Kishi Rahama Ne Ko Azaba //03

    iii) Son kai: Lokacin da mutum yake son yabo, a ayyukansa, shigarsa, maganarsa, zabinsa da sauransu. In dai wannan ya yi kaka-gida a zuciyarsa to dole ya yi fito na fito da duk a  abin da zai saba wa hakan da wannan kishinsa zai bayyana. Kamar mace ce a cikin gida, wata ba za ta damu ba a ce duk duniya sun fi ta kyau amma kar maigidanta ya kuskura ya furta cewa wata ta fi ta. Saboda ta yarda wa kanta a duniyarsa cewa daga ita kuma sai dai a yi fatiha a tashi.

    Kishi mai kyau kan iya shigowanan amma bai cika yin tasiri ba, da a ce wata mace za ta sha lalle wanda ko mata kan yi sha'awa bare namiji, ta fito, sai kika lura cewa maigidanki yana kallo ba ki da buƙatar yin fada da ita don ba ta hana ki yin irinsa ba, kuma ba ta ce maigidanki ya kalla ba. Shi ya kamata ki ƙalubalanta shi ne naki. Tambayrsa kawai za ki yi, nan take zai rude ya fara ƙoƙarin ƙwatar kansa: "Lallen ya ba ka sha'awa ne?" Bar shi ya yi ta inda-indarsa, in za ki iya sayen irinsa saya ki burge shi in ba za ki iya ba roƙe shi ya sayo miki.

    Kamar mace a tsakaninta da maigidanta za ka taras ba ta son wata macen ta rabe shi in ba ita kadai ba, kyawunta kadai zai gani, abincinta kadai zai ce yana da dadi, kuma da ita kadai zai zauna. Wannan kam son kai ne. Mace ba ta damuwa da hakan ko da a gabanta akwai mata biyar zuwa shida dake fatar su sami mijin aure. Ita dai kar a shigo mata da wata. Anan mata kan kasu gida biyu, akwai wace ba ta son kishiya, amma ba ta damu ba in diyarta za ta zama ta hudu a wani gidan. Akwai wace duk in ta ji wani na auren mata biyu zuwa sama to mugu ne azzalumi, ba yadda za a yi diyarta ta auri mai mata.

    Duka dai nau'o'i ne na son kai. ko da yake da wahala ka ji mace ta ce ba ta Æ™aunar kishiya ne kawai a rayuwarta, ita kadai take so ta zauna. Sai dai ka ji ta ce tana tsoro ne. Za mu tattauna wannan a gaba. Da yawa za ka iske maigida da uwargida a zaune ba mai magana da wani, dalili kuwa wai maigidan ya ci abinci a waje bayan ya san za ta girka masa a gida. Ko kuma ya yabi wani abincin, wato nata bai kai shi dadi ba kenan,  abin da take so shi ne daga nata ba wani.

    Duk lokacin da mace ta ga mijinta na kallon wani abu a wajen wata in tana son yin kishin ne da gaske ta yi  abin da wancan ke yi ta wuce wurin, ba ta da buÆ™atar yaÆ™arta ko ta juyo wurin maigidanta ta yaÆ™e shi, ta yaÆ™i kanta kawai ta yarda da cewa lallai maigidanta na buÆ™atar  abin da yake kallo kuma dole kuma ta iya shi. Za ka iske wata macen shekara 54 amma ta saka takalmi kambas a cikin gida, ta sha Æ™ananan kaya ta ci kwalliya, a daidai wannan lokacin ko 'ya'yanta mata suna da yara. Ba sha'awar shigar take yi ba kishi take don kar wata a gefe ta yi hakan ta sace mata hankalin miji.

    In abinci ne kika ga yana yawan ci a waje, yi ƙoƙari ki san bambancinsa da naki, koyo yadda ake dafa shi, ko ki sayi kayan da da wancan take zubawa don ki dawo da shi wurinki. Ƙila a kira wannan da kishi amma ya fi wanda za ki tsaya kina fada bayan ga mafita a hannunki, tabbas rashin iya adon da namiji ke muƙata, ko girki, ko magana duk sukan sa namiji ya fara neman wace za ta yi daidai da shi. Na san namijin da ya ƙara aure saboda matarsa ba ta iya girki ba, na san wanda ya ce zai ƙaro saboda ta gidan ba ta yi masa shigar da yake buƙata ba, kishi na haƙiƙa anan shi ne ki rufe ƙofar ba tare da kin yi wata hayaniyar da za ta dame ki ba.

    Wannan masaniyar da maza ke da ita ta irin wannan kishin ke saka su su hada fada ba tare da sun sani ba, ba yadda za a yi ka kushe wata ba tare da maganar ta koma mata ba, lokacin da za ka ce wa amaryar kana son shigo da ita ne don uwargidanta ƙazama ce, ko ba ta iya girki ba, ko ba ta iya gyaran shimfida ba, ko ba ta kula da kai ko 'ya'yanka duk lokacin da wani abu ya hado su cewa za ta yi ke da kike kaza da kaza ma? Wa ya ja mata? In wani yana son ya gamsar da uwar gidan sai ya ce wallahi ta nace min ne na rasa yadda zan yi, ko uwayenta suka matsa masa ya auro ta shi ba so yake ba. Ko ya nemo wata ƙissar da zai nuna ba ta ransa don kawai ya gamsar da uwargida, maganar za ta tashi.

    Tabbas mace na son kanta fiye da kowa masamman a gidan miji ko a gaban wanda take so, babu laifi idan masoyinta ya amince da haka, amma kar ya zaƙe, yarda da manufofinta na ita kadaice ba kowa, da tafiya a kan haka yana daya daga cikin dalilin da suke motsa mata kishi a lokacin da aka nemi a saba hakan. Haka duk wanda ya amince wa kansa cewa babu kamarsa zai yi ƙoƙarin tabbatar da hakan a aikace, da yaƙar duk wanda yake neman ya yi tarayya da shi.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.