ALAƘAR SHEDAN DA KISHI
Gaskiya in za
a tabi wannan batun sai an raba shi zuwa gida biyu, wato shedanin aljani da na mutum.
1) Wasu
lokutan in mace na da iska sukan ce za su taimaka mata, dan abin da bai taka kara ya karya ba za ka ga
mai aljanu tana rigima da mutane, wannan cuta ce kuma akan yi magani a sami
lafiya, akwai shedanun aljannu dake sanya mace ta riƙa wasu ayayyakai na
mummunan kishi har ya kai inda maigidan zai gaji da ita ya sake ta, yadda a ƙarshe
za ta ci gaba da zama ita kadai ba tare da namiji ba. abin da suke so ke nan kuma samu.
2) Wasu
lokutan ba iskar ce da kanta ta kama mace ba, bokaye ne suka tura mata kamar
yadda wata ko wani suka nema, in daga mace ne to mummunan kishi ne kan sa ta
nemi a tura mata, in kuwa namiji ne ya kasu kashi biyu; kodai ya sa a tura mata
don ta rabu da wancan ta dawo masa, ko kuma ya dauki matakin ranuko da tunanin
ta yaudare shi, yadda ya rasa ta ita ma ta rasa wancan. In har za a je gaban
boka dama ba maganar imani ake yi ba bare a ce za a yi maganar abin da ya dace a shari'a. Sai dai a ga mace
na yin abin da bai kamata ba a ce ta
cika zazzafan kishi.
To da yake
kowa ya san hakan na faruwa mata kan yi amfani shi wurin aikata barnar da suke
so, a ƙarshe su ce magani aka yi musu ba da son ransu ba ne, a gaskiya ba wani
magani son kai ne kawai da aka fassara shi da kishi. Wata kan fara dauke-dauke,
tabbas akan yi wa mace sihiri ta yi hakan don a raba ta da maigidanta, sai dai
wata halinta ne, yadda ake ganewa kuwa sanin mutum da dabi'arsa kafin aure, ko
kafin zama da kishiya. Mai halin dan bera bai iya rabuwa da halinsa.
Wata akan saka
ta ƙazanta ne, a duk sha'aninta babu tsabta, duka dai ana iya ganewa ta yadda
aka san mace a dabi'arta tun tale-tale. Haka saurin fushi da gaba da mijin ba
gaira ba dalili. Ni dai a tawa masaniyar an yi wasu masoya da kowa ya tabbatar
da yadda suke ƙaunar junansu amma dab da auren sai komai ya lalace, uwayen suka
ce ba gudu ba ja da baya, me ya sa ta bari tuntuni ba ta yi wani abu ba sai
yanzu da ta ga an zo aure? Suka ce ba za ta raina musu hankali ba.
To an daura
auren amma da zarar ya kusa da inda take sai komai zai canza, sai ta daure
masa. Mutane na ganin kamar shegantaka ce kawai tunda ta fara nuna ba ta son
auren dab da lokacin. Ina ganinta na fahimci akwai matsala, na kuma ba su
shawarar neman magani, cikin ikon Allah an sami karbuwa da ga Allah ta warke
sarai. ke nan wasu ayiyyukan ba fada ko wa'azi ke maganinsu ba, a Islamic kemis
za a samu.
Bari ki ga
inda shedanun mutane ke taka rawa wurin fitar da mace daga gidanta, wata ce ƙawayenta
suka yi ta zuga ta cewa maigidanta na yin kaza da kaza, ita ce fa tare da shi,
amma tana jira waÉ—anda ke nesa su ne za su gaya mata ga yadda yake ga abin da yake yi. Haka suka yi ta ingiza ta
tana tara masa baƙin ciki har ya gaji ya sake ta ta dawo gida, a ƙarshe ya auri
daya daga cikinsu. Tambayar anan da ma suna son su fitar da ita ne ko kuwa daga
baya sun fahimci duk abin da yake yi bai
kai a yi kishin da mace za ta ƙi zama da namiji ba ne?
Ba a cewa
akwai shedanun uwaye, amma tabbas akwai uwayen dake korar 'ya'yansu daga
gidajensu. Babban abin da zai ba ka
mamaki ta ina mace za ta saka wa mijin 'yarta ido har wani lokaci ta shiga
tsakiya tana hukunci wai yana neman mata? Kuma a daidai wannan lokacin tana
tare da fahimtar diyarta wace ta gaya mata komai na abubuwan da mijin yake yi
mata kuma suka zage shi gaba daya wai kuma bayan ya zo ne za ta yi hukunci!
Daya daga cikin dalilan da suka sa ba a son mace ta riƙe gida kenan, domin
wannan in ba a yi sa'a ba ita za ta ba ta auren.
Maƙwabta ma
kan zuga mace ta yi ta yi wa maigidanta dibar albarka da sunan kishi. Wanda ya
fi ba da haushi shi ne yadda wata nurse da maƙwabciyarta da suka zauna a gidan
haya tare, ta riƙa ganin yadda nurse din take sakaci da mijin, haka ta shige
masa a hankali har ta samo shi, kishin wancan ya raba ta da gidanta, ita kuma
ta kashe aurenta ta aure shi. Meye wannan in ba shedanci ba?
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.