Abubuwan Da Suke Taimaka Wa Mutum Rage Yawan Fushi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, ya aiki? dan Allah ina niman alfarmarku, ina so ku ba ni wata addu'a saboda idan mutun ya yi min kuskure ko dan kaɗan ne wallahi sai na rama nake samun sukuni a zuciyata, ko da mijina ne idan yai min sai na rama ko da za mu samu matsala da shi sai na rama nake jin daɗi. Ni kuma ban san me ya sa nake yin haka ba, wallahi ni kaina ba na son hakan, saboda sai bayan na rama sai daga baya na dawo ina nadamar abin da na yi, na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

     Wa'alaikumus Salamu, Baiwar Allah yana da kyau ki sani cewa ba a son rama mummuna da mummuna, daga cikin kamalar mutum ya zama idan aka munana masa ba ya saurin ɗaukar matakin ramawa har sai ya yi uzuri iya uzuri, daga bisani sai ya ɗauki mataki ta hanyar maslaha, idan kuma abin da ake yi masa bai kai ya komo ba, to yin haƙuri ya fi alheri a zance na gaskiya.

    Tabbas matuƙar kika yi haƙuri, duk wani mai cutar da ke sai Allah ya saka maki a kwana a tashi in Allah ya so, saboda haka ki ji tsoron Allah ki riƙa haƙuri da abokan mu'amala, musamman mijinki da kishiyoyinki idan kina da su, da abokan arziƙinki a ko'ina suke, wani mutum ya zo wurin Manzon Allah ﷺ ya ce masa ya yi masa wasiyya, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa 'Kada ya yi fushi', ya kuma maimaita masa da yawa cewa 'Kada ya yi fushi', kamar yadda Abu Hurairata ya ruwaito.

    Duba Sahihul Bukhariy 6116.

    Sannan daga cikin abubuwan da suke taimakawa wajen rage yawan fushi sun haɗa da:

    1. Yawaita yin addu'a a kan Allah ya raba mutum da yawan yin fushi, domin zukata suna hannun Allah ne.

    2.Yawaita neman tsari daga Shaiɗan, saboda shi ne yake kunna wutar fushi a zukatan mutane, wato yawaita faɗin (A'uzhu Billahi Minas Shaiɗanir Rajeem).

    3. Yawaita tuna sakamakon da Allah ya tanadar wa masu kame fushinsu.

    4. Ƙaranta yawan yin magana, da canjawa daga yanayin da mutum yake a lokacin da ya fusata, wato idan yana tsaye ne ya samu wuri ya zauna, idan kuma yana zaune ne sai ya kwanta.

    5. Nisantar duk abin da zai iya haifar masa da fushi ɗin, da barin tunanin abin da ke haifar masa da fushin.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.