Kishi Rahama Ne Ko Azaba //10

    5) CUTARWA: Wannan ya hada har da cutar kai, tunda akwai lokacin da alkhairi zai zo, Æ™iri-Æ™iri mutum ya Æ™i shiga a dama da shi saboda masifar kishi. Ina malamin makaranta mai koyar da harshen Larabci wani mutum ya kawo matansa biyu, haka dayar daga cikinsu ta ce ba ta son makarantar, ya yi iya Æ™oÆ™arinsa wurin gamsar da ita amma ta Æ™i, a taÆ™aice dai karatun da ba ta yi ba kenan. Tunda ta zabi wata makaranta da ta ga ba ta samun  abin da take so ta watsar da karatun gaba daya.

    Sau da yawa maigida kan kawo abu ya raba wa matansa dukansu, wata ta yi tsalle ta ce ba ta so, ita sai dai a kawo mata nata daban ba za ta saka  abin da sauran suka saka ba, Æ™arshe ka ga maigidan ya ware ta gefe guda saboda halinta, ita kuma ta kasa ganewa bare ta canja. Irin wannan dabi'un kan sa wasu matan su hade kansu su fuskanci mace guda su yi Æ™oÆ™arin yin maganinta.

    Akan sami lokacin da mace za ta sayo wa dan kishiyarta abu, amma ta hana yaron yin amfani da shi, kuma har ga Allah ta san cewa ba cutar da shi za ta yi ba, kawai a ganinta ba ta buƙatar komai daga kishiyar, ko da kuwa ba ta fi ƙarfin abin ba, ba za ta iya kawo wa yaron wanda ya fi shi ba. Irin wannan kan sa uba ya saka yaransa a makaranta mai kyau ta tayar da fitina sai an cire yaronta an kai shi wata makarantar, a ƙarshe ka iske wancan din ba ta kai makarantarsa ta farko ba.

    Sau tari za ka ga ana zagin maigida wajen wariya, kullum sai ya yi wa mace daya kaza dayar kuwa kamar ba matarsa ba, ba a san cewa ita ce da ƙarfin tsiya ta zabi haka ba, misali: Kullum a gan shi a kasuwa ya je sayo wa matarsa kayan abinci da na cefane, dayar kuwa sai dai ta wanke ƙafa ta bazama kasuwar kamar ba mijinsu guda ba. Wannan abin zargi ne yadda ya kasa daidaita ma'amallarsa da su.

    A zahiri kuma ita ce ta nemi a ba ta ta sayo da kanta, ba ta son a riƙa hada kayanta da na wasu, maigidan bai cutar da ita ba, in hakan cutarwa ce to ita ta cuci kanta. Hatta a al'amuran yau da kullum za ka ga wata duk sha'anin kishiyar takan yi ƙoƙarin zuwa, amma ba a taba ganin ƙafar kishiyar a sha'aninta ba, ya nuna cewa kishiyar ba ta damu da komai nata ba. Sai ka bincika ka ga cewa ita kishiyar ke kiranta a komai amma ita ba ta iya kiran kishiyar a wani sha'aninta.

    Akan yi wasu lokuta waÉ—anda mace za ta je neman  abin da yake da mahimmanci ga rayuwarta ko na 'ya'yanta, amma idan ta lura cewa kishiyarta na ciki shi ke nan ta fasa a kai kasuwa, ko da tana sane cewa kishiyar ba za ta cutar da ita da komai ba. Duk wadannan matan idan aka saka idon kula za a taras cewa su ke cutar kansu da kansu saboda azababben kishi.

    An taba kawo wata ragadada mai masifar yaji da ta gagari kowa, da yake kishiyarta ta aibanta abin sosai sai ta ce ita ya yi mata dadi za ta ci, haka ta yi ta sharbarta a ƙarshe ta ƙare da zawon da sai da aka kai ta asibiti. Ta sha wahalar ragadadar kai tsaye ga kuma allurori da ƙarin ruwan da ta ja wa kanta ba gaira ba dalili, duk da haka bai sa ta gano cewa masifar kishinta ya jawo mata ba, sai cewa take ƙaddara ce.

    Wace take iya cutar da kanta a dalilin kishi cikin sauÆ™i za ta cutar da wata ko da cutarwar ba za ta Æ™ara mata komai ba. Kamar ta Æ™ara wa kishiya gishiri ko yaji a miya, ko saka mata  abin da zai kayar da ita a hanya, ko ko ta Æ™ullama  abin da zai gagare ta kwancewa a wajen maigidansu. Dadinta dai mugunta jifa ce a sama dake dawo wa wanda ya yi ta. In ma da nasara to ba ta wuce ganin an saka mutum a matsala ba, a Æ™arshe wanda ya Æ™ulla ya saurari nasa don zai zagayo.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba,

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.