Shin Malam Yaya Mai Yawan Saɓon Allah Zai Kyautata Halinsa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Malam Yaya Mai Yawan Saɓon Allah Zai Kyautata Halinsa?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله رب العالمين، وصلى الله على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.

    Babu shakka saɓon Allah abune dake haifarwa da bawa matsaloli masu yawa, amma kuma Allah mai yalwar falalane matukar mutum ya yi nadama yagane kuskuren sa ya tuba to lallai Allah mai yawan gafarta zunubaine, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

    (وتوبو إلى الله جميعا أيها المؤمنون لعلكم تفلحون)

    Kutuba zuwa ga Allah gaba dayanku yaku muminai Zaku samu tsira da rabauta.

    yasake cewa:

    (قل يا عبادي الذين أسرافوا على أنفسهم لا تقنطوا من رحمة الله إن الله يغفر الذنوب جميعا)

    Kace dasu yaku bayin Allah waɗanda kukayi Laifukawa kawunan ku kada kuɗebe zaton tunanin Allah ba zai iya yafe muku ba, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya kuma shi Allah mai yawan gafara ne dajinkai ga bayinsa.

    Kalmar tuba tana da girma da dalililai masu zurfi, bakamar yanda wasu dayawa suke ɗauka ba, kawai kafurta da harshe kuma kaci gaba da aikata laifuka, ka lura ka kula dafadar Allah maɗaukakin sarki:

    (وأن استغفروا ربكم ثم توبوا إليه )

    Kunemi gafarar ubangijinku sannan kutuba zuwa gareshi, zakasamu awannan aya cewa shi tuba wani al'amarine dayake karuwa tahanyar neman gafarar ubangiji.

    Kuma saboda duk wani babban al'amari zaka sameshi yana da sharudda saboda haka malamai suka ambaci sharuddan tuba, waɗanda suka dakko daka Alƙur'ani da hadisai.

    1- Barin zunubi da gaggawa

    2- Yin dana sani akan abun da ka riga ka aikata na laifuka.

    3- Ƙudurta niyyar ba za ka sake komawa wannan laifi ba.

    4- Maida haƙƙin wanda ka zalunta, ko barranta daka azzallumai idan da kaine kake taimaka musu.

    Bayan waɗannan kada mutum ya manta dawasu al'amuran nadaban waɗanda sunada mahimmanci kwarai wajen tabbatuwar tuba nagartacce,

    1- Ya zamto dan Allah mutum yatuba daka zunubi, badan wani abu yabar laifin ba kodan bashi da ikon aikata laifin, ko kuma kabar zunubi dan tsoran maganar mutane, batuba bane wanda yabar zunubi dankare mutuncinsa wajan mutane, kodan bashi da iko, kodan kare lafiyarsa daka wata cuta da'ake samu daka zunubinba, ba a kiran wanda yabar cin hanci ko karbar rashawa danyana tsoran kada akamashi yasha tozarci, haka wanda yabar zina dankada yadau cutukan datake haifarwa, komai shangiyar dayabar shanta dan illolin datake haifarwa, ko barawon dabashi da ikon yinsata ko danfashin darashin samun dama ce tasa ya tuba, duk wani laifi indai badan tsoran ukubar da Allah yatanadar akai ba ka tuba daka gareshi, to bakayi tuba wanda Allah yakeso ba.

    2- Wajibi ne kadunga jin bakin ciki duk lokacin da katuno aikin zunubin daka aikata abaya da kuma illar sa,

    Ana nufin tuba ingantacce baya yi wuwa tare dakana jin daɗin abun da ka aikata abaya inkatuna, koma kadunga burin inama ka sake komawa nan gaba.

    Ibnul ƙayyeem a cikin littafinsa Adda'u waddawa'a yakoro bayani akan illar zunubi da kuma cutukan dayake haifarwa, daka ciki ya ce:

    Haramtawa mutum ilmi, zunubi nasa kakasa samun nagartaccen ilmi ko kasamu ilmin amma mara amfani, rashin kwanciyar hankali, Kuncin al'amura, cutar jiki, zunubai na sanya Allah yahanawa ɗan adam ikon aikata abun da yake biyayyah ne ga Allah, dakuma rashin albarka arayuwa, da karancin dacewa cikin duk abun da mutum zai yi, da kuncin rai, da zakkewa zunubai, dakuma aikata kananun laifuka, Bakin cikin mai zunubi game da Allah da bakin cikinsa da mutane, da tsinuwar da dabbobi za su dunga yi masa, da rigar kaskanci dazai shiga, da bushewar zuciya dashiga karkashin la'anta, dakin amsa addu'arsa , da aikata ɓarna afili da ɓoye, da rashin kishi, da gushewar kunya atare da mutum, da gushewar ni'imomi, dasaukar bala'i da saukar datsoro da firgici azuciyar mai saɓo, dafadawa cikin tawagar Shaiɗan da mummunan karshe da kuma azaba alahira.

    Inkasan waɗannan illoli na zunubi zaisa kabar aikata laifi gaba ɗaya, domin wasu mutane idan suka bar laifi saisu koma wani wanda aganinsu ma'aunin su ba ɗaya bane da wanda suka bari, suna ɗaukar yafi sauki sauki akan wanda suka daina sauki.

    Bayan duk kabi matakan tuba idan kanada wasu abokai da kuke aikata wannan zunubi wajibi ne ka canjasu da wasu, domin dayawa mutum kan tuba daka zunubi amma sanadiyyar rashin rabuwa dawanda suke aikata laifin tare sai mutum yakoma yasake fadawa cikin ɓata sama dawanda yake abaya, ko gurine ko majisa dakake tasirantuwa da ita wajibi ne ka kaurace mata kacanza dawata wacce zaka samu ingantuwar tubanka da imaninka, kasamu abokai nagari masu addini waɗanda ko da basu umarceka da kyakkyawa ba zaka tasirantu dasu wajan aikata mai kyau kaima.

    Ka yaiwata aikata kyawawan ayyuka domin kyawawan ayyuka suna share munana.

    Allah maɗaukakin sarki a cikin suratul Furƙaan bayan jero dangin manyan zunubai wanda muminai nagari basa aikatawa kuma duk wanda ya aikata su za a rufanya masa azaba sai ya ce:

    (إلا من تاب وآمن وعمل عملا صالحا فأولئك يبدل الله سيىاتهم حسنات وكان الله غفورا رحيما)

    Sai waɗanda suka tuba suka yi aiki nagari waɗannan sune Allah kecanza munanan ayyukansu su koma kyawawa Allah ya kasance mai gafarane mai jinkai.

    Muna rokon Allah ya shiryar damu zuwa ga abun da yakeso kuma ya yarda dashi, yakarbi tuban mu gaba ɗaya domin shi mai yawan karbar tuba ne mai jinkai.

    سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

    📝 Tambaya Da Amsa Abisa Fahimtar Magabata Nakwarai

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.