4) RUSA GIDA: In kana neman abin da ke wargaza gida daga sama har ƙasa da ka sami kishi daya kenan, ƙila ma ba ka da buƙatar neman wani. A duk lokacin da muka kira wani mummunan abu muka hada shi da kishi to mummunan kishi muke nufi, shi ne wani lokaci maza ba sa gane shi, har sai ya yi lahanin da ba zai taba gyaruwa ba. Wata macen kan sa namiji ya kori uwar 'ya'yansa kuma ba za ta iya riƙe su ba, kwanannan ba a yi shekara ba wata ta bar gidanta ta auri wani amma ta kasa riƙe masa 'ya'yansa, ita ma inda ta bari din wata ta kasa riƙe mata nata, dukansu ba wace ba a sake ta ba. Wannan ba wani abu ne ba banda son kai wanda shi ake kira kishi.
Da mace na da
wayau ai an bar mata 'ya'ya kyauta yadda za ta tarbiyantar da su ta fuskar da
take so, ta kuma ci gajiyarsu, amma baƙin kishi ya hana. Irin wannan kishin kan
sa namiji ya rabu da 'yan uwansa, yadda mace za ta shiga tsakiya daga ita sai
maigidanta, ba ruwanta da 'ya'yan kishiya ma bare 'yan uwansa. Na taba jin wata
na sumbatu wai duk abin da take wa 'yan
uwan mijin ba sa gani, ba ta san me ya sa suke son shiga mata sha'anin gidanta
ba. Ta manta cewa ita ce aka auro, waÉ—anda take ganin bare su ne masu gidan,
mutuwa ko saki daya zai sa ta kama gabanta ta bar musu gidan.
Shekarun baya
wasu yara suka kawo min kukan babansu, ya yi ritaya ya karbi kudinsa ya bude
shago yana zama a ciki, amma ba su isa ko biskit su samu a shagon ba, sai dai
'ya'yan kishiyar mamansu, a ƙarshe ma ta hana su zuwa gidan gaba daya da yake
duk sun yi aure. In suna son ganinsa sai dai su same shi a shago, in wani abu
zai ba su dole sai a gabanta, kuma sai
abin da ta ce a bayar, duk abin
da ya ba su sai ta sa an rage wai yaranta fa? Ta kakkame komai, wani sa'in sai
dai baban nasu ya saci ciki ya fita in zai ba su wani abu ya ba su a waje in ba
haka ba matar ta hana.
Yarinyar ta ce
"Babban abin da ya saka ni kuka shi
ne yadda na sami babana a shago na zauna cikin farin ciki muna ta hira da zan
tashi ya dauko (abu) ya ba ni, ashe a kan idonta ne ta hango, kamo hanya da ta
yi ya ganta, ai kuwa ya ƙwace ya fara ce min: Fita-fita, maza ki je gida na
gaji haka. Haka dole na fita ina kuka" daganan ta ce gidan ya ishe su gaba
daya ba sa ma sha'awar zuwa, tunda uwarsu ma ta dade da rasuwa uban kuma ba ya
buƙatarsu.
Duk tambayoyin
da na yi mata ta ba da amsa da kanta cewa babansu na son su, amma kishiyar
mamansu ce ba ta buƙatar ganinsu a gidan gaba daya, kuma ta yi duk abin da za ta yi ta raba su da gidan, ta
tabbatar wa uban da cewa to fa 'ya'yansa ke nan wadannan dake gabansa, sauran
kuma oho. Na ce mata "A gidanku duk kuka girma?" Ta ce "I"
"Kuna zaman lafiya da mazajenku?" Ta ce "Alhamdu lillah duk
mazajensu sun san matsalolinsu kuma suna iya bakin ƙoƙarinsu"
Daganan na ce
"To ku gode wa Allah ku miƙa masa lamarin, babu abin da bai da iyaka ba zai bari ya wuce haka
kawai ba" wannan fa ya fi sauƙi sama da wace ta ga ba ta da yara ta sa
mijin ya sayar da gidan ya kama musu haya, ta karbe kudin ta ƙara gaba ta bar
shi da uwargida da dumbin yara, a ganinta ta cutar da kishiyar. Wata kuwa ta
kai yadda maigidan ya ja wa 'yan uwansa layi da cewa kar wata ko wani daga
cikinsu ya ƙara taka masa gida ko ya tambaye shi wani abu, ƙila anan a ce sun
ci riba amma gaba fa?
Wanda ya fi
muni a duk wadannan shi ne wanda matan za su hana 'ya'yansu su yi zumunci, ƙila
wanda ake kishin dominsa ya mutu, yaran kuma su taso kansu a rabe, mutum da dan
uwansa amma ya fi son ya kyautata wa bare, in da dan uwan zai sami wani budi
daga Allah sai ka ga ransa ya baci sam bai yi masa fatar alkhairi, ya gaji
mummunan kishi daga mahaifiyarsa. Da za ka tsare shi ka tambaye shi me ya yi
masa bai da kalmar da zai iya gaya maka, sai dai ya yi ta kame-kame, mummunan
kishi ne kawai da aka gada daga mahaifa.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.