6) AZABA A LAHIRA: A duniya dai akan kau da kai a kan duk abin da mace ke yi da sunan kishi, sau tari ba wani mataki kuma da ake dauka, hakan ta sa masu kishin suka sami damar bin mazansu har tsakiyar kasuwa su zazzage shi su koma gida su yi zamansu ba abin da zai faru. Na ga wace ta fasa wa maigidanta babban gilashin mota na baya kuma ba abin da ya yi. Wata ta ƙona kayansa gaba daya kuma aka zauna lafiya wai kishi ne.
Wata kuwa
kekketa shi ta yi da wuƙa kuma ya zuba mata ido wai uwar 'ya'yansa. Na yi hira
da wace ta ce kishiyar mamansu ta zuba musu kalanzir ƙyasta wutan ne kawai ba
ta yi ba Allah ya ƙwace su. Akwai matan da suka kashe kansu don kishi, to ko
wannan Allah ba zai yafe ba bare wanda ta yi wa wani ƙeta. Na ga matar da ta riƙa
kwasan kayan mutane tana saka wa kishiyarta don a zarge ta da sata. Wata ta riƙa
ƙala wa kishiyar wai tana zuwa neman maza. In aka ce kishi ne shi kenan.
Amma fa ba
iyakarta ke nan ba, mutane za su iya mantawa, shi kuwa mahaliccinsu ba zai yafe
ba. Ko bai bi musu kadi anan duniya ba akwai ranar hisabi, babbar matsalar
kishi ba a iya roƙon kishiya ta yafe sai an hadu a lahira. Misali wace ta raba
wata da mijinta ko da boka ko da kisisina hisabinta daban ne a wurin Allah,
wanda galibin mata masu kishi ba su da buri kamar matar da aka auro ta saku, ko
ita da shigo daga baya ta fitar da ta cikin, ba tare da sanin irin azabar da za
ta hadu da ita a lahira dalilin hakan ba.
Hadisin Jabir
wanda Muslim ya rawaito ya ce: "Shedan kan dora gadon mulkinsa a kan ruwa
ya tura 'yan kanzaginsa, fitinannun ne fadawansa na kusa: wani zai zo ya ce
"Ai na yi kaza da kaza" ya ce "Ba ka yi komai ba" sai wani
ya zo ya ce "Ai ban bar shi ba sai da na raba shi da iyalansa" sai ya
jawo shi kusa ya ce "Yauwa! Kai ka yi abin yabo". To ta ya za ki raba
mutum da matarsa ba ki yi tunanin kin zama daya daga cikin fadawansa na kusa
ba? Ai kina cikin shedanun mutane.
Wace za ta
daga murya tana zagin kishiyarta ba tare da ta yi mata komai ba, a dole ita
kishi ne take yi, ai ta shiga cikin waÉ—anda Allah SW ya fada a Suratul Ahzab
cewa sun ja wa kansu laifi da zunubi bayyananne. ke nan za a hadu da Allan, to
bare kuma masu yi wa kishiya ƙazafi, ko hassada dake cinye kyawawan aikin
mutum, abin tsoron hassadar ta fi ƙarfi a tsakanin kiyoshi. Ba sa ƙaunar ganin
kishiyar da alkhairi, ko kuma ta yi ta burin arziƙin da ta samu ya gushe.
Wani zunubi ne
mafi girma kamar zuwa wurin boka da sunan an je karbo taimako? Ko an tashi a
tsaye don kare kai? Da yawa mata kan fake da cewa sun je neman taimako ne don
kare kai daga kishiya, alhali tsafi ne dake shigar da mutum wuta. Akwai wace za
ta ce a hana wata haihuwa gaba daya sai dai ita, ga laifin zuwa wurin boka ga
na barnar da za a yi wa kishiya wanda ba yadda za a yi sai in ita kishiyar ta
yafe.
Duk wata
matsalar da za a tura wa kishiya an yi aiki da aljani ne, wanda ta sani ga
shinan a Ƙur'ani ƙarara Suratul Baƙara mai yin hakan ba ta da rabo a lahira, an
yi tir da abin da take aikatawa. A taƙaice
dai bayan matsalolin kishi da mace kan fuskanta a a zamantakewarta ta duniya da
mutanen dake kewaye da ita, ko a lahirar ma wasu matsalolin ne na daban. Don
kuwa Allah SW ba zai bari ya wuce haka kurum ba.
To macen da ta
je yi wa kishiyarta mugunta ya dawo kanta Allah SW ba zai yafe ba bare wance ta
yi din kuma ya kama kishiyar? Ina jin wata malama na magana take cewa galibinmu
kishi ke kai mu wuta, tunda ba kalar sabon Allan da ba ma yi a kansa, ta ce abin
takaicin ba wani dadi muke ji ba in mun yi, ba kuma wani darasin da muke dauka
in ya rikice wa wata. Maganar sakamakon duniya da lahira duk mun sani amma ba
ma yin la'asar. Malaman cikimmu ba su tsira ba bare waÉ—anda ba su dauki shari'a
a matsayin magwaji ba.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.