Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Siyar Da Kaya Kafin Su Zo Hannu (Pre-Order)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam tambaya ce game da masu siyan kaya online ko kuma wanda suke kira pre-order, za a turo maka da hoton kaya ka zaɓi wanda kake so sai ka tura kuɗinka, sai a siyo, a dora riba, sannan a baka, saboda babu kayan a kasa lokacin da aka siyar maka, yawancin waɗanda suke harkar ba su da kuɗin da za su mallaki kayan kafin su siyar, da kuɗin Kwastomomi suke siyo kayan, ya halasta ko ya haramta ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam

A zahirin nassoshin Sharia wannan Nau'i na cinikayya haramun ne, saboda siyar da abu ne kafin mutum ya mallake shi.

Hakim Bn Hizam ya tambayi Annabi ﷺ cewa: Mutum ya kan tambaye shi Hajar da ba shi da ita sai su yi ciniki ya sayar masa, sai ya je kasuwa ya sayo, sannan ya ba shi, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa: " Kada ka siyar da abin da ba ka da shi" Kamar yadda Abu-dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Imamu Ahmad suka rawaito.

Musulunci ya hana wannan Cinikayyar ne saboda akwai rashin tabbas a ciki, Idan aka samu macuci zai iya guduwa da kuɗin, sannan ba dole ba ne a samu kayan in an je kasuwa .

Duk cinikayyar da za ta kawo hatsaniya da saɓani tsakanin musulmai haramun ce, wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai azurta shi ta inda ba ya zato, kamar yadda ya fada a suratu Addalak.

Allah ne mafi sani

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments