya ishe shi zai yi aurensa komai
ta fanjama-fanjam. Ta ja kunnensa da cewa za ta kashe kanta, gwara ta mutu da
ta ga wannan mummunar ranar. Magana ta kai har zuwa ga mahaifanta kuma sun
shiga tsakiya suka nuna mata ba ta da hurumin da za ta hana mijinta aure matuƙar
yana da niyyar hakan. Wannan ya sa ta kashe kanta saboda gudun bacin rai.
Ni nakan
fahimci wannan wautar cikin sauƙi, wace samsam ba na fahimtarta ita ce macen da
za ta kashe wani saboda kishi. Misali in aka ce za a yi mata kishiya sai ta
kashe kishiyar, a ƙarshe kuma sakamakon kisar ko ba a kashe ta ba za ta ƙare a
gidan yari, wato ita ma ta bar gidan mijin. To meye amfanin wannan kishin? In
ta yi ne don ta rayu da maigidan ko bai sake ta ba hukuma ba za ta bar ta a
gidansa ba, tanacan tana shan azaba a kurkuku ga wulaƙanci da bacin suna ga
damuwa sakamakon kisar rai. Bare kuma daga ranar ko za ta fito maigidan ba zai
zauna da ita ba.
A daidai wannan
gabar yana da kyau a rabe tsakanin masifaffiyar ƙauna da kuma son kai, macen
dake masifar son mijinta shi din kawai take kallo, duk abin da zai amfane shi tana wurin, ko da kuwa
auren zai ƙara, za ta iya batawa da kowa don ganin farin cikin maigidanta, mun
ga waÉ—anda ko uwayenta ba sa iya yi da shi a gabanta, sai in ta bar wurin, abin
mamaki ba abin da yake ba ta tsabar ƙaunarsa
ce kawai.
Irin wadannan
matan duk da wannan ƙaunar ƙwaƙwalwarsu kan nuna musu mahimmancin uwayen miji,
da 'yan uwansa, duk sukan riƙe su don kar su saba da mijin, idan suka ga
hankalinsa ya karkata ga sai ya ƙaro aure, sukan yi ƙoƙarin riƙe shi ta
bangaren da suka san yana da rauni don ci gaba da rayuwa da shi. Na taba ganin
wace aka tambaya "Wa kika fi so da ƙauna wanda ba ki son rabuwa da shi ko
da da ƙiftawar ido ne?"
.
Na zaci zan ji
ta ce "Uwata" galibin amsar mata kenan, ko su ce "Uba" maza
ne ake samun kaso mai girma da suke iya cewa "Iyalina" kai tsaye.
Amma matannan ta ce "Maigidana, uban 'ya'yana" na so dan jaridan ya tambaye
ta dalili, sai ya yi mata wata tambayar. Ita ina ta bar kishin? Ba ita ce ta
biyu ba, ita ce ta farko? Duk dadewar da mace za ta yi a gidanka in ka ji ta ce
"Gidammu" gidan mahaifanta take nufi. To wanda za a yi mummunan kishi
a kansa ya cancanci ya zama maigida ko da yaushe. Son kai kuwa mace ta ce: Ba
za a ƙaro mata kishiya ba. Ita kadai za ta rayu in ba haka ba ta janye duk abin da take masa.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.