Ticker

6/recent/ticker-posts

HUKUNCIN WANDA YA YI MAGANA A LOKACIN DA LIMAN YAKE HUDUBA A RANAR JUMA'A

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu Alaikum Malam. Ya Hukuncin Wanda ya yi Magana Ko Danna Waya A Lokacin Da Liman Ke Huduba Ranar Juma’a.??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Wanda ya yi magana ranar juma'a ko wasa, ko danna waya, ahalin liman yana huduba, babu shakka ya yi laifi wato ya yi lagawu wato yashasshen zance na wargi.

Domin shi sauraren huduba ranar juma'a ibada ne yana cikin hukunce hukuncen da juma'a ta keɓanta dasu da sauran ranaku, kuma hadisi ingantacce ya razanar dangane da masu zance ko wasa da wani abu wanda zai dauke hankalinsu daka sauraren huduba lokacin da liman ke huduba, kuma basu da ladan juma'a kawai dai sun yi azahar ne.

Maganar nan kuwa koda ta nusar wace koda wani dan'uwanka ne yake wani abu da bai daceba kace yabari ko ya yi shiru to kayi lagawu, kuma baka da ladan sallar juma'a.

Allah kayi salati da sallama abisa Annabi muhammad da alayensa da sahabbansa.

Wallahu a’alam.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments