ME BAƘIN KISHI KE KAWOWA
1) MUMMUNAR
SHAƘUWA: abin da ya sa aka kira ta da
mummuna kuwa domin duk abin da ya wuce
iyakar da ake buƙatarsa bai da amfani, kamar gishiri a miya, ko sukari a zobo,
ko sanyi a ruwa, ko yaji a abinci, na yi zamani da macen da ba ta iya barin
mijinta ya tafi wurin aiki sai dai ta dauki yarinyarsu su tafi tare, ba za ta
iya zama a gida ba, malami ne mai koyarwa, duk ajin da zai koyar tana ciki, ga
shi ba shi da dama ya yi magana da dalibansa mata, masamman waÉ—anda suka saba
kafin ma ya san ta. Su kuma da suka gano dabi'arta sai suka fara yin wasu
abubuwa don tura mata haushi, kan ka ce wani abu alaƙar ma'auratan ta fara
neman tabarbarewa. Kishi na neman ba ta gida.
2) SAURIN
HASALA KAN abin da BABU TABBAS: Da zarar
dayan masoya ya ga abin da bai da tabbas
a kai nan da nan zai dauki zafi, wata ƙila ma ya dauki hukuncin da zai dawo
yana nadama daga baya: Kamar matar da ta soka wa mijinta wuƙa saboda ta kama
shi da wata, wai ya ci amanarta! Ga shi ya mutu ya bar ta da yara, in suka
girma me za ta ce musu? "Ubanku manemin mata ne shi ya sa na kashe
shi!" Ko wannan ya isa, to bare kuma ita ma za a kashe ta su bar yaran
marayu, kuma za a gaya musu cewa ta keshe ubansu. Kishi bai amfani ba.
3) KIBIYA MAI
LAHANI: Irin wannan kishin kan sa masoyi ya ba ta masoyinsa, domin a ƙarshe
matar za ta kira mijinta da manemin mata ne, amma duk da haka ba za ta fita ba,
kuma ba za ta bari wata ta shigo su rayu tare ba. Haka shi ma zai fara
bibiyarta duk inda za ta, ko ya fara saka wa a yi masa bincike, anan me zai
fara zuwa ƙwaƙwalwar waɗanda aka saka su sanya mata ido? In dai akwai gasgata
juna me zai kawo bincike? Matsalar irin wannan da wahala ka ga mutum na abu bai
yi fatar ya ga ya cimma abin da yake son
gani ba.
4) MANTAWA DA
ALKHAIRI: A duk lokacin da mai kishi ta fara fitar da abin da ke cikinta da wahala ta fadi
alkhairin wanda take suka. An yi wata da ta kawo ƙarar mijinta, sai mahaifinta
ya ce gaskiya bai ji dadin abin da maigidanta
yake yi ba, kuma ba zai bari a jajubo masa
abin da zai ba ta masa zuriya ba, don haka ta yi zamanta zai sa a kirawo
shi in gari ya waye a raba auren. ko da gari ya waye sai mahaifiyarta ce ke
gaya masa cewa "Ta koma dakinta tun daren jiya" kai da ji ka san da
ma uban ba da gaske yake yi ba kuma ya san
abin da zai faru kenan.
5) WUCE GONA
DA IRI: Shi ne mace ta fara addu'ar kar Allah ya yi wa maigidanta wadata ko kar
ya ba shi wani aiki don kar ya sami abin
da zai yi mata kishiya. Ko ta ce ba zai fita ba sai ta san inda zai je da abin da zai kai shi. Daga cikin irin wadannan
matan akwai wace ba ta ƙaunar ta ga maigidanta ya saka kaya mai kyau saboda kar
wata ta gan sa ta yi sha'awa. Dan jinkirin dawowa in ya yi sai ta ji inda ya
tsaya da dalilin hakan, ko ƙanwarsa da suke uwa daya da shi ba ta so ta ga sun
zauna suna hira suna dariya bare sauran dangi.
A irin wannan
wasu mazan ka yi na su, ko da yake kishin namiji addini ma ya kwadaitar da shi,
amma za ka ga wasu abubuwan ko malaman addinin ma ba sa hakan. Na ga wanda
matarsa ta zo yin hoto a wurin ƙidaya, amma fa bai yarda jami'in ya kalle ta
lokacin da zai dauki hotonta ba. Ya ce a dauke ta da niƙabin, malamin ya ce
"Kodai ta daga ko a fasa" haka ya yi ta nuƙu-nuƙu yana kakkare ta kar
a ganta, ga shi a cikin layin mata yana kallon matan wasu lokacin da yake ƙoƙarin
kare ta shi. A ƙarshe dai ta daga niƙabin yana ta tafarfasa.
6) KISHI DA
MAKUSANTAN MIJI: Lokacin da mace ta fara kishi da uwar-miji, ko mahaifinsa da
wahala ta fada wa mijin alkhairinsa. In kuma mai shige-shige ce ta tura masa
aljani da zai riƙa juya shi a duk abin
da take so. In ya yi niyyar kyautata wa mahaifinsa ta ce kar a yi an gama
kenan. Bisa wadannan dalilan ya sa wata uwar-mijin kan dafa abincinta alhali ga
matar danta na zaune, komai nata ita ke yi ga masifar uwargidar. Wata kan hana
maigidan ya kyautata wa mahaifinsa ma, amma in ya yi wa nata ta yi godiya.
Mun sami wace
ba ta ƙaunar maigidanta ya shiga wurin mahaifiyarsa bare ya ba ta wani abu. Da
zai ce ya ci wani abu a wurinta ranar matar tasa ba za ta yi magana da shi ba.
In wani abu ya yi mata ta nuna godiyarta ya kuskura ya ce mahaifiyarsa ta ba da
shawarar a yi to in ba sa'a aka ci ba sai dai ya sa hannunsa ya dauki abin da ya kawo da kansa. Wannan kam mummunan
kishi ne ba ko shakka. Ko za ta yi da ƙanninsa mata ko wasu makusanta wannan
kam daban, amma da uwayensa abin ya baci.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.