Kundin binciken da aka gabatar a Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Tarayya Gusau, saboda cike wani gurbi, domin samun shaidar kammala digirin farko na fannin nazarin harshen Hausa (B.A. Hausa) (Oktoba, 2021).
Bikin Saukar Alƙur’ani A Garin Gusau
Na
Makiyu Balarabe
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan aiki
nawa zuwa ga mahaifana Marigayi Malam Musbahu Balarabe Rogo da mahaifiyata
Rukayya (Gambo), domin su suka bani ƙwarin
guiwa dan ganin na mai da hankali a kan karatuna da kuma irin addu’o’in da suka
yi. Da fatar Allah (SWT) ya jaddada harama a gareshi da sauran Musulmi baki ɗaya.
GODIYA
Ina miƙa godiya
ga Allah (SWT) mai kowa mai komai, mai iko a kan kowa, wanda ya ƙaddare
ni da kammala kundin Digirina Farko. Ina Salati marar iyaka ga jagoran al’umma
Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa da sahabbansa, da kuma waɗanda
suka bi tafarkin sa har ya zuwa ranar ƙiyama.
Ina miƙa godiya
ta musamman, ga madugu uban tafiya, wato ubanmu, kuma shi ne ya yi ƙoƙarin ɗora ni a
kan hanya don ganin an yi nasarar wannan aiki, wato Dr. Adamu Rabi’u Bakura.
Haka kuma ina godiya ga sauran Malamai na sashe kamar Malam Musa Zaria, Mal.
Isah S. Fada, Malam Bashiru Abdullahi da Malama Halima da Dr. Aliyu Dangulbi.
Godiya ta musamman ga Shehi
na kuma Murabbina wanda shi ne mai tarbiyantar da ni Sheikh Mal. Abdullahi
Abubakar Yabo, Zawiyya, Gusau, da kuma mai ɗaki na
Rahinatu Muhammad Bello (Baby), da yaranmu Makiyya da Muhammad Abdullahi
(Murad) da ma duk wanda ya taimaka a kan wannan nasara da Allah ya bani ta
kammala wannan Digiri na Farko, Allah Ubangiji ya saka maku da mafificin
Alkhairi amin.
TSAKURE
Wannan bincike mai taken
Bukin Saukar Alƙur’ani a
Garin Gusau, ya sha banban da sauran bukukuwan ƙasar
Hausa, domin ana gabatar da shi ne, a sanadiyar sauke Alƙur’ani ko haddace shi da ɗalibai
kanyi. Ya yin gudanar da wannan bincike, an yi waiwaye domin duba ayyukan
masana da manazarta, kama daga bugaggun littafai, kundayen bincike, mujallu da
muƙalu. Wannan bincike ya bayyana ma’anar kalmar
biki, sauka, Alƙur’ani,
gari, Gusau, daga bisani an kawo ire-iren bukukuwa da kuma tasirin da zamani ya
yi game da bukin saukar Alƙur’ani,
haka kuma an bayyana yadda ake aiwatar da bukin saukar Alƙur’ani a Garin Gusau Jiya da yau.
BABI NA
ƊAYA
GABATARWA
1.0 SHIMFIƊA
Dukkan yabo da
godiya sun Tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai kowa mai komai wanda ya ƙaga halittar ɗan-Adam
ya kuma Sanar da shi abin da bai sani ba. Salati da Aminci su ƙara tabbata ga jagora Annabi
Muhammadu (S.A.W.) da Alayansa da sahabbansa da masu bin su har zuwa ranar
tsayuwa, Ina kara godiya ga Allah da ya ƙaddara gudanar da wannan bincike a fannin Ilimi
domin kammala karatun digiri na farko.
A wannan babi mai
suna "Gabatarwa" za a yi bayanin abubuwa muhimmai kamar haka: manufar
bincike domin babu wani aiki da za a gudanar ba tare da wata manufa ba. Saboda
haka wannan aiki akwai manufar gabatar da shi idan an shiga cikin aikin za a ga
manufar. Haka kuma an yi tsokaci a kan hasashen bincike, Farfajiyar bincike,
matsalolin bincike, haka kuma an kawo Muhimmancin Bincike, Hanyoyin gudanar da
bincike, daga ƙarshe naɗewa.
1.1 MANUFAR
BINCIKE
Duk wani abu da ɗan Adam
zai yi to yana da manufa ko Dalili , babu shakka duk wani abu da aka yi shi
babu maunufa to wannan abu ko ba shi da ma'ana kuma ba shi da amfani.
Wannan bincike
yana da manufar da tasa aka gudanar da shi. Manufar gudanar da wannan bincike
sun haɗa da:
cike girbin kammala karatun samun shedar digiri na farko a fannin Hausa (B.A.Hausa).
Haka kuma akwai ƙudirin bayyana yadda ake Bikin saukar Alkur'ani a
garin Gusau, wata kuma manufar ita ce domin a zaƙulo muhimman bayanai da suka shafi bikin sauka da
ire-iren ta ko kashe kashenta. Domin a fahimtar da al'umma yadda Addinin
Musulunci da ilimin Al-ƙur'ani
suke da muhimmanci da matsayi a rayuwar Hausawa, dan gane da yadda suke gudanar
da bikin saukar Al-ƙur'ani musamman in mun
kalle shi ta fuskar jiya da yau (da da yanzu) a garin Gusau.
1.2 HASASHEN
BINCIKE
A yayin da aka
kammala wannan aikin ana hasashen binciken zai fito da hoton yadda ake gudanar
da bikin saukar al-ƙur'ani ƙarara a garin Gusau, ya zama wata manazarta ga
masu bincike game da bikin saukar Al-ƙu'ani
da sauran bukukuwan Hausawa.
Bugu da ƙari ana hasashen ya zama wani
madubin dubawa na lura da abin da ya kamata a yi koyi da shi musamman dan
girmamawa ga Al -ƙur'ani dangane da airin
abubuwan da ake aiwatarwa a wajan wannan biki na sauka. Daga ƙarshe ana hasashen a kallo irin rawar da uwayen
yara da malaman su suke takawa a wajan saukar ɗaliban
dangane da karrama su
1.3 FARFAJIYAR
BINCIKE
Kafin Shiga cikin
aikin ya kamata mu leka taskar malamai ko masana domin mu san Ma'anar “Farfajiya/Muhallai".
Sabo (2005) ya ce"Muhalli
shi ne mazaunin da ke kewaye da mutum da dukkan Abubuwan da suke taimaka wa
rayuwarsa ta yau da kullum, Muhalli ya samu ne ta hanyar basira da Allah ya yi
wa ɗan
Adam. Muhalli awannan bincike shi ne
Farfajiya, ko bagiren da aka gabatar da wannan bincike.
Wannan aiki an
gudanar da shi ne a fannin al-adun Hausawa, da suka danganci bukukuwan sha'anin
addini. Sannan an keɓance shi ne a garin Gusau domin samun sauƙin bayyana yadda ake yin bikin saukar Al’kur'ani.
1.4 MATSALOLIN
BINCIKE
A nan matsalolin
bincike sun fara ne tun daga lokacin da aka aminta da wannan batu da za a yi
magana a kai, kafin shiga cikin wannan ya kamata mukalli maa'nar
"matsala"kamar yadda masana sukayi tsokaci akai. Fulani da wasu
(2014) sun ce: " Matsala na nufin duk wani abu da ya zo ya takura wa
rayuwar ɗan Adam
ya hana mutum ya kasa cimma burinsa ɗari bisa ɗari".
Matsala na iya zama tawaya ga duk wani abu da mutum zai yi ko ya yi ko kuma
yake yi. Bisa ga wannan ra'ayi za a'iya cewa "Matsala"na nufin duk
wata ƙuntatawa a rayuwa da akan shiga ta fili ko ta
boye.
Haƙiƙa an
yi karo da matsaloli da dama. Daga cikin su akwai: Rashin kuɗi da
rashin samun haɗin kai awajan mutanen da aka buƙaci a yi fira da su da kuma rashin samun
wadatattun ɗakunan
karatu da rashin samun littatafai masu alaƙa da aikin binciken namu, rashin samun hasken
wutar lantarki da rashin tsaro.
1.5 MUHIMMANCIN
BINCIKE
Muhimmanci ya na
nufin amfani, kamar yadda ƙamusun
Hausa (2006)
ya bayyana ma'anar muhimmanci da cewa "Abu ne mai daraja kwarai ko amfani
kwarai da gaske. Aikin bicike yana da matukar muhimmanci musamman ga dalibai
masu karatu a gaba da sakandare. Domin shi bincike ya na ba da damar a gano
matsala da kuma samun waraka a kan wannan matsala. Daga cikin muhimman cin
wannan bincike zai taimaka wa ɗalibai masu nazarin al'ada musamman
na gaba da makarantun sakandare.
1.6 HANYOYIN
GUDANAR DA BINCIKE
Akan bi hanyoyi da
dama, domin gudanar da bincike, To a wannan binciken an bi hanyoyi da dama
domin samun nasarar wannan bincike. Daga cikin hanyoyin da a ka bi an leƙa ɗakunan karatu domin kalato bayanai
a bugaggun littafai da kundayen bincike
da mujallu da muƙalu da muhimman bayanai da za su taimaka don gudanar
da wannan aiki. An kuma shirya yin fira da masu ruwa da tsaki ga lamarin wato malamai, da Uwayen yara, hatta da su kan su ɗaliban
an yi kokarin jin ta bakin su.
1.7 NAƊEWA
A wannan babi mai
suna gabatarwa, ya na matsayin shimfiɗa ne ga aikin
binciken, kuma yana matsayin tsanin takawa wajen gudanar da wannan aiki. A
cikin wannan babi an kawo shimfiɗa, manufar bincike, hasashen
bincike. Haka kuma an kawo farfajiyar bincike, da kuma matsalolin bincike,
muhimmancin bincike, da hanyyoyin gudanar da bincike, daga ƙarshe
naɗewa.
BABI NA
BIYU
BITAR
AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 SHIMFIƊA
A wannan babi mai
taken bitar ayyukan da suka gabata za ayi laluben wasu daga cikin ayyukan
magabata, kama daga bugaggun littafai da kundayen bincike mujallu da muƙalu,waɗanda su ke suna da alaƙa da wannan bincike namu, alaƙar ta kai tsaye ko kuma ta wani ɓangare
ce, to anan za muyi ƙoƙarin fito da wannan alaƙa. Sannan za a yi tsokaci a kan hujjar
cigaba da bincike daga ƙarshe
a zo da naɗewa.
2.1 BITAR AYYUKAN
DA SUKA GABATA
Magabata sun yi
rubuce-rubuce da wallafe-wallafe dangane da abubuwan da suka shafi biki da ma
bukukuwan al-adun Hausawa amma masu alaƙa da wannan aikin bincike waɗanda
hannun mu ya iya kaiwa gare su akwai irin Ƙofar Nasarawa,
(2006)".Tsarin Tsangayun Al-kur'ni a Arewacin Najeriya". In da
mawallafin a sashe na ɗaya babi na ɗaya ya ɗakko
abun tun asali in da ya yi maganar asalin zuwan Musulunci a Arewacin Najeriya. Ya
kuma yi bayani game da bikin sauka da sadaka a matakai daban-daban. Haka ya taɓo
bayanin malaman Al'kur'ani na jihar Zamfara.
Muhammad, A. (1998)
A littafinsa mai take: "Aure da Biki A ƙasar Hausa. Ya yi maganganun da suka shafi
bukukuwan Hausawa na Al-adun su a farkon
littafin ya yi magana a kan ma'anar biki da kuma ire-iren biki. In
da mu kuma aiki na yana nazari ne a kan
wani nau'i na biki.
Ɗangambo,
(1984) A littafisa mai take: Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancin sa ga
rayuwar Hausawa. Wannan littafi shi ma yana da Alaƙa da wani ɓangare
na aiki na, dan aikin nawa ya shafi wani ɓangare
ne na adabi.
Gusau, (2012)
Bukukuwan Hausa, wanna littafi ya tattauna sosai musamman a kan al'adun
bukukuwan da Hausawa su ke yi da kuma Muhimmancin su ga rayur Hausawa. A nan nima
zan kalli irin muhimmancin Bikin Saukar Karatun Alƙur'ani.
Kundayen Bincike,
A nan a na buƙatar aduba kundaye daban-daban domin gano irin
gudummuwar da suka bayar game da bikin saukar karatun Al'ƙur'ani ko kuma abun da ya yi kama da haka .da
farko za mu kalli
Alhasan, M. (1994).
Bambance-Bambancen Al-adun Bikin Aure tsakanin Al-ummar Hausawa da yarabawa. Kundin
Digiri nafarko wanda aka gabatar a sashen harsunan Najeriya, Jami'ar Bayero, Kano.
Wannan kundi ya yi tsokaci a kan irin bambance-bambancen da ake samu cikin
bikin Aure.
Tahaka ne, nima
zan kalli irin ‘yan bambance-bambance
da ake samu a tsakanin makarantun Allo da na Islamiyyoyi dangane da al’adun bikin
saukar karatun Alƙur'ani mai girma.
Muhammad, (1992)
Kundin Digirin farko, wanda aka gabatar a Jami'ar Maiduguri. A sashen nazarin
Harshen Larabci. Wannan kundi kai tsaye ya yi bayani sosai dangane da abinda ya
shafi bikin saukar karatun Al’ƙu'ani Maigirma,
a garin Maiduguri dan haka ya na da alaƙa ta kai tsaye da wannan aikin nazari nawa. Duba
da irin wannan ne ake ganin tahaka ne za a iya gano irin nasara ko
gudummuwar da sukabayar a cikin binciken su,sannan kuma shi wannan aiki nawa ya
san in da zai dora domin bunƙasar
irin wannan nazari.-
Kundin
Tsare-Tsaren Inganta makarantun Allo da na Isalamiyyoyi wanda Gwamnan Kano
Malam Ibarahim shekarau ya kaddamar a ranar 23/10/2003 P.TT. Wannan kundi ya yi
magana a kan yadda ake gudanar da wasu abubuwa dangane da karatun Al-kur'ani Maigirma.
Mujallu da Muƙalu Kuwa
Malamai masana da kuma
Ɗalibai yan uwana sun gabatar da muƙalu da dama
da kuma rubuce-rubuce a kan irin wannan aiki sai dai hannuna
baikai ga takardar da a ka yi kai tsaye a kan wannan aiki da ke nazari akai ba,
na bikin saukar Alƙur'ani a garin Gusau
ba amma dai an samu masu kama da su
,kamar irin su:
Hassan, (2013)
Nason baƙin Al-adu a kan Al’adun Aure da haihuwa
da mutuwa na Hausawa. Muƙalar
da aka gabatar a taron ƙarawa
juna sani na ƙasa, a sashen harsunan Najeriya. Jami'ar Ummaru
musa ‘yar Aduwa.
Tabbas ta fannin
nazarin mu wato bikin saukar karatun Al-ƙur'ani ana samun baƙin al’adu a cikin su, dan haka ne wannan
Takardar muƙala ta na da alaƙa da wannan aiki nawa.
Bunza, (2004),
Takarda a kan Ilimin Tsubbu a ƙasar Hausa, jiya da yau. Angabatar da ita ne a
Jamiar' Bayero Ranar 7, ga watan yuli 2004.
Bunza, (2013).Zama
da Maɗaukin
Kanwa ke sa farin kai; Nason Baƙin
Al-adun Auren Hausawa. Mukalar da aka gabatar a Taron ƙarawa juna sani na ƙasa a sashen Harsunan Najeriya,Jami'ar Ummaru
Musa Ƴaa'duwa.
2.2 HUJJAR CIGABA
DA BINCIKE.
Kasancewar masana
da manazarta sun yi aikace-aikace a kan abinda ya shafi biki ko bukukuwan al’adun
Hausawa a nan garin Gusau amma ba a samu
wani da ya yi aiki a kan bikin sauka ba, musamman a nan Jami'ar Tarayya Gusau.
Masu nazari waɗanda su
ka gabace mu ba su karaɗe ko ina ba dan haka sun bar giɓi wanda
ya zamar mana hujja ta mu cigaba da yin bincike akai. Ina kira ga ɗalibbai
‘yan'uwana da su cigaba da bincike don su ma su
cika sauran gurbin da hannun mu bai kaiba.
2.3 NAƊEWA
A wannan babi na
biyu an yi ƙokarin zaƙulo bitar ayyukan da suka gabata wanda suka ƙunshi bugaggun littafai da kundayen bincke da
mujallu da muƙalu.Bugu-da-ƙari anyi tsokaci kan hujjar cigaba da bincike
daga ƙarshe an rufe babin naɗewa.
BABI NA
UKU
FASHIN
BAƘI AKAN MA’ANONIN DA SUKA SHAFI
TAKEN BINCIKE
3.0 SHIMFIƊA.
A wannan babi an
kallo ma’anonin da suka shafi taken bincike a inda aka mai da ƙarfi
wajen fayyace ma’anonin kalmomi, da su ne
aka haɗa a ka
samar da sunnan wannan bincike. Saboda haka ne suka zama tubalan ginin wannan
bincike.
3.1 MA’ANAR KALMAR
BIKI
Masana da dama sun
tofa albarkacin bakin su dangane da maa'nar "biki" kamar yanda za a
gani ɗaya
bayan ɗaya:
Gusau, (2012) ya ce
"Biki wani taro ne na mutane da suke shiryawa, su gudanar don nuna
farincikinsu a kan wata bai wa da Allah (s.w.t.) ya yi mawa wani daga cikinsu
ko ya yi wa wasu " ya ƙara da
cewa biki ana yin sa don a nuna irin farin cikin da ake da shi ga wani abu ko
don nuna farin ciki ga wani abu da ya faru ko don tunawa da wani abu muhimmi,
ko don zagayowar wata rana.
Bayero, (2006)
biki (sn,nj,jam'i bukuwa) An bayyana
1- Biki: shagalin
farin ciki ko murna 2-kyauta ko gudummuwa wacce yawanci mata kan yi wa ‘ya’yansu
yayin wata hidima da ta same su.
B.U.K.(2006:46)
(Biki,sn,nmj,jam'i bukukuwa/bukunkuna) shagali na nuna farin ciki,Aure,ko
suna,ko naɗin
sarauta,ko salla, ko al’adun gargajiya. Garba (1990) (sn)"Annushuwar da
ake yi don murnar wani abu". A tawa
fahimta, biki shi ne duk wani taro da ake yi domin taya murnar a kan wani abin
farin ciki da ya samu.
3.1.1 Bikin Aure
Bikin Aure biki ne
mai faɗin
gaske, kuma biki ne wanda duk wasu ƙananun
al’adu ba akan bar su ba sai an yi, saboda haka zamu dubi yadda tsarin Aure
yake a Al-adar Bahaushe.
Aure Muhimmin abu
ne a tsarin rayuwa, saboda haka, akwai hanyoyi ayyanannu da ake bi
wajen atabbatar
da shi, waɗannan
hanyoyi sun haɗa da:
·
Zance
·
Baiko
·
Sarana
·
Kamu
·
Kunshi /wankan Amarya
·
Ajo
·
Ɗaukar
Amarya
·
Sayen baki
·
Buɗar kai.
Kowanne daga cikin
waɗannan al’adun
na aure, na da bayanin yadda ake yin su da irin waƙokin da ake yi lokacin wasu daga cikin su, musamman
ma lokacin kamu da ƙunshi da wankan Amarya.
3.1.2 Bikin Suna
Zanen suna al’ada
ce da Bahaushe ke bi yana raɗa wa abin haihuwa wanda ka iya zama
yaro ko yarinya suna.
Bunza, (2002), ya
ruwaito cewa wannan al’ada daɗaɗɗiyar
al’ada ce da ta wanzu a Ƙasar
Hausa tun kafin kowane sauƙaƙƙen addini. Ana yin wannan al’ada ne ta hanyar
samun wasu dattawa/dattaɓai su yi zane-zane a jikin kararen
rama ɓararru
guda bakwai, sannan sai a ɗauka a kaiwa mai jego, wanda duk ta
zaɓa sai a
yi amfani da zanen da ke jikinsa a raɗa wa jaririn ko jaririyar suna.
Wannan al’ada ta
zanen-suna ta samu sauye-sauye da dama. Daga ciki akwai sauyin farko da ta samu
yadda ya koma kawai jama’a na taruwa a ƙofar gidan da aka yi haihuwa, sai a rarraba musu
goro da sauraran abubuwan da suka samu, sannan liman ya ce an sawa yaro ko
yarinya suna wane ko wance. Sai kuma maroƙi ya faɗa da ƙarfi kowa ya ji. Sannan a yi addu’a, sai kuma
kowa ya watse. Su kuma yara a lokacin da ake yin wannan addu’a, sai
su ruga da gudu su shiga cikin gida wajen mata su gaya musu cewa an saka wa
jariri ko jaririya suna wane ko wance. A lokacin da suke gudun suna ambatar
Allah ya raya wane ko wance. Duk yaron da ya yi sauri ya fara isa ya je ya
sanar cewa wane ko wance aka saka, akan bashi tukuici wanda kuɗaɗe ne da
alewa da goro amma ba masu yawa ba. (Malam
Isah, 2021).
Sai kuma a halin
yanzu da Musulunci ya yi ƙarfi,
a mafiya yawan gurare musamman birane, ba a ma taruwar sai dai a raɗa sunan
a masallaci.
Ta fuskacin biki
kuwa, akan yi shi hawa-hawa. Akwai wanda ake yi nan-take da zarar an raɗa
sunan. Akan fito da abinci jama’ar da suka taru su ci, su kuma maroƙa da makaɗa suna
kaɗe-kaɗensu.
Bayan kuma an gama
wannan, sai su ma mata su haɗu yawanci har zuwa maraice, suna
‘yan kaɗe-kaɗe, da
waƙe-waƙensu
na mata, suna guɗa da sauransu. Sannan kuma sukan zo da kyaututtuka a
matsayin gudunmawa ga ita mai haihuwar. Wannan taro na mata bai cika kaiwa faɗuwar
rana ba.
Idan kuma haihuwar
fari ce, to, akan samu mata su taru a gidan iyayen mai jego; wato gidan mata
kenan, su haɗo nasu
abubuwan. Bayan sun tattara abubuwan da suka tara, sai kuma su ɗauko
shi da maraice zuwa gidan da aka yi haihuwa, gidan maza kenan, su zo su rarraba
ga iyaye, da sauran dangin miji. Wannan rabo shi ake kira tsaraba.
Abun Lura: Akan
samu saɓawar
wasu abubuwa daga wani gidan zuwa wani ko kuma daga wani yankin zuwa wani
yankin wanda ka iya zama ƙari ko
ragi a kan abubuwan da aka zayyana a cikin wannan rubutun.
3.1.3 Bikin Salla Ƙarama
Bikin salla ya
shigo ƙasar Hausa ne bayan shigowar addinin Musulunci.
Wannan biki, jerin bukukuwa ne da ake gudanarwa a lokutan Idin Ƙaramar Salla. Waɗannan
bukukuwa da ake yi suna da yawa; akwai hawan salla da sarakuna ke yi da
dawakai, akwai kuma bukukuwan da sauran jama’a ke yi waɗanda
suka shafi kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, da
gaishe-gaishe da kuma kyaututtuka da ziyarce-ziyarce.
Shi hawan salla
biki ne da Sarakuna ke gabatarwa, a ƙasar
Hausa, akan fara bikin hawan salla ne daga filin idi. Sarkin
yanka yakan yi hawa da hakimansa da dagantansa da sauran masu riƙe da muƙaman
sarautar gargajiya.
Kowane ɗaya
daga cikinsu zai hau dawakai da tawagarsa cikin kwalliya daga su har dawakan
nasu, suna tafiya jama’a kuma na kewaye da su suna kallo suna miƙa gaisuwa. A ranar farko akan tashi daga filin
idi zuwa gidan sarki. Idan aka je gidan sarki, sai a jira sarki ya zo ya sauka,
sannan duk sauran hakimansa ɗaya-bayan-ɗaya su
je su yi gaisuwa. Bayan an kammala kuma sai sarki ya yi jawabi ga jama’ar ƙasarsa baki ɗaya
sannan a sallami kowa ya watse.
Idan aka gama
wannan a ranar farko, to washegari kuma sai a ci gaba, wanda wannan yakan
bambanta daga masarauta zuwa wata masarautar. Kowace masarauta akwai takamaiman
wani guri da sarki ke zuwa a wannan rana, su kuma jama’a su fito gefen hanya
suna miƙa gaisuwa ga sarki, fadawa kuma suna karɓa.
Daga cikin sauran
bukukuwa da mutane kan yi a lokutan salla akwai kiɗan
kalangu da ake yiwa ‘yan’mata suna rawa, akwai makaɗa da
mawaƙa da suke gudanar da wasanni ciki har da makaɗan
ban-dariya, da makaɗan jama’a.
3.1.4 Bikin Salla
Babba
Bikin salla babba
anayin wannan biki ne a watan shabiyu na kalandar musuluncin ko wacce shekara
wato "Zulhajji "ya yin da watan ya yi kwana goma. Shi ma yana ɗaya
daga cikin bukukuwan da addinin Musulunci ya zo da shi. Kamar dai sauran
bukukwa shi ma ya na tattare da irin nashi al’adu kama daga yin sabbin ɗunkuna
yanke-yanke (layya) ziyartar yan uwa
da abokan arziki. Sannan a cikin wannan watan ne ake aiwatar da ɗaya
daga cikin shika shikan musulunci guda bayar da ake da su, wato aikin hajji
wanda yake wajibi ne ga dukkan mutum, musulmi, baligi maihankali, kuma wanda
Allah ya horewa kuɗin zuwa.
3.1.5 Bikin
Mauludi
Bikin Maulidi biki
ne wanda shi ma ya na ɗaya daga cikin bukukuwan da suka
samu sakamakon zuwan addinin Musulunci a ƙasar Hausa. A na yin bikin mauludi ne a cikin
watan Rabi'u Auwal wato watan uku na kowa ce shekarar Musulunci. Anayin wannan
biki ne a sha biyu ga watan rabu'u Auwal ana yin bikin ne sabo da tunawa da
zagayowar ranar da aka haifi fiyayyen hallita Annabi Muhammadu (S.A.W) wasu
suna yin bikin sau biyu bayan na ranar haihuwa har da na ranar suna suke yi. Bikin
Mauludi yana tattare da al’adu a cikinsa kamar: Yanke-yanke kaji da raguna da shanu
Akan shirya abinci iri-iri ana yin sababbin ɗukina.
Ana raya dare da karance karancen yabon Annabi.
Ana karatun
tarihin Annabi Muhammad (S.A.W.) ‘yan mata
sukan shirya abinci ga samarin su masu neman auren su.
3.2 MA’ANAR KALMAR
SAUKA
Masana sun bayyana tasu ma’ana dangane da kalmar
"sauka". Kamar yanda za a gani kamar haka:
Bayero (2006:394)
ya nuna cewa kalmar Sauka (Sn, Mc) 1-Jiɗa 2-Baƙuntar wani gida 3-kammala kartun Al-ƙur'ani maigirma gabaki ɗayan
sa.4-Bai wa baƙo abinci saboda zuwan sa.
A tawa fahimta, kalmar
sauka na nufin kammala wani abu da ya zama dole musamman idan muka kale ta a matsayin
"sauke "misali sauke farali (zuwa aikin haji ga wanda Allah ya ba
ikon zowa).
Kalmar sauka ana
amfani da ita wajan tashi, ko hauhawar fara shin kayan masarufi. Wanda ida sun
yi sau ƙi akan ce ai kaya sun "sauka ".
3.2.1 Ma’anar
Kalmar Al-Ƙur'ani
Al-ƙur'ani zancen Allah ne, wanda aka saukar da shi
ga Annabi Muhammadu (S.A.W.) ta hanyar malaika Jibrilu, cikin harshen Larabci, abin
karantawa daki-daki, wanda karanta shi ibada ce.
Alƙur'ani yana da sunaye daban da ban kamar yadda ya
zo a cikin alƙur'ani
1.Al-ƙur'ani (القرآن ).
kamar yadda Allah
ya ambace shi a cikin Suratul-Baƙara aya ta 185
ãöky
tb$ÒtBu
üÏ%©!$#
tAÌRé&
ÏmÏù
ãb#uäöà)ø9$#
Wèd
Ĩ$¨Y=Ïj9
;M»oYÉit/ur
z`ÏiB
3yßgø9$#
Èb$s%öàÿø9$#ur
4
Fassara:
Watan Ramadana ne
wanda aka saukar da Alƙur’ani
a cikin sa, yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da
rarrabewa. (2:185)
2.Alfurƙan ( الفرقان)
Kamar yadda ya zo
acikin suratul furƙan aya ta 1,
Fasssara; Albarka ta tabbata
ga wanda ya saukar da( littafi)mai rarrabewa
akan bawan sa, domin ya kasance mai gargaɗi ga
halittu.
3.ZIKR(ذكر) kamaryadda yazo a suratul
Hijiri ayata 9
Fasssara: Lalle
mu ne muka saukar da Ambto (Al-kur'ni)kuma lalle haƙiƙa mu masu kiyayewa ne gare shi”.
4.KITAB (الكتاب)
Kamar yadda ya zo a cikin suratul khahfi Aaya ta 1
Fassara:
“Godiya ta tabbata
ga Allah, wanda ya saukar da littafi akan bawansa, kuma bai sanya karkata ba
agareshi”
3.3 MA’ANAR KALMAR
GARI
Bayero (2006:
159), ya nuna cewa kalmar “Gari” na cikin jerin sunaye na maza, jam’i kuma
garrumma, a wani Karin halshe akan ce garurruka, ko garurra. Kalmar na nufin
wurin da mutane suka zauna suka yi gidaje.
3.3.1 Kalmar Gusau
Dangane da ma’anar
kalmar Gusau kuwa, har ila yau bayero (2006: 177), ya bayyana cewa kalmar na
cikin jerin kalmomin suna jinsin mace, ya kuma nuna kalmar na ɗauke da
ma’anar: “Sunan babban Birnin Jahar Zamfara.
3.3.2 Kafuwar Garin
Gusau
An kafa Garin
Gusau a shekarar (1811) bayan tasowa daga “Yandoto
a shekarar (1806) garin Gusau na ɗaya daga cikin manyan garuruwan
tsohuwar jihar sakkwato, kafin daga bisani yazama babban birnin jihar Zamfara a
she karar (1996) kamar yadda kudin tarihun ƙasa na (1920) yanuna, garin yana bisa kan hanyar
sakkwato bisa
titin Zariya, kilomi kilo mita 179 tsakanin shi da Zariya, kilomita 210 tsakanin
shi da sakkwato. Daga gabas ya yi iyaka da ƙasar Katsina da Ƙwatarkwashi daga Arewa ya yi ika da ƙasar Ƙaura, daga
yamma yayi iyaka da Bunguɗu ta ɓangaren
kudu kuma yayi iyaka da ƙasar Ɗansadau da Tsafe. Gusau , (1912:7).
Kasancewar
Almajiran shehu Usaman Ɗanfodiyo
ne wato Malam Sambo ƊanAshafa, shi da
jamaar'sa suka kafa Gusau ya sa ba a samu baragurbi ba a ƙasar dangane da bautar gumaka ko bautar tsafi da
iskoki irin na jahiliyya ba .Hakan ya sa duk Al-adun Gusau al’adu ne irin
na Addinin Musulunci, kuma shi duk da shigowar baki a cikin garin na Gusau ba ta
sa al’adun nasu sun gurɓata ba, mafi yawan bakin da suke
shigowama malamai ne na Addinin musulunci. Ta ɓangaren
yaƙi kuma duk abin da zai taso to zayi
maganin shi ne cikin dabara da abin da Musulunci ya yadda da shi wato
"sulhu "don kyakkyawon ɗabi'u irin nasu.
Gudummuwar da
sarkin katsinan Gusau ya ba yar a (1867m/1282h-1877m/129h) Malam muhammadu
modibbo an samu kwararar baƙi Da ƙungiyoyi daban daban wanda hakan ya sa haɓakar
garin Gusau a cikin ƙanƙanin lokaci. Zuwan Bature da Turawa a ƙasar Hausa ya sa an shimfiɗa
tsarin makarantun boko wanda ya haifar da samuwar wasu al’adu. Kwatsam! anan
sai ga shariar musulun ci ta sake kunnu kai ta gwadaɓe
tajdidin wannan lamari, shi ma ya ƙara
kawo canje-nacanje na Alheri a Ahlin mutanen garin Gusau amatsayin su na babban
birnin jiha.
Garin Gusau tana
da babbar masarauta guda ɗaya(1) tana da wakilan uwayen ƙasa guda goma sha uku (13) ƴan majalissa sha takwas (18) sarautun
fada kuma akwai kimanin ɗari ɗaya da
huɗu (104)
Masallatan juma’a ashirin da (23)kananan makarantun boko sittin da huɗu (65) mutsakaita
kuma arba'in da uku (43). Haka kuma akwai kasuwanni guda uku (3). Daga lokacin
da aka kafa garin Gusau an yi sarakuna da dama kamar haka:1-Malam Muhammadu
Sambo (1806-1827) 2-Malam Abdulƙadir
(1827-1867) 3-Malam Muhammadu Modibbo (1867-1976) 4-Malam Muhammadu Tubari
(1876-1887) 5-Malam Muammadu Giɗe (1887-1900) 6-Malan Muhammadu
Murtala (1900-1916) 7- Malam Muhammadu (1916-1917).
Sai waɗanda
suka yi sarautar Gusau ba daga gidan
Malam Sambo ba, sunhaɗa da; 1-Malam Umaru malam
(1916-1929) 2-Malam Muhammadu Mai Akwai
(1929-1943).3-Usman Ɗan samaila(1943-1945)
4-Ibrahim Marafa (1945-1948) 5-Muhammadu sarkin kudu (1948-1951)
6-Alhaji Sulaiman isa (1951-1984). Daga nan
kuma sai sarautar ta sake dawowa gidan bayan wannan tsawon lokacin, inda ta faɗa a kan
1- Alhaji Muhammadu Kabiru Ɗanbaba
(1984-2015) 2- Alhaji Ibrahim Bello (2015-to date) Ataƙaice dai wannan shi ne tarihin garin Gusau tun
bayan ta sowa daga ƴandoto.
3.4 NAU'O'IN'
MAKARANTUN MUHAMMADIYYA.
A nan ana maganar
hanyayoyi ne kamar yadda aka ambaci sunan da "Muhammadiyya "wato
hanyar da ake bi wajen aiwatar da karatun Musulunci ko muce na Addinin Musulunci,
wanda Annabi Muhammadu, shi ne ya zo da wannan Addini, Dan haka ne ake kiran
karatu da "karatun muhammadiyya.
Haƙiƙanin gaskiya akwai hanyoyi da
nau'o'i da dama da ake bi wajan karatun Addinin Musulunci a ƙasar Hausa, kuma cikin su duk hanyar da mutum ya bi
ko ya tashi ya samu kansa a ciki to zai iya cimma duk wani matsayi dangane da
karatun ko ilimin Addinin Musulunci. Akwai Nau'i daban daban na
makarantun Addinin Musulunci kamar haka:
1-Makarantun zaure
2-Akarantun Allo /Tsagaya
3-Makarantun isalamiyya.
3.4.1 Makarantun
Allo /Tsangaya
Makarantar Allo
ita ce tsohuwar hanyar koyo da koyerwa a ƙasa Hausa a manyan garuruwa kamar
Kano da Katsina da Zariya, a Kano ana kyautata zaton an kafa makarantu kusan
shekaru ɗari
shida da sittin da suka shuɗe abaya, zamanin Sarki Yaji da
Tsamiya (1349-1385) wato a daidai lokacin da Fulanin Wangarawa suka zo garin
Kano .
Katsina kuwa Ana
ganin tun shekaru ɗari shida da sittin da uku a baya da suka wuce wato a
zamanin Sarki Muhammadu Korau (1384-1398) lokacin Sheikh Abdurrahaman Zaite da
jama’arsa suka je Katsina. Wannan makaranta a cikinta ake koyon karatu da rubutu,
da kuma Haddace Al-Ƙur’ani baki ɗayan sa,
Malaman Makarantar allo su suke rubuta Ƙur'ani ko dai da ka, ko kuma ta hanyar
mai-da-kama. Makarantun allo makarantu ne masu tsari irin nasu, a kan kai yaro
makarantar allo idan yaro ya kai shekaru shida (6) ko bakwa (7) da haihuwa
wanda idan namiji ne an yi masa kaciya (bante) idan a ka kai yaro to
shi ke nan yaro ya zama ɗan makaranta wanda ake kira
Almajiri.
A makarantar allo ɗalibai
kala biyu ne a kwai waɗanda ke kwana a makaranta akwai
kuma waɗanda su
ke komawa gidajen iyayensu su kwana, kamar dai yanzu yadda aka da tsarin makarantun
kwana da kuma jeka-ka-dawo a makarantun boko.
Lokutan karatu:
Akwai lokutan
da ake gudanar da karatu amakarantun tsangayu da
na Allo kamar haka;
1. Ana karatu tsakiyar dare wato (tayi)
kawai za a tayar da Almajirai suna tsakiyar bacci cikin dare ko gab da
Asuba wanda zai kai har bayan Asuba ko
har gari ya waye, amma yanzu ba kasafai ake samun wannan ba.
2. Lokacin
karatu na biyu shi ne idan hantsi ya yi sai a zauna wasu kuma awannan lokacin
ne suke tafiya bayan gari wato ƙiskali
ɗaki ne
da ake yin shi da kara da yayi a bayan gari ko cukin gonaki.
3- Zama na bayan Laa'sar
4- Sai zama na ɗare.
Tsarin Koyon Karatu
1-
GWAJI: Shi ne mataki na farko da ake ɗora
sabon Almajiri akai ana koya masa Fatiha zuwa Alamtarakaifa. Galibi yara sukan
iya wannan surori da ka wasu ma sama da waɗannan,
alhali kuwa ba su ma fara riƙe allo
ba.
2-
BABBAƘU: A wannan mataki ne yaro ko yarinya ke fara
amfani da allo, matakin babbaƙu kamar yanda sunan ya nuna mataki ne na sanin baƙaƙen Alƙur’ani.
3-
FARFARU: Shi ne mataki na uku wanda ake
koyawa almajiri laƙantar wassulla, a
nan akan mai da yaron da ya kammala sanin ɗaiɗaikun
haruffa a matakin babbaƙu baya,
ma’ana sai a sake rubuta masa Ta’awizi da Basmalah zuwa Suratul
Fili tare da wasullah. Matakin farfaru yana da wahala domin kuwa a nan ne
yara da yawa kan jima basu ficeshi ba.
4-
Hajjatu: Bayan yaro ya laƙanci
sanin baƙaƙe da
kuma iya karantasu da wasullah, Sai matakin Hajjatu Malami kan yi la’akari da
cewa a yanzu idon yaro ya buɗe, don haka sai ya biya masa kamar
layi ɗaya ko
biyu na allonsa tare da ɗora yatsan yaron akan kalmomin da
ake biya masa.
5-
Darasu: Almajiri kan je wannan mataki ne,
ya yin da idan ya yi ƙwari
wajen haɗa baƙaƙe
da ta dasu, yara masu hazaƙa kan
yi ƙoƙarin
karanta guraren da ma basu kai ba a cikin Alƙur’ani.
6-
Gardi: Shi ne makarancin da ya wuce
shekara 25, kuma karatunsa ya yi nisa, kuma a wannan mataki ne ake haɗa harda
ta zauna daram.
7-
Satu: Kalmar barebari ce da ke nufi iya
rubuta baƙaƙen Alƙur’ani
bayan an hardace, makaranta a tsarin tsangayu ba sa fara rubuta Alƙur’ani
har sai sun kai matakin yin satu.
8-
Alaramma: Matsayi ne na wanda ya hardace
Alƙur’ani har ma ya rubuta shi, ma’ana dai ya
laƙanci duk wasu ilimai da luggogi na Alƙur’ani,
kuma har yana da wasu dunƙulallun
kalmomi da makaranta ke amfani da su, na hisabi da makaranta Alƙur’ani
ke amfani da su, dan tantance adadin kalmomi ko baƙaƙen
Alƙur’ani.
9-
Gwani: Shi ne matakin ƙoli
cikin azuzuwan makaranta a tsarin tsangayu, makaranci kan zama gwani bayan ya
kai matakin gardi har zuwa matakin alaramma, bayan alaramma ya yi shekaru da
yin fice a fagen Alƙur’ani, makaranta
kan ayyana shi a matakin gwani a cikinsu.
10-
Gangaran: Akwai saɓani a
wasu lokutta wurin wasu malamai a tsakanin gwani da gangaran wanne ne a gaba?
Wannan ya biyo bayan wani shahararren makarin zance “Gangaran kafi Gwani” ala
ayyi halin gwani shi ne mafi karɓuwa a azuzuwan makaranta, amma fa
wanda makaranta ke kira da gangaran to ya fi gwani.
3.4.2 Makarantun Zaure
A nan ya zama
wajibi mu kalli maa'nar zaure shin mene ne "Zaure"? Zaure wani ɗaki ne
wanda ake yin shi a farko shigowa gida kuma dole sai an bi ta zauren nan ida za
a shiga cikin gida. Ga al’adar Hausawa zaure ɗaki ne
mai matuƙar muhimmanci mafiyawan malaman zaure suna
karantar wa ne a zaure kuma mafi yawansu dattijai ne haka nan kuma
mafi yawan masu ɗaukar karatun a zaure za a cimma
magidanta ne ba kamar makaran tun allo ba.
3.4.3 Makarantun Islamiyyah
Tarihi ya nuna
cewa, karatun Islamiyya ya shigo ƙasar
Hausa a cikin ƙarni na 20, wajen shekara ta 1930. Wannan
ya nuna cewa karatun Islamiyyah bai daɗe da shigowa ba a ƙasar
Hausa ba ganin waɗannan shekaru ba su da yawa idan an
kwatanta da hasashen shigowar addinin Musulunci a ƙasar
Hausa. Ba ko shakka, a makarantun Islamiyya ne aka fara koyar da yara da matasa
‘yan makaranta karatun Alƙur’ani
ta hanyar karatun tajwidi. Abin da ya bambanta karatu a makarantun allo da
karatu a makarantu Islamiyya shi ne, a makarantun allo yara na karatunsu da
allo ne (wanda massaƙa suke sassaƙawa
da icce) har sai sun kai Suratul Amma ko Tabara, suna ɗaukar
karatu da bita sannan Malamansu su riƙa
barinsu suna zuwa makaranta da Alƙur’aninsu,
don karantawa. Amma makarantun Islamiyyah kuwa, ana faraway yara karatunsu a
kan allon bango irin na makarantun boko, su kuwa ɗalibai
suna rubutawa a cikin littafinsu kamar yadda ake yi a makarantun boko. Don haka
bikin yaye ɗaliban
makarantun Islamiyya ba ya da wasu al’adun Bahaushe masu yawa a ciki. Don haka,
za mu danganta tarihin samuwar makarantun Islamiyyah da zuwan Sarkin Kano, Alhaji
Abdullahi Bayero ƙasar Masar.
Sun ziyarci ƙasar
Masar, inda aka shirya da wani Balarabe mai suna Abu Sa’ud cewa zai zo Kano ya
tsara yadda za a gudanar da irin wannan makaranta da ma’aji Suleimanu ya
shawarci Sarki a kan a kafa ta. To da Abu Sa’ud ya iso Kano sai aka yi amfani
da waccan Makaranta ta Elementary ta ƙofar
kudu, aka buɗe ajin
manya don a tafiyar da irin wannan tsari na Misirawa, sai ya zamana an ɗauki ɗalibban
wannan makaranta ta safe su ne suke komawa da yamma, ana karantar da su
Arabiyyah da koyar da addinin musulunci. (Sufi: 1993:217).
Shi Malam Wada
wanda yake yin Headmaster sai ya dawo ya ci gaba da tafiyar da wannan makaranta
ta boko ta safe tare da waɗancan Malamai nasa, su Malam Baƙo
Bauchi, da Malam Abba (Ka), akwai kuma Malam Umaru Ɗan
Madaki, sai Malaman Arabiyyah, Malam Ɗan Amu
da Malam Nasiru Kabara, a lokacin ana kiransa Malam Nasiru Namagangara, da kuma
Malamin sa’ana Malam Alhaji na Soron ɗinki.
Ita kuwa wannan
makaranta ta yamma ta Arabiyyah (Islamiyyah), wani Bazazzagi Almajirin Ma’aji
Suleiman wanda aka fi sani da M. Abubakar Na-Wali ko M. Abubakar Maisaje, shi
ne yake shugabancinta. Ana karantar litattafan fiƙihu kamar
As’halul Masaliki da Durusun Nahawiyya, da wani littafin koyan Larabci da ake kira:
“Ƙira’atul Asarariyyah”. Ya yin da Bamisire,
yana koya wa waɗannan yan makaranta wasannin motsa jiki,
amma da harshen Larabci, ana yin guje-guje da tsalle-tsalle a kowace ranar
Alhamis da yamma, duk kuwa kowane yaro yana sanye da farar yar taguwa mai
gajeran hannu mai wuyan kwala, da wani ɗan
gajeran wando fari, kamar yadda Sufi (1993:218) ya nuna.
Ana yin wannan
guje-guje ne da tsalle-tsalle a wannan ƙaton
sararin da ake cewawa da shi filin gawo, wani lokaci ma sai ɗalibai
su dinga zagaye wannan ɗaurin guga na Filin Gawo da ake
cewa da shi “Soron Zauna Lafiya” wanda aka faɗe shi a
baya, sai su riƙa zagayashi a
guje. A cikin waɗannan daliban makarantar akwai wani ƙaton
yaro ɗan
sarkin Muri ana ce da shi Misa. A wani lokaci kuma sai wannan Balarabe ya dinga
koyawa waɗannan
yara rawa irin ta ‘yan sanda ko soja, sai yaran su dinga tafiya suna ɗaga ƙafar
hagu da ta dama, shi kuma yana cewa SHIMAR YAMI, wai hagu da dama, kenan idan
sun yi yar tafiya sai yace ILAL HALAF ILTAFIT sai yaran su juya baya suna cewa
WAHIT NIN sai kuma ya ce ‘ILAL AMAM SIR” sai yaran su miƙe
da tafiya darkwai sai ya ci gaba da faɗin SHIMAL YAMIN.
Haka za a ta yi sai lokacin da yace a tashi daga wannan rawa.
3.5 NAƊEWA
Wannan babi ya
kunshi muhimman Abubuwa kamar samuwar ko kafuwar makarantun allo a garin Gusau
da kuma nau'o'in makarantu Muhammadiyya da muke da su da kuma irin tsarin
karantarwarsu da matakin da yaro ya ke kaiwa kafin a sashi a makarantar allo ko
islamiyya.
BABI NA
HUƊU
BIKIN
SAUKAR ALƘUR’ANI A GARIN
GUSAU
4.0 SHIMFIƊA
Kamar yadda babin
da ya gabata aka yi bayanin ma’anar kalmar biki tare da kawo wasu ire-iren
bukukuwan Hausawa tare da yin tsokaci game da kalmar gari da taƙaitaccen
tarihin garin Gusau. A wannan babi na huɗu za a
kawo shimfiɗa da
asalin bikin saukar Alƙur’ani
tare da bayanin waɗanda suka fara aiwatar da bikin. Haka kuma
za a yi bayanin yadda bikin saukar Alƙur’ani
yake a da, sannan yaɗuwarsa da bunƙasarsa,
sannan kuma an kalli irin tasirin da zamani ya yi game da bikin saukar Alƙur’ani.
Bugu da ƙari,
an kawo bayani dangane da irin rawar da uwaye, da Malamai da ɗalibai ke
takawa duk a wajen bikin saukar Alƙur’ani,
daga ƙarshe a zo da naɗewa.
4.1 ASALIN BIKIN
SAUKAR ALƘUR’ANI
In ana magana kan
asalin bikin saukar Alƙur’ani
to abin da ya kamata a sani nan shi ne, a sani shi, Allah ya saukar ma Annabi
Muhammad (SAW) Alƙur’ani mai tsalki ta
hannun Mala’ika Jibril (AS), “Manzon Allah (SAW) ya kasance idan Alƙur’ani
ya sauka gare shi yakan karantar da Sahabbai abin da ya sauka, kuma ya umarce
su da su rubuta shi. Ubangiji maɗaukaki ya yi wa Annabi da Sahabbai umarni
da su karanta Alƙur’ani kuma su yi
aiki da shi. Wannan ya sa sahabbai da yawa sun haddace Alƙur’ani
a ƙirajensu (K/Nasarawa 2006:4). Da wannan ne
mu ke cewa bikin Saukar Alƙur’ani
ya samo asali ne tun zamanin Sahabban Manzon Allah (SAW); saboda “Sayyidina
Umar yardar Allah ta tabbata a gare shi, lokacin da ya haddace Suratul Baƙara
ya yanka raƙumi domin nuna godiyarsa ga Allah da
wannan ni’imar” da ya yi masa” (Tafsirin Imamu Kurɗabi).
Da wannan ne muke
jingina hujjar cewa bikin Saukar Ƙur’ani
ya samo asali ne tun zamanin sahabbai, kuma kasancewar Addinin musulunci ya na
da tsarin da Annabi Muhammad (SAW) ya ɗora shi bisa ga
umarnin da Allah ya yi masa da koyarwarsa da kuma koyarwar Sahabbansa, domin ya
faɗi cewa
a bi Allah da kuma shi (Annabi Muhammad (SAW) da kuma Sahabbai. (Sahihul
Bukhari Ɓol. 4, Hadish No. 645) (Ƙur’an 4
ɓerse 136).
To daga nana abin ya
cigaba har ya kawo ga al’ummar Annabi Muhammad (SAW) kuma har gobe ana gudanar
da bikin saukar Alƙur’ani mai girma a
cikin duniya, sai dai ya danganta da irin yadda ake aiwatar da bikin ta hanyar
al’adar al’ummar kowane wuri da ƙarfin
tattalin arzikinsu da kuma sauyin da zamani ya kawo masu.
4.1.1 Waɗanda
Suka Fara Aiwatar da Bikin Saukar Alƙur’ani
Kasancewar Annabi
Muhammad (SAW) shi Allah ya saukar ma Alƙur’ani
ta hannun mala’ika Jibrilu (AS) kuma Annabi (SAW) yana karantar da sahabbansa
ya kuma umarce su da su rubuta shi, dan haka kafin kowa ya fara sanin ƙur’ani
bayan Manzon Allah, to sahabbansa su suka fara sanin Alƙur’ani
da haddace shi, domin ko akwai wasu daga cikin sahabbai da suka haddace Alƙur’ani
“Mahaddata Alƙur’ani cikin sahabbai Muhajirai sun haɗa da
halifofi huɗu Sayyidina
Abubakar, Sayyidina Umar, Sayidina Usman da Sayyidina Aliyu da “Dalha da Sa’ad
da Ibn Mas’ud da Huzaifa da Salim da Abuhuraira da Abdullahi bn Sa’ad da A’isha
da Hafsa da Ummu Salma (RA). A cikin mutanen Madina wato Ansar an samu Mahaddata
Alƙur’ani cikin Sahabbai waɗanda su
ka haɗa da
Ubaidatu bn Samit da Mu’az (Abu Halima) da Mujammi’i bn Jariya da Fudhala bn Ubaida
da Muslama bn Mukhalad. Kodayake wasunsu sun kammala haddarsu ne bayan wafatin
Annabi (SAW) akwai kuma waɗanda da yawa da suka haddace Alƙur’ani
cikin sahabbai (RA) ko da yake su suka yi fice da shahara domin riwayoyin
kira’o’i goma na Alƙur’ani na komawa
gare su”. (K/Nasarawa 2006:9).
Da wannan ne za a
tabbatar da cewa kafin kowa ya fara bikin Saukar Alƙur’ani
to Sahabban Manzon Allah (SAW) su suka fara aiwatar da bikin saukar Alƙur’ani
har ya kasance ake koyi da su domin duk abin da suka yi sunna ne kuma shari’a
ta yarda da shi tamkar yarda da hadisin Annabi (SAW) ne. Kuma bikin saukar Alƙur’ani
ya cigaba bayan wucewarsu. Kuma wannan ne ma ya sa ake kallon wanda ya sauke ƙur’ani
wani babba a cikin al’umma, baya ga irin hidima da uwaye ke yi na nuna jin daɗin ɗansu ya
sauke Alƙur’ani, ‘yan uwa da abokan arziki na zuwa
wajen taya murna da sauran mutane makusanta.
4.1.2 Samuwar Makarantun
Al-Ƙur'ni A Garin Gusau
Kasancewar
masarautar Sakkwato ta kafu ne daga baya-bayan nan idan andanganta ta da
masarautar gobir da zamfara da kebbi hakan ya sa, tarihin Al-ƙur'ani da ilimi yana koma wa ga malaman ‘Yandoto.
Wani muhimmin abu
da ya ƙara haɓɓaka
sha’anin Malamanta da samuwar Malamai ya ci gaba da haɓɓaka,
sannu a hankali shi ne, samuwar Daular Sharifai a ‘yandoto wadda ta zama
matattara ta gaggan Malamai masu ƙoƙarin
yaɗa
ilimin Addinin musulunci, Lamarin da ya haifar da yawaitar gaggun Malamai na
kowane fanni a wannan daula ta jahar Zamfara. Ita wannan daular Yahaya Ɗannafsuzzakiya
ɗan
Aliyu Zainul Abidina ɗan Sayyadina Hussaini ɗan
Sayyadina Aliyu Bn Abi Thalib daga wajen Nana Faɗima,
shi ya ka fata. Sharif Yahaya ya kafa daular ne a ƙarni na
takwas miladiya. Kuma yana ɗaya daga cikin Malaman Imamu Malik.
Wannan ya taimaka wajen kakagidan da Mazhabar Malikiya ta yi a ƙasashen
Hausa, kamar yadda Ibrahim (2009:16) ya nuna, daular ta gudana har zuwa zamanin
Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo.
Kasancewar garin
Gusau gari ne mai cike da baƙi
musamman ta ɓangare
makaranta tarihin kafuwar makarantun Al-ƙur'ani bai ɓuyaba, dan
kuwa, Akwai manya-manya makarantu acikin birnin Gusau kamar haka:
1.
Makarantar Malam Almu Ɗandurmi
2.
Makarantar Malan Yahuza Filin Nayawo
3.
Makarantar Malam Nakanoma Sabon Fegi
4.
Makarantar Malam Idi na Mal. Mukhtar Kofar
Jange
5.
Zawiyyar Sheikh Balarabe, Gusau
6.
Zawiyyar Malam Aliyu Mai Kanti Shiyar
Mayana
7.
Makarantar Malam Fari Ɗandutsen
Gabas
8.
Makarantar Malam Hamisu, Kusa da Gidan
Makaranta
9.
Makarantar Malam Ango Lungun Malamai
10. Makarantar
Malam Musa mai Almajirai Tudun Wada
11. Makarantar
Gidan Malam Nadango Kanwuri, Gusau
12. Makarantar
Malam Ibrahim Nagangare
13. Makarantar
Malam Nazoma Albarkawa
14. Makarantar
Malam Lawali Jibiya, Bakin Silima
4.2 YADDA BIKIN
SAUKAR ALƘUR’ANI YAKE A DA
Tun zamanin
sahabbai ana gudanar da bikin saukar Alƙur’ani
ne ta haddace wani ɓangare ba wai sauke shi gaba ɗaya ba,
kuma bayan wucewarsu abin ya ci gaba da gudana a haka, domin ko in aka ce yaro
ya zo sabbi to akwai ɗan dafe-dafen da za a yi domin ana
ganin ya taka wani matsayi da kuma jin daɗin da
uwaye ke ji harma ana ma saukar sabbi kirari da cewa “Sabbi Saukar Mata” (Bunza
2009). Wai kamar in mace ta iya sabbi ta sauka, sannan haka aka cigaba da koyon
Alƙur’ani in an zo kowane izu da kwai abin da
ake yi na farin ciki, to amma in aka sauke Alƙur’anin
gaba ɗaya to
irin bikin da ake yi ya banbanta da na baya, (wato kafin a sauka).
Sannan kuma yadda
ake aiwatar da bikin ya banbanta domin ko kowane gari suna da irin yadda suke
yin bikin su, amma ga yadda wani Malami ya yi bayanin yadda ake bikin saukar Alƙur’ani
a da kamar haka: “Idan mutum ya sauka ana ba malami tuwo misalin malmala biyar
ko shidda, da kuma dawo huɗu ko biyar kuma ana ba shi masa
guda talatin ko arba’in ko hamsin sannan kuma da goro talatin ko arbi’in ko
hamsin daidai gwargwadon karfin gidan wanda ya sauke alƙur’ani.
Sannan kuma ana ba Malamin kai na bisar da aka yanka da ƙafafu,
kuma ana bashi kuɗi dai dai gwargwado. Ranar bikin za a tara
jama’a daga ɓangare
na ‘yan uwa da abokan arziki domin su zo su shaidi cewa lallai wannan yaron ya
sauka, sannan kuma ‘yanuwan yaron da ya sauka na ba da gudummawa domin taimako
ga wannan bikin saukar Alƙur’ani.
Bayan haka ana rarraba abinci ga waɗanda suka halarci
taron bikin saukar Alƙur’ani
da abin sha.
Bugu da ƙarim
ana yi ma wanda ya sauka ɗinkin sutura da suka haɗa da babbar
riga da tagguwa da wando a naɗa masa rawani ya fito kamar wani
Malami domin ana yi masa kallon ya fara taka wani mataki na shiga sahun
malanta. Sannan sai ya karata Fatiha da wani ɓangare
na Alƙur’ani, wato Farkon Suratul Baƙara
sai kuma Malamai su yi masa nasiha, bayan an gama nasihar sai shi yaron da ya
sauke Alƙur’ani ya hau saman durum ko shigehwa
domin ya yi ma mutanen da suka zo shaidar wannan bikin saukar Alƙur’ani
watsin sababbin kuɗi da nuna murna da jin daɗinsa a
wannan rana, da kuma jawo hankali ‘yan’uwansa da abokansa da basu sauka ba, da
su dage su zage dantse don suma su ga sun sauka” (Malam Usman Tambuwal, 2021).
Kasancewar a da
ana samun ƙarancin masu sauka shi ya haifar da yin
bikin a gidajen waɗanda suka sauka, amma dai a hankali har ya
dawo makaranta ke shirya yadda za a yi bikin, kuma a harabar makaranta, sai dai
uwaye, da yan uwa su zo makarantar da yaran su suke don shaidar ganin bikin
saukar alƙur’ani da ɗansu ya
yi.
4.3 YAƊUWAR SA DA BUNƘASAR BIKIN
SAUKAR ALƘUR’ANI A GARIN
GUSAU
Kasancewar
Al’amarin karatun Alƙur’ani da bikin
saukar duk abubuwa ne masu asali tun zamanin Annabi Muhammad (SAW) da
sahabbansa, to amma anan Afrika kuwa, yaɗuwar
karatun Alƙur’ani ta bayyana ne a hannun Murabiɗun
ma’ana (Mayaƙan da ke dako kan iya kokin musulmi) bayan
zuwan Uƙuba bn Nafiu, a duk sannanin da waɗannan
mayaƙa suka taru za ka samu babu abin da suke
yi sai karatun Alƙur’ani. (K/Nasarawa:
2006:5)
Wannan shi ne
asalin samuwar cibiyoyin Alƙur’ani
a Afrika da kuma dalilin da ya sa tsangayun Alƙur’ani
ke keɓanta
kansu nesa da jama’a. Kamar kuma yanda zamu ga ita kanta kalmar ta tsangaya (Sangaya/
musanghi) a wurin barebare tana nufin masu jira ko tsammani, wanda ya yi daidai
da masu ribaɗi ko
murabiɗun a
wancan lokacin. A taƙaice dai karatun
Alƙur’ani a tsarin tsangaya, ga manya ko ƙananan
yara, ya samo asali ne daga zamanin Annabi da sahabba da mabiyansu. (Sanusi
Yuguda Kofar Nasarawa 2006:6).
Amma in ana
maganar bunƙasarsa da yaɗuwar
bikin saukar Alƙur’ani sai a fara
kallon a nan najeriya duk wanda ake so ya san Alƙur’ani
ya kuma yo karatunsa, a wancan lokacin to dole sai an kai shi ƙasar
Barno (Maiduguri) domin zamowar ƙasar
wata babbar cibiya ta Alƙur’ani.
Kuma in mutum ya sauke ya dawo garinsu, shi ke nan sai a yi masa biki, daga nan
shi ma ya zama malami sai ya cigaba da koyar da wasu don su ma su samu ilimin Alƙur’ani
ta hannunsa.
Amma yaɗuwa da
bunƙasar bikin saukar Alƙur’ani
to yana da alaƙa da zuwan zamani da canza salon koyarwa
daga makarantun allo zuwa makarantun Islamiyyah, ta la’akari da wancan lokacin
ana amfani da allo wajen rubutawa da karanta ma yara, amma dawo da tsarin
Islamiya sai kawai aka fara amfani da ƙur’ani cikakke
sakamakon bunƙasar maɗaba’a
da yawaitar Alƙur’ani bugun dutsi (Ɗan
Misira) a ka rinƙa karantar da
yara, in sun dawo su biya aka fahimci sun iya sai a yi masu ƙari,
ta haka abin ya ci gaba da wakana, in yaro ya kai izu biyu sai ya ce ma
uwayensa a fanso (sayo) masa izu biyar. Haka dai har yara su kammala izu
sittin, to daga wannan lokacin sai a ce yaro ya yi saukar zuƙu,
ma’ana yana iya karanta Alƙur’ani
tare da dubawa.
Kuma wannan ba ƙaramin
yaɗuwa da
bunƙasa karatu da bikin saukar Alƙur’ani ya yi ba, domin ko a faɗin
jihar Zamfara garin Gusau kaɗai yana da yawan makarantun da sun
fi guda ɗari da
hamsin (150) da duk bayan shekara sai an gabatar da bikin sauka ma ɗalibai
kuma makarantar Zawiyyar Sheikh Balarabe Gusau a duk shekara ana iya samun ɗalibai
sama da yara ɗari uku
da ake ma bikin saukar zuƙu,
bayan kuma ana iya samun Alarammomii wato waɗanda
suka haddace ƙur’ani ba tare da dubawa ba a ƙalla
yara arba’in zuwa hamsin (40-50).
4.4 TASARIN ZAMANI
Kafin kawo bayanin
tasirin zamani to ya kamata mu ɗan haska ma mai karatu game da
kalmar zamani. “Asalin wannan kalmar ta aro ce daga Larabci wato ZAMAN, dake nufin lokaci. Hausawa suka ara, suke
amfani da ita daidai da ma’anarta ta larabci. A wajen wasu zamani shi ne sabon
abu, wannan dalili ne ya sa duk wani abu da ya faru ya wuce sai a ce ai wannan
tsohon yayi ne. Haka kuma wasu na fassara zamani da ikon Allah, musamman
tsoffi. Mai yuwuwa wannan na da alaƙa da
yadda idan sabon abu ya shigo yake game dukkan al’ummar da ke amfani da shi
musamman matasa. Saboda haka zamananci na nufin lokaci ko yayi. (Ɗantumbishi,
p 76-77).
Amma game da irin tasirin da zamani ya yi dangane da bikin saukar Alƙur’ani musamman a garin Gusau to ana iya cewa irin yadda ake yin anko (ɗinki kala ɗaya), tun daga masu bikin Saukar Alƙur’ani da kuma ahalinsu na kusa da na nesa. Sannan kuma ana yin hotuna da ake sanyawa a waya (stiker) da kuma Kalanda (clander) da ake sanyawa a ɗaki, ga mai hali har littafi ake yi mai ɗauke da hoton wanda ya sauke Alƙur’anin ko kuma mai saukar Alƙur’anin. Bugu da ƙari ana amfani da wayoyin hannu tafi da gidanka ana ɗaukar hotuna, sannan kuma ana haɗa maza da mata wajen taron, tun daga yaran da za a yi ma bikin da kuma ‘yan uwansu maza da mata manya da yara. Sannan kuma ana gayyato manyan mutane da malamai, da ma’aikatan hukumomin gidajen radio da na Talabijin (TƁ) irin su Gamji da sauransu. Ana rarraba abubuwan lashe-lashe da tanɗe-tanɗe da na ci da sha ga baƙin da aka gayato. Sai kuma wasu ‘yan shirye-shiye da ake tanada da suka haɗa da was an kaikayo da ɗaliban makaranta ke aiwatarwa domin nuna ma al’umma muhimmancin ilimin da suka koya.
Hoton ɗalibai maza masu sauka
Kalandar Malamai da ɗalibai maza da mata masu sauka
Hoton ɗalibai mata masu sauka
Hoton Malami mai jawabi a wajen bukin sauka Alƙur’ani
4.5 RAWAR DA IYAYE
KE TAKAWA
Rawar da Iyaye ke
takawa wajen Gudanar da bikin saukar Alƙur’ani
ta ‘ya’yansu. A nan za a kalli abin tun daga farko, wato tun daga lokacin da
iyaye suka sa yaro makaranta za a ga cewa sun bayar da gudummawa ta hanyar
tanada masa abubuwa irin su littafai kuɗin
mashin idan ba kusa yake da makaranta ba, da ba yaro kuɗin
tara, wasu iyayen na dafa ma yaron abinci ne saboda tsawon lokacon da yaro ke
yi a makaranta.
Haka, ɗinkin
makaranta da sauran abubuwa, kama da biyan kuɗin
wata, laraba da sauran kuɗaɗen da
makaranta za ta buƙata daga wajen
iyayen yara. Ta gefen bukin saukar Alƙur’anin
kuma, za a tarar cewa tun daga lokacin da makaranta ta tabbatar da cewa yaronka
ya sauka za a fara yin zama na musamman a tsakanin uwayen yara da malaman
makaranta, domin tsara yadda za a tunkari hidimar bikin. A ƙarshe
kuma za a tsayar da adadin kuɗin da ko wane uba zai bayar na game
da ɗansa
Wasu uwaye kan tanadar
da bisa (dabba) da za a yanka ma yaro, wani lokaci ana kai wani sashen naman
bisar makaranta, wannan ya danganta da zarafin iyayen wanda ya sauka. Haka
kuma, iyaye kan dafa abinci don tarbar baƙi wato
‘yan ‘uwa da abokan arziki na kusa da na nesa. Wasu iyayen na yi wa ‘ya’yansu
kalandu da sitika da sauran ababen da za a raba ga waɗanda
aka gayyata domin nuna farin ciki, murnar baiwa.
Sannan kuma iyaye
na yi ma ‘ya’yansu ɗinkin kalar tufafin da hukuar makaranta ta
ayyana, wanda za a yi amfani da su ranar buki.
4.5.1 Rawar da Malamai ke Takawa
Kasancewar Malami
na da muhimmanci ya sa aka ce “in yaro ya hango malaminsa da kaya, kuma ga
mahaifinsa da kaya, to ya karɓi kayan Malaminsa ya kyale babansa,
(Littafin Ta’alimin Muta’allim).
To amma in ana
maganar game da irin rawar da Malamai ke takawa a wajen bikin saukar Alƙur’ani
to ɗaliban
makarantarsa, ya fara ne, daga koyar da yaran tun daga farko har ya zuwa
lokacin da yaran suka sauka. Kuma daga cikin irin rawar akwai shirya wurin da
za a gudanar da walimar bikin saukar Alƙur’ani,
inda makaranta ta tanada, kuma suke da haƙƙin
gayyato manyan malamai da manyan baƙi da
ake son su samu halartar bikin saukar Alƙur’anin.
Su ke gabatar da
duk wasu karance-karance da jawaban da manyan baƙi za su
gabatar a wurin, sannan kuma suna tanadar kayan tanɗe-tanɗe da
lashe-lashe da za su raba ma baƙin da
suka gayyato. Haka Malaman nan su ke gayyato ‘yan gidan rediyo da TƁ
a wajen domin ɗaukar
bikin saukar a tsakanin al’umma.
A ƙarshe
bayan taro ya tashi malamai ke tattara duk kayan da aka yi amfani da su tare da
maida ma masu su da kuma yi masu godiya sai kowa ya tafi gidansa. (Sheikh
Munnir Muhammad 2021)
4.5.2 Rawar Da Ɗalibai Ke Takawa
Rawar da ɗalibai
ke takawa a wajen bikin saukar Alƙur’ani
ta fara ne tun daga wurin da suka dage suka mai da hankali ga karatun su har
Allah ya kaisu lokacin da aka kai ga saukar Alƙur’ani,
domin sau da yawa yara da dama na fara karatu tare, amma ba kowannen su ke
samun damar kai ga matsayin kammalawa ba, domin ko abin baiwa ne. Haka kuma,
zuwa makaranta ba dare ba rana ruwa da iska ba su hana su, ita ma wata horewa
ce ga Allah. Yaran su kan gayyato abokansu da kuma yi masu tanadin abin da za
su ba su bayanan kammala bikin. Sannan kuma suna taka rawa a wajen biki na yin karance-karance
da makaranta ta tsara domin ɗaliban su gabatar a bainar jama’a.
4.6 NAƊEWA
A wannan babi mai
suna bikin Saukar Alƙur’ani a garin Gusau,
an yi bayani game da asalin bikin saukar Alƙur’ani
tare da waɗanda
suka fara aiwatar da bikin saukar Alƙur’ani.
Haka kuma, an kawo bayanin yadda bikin saukar Alƙur’ani
ya ke da, da kuma yaɗuwarsa da bunƙasar
bikin saukar Alƙur’ani a garin
Gusau. Bugu da ƙari, an kawo
tasirin zamani a kan bikin saukar Alƙur’ani,
tare da bayanin irin rawar da iyaye, da malamai da su kansu ɗaliban
ke takawa a wannan fage.
BABI NA
BIYAR
SAKAMAKON
BINCIKE
5.0 GABATARWA
Kasancewar wannan
babi na biyar shi ne babi na ƙarshe,
an taɓo muhimman
abubuwa kamar haka, bayan gabatarwa anyi sharhi akan sakamakon bincike, da
shawarwari daga ƙarshe naɗewa.
5.1 SAKAMAKON
BINCIKE
Kasancewar duk
wani bincike da aka gabatar dole ne a ƙarshe a
samu samakon bincike. Wannan bincike an yi ƙoƙarin
gano asalin kalmar biki, da kuma sauka, da Alƙur’ani
da kuma waɗanda
suka fara gabatar da bukin saukar Alƙur’ani,
haka kuma an kawo wasu sunaye da ake yi ma bukin saukar Alƙur’ani.
Bugu da ƙari an yi bayani irin rawar da iyaye da
Malamai da kuma ɗalibai ke takawa wajen bukin saukar. A ƙarshe
an nuna yadda ake aiwatar da bukin saukar Alƙur’ani
jiya da yau a garin Gusau
5.2 SHAWARWARI
Duk wani aiki da
mutum ya gabatar ko ya gudanar, akwai buƙatar
shawara daga gareshi domin cin gajiyar wannan shawarwari ga al’umma, saboda
haka ina ba duk wanda Allah ya baiwa ikon zai yi nazari a wannan fanni shawara
cewa, in dai ya ci karo da wannan kundin kuma har binciken sa yana da alaƙa
da wannan da ya yi ƙoƙari
ko suyi ƙoƙarin ɗorawa
daga inda wannan bincike ya tsaya, kar su ce su kwashe kawai, domin ko yin
hakan baya taimakawa a fagen nazari, kamar yanda aka zaƙulo
wannan taken na bikin Saukar Alƙur’ani
a Garin Gusau a ka yi ƙoƙari
har aka tattaro bayanan da suka gina wannan kundi, ya zama abin karatu ko
nazari ga yan uwa na ɗalibai, to lallai suma ya zama
wajibi su dage don su samar da wani abu mai amfani ga al’umma.
Sannan kuma
kafafen sadarwa na zamani suna da rawar da zasu taka wajen zaburar da sauran
yara da ba su sauka ba, domin ta hanyar nuna abin a gidajen TƁ
yana sa yara su ji daɗi da kuma ƙara
dagewa, haka kuma iyaye da Malamai ya kamata su kalli wasu abubuwa da ake
aiwatarwa kamar abin da bai da kyau, to su yi ƙoƙarin
hanawa domin kawo cigaba a cikin addini.
5.3 NAƊEWA
A wannan babi na
biyar kuma babi na ƙarshe, ya fara da
gabatarwa da shimfiɗa, bayan nan ya yi bayanin kundin gaba ɗaya,
amma a taƙaice, sannan ya kawo shawarwari, daga ƙarshe
naɗewa.
MANAZARTA
Al-Ƙur’ani
Maigirma
Adamu,
M.T (1998) “Aure da Biki a ƙasar
Hausa” Kano: Ɗansarki Kura Publishers Nig. Ltd.
Abubakar,
T.A (2015) “Ƙamusun Harshen Hausa” Zaria: Norther
Nigeria Piblishing Company Limited.
Al-Hassan
M. (1994) “Banbance-Banbance Al’adun Bikin Aure Tsakanin Al’ummar Hausawa da
Yarbawa” Kundin Digiri na Farko Jami’ar Bayero, Kano, Sashen Harsunan Nijeriya.
Bunza
A.M (2017) “Dabarun Bincike: A Nazarin Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa”
Zaria Ahmadu Bello Uniɓersity Press Limited
Bayero
J. (2006) “Ƙamusun Hausa” Kano Cibiyar Nazarin
Harsunan Najeriya, Jami’ar Bayero.
Ɗanfodiyo J. (2005) “Ɗunɗaye”
Mujallar Nazarin Hausa juzu’i na Ɗaya
Fitowa ta Biyu December, 2005. Department of Nigerian Langauge, Usman Ɗanfodiyo
Uniɓersity, Sokoto.
Gusau, G.U (2012) “Bukukuwan Hausawa” Gusau Oral Faith Printis.
Gusau G.U (2010) Tasirin Al’adu cikin Makarantun Allo a Ƙasar Hausa Journal of Language Education Ɓol. 3, Katsina: Isa Kaita
College of Education Katsina State.
Kabiru A.M (2019) “Zamfarci da Rabe-Rabensa”, kundin Digiri na
Farko, Sashen Nazarin Harsuna da Al’ada Jami’ar Tarayya Gusau.
MUTANEN
DA AKA YI FIRA DA SU
1.
Sheikh Abdullahi Abubakar Yabo, Zawiyyah,
a Zawiyyar Sheikh Balarabe 20/1/2021 : 9:00am
2.
Sheikh Mal. Abubakar Abubakar Abi, a
Gidansa Asibitin Shagari, Gusau 22/1/2021:10:00am
3.
Sheikh Mal. Muniru Muhammad Ɗaibah
Asibitin Shagari, Gusau 24/1/2021 -
12:00am
4.
Mal. Mansur Ahmad Makaranta, a Gidan sa da
ke Tudun Wada Gusau 24/1/2021 – 10:00am
5.
Sheikh Mal. Usman Tambuwal a Zawiyyar
Sheikh Balarabe 27/1/2021 – 12:00am
6.
Sayyidi Malam Aliyu Uwaisu Rogo, a
Zawiyyar Sheikh Balarabe 4/2/2021 9:00am
7.
Alh. Hafiz Alaramma Murtala Aliyu Dabbagi,
a Sabon Gari, Gusau 10/3/2021 10:00am
8.
Mal. Aminu Aliyu Hizburrahim S/Gari
11/3/2021 – 12:00am
9.
Mal. Abdulrahman Ibrahim, Hizbirrahim
Dandutse 20/4/2021 1:00
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.