𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin a
Shari'ance Mene ne hukunci gameda karin gashi da Mata sukeyi a Kansu?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dukkan
Mālamai sun yi Ittifāƙi akan cewa bāya halatta ga dukkan wata Mace ta yi amfāni
da gāshin wani Ɗan-Ādam Mace ko Namiji don ta yi Ƙārin-Gāshi dashi a kanta,
wannan kam harāmunne Ƙaulan-Wāhidan, Mālamai sunkafa Hujjarsune da Hadisan
Mαиzoи Aʟʟαнﷺ da sukazo akan haka, daga cikinsu akwai wannan Hadisi da Aηηαвιﷺ
Yake cewa:
لَعَنَ اللَّهُ
الْوَاصِلَةَ وَالْمُسْتَوْصِلَةَ......إلخ
MA'ANA:
Aʟʟαнﷻ Yā
tsīnewa Mātar datake (sana'ar) Ƙārin-Gāshi, dakuma Mātar da'akeyiwa
Ƙārin-Gāshin......
Danhaka
harāmunne bai halattaba, to amma Saidai Mālamai sun yi Saɓāni akan cewa Shin
wannan haramci yashafi dukkan kowanne irin nau'in Gāshi* ko wani abu da Mace
zata iya amfani dashi ta yi Ƙārin-Gāshi a kanta, kokuma ā'a haramcin yā
taƙaitane kaɗai akan yin amfani da asalin Gāshi-Mutum? wani Sāshe na Mazhabobin
Hanafiyya da Hanābila suntafi akan cewa indai ba Gāshin-Mutum bane to yā
halatta Mace ta yi amfani dashi, wāto kamar irin su Zaren-Ūlu, Zaren-Roba,
Ƙyallen-Yādi, Gāshin-Dabbōbi, dadai sauran makamantansu, amma Mazhabin
Mālikiyya tāre da mafi yawa daga cikin Mālamai sun ɗauki (Umūm) na wannan
Hadisine, danhaka sukace wannan haramci yashāfi kowanne irin nau'i na Gāshi, ko
wani abu dabam wanda za'ahada dashi ayiwa Mace kitso a kanta, sukace haramun ne
bai halattaba ayi, dalilinsu kuwa shi ne, baya ga (Umūm) na wancan Hadisi,
sukace akwai wani Hadisin da Al-Imāmu-Muslim ya ruwaito wanda Yake cewa:
زَجَرَ النَّبِيُّ
(ﷺ) أَنْ تَصِل الْمَرْأَة بِرَأْسِهَا شَيْئًا
MA'ANA:
Mαиzoи Aʟʟαнﷺ
Yā tsāwatar gameda cewa kada wata Mace ta haɗa Gāshinta da kowane irin abu,
Sukace wannan Hadisi yā game Kōmai-da-Kōmai bawai sai Gāshin-Mutum kaɗaiba,
sukace kōma mene ne bai halattaba, kamar Mace take amfani da Gāshi irin na
Company da'ake sayarwa a Kanti, hakanan wasu daga cikin Mālamai sukace haramun
ne Mace ta yi amfani da dukkan wani abu wanda zaisa kanta ya yi tudu aga kamar
cewa ai tana da Gāshi ne dayawa a kanta, alhāli kuma ba yawan Gāshi bane, kawai
*āyi cōge ne da algus, hakanan harāmunne Mace-Musulmā tasa Hūlar-Gāshi a kanta,
wacce ake ƙiranta da Lārabci (الباروكة) domin kuwa itama hukuncinta yashiga
cikin wancan Hadisi, ko da yake akwai Mālamanbda suke ganin ya halatta a yi amfani
da'ita, amma magana mafi inganci haramun ne, Sannan kuma sanyata ya zama anyi
kamanceceniya da Mātan-Kāfirai, wanda wannan ma kaɗai yā isa ya zama Hujja na
haramcin yin amfāni da'ita, to amma idan ya kasance Mace tasamu wata larurar da
tasa gaba ɗaya Gāshin-Kanta yazube, kanta ya zama ba Gāshi kamar anyi mata aski
Ƙwal-Ƙwal, kokuma Mātar datake da Sanƙo a kanta gaba ɗaya ba Gāshi, anan sai
wasu daga cikin Mālamai sukace ya halatta ta yi amfani da Hūlar-Gāshi dan
tarufe aibun dake tare da'ita, domin batayi hakan da nufin ado ba dan taƙāra
kyau, saidai tayine dan tarufe larurar dake kantane kawai, to amma Saidai mafi
yawan Mālamai suntafine akan cewa ko da kanta Ƙwal-Ƙwal yake bābu Gāshi to duk
dahaka bai halattaba ta yi amfani da Hūlar-Gāshi.
Doмυп пεмαп
ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
كفاية الطالب
الرباني" (2/459)
فتاوى اللجنة
الدائمة" (5/191)
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
AMSAWA
Mυѕтαρнα
Uѕмαn
08032531505
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.