Shin Yaushe Ake Yaye Yaro Daga Nono?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam, tambayata ita ce, shin akwai ranakun da muslunci ya ware don a yaye yaro saboda na ga wasu na cewa ba a yaye sai laraba ko juma'a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu, Yaye yaro daga nonon uwa ba sai ranar Laraba ko Juma'a ba, wannan kawai al'ada ce ta waɗanda suke zaton ranar Laraba tana da wata falala ta musamman, duk da cewa ranar Juma'a rana ce mai daraja, to amma ita ma ba a ce sai a wannan rana za a yi yaye ba. Kawai dai abin da nassin Alƙur'ani ya tabbar game da yaye yaro shi ne, iyaye mata su shayar da ‘ya’yansu na tsawon shekaru biyu cikakku, ga wadda ta yi nufin cika shayarwar, kamar yadda aya ta 233 ta Suratul Baƙara ta bayyana.

    Mafi kyawon lokacin da ya fi kamata a yaye yaro shi ne a lokacin da yanayi ya daidaita, wato ba lokacin tsananin zafi ba, ba kuma lokacin tsananin sanyi ba, kuma ya zama bayan haƙoran yaro da dasashinsa sun yi ƙarfi, yaye yaro a irin wannan lokaci ya fi ma yaron daɗi kamar yadda Ibnu Ƙayyimil Jauziyya ya tabbatar.

    Duba Tuhfatul Maudood Bi'ahkamil Maulood 199-200.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.