Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Ke Ƙaurace Wa Mijinta A Shimfida?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum dan Allah malam laifi ne dan mijin mace ya ɓata mata rai ta yi yaji ta ƙaurace masa a wajen shimfida?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, 

'Yar uwa a gaskiya abin da shari'a ta nuna shi ne bai halasta mace ta ƙaurace wa mijinta a shimfiɗa ba ko da ya ɓata mata rai matuƙar ya kiyaye haƙƙoƙinta da Allah ya wajabta masa, saboda hadisi ya tabbata daga Abu Hurairah Allah ya ƙara masa yarda ya ce:

Manzon Allah ﷺ ya ce:

"Idan namiji ya kira matarsa zuwa shimfiɗarsa sai ta ƙi, har ya kwana yana fushi da ita, to Mala'iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari".

Bukhariy (3237), Muslim (1436).

Saboda haka, lallai mata su guji ƙaurace wa mazajensu a lokacin da suka buƙace su, saboda kauce ma wannan tsinuwa na Mala'iku, su kuma mazaje su ji tsoron Allah su daina ƙuntata wa matayensu.

Abubuwan da suke zama uzuri ga macen da mijinta ya neme ta ta ƙi su ne, kamar mace tana jinin haila, ko jinin biƙi, ko rashin lafiyar da idan ta yi jima'i za ta cutu, ko abin da ya yi kama da haka na uzuri karɓaɓɓe a Shari'a, sai dai shi jinin haila da na biƙi ɗin suna hana saduwa ne, amma ba sa hana jin daɗi daga abin da ke saman gyauto.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments