Ticker

6/recent/ticker-posts

Laluɓen Al’adun Hausawa A Cikin Wasu Waƙokin Musa Ɗanƙwairo

Kundin bincike da aka gabatar a Sashen Koyar Da Harsuna Da Al’adu, Tsangayar Fasaha Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau, don samun shaidar kammala digiri na ɗaya (BA.HAUSA).

Laluɓen Al’adun Hausawa A Cikin Wasu Waƙokin Musa Ɗanƙwairo

NA

Binta Gambo

Alhaji Musa Ɗanƙwairo

GODIYA

   Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa mai  komi da yayi ni’ima a garemu tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da iyalansa da al’ummarsa baki ɗaya.

          Bayan haka, wannan aiki na bincike yana da wahala mutum ya aikatashi ba tare da ya samu mataimaka ba, dan haka ya zama dole in mika godiya ta ga waɗanda suka bani gudunmuwa wajen ganin na kammala wannan aikin mai matuƙar wahala.

          Hausawa na cewa “Bin na gaba bin Allah” don haka dole ne in miƙa godiya ta ga mahaifana bisa ɗaukar ɗawainiya ta da suka yi tun daga haihuwa ta har zuwa ganin na samu ilimi tare da bani gudunmuwar addu’oin su a kaina har zuwa wannan rana.

          Har  ila yau Hausawa na cewa “Iyakar gudu ƙuryar ƙaki” ya zama dole in mika godiya ta zuwa ga malammaina da jinjinar ban girma a gare su tun daga aji daya har zuwa aji huɗu da kuma malama ta musamman wadda ke duba ni da aiki na na bincike wato malama Halima Mansur Kurawa bisa ga juriyar duba wannan aiki tun daga farkon sa har zuwa ƙarshe, da kuma gyara da shawarwari irin na ɗiya da uwa domin ganin wannan bincike haƙarsa ta cinma ruwa.

          Haka zalika ina miƙa godiya ta ga ɗaukacin malammaina da hukumar wannan jami’a da fatar alkhairi a garesu baki ɗaya Allah ya saka masu da alkhairi.

          Har ila yau, ya zama dole inyi jinjina ta musamman ga maigida na Ibrahim Shehu wanda ya bani damar yin wannan karatu tare da bani ƙwarin guiwa da shawarwari da biya mani kuɗin makaranta da riƙa mani iyalaina wajen ganin na samu abinda nike nema Ubangiji Allah ya saka mashi da gidan Aljanna ya bashi abin da yake nema duniya da lahira kuma ya bashi abin da zai ci gaba da ɗawainiya damu Amin.

          Bugu da ƙari ya zama dole in mika godiya ta ga mahaifana da ‘yan uwana da makota na da addu’oin da suke tayi min ganin cewa na kamala karatuna da fatar alkhairi da suke man na gode Allah ya saka masu da alkhairi baki ɗaya. Amin.

 

SADAUKARWA

Ni Binta Gambo “Yarlele” wato Maman Amir. Na sadaukar da wannan kundin bincike, mai taken “laluben Al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun” ga mahaifana musamman Alhaji Dahiru Gambo Ahmad da mahaifiyata Hajiya Asiya Dahiru da ƙannen mahaifiyata marigayi Bello Mainasara da malamina na islamiya marigayi malam Dalhatu Ahmad bisa ɗawainiyar da suka yi dani tun ina ƙarama har kawo yanzu.

          Haka kuma na sadaukar da wannan bincike zuwa ga kakata Hajiya Hassana da ƙanwata Jamila Dahiru da Zainab Aliyu da ƙanena            

TSAKURE

          Kasancewar waƙoƙin baka suna daga cikin muhimman ɓangarorin adabin da Hausawa ke ɗauka da muhimmanci saboda kasancewar su tamkar wasu madubai daga cikin maduban da ake dubawa domin gano irin hanyoyin rayuwar ita wanna al’umma.

          Don haka ne ma, ba kamar rubutattun waƙoƙi ba, su waƙoƙin baka sun fara ne lokaci mai tsawo da ya gabata kuma hasashe na tarihi ya nuna sarakuna suna daga cikin waɗanda aka fara yiwa kiɗa da waƙa.

          Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da aka aiwatarwa don ilmantarwa ko sadaukarwa ko nishaɗantarwa ko ba da wata gudunmuwa ta musamman, kusan kiɗa yayi ruwa da tsaki ya durmuya sosai  a cikin rayuwar Bahaushe , musamman rayuwar da ta ƙunshi zamantakewa da sana’oi da bukukuwa da lokutan shakatawa.

          Wannan aiki ya ƙunshi laluben al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗan ƙwairo Maradun.

       Bugu da ƙari shi wannan aiki an kasa shi gida biyar ya ƙunshi gabatarwa, dalilin bincike, iyakancewar bincike da kuma tarihin mawaƙi haihuwa da mutuwarsa, da bayani kan al’adun Hausawa da ma’anar al’ada da ire-iren al’ada da al’adu a cikin wasu waƙoƙinsa har zuwa babi na biyar wanda ya kunshi kammalawa da sakamakon bincike da shawarwari  da manazarta.

 

BABI NA ƊAYA

1.0   SHIMFIƊA

    Da sunan Allah mai rahama mai jinkai tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaban halitta Annabinmu, Annabi Muhammadu (S.A.W), tare da alayensa da kuma sahabansa amin.

    Waƙoƙin baka suna daga cikin muhimman ƃangarorin adabi da Hauwasawa ke ɗauka da mahimmanci saboda kasancewar su tamkar wasu madubai daga cikin maduban da ake dubawa domin gano irin hanyoyin rayuwar ita wannan alumma. Wato dai waƙoƙin baka suna daga cikin manyan rukunan adabin baka na Hausa da suke taimakawa wajen fahimtar shi kansa adabin wannan al’umma so sai da so sai.

    Don haka ne ma,ba kamar rubutattun waƙoƙi ba, su waƙoƙin baka sun fara ne lokaci mai tsawo da ya gabata kuma hasashe na tarihi ya nuna sarakuna suna daga cikin waɗanda aka fara yiwa kiɗa da waƙa.

     Kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa wani ginshiƙin abu ne da aka aiwatarwa don ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gudunmuwa, ta musamman, kusan kiɗa yayi ruwa da tsaki ya durmuya sosai a cikin rayuwar Bahaushe, musamman rayuwar da ta danganci zamantakewa da sana’oi da bukukuwa da lokuntan shaƙatawa.

   Wannan aiki ya ƙunshi laluben Al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun. Kuma shi wannan aiki an kasa shi ne a manyan kaso har guda biyar.

Babi na ɗaya : An yi Magana a kan manufar bincike, da hasashen bincike, da  farfajiyar bincike, da matsalolin da ake fuskanta yayin gudanar da wannan bincike da kuma hanyoyin da ake bi wajen tattaro bayanai sai kuma jawabin naɗewa, wato takaita abin da babin ya  ƙunsa.

Babi na biyu : Wannan babi ya ƙunshi ayukan da suka gabata, masu dagantaka da wannan aikin. Misali littattafai da kundaye da kuma maƙalu.

Babi na uku : Ya na ƙunshe da tarihin makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun wanda ya haɗa da haihuwarsa, rayuwarsa, iyalinsa, da fara kiɗa, da nau’oin waƙoƙinsa, waɗanda suka haɗa da waƙoƙi a kan Al’adun Hausawa.

Babi na huɗu: Ya ƙunshi ma’anar Al’ada, da ire-iren Al’adun Hausawa da kuma nazarin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo a kan Al’adun Hausawa da saƙon da suke ɗauke da shi.

Babi na Biyar: Babi na ƙarshe kuwa, yana ɗauke ne da jawabin kammalawa da sakamakon bincike wato abinda bincike ya gano, da kuma shawarwari don inganta ayukan masu zuwa a ƙarshe wannan aiki anzo da manazarta, inda aka kawo littattafai da kundaye da maƙalu waɗanda ake dubawa yayin aiwatar da wannan bincike, an kuma kawo ratayen waƙoƙi da aka samo misalan daga cikinsu.

1.1 MANUFAR BINCIKE

Akwai mahimman hujjoji ko dalilai waɗanda suka sanya a gudanar       da wannan bincike kamar haka:

  Dalili na farko, shi ne ina da matuƙar sha’awar sauraron waƙoƙin makaɗa da mawaƙan   Hausa, musamman Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo.

Wani dalilin kuma, domin a ƙara fito da baiwar wannan makaɗi a fili, a fahimci hikima da fasarar da Allah Ubangiji maɗaukaki ya yi masa ta waƙa in da har ya fito da Al’adun Hausawa masu kyau da nufin faɗakarwa wajen kiyaye su, dalili na uku shi ne taskace wasu waƙoƙinsa da ya yi a kan Al’adun Hausawa don ‘yan baya masu nazari ko neman wasu bayanai su amfana. Haka kuma wannan binciken an yi shi domin cike wani gurbi na samun shaidar kammala digiri na farko a fannin Hausa wato  (B.A Hausa).

1.2   HASASHEN BINCIKE

Babbar manufar wannan bincike ita ce labubo wasu Al’adun Hausawa daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗankwairo. Sannan a yi hasashen ko Hausawa suna riƙe da wannan Al’adu? Da kuma alfanun riko da su, idan kuma sun watsar da al’adun to wannan jan kunne makaɗin ya yi kuma a wane hali a ke ciki yanzu.

1.3 FARFAJIYAR BINCIKE

Wannan bincike zai ta kaikawo a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanwairo Maradun, kuma binciken zai kalli wasu Al’adun Hausawa da mawaƙin ya yi amfani da su a cikin wasu waƙoƙin na sa.

Don haka duk abin da bai shafi Al’ada ba a cikin wasu waƙoƙin  ba za’ayi maganar su ba.

1.4  MATSALOLIN BINCIKE

1.     Rashin wani wanda ya gaba ce ni wajen aikin lalubo wasu Al’adun Hausawa.

2.     Matsalar mutane sun watsar da Al’adun su wajen lullubi da sa kaya irin na Al’adun gargajiya.

3.     Matsalar wajen tattaro waƙoƙin mawaƙin

4.     Mutane sun watsar da al’adun su na sauraren waƙoƙin makaɗan gargajiya.  

1.5 MAHIMMANCIN BINCIKE

Bincike wata hanya ce  da ake ƙudurta ta ta hanyar yin nazari akan wani abu da ake ganin ya cancanta domin a gano wani sabon al’amari don cigaban al’umma. To in ko haka ne a yayin gudanar da bincike yana buƙatar tunani shin ko binciken nan zai yi amfani ga al’umma?

Don haka akwai waɗansu mahimman abubuwa da suke iya zama ko kuma suke da inganci abincika kamar haka: Domin a fito da hanyoyi masu sauki na gudummuwar da mawaƙan Hausa na baka suke bayarwa zuwa ga al’umma haka kuma wani mahimmancin wannan binciken shi ne Habaka ko bunƙasa adabin Hausa. Wannan binciken yana da mahimmanci domin a ƙarawa malammai da ɗalibai ƙwarin gwuiwa wajen farfado da kuma raya Al’adun Hausawa. Daga ƙarshe wannan bincike ya na da mahimmanci wajen nuna bunƙasar ko cigaban da harshen Hausa ya samu a yau ta bangeren adabi.

1.6  HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Hanyoyin da ake bi wajen gudanar da bincike sun haɗa da :

1.Duba kundayen bincike da aka gabatar don samun digiri na ɗaya zuwa na uku masu dangantaka da wannan aiki.

2.Amfani da littattafai da maƙalu da aka gabatar a tarukka daban-daban.

3.Sauraron kaset- kaset masu ɗauke da waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo waɗanda suka shafi Al’adun Hausawa.

4.Hira da masana da masu sauraron waƙoƙin Musa Ɗankwairo.

1.7  NAƊEWA

A wannan babi an yi bayani ne akan shimfiɗa,manufar binkice,hasashen bincike,farfajiyar bincike,matsalolin bincike da ya samu wajen gudanar da shi da kuma hanyoyin gudanar da bincike da naɗewa duk acikin babi na ɗaya.

BABI NA BIYU

2.0 SHIMFIƊA

A wannan babi na biyu za’a yi bayani akan bitar ayyukan da suka gabata makamantan wannan aikin bincike.

Inda za’a yi bayani dangane da littattafai da muƙalu da kundaye, haɗi da bayanin hujjar ci gaba da bincike da kuma naɗewa duk a cikin wannan babi na biyu.

2.1 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

Babu ko shakka ko wata tantama akwai wasu ayyuka da aka gudanar game da waƙoƙin wannan shahararren makaɗi wato, Makaɗi Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Domin zai zama abin mamaki a ce mashahurin mawaƙi na ƙasar Hausa kamar makaɗi Alhaji musa Ɗanƙwairo ba a yi wani nazari a kan waƙoƙinsa ba sam-sam.

          Hausawa suna cewa ‘Daga na gaba ake gane zurfin ruwa’.ko da na gaban wada ne haka kuma sun ce “inda Akuyar gaba ta sha ruwa haka nan  ta baya ke sha” wannan kuwa haka yake babu shakka ansha gudanar da bincike da kuma rubuce rubuce a ciki da wajen sassan adabin Hausa na waƙoƙin baka da rubutattun waƙoƙin Hausa daga malamai da manazarta daban-daban domin dada zurfafa aiki don cigaba da gudun maimaici.

          Haka kuma akwai littattafai da muƙalu da kundayen Digiri na ɗaya har zuwa na uku da aka yi a jami’oi daban-daban don haka zan diba wasu ayukan da suka gabata domin su zama jagora wajen wannan nazari da kuma taimakon mai duba aikin.

2.1.1 BUGAGGUN LITTAFAI

Masana da manazarta da dama sun rubuta littattafai da yawa da suka shafi adabin Hausa musamman na baka.

          Ɗangambo (2007)  A cikin littafinsa daya wallafa mai suna “Ɗaurayar Gadon feɗe waƙa” ya bayyana yadda a ke nazarin rubutattun waƙoƙi a ciki ya yi bayanin salo da sarrafa Harshe da abinda ya kunsa da kuma bayanin Awon Baka (zubi da tsari) da sauransu.

          Wannan aiki ya yi kama da wannan saboda duk suna Magana ne a kan adabi, kuma wanda ya ƙunshi waƙa.

Sai dai kuma inda suka bambanta shi ne aikin yana magana ne a kan yadda mawaƙi ke waƙa Al’adun Hausawa a ciki waƙoƙin baka musamman na Hausa.

          Gusau(2005) a cikin littafinsa mai suna makaɗa da mawaƙan Hausa ya yi bayanin yadda mawaƙan Hausa suka rabu ya kasa littafai har kashi biyar.

1.     Kashi na ɗaya makaɗan yaƙi

2.     Kashi na biyu makaɗan sarakuna na I

3.     Kashi na uku makaɗan sarakuna na II

4.     Kashi na huɗu makaɗan jama’a sai

5.     Kashi na biyar makaɗan sana’a.

          Wannan aiki ya yi kama da wannan da yawa saboda duk suna magana ne akan mawaƙan baka na Hausa. Sai dai bambancin su shi ne mun ɗauki mawaƙi ɗaya ne mu yi nazarin laluben al’adun Hausawa a cikin wasu waƙoƙinsa.

          Bunza A,(2009) ya wallafa littafi mai suna Narambaɗa. Wannan littafi, Bunza ya fito da muhimman bayanai da suka shafi tarihin rayuwa da ayyukan Ibrahim Narambaɗa Isa, tare da yin sharhi mai gamsarwa na ilimi da kuma rarrabe wasu waƙoƙin nasa a mahangar al’ada da tarihi. Haka kuma ya yi ƙoƙarin fito da wasu hikimomi a cikin Littafin.

          Wannan aiki ya yi kama da wannan saboda duk muna magana a kan mawaƙan baka na Hausa. Sai dai inda suka bambanta shi ne shi yana magana ne akan Ibrahim Narambaɗa, shi kuma wannan aikin yana magana ne akan Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

2.1.2 KUNDAYEN BINCIKE

Masana da manazarta da dama sun rubuta kundayen bincike masu alaƙa da wannan bincike.

          Kurawa,(2004) ta gudanar da binciken ta, a cikin kundin Digirinta na farko a kan “Adon Harshe cikin waƙoƙin sardauna” na makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo a wannan bincike ta kawo ma’anar Adon Harshe daga masana daban-daban sannan kuma ta yi nazarin wasu tubalan Adon Harshe.

          Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aikin, domin duk ana magana ne akan mawaƙi ɗaya wato, Musa Ɗanƙwairo. Sai dai inda aikin namu ya bambanta shi ne namu aikin yana Magana ne a kan laluben al’ada acikin wasu waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo.

          Sankalawa (1994) ya gudanar da bincikensa a cikin kundin Digiri na farko akan “Nazarin rayuwar makaɗa sani sabulu” da falsafar waƙoƙinsa marubucin ya yi bayani a kan rayuwar makaɗa Sani Sabulu a matsayinsa na makaɗi da yanaye-yanayen waƙoƙinsa ta fuskar turke da awon baka da salo da sarrafa Harshe.

          Wannan aiki yana  kama da wannan  domin duk aikin ya na  magana ne a kan makaɗan Baka na Hausa. Don haka wannan aikin ya na da alaƙa da wannan sai dai kuma inda suka bambanta shi ne wannan aikin yana bayani ne akan laluben Al’ada a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

          Adama (2012) a cikin aikinta na kundin Digiri na biyu mai taken “Salo da sarrafa Harshe a cikin wasu waƙoƙin Jam’iyyun A.N.P.P da P.D.P a jihohin kano da jigawa” ta yi tsokaci akan a salin rubutattun waƙoƙin siyasa da samuwarsu da kuma bunƙasarsu. Daga nan sai mai nazarin ta duba ma’anar salo da sarrafa harshe da ire-irensa bisa ra’ayoyin masana daban-daban.

Haka kuma ta kawo misalan yadda wasu mawaƙan siyasa musamman a jihar Kano da jigawa suke sarrafa hikimominsu ta hanyar Salo da sarrafa harshe.

          Wannan aiki yana da alaƙa da wannan. Sai dai yana bayanin laluben al’ada a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

         Yakubu,(2012) ya gabatar da aikin bincike don neman digiri na biyu mai suna “Adon Harshe a waƙoƙin Mamman Shata na masu sarauta.” A cikin wannan aiki an fara gabatar da asali da wanzuwar waƙar baka a ƙasar Hausa. Sannan ya yi bayanin wasu daga cikin ra’ayoyin masana dangane da haka. Daga nan sai ya duba tarihin makaɗa mamman Shata, tare da bayani a kan wasu daga cikin nau’oin adon harshe da Mamman Shata ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa na masu sarauta.

          Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aikin sai dai inda suka bambanta shi ne, wannan  aikin yana magana ne akan laluben al’ada a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

A dunƙule, dukkan waɗannan kundayen bincike da bugaggun littattafai da muƙalu na ilimi da aka ambata a sama suna da dangantaka ta kusa da wannan aikin da aka gabatar. Domin kuwa mafi yawansu sun yi bayani ne a kan makaɗa da mawaƙan baka na Hausa. Haka kuma za su taimaka ƙwarai da gaske wajen fito da martabar wannan aiki , wanda ya kunshi laluben Al’ada a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

         Dumfawa A.A. (2003) ya gabatar da aikin bincike don neman digiri na uku mai suna “Waƙa a tunanin Yara” a jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato. A cikin wannan aiki malamin ya yi gabatarwa inda kuma ya kawo ma’anar waƙa tare kuma da yin bayanin tunanin Yara a game da waƙa.

          Wannan aiki yana da alaƙa da wannan aiki, domin duk suna magana ne akan adabin Hausa, wanda ya shafi waƙa. In da kuma aikin ya bambanta da nashi shi ne wannan aiki yana magana ne akan wasu al’adun Hausawa a cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

          Garba, S.(2001) ya gabatar da aikin bincikensa don neman digiri na uku. Mai taken “Salon sarrafa harshe a waƙoƙin Aƙilu Aliyu. Sashen Harsuna da al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello Jihar Kaduna, Nijeriya. A cikin aikin nasa ya kawo ma’anar salo da nau’o’insa ya kuma kawo bayanin hikima da sarrafa harshen da shi mawaƙin ya yi a cikin wasu waƙoƙinsa.

          Wannan aiki ya yi kama da wannan aiki, saboda duk suna magana ne akan adabi a cikin waƙoƙi. Sai dai inda wannan aikin ya bambanta da nashi shi ne, wannan aikin ya na magana ne akan wasu al’adu a cikin waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo shi kuma nashi aikin yana magana a kan Salon sarrafa harshe a waƙoƙin Akilu Aliyu.

2.1.3 MUƘALU

Malamai da masana da dama sun gabatar da muƙalu a kan adabin baka wanda ya shafi waƙar baka.

          Gusau(2013) ya gabatar da muƙala mai suna “ Dangantakar waƙoƙin Baka da Al’adun Hausawa Bunƙasa ko koma baya” Wannan takarda cike  take da ɗimbin bayani akan Al’adun Hausawa da matsayin waƙoƙin baka a wajensu, tare da misalan kaɗe-kaɗen Hausawa. Haka kuma ya nuna irin bunƙasar da wannan waƙoƙin suka samu tun daga wancan lokaci har komo wa yanzu, sannan kuma ya rufe takeda da kowa halaye da dabi’u waƙoƙin masu hikima da armashi waɗanda al’ummar Hausawa za su amince da su.

          Aikin nasa ya yi kama da wannan aiki sai inda suka bambanta shi ne wannan aiki yana bayani ne akan laluben al’adun a wasu waƙoƙin Musa Ɗankwairo.

Gusau (2011) ya gabatar da muƙalarsa mai suna tasirin Al’ada da adabin Hausa a kan tufafin Hausa. Maƙalar ɗauke take da dinbim bayanai akan ma’anar Al’ada da kuma ire-iren tufafin Hausawa na gargajiya ya rufe takardar da kawo mahimmancin tufafi ga rayuwar al’umma.

          Aikin nasa yayi kama da wannan domin duk suna magana ne akan Al’ada a adabin Hausa. Sai dai inda aikin ya banbanta da wannan aikin shi ne aikin yana magana ne akan laluben al’ada a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

2.2 HUJAR CIGABA DA BINCIKE

Akwai muhimman hujjoji ko dalilai waɗanda suka sanya a gudanar da wannan aikin na bincike gasu kamar haka:

Dalili na farko shi ne akwai matuƙar sha’awar sauraron makaɗa da mawaƙan Hausa, musamman waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Saboda haka akwai sha’awar gabatar da bincike a wasu daga cikin waƙoƙin wannan mawaƙi wanda ana iya cewa sananne ne a waƙoƙin fada.

Wani dalili kuwa da yasa aka gudanar da wannan bincike akan wannan makaɗi shi ne domin a ƙara fito da wannan makaɗi a fili duniya ta ƙara saninsa ta kuma ji irin fasaha da hikimar da Allah (S.W.T) ya ba shi.

Dalili na gaba shi ne ƙara bada ƙwarin guiwa wajen gudanar da bincike akan wannnan makaɗi shi ne duk da cewa ya rasu, to don kada a manta da shi da kuma irin fasahar da Allah ya ba shi saboda a tuna dashi, haka ya dace a ɗauki wasu daga cikin waƙoƙin da ya yi domin tunawa da shi da kuma nuna ma al’umma irin fasahar da yake da ita a fagen kiɗa da waƙa.

2.3 NAƊEWA            

A ƙarshe wannan babi na biyu an kawo bayanai da suka shafi bitar wasu ayyuka da suka yi kama da wannan aikin bincike Inda bayanin ya ƙunshi waiwaye ga wasu ayyukan makamantan wannan aiki inda suka haɗa da kawo littattafai da kundaye da kuma muƙalu.

 

 

 

                                                BABI NA UKU   

RAYUWAR MAKAƊA MUSA ƊANƘWAIRO DA MATASHIYA A KAN MA’ANAR AL’ADA.

3.0 SHIMFIƊA  

          Al’ada wata sabbabiyar hanya ce ta gudanar da rayuwar kowace al’umma ta duniya. Sai dai kowace al’umma da irin tata Al’ada, amma kusan akwai dangantaka ta kusanci tsakanin al’adun al’umma. Hausawa mutane ne masu alfahari da tasu al’ada kamar sauran al’umummomi.

3.1 MA’ANAR AL’ADA

          Yana da mahimmanci a fahimci mece ce Al’ada. Ma’ana shi ne madubi da zai haskaka a samu damar ƙyallaro wasu al’umma da hakan zai yi tasiri a gare su.

Muhammad da Bashar, (2004:21)) suka ce  ‘Al’ada ita ce hanyar da mutane suke bi domin tafiyar da rayuwa’.

          Umar, (1987). Cewa ya yi “dukkan abubuwan da akasarin jama’a na kowace al’umma suka amince da yin su, ko yin amfani da su su ne Al’adunsu’

           Bunza, (2006)  shi ko yace “ Al’ada tana nufin dukkan rayuwar ɗan adam tun daga haihuwarsa har zuwa ƙabarinsa” Sai ya ƙara da cewa  ko ina mutun ya samu kansa duk wata dabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu ko yake rayuwa ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai.

          Kuma babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa face tana da Al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe ta da wata da ba ita ba.

          Masana daban-daban sun yi bayanin abin da suka fahimta ga Al’ada. Alal misali Muhammad Sani Ibrahim ya bayyana al’ada da cewa:

          “Ita kalmar al’ada asalinta larabci ce amma da Hausa tana nufin hanyar rayuwar al’umma, musamman hanyoyin rayuwa ta yau da kullum wanda al’umma ta saba da yi” (Ibrahim, 1985:1).

          Ya ƙara da cewa al’ada ta kasu kashi biyu a wurin Hausawa. Akwai Al’adun gargajiya waɗanda Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni, irin waɗannan al’adu yawanci kowace al,umma tana wulaƙanta wanda ya wulaƙanta su.

          Kashi na biyu kuma su ne baƙin Al’adu irin waɗanda Hausawa suka koya bayan cuɗanyarsu da wasu baƙin ƙabilu musamman turawa. Irin waɗannan al’adun daga cikinsu akwai masu kyau, akwai kuma munana. To amma saboda bambancin addini da wayewar kai da ke tsakanin Hausawa da Turawa, munana da suka koya daga wurin turawa sun fi kyawawan yawa.

          Don haka ne a kullum suke ƙoƙarin kautar da ‘ya ‘yansu daga bin irin waɗannan al’adu.

          Shi kuwa Abdulƙadir Ɗangambo ga yadda ya bada ma’anar al’ada.

          “Al’ada ita ce abar da aka saba yi yau da gobe”   (Ɗangambo, 1980:38)

          Ya daɗa faɗaɗa tunaninsa in da ya ce akwai al’adu da ɗabi’u da yawa da Hausawa suke yi. Misali al’adu da suka shafi aure ko haihuwa da zumunci da sauransu. Ya kuma ƙara da cewa al’ada wani yanki ne na rayuwa. Ta ƙunshi wasu halaye da ɗabi’u da aka saba yi yau da kullum don rayuwa. Akwai masu kyau da marasa kyau.

          Shi kuwa Nasiru Ibrahim cewa ya yi Al’ada ita ce baki ɗayan hanyoyin rayuwar al’umma” (Yaro, 1997:3)

          Dangane da wannan bayani za a fahimci Al’ada ta haɗa baki ɗayan rayuwa tun daga haihuwa zuwa mutuwa. Don haka ma’ana babu girma babu ƙanƙanta har wayau babu Al’ada guda ɗaya ta dukkan al’ummomin duniya da ta yi kama da wata wannan shi ya haifar da bambance-bambance al’ada ta fara da alama tun ran gini tun ran zane, al’ada abu ne mai yaɗo, Kuma wanda yake tafiya da yanayin rayuwa. Al’ada ta danganci wasu abubuwa wanda ba za a iya gani ba, ballanta ma a taɓa don haka ta haɗa da abubuwa irin su matakan rayuwa da haihuwa da aure da mutuwa da hanyoyin gudanar da shugabanci. Hanyoyin tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Haka kuma al’ada ta tarar ta kuma daddasa duk ra’ayoyinta da halayyarta da sauran abubuwan da ta ƙunsa. Wannan zai haifar da canje-canje cikin al’adar da aka tarar, wato ta zama ta sake siffa, ko kuma mu ce ta sami gauraye. Irin wannan sauyi ya sami Hausawa da Hausa har sau biyu. Kashi na farko, Shi ne lokacin da musulunci da halayyar Larabawa suka shigo ƙasar Hausa, daga wajen ƙarni na 12/13 zuwa karni na 19 muka ga yadda suka shafi al’adun gargajiya na Hausa da rayuwar Bahaushe. Kashi na biyu kuwa shi ne mun ga yadda Turawa da wasu Al’adu nasu suka shigo ƙasar Hausa da kuma yadda suka shafi Hausawa a wannan karni na 20 (Ɗangambo,1984:1)  

3.3.1 IRE-IREN AL’ADA

Akwai rassan Al’ada guda bakwai.

1.     Addini : Abin bauta irin na gargajiya misali, kan gida ko tsafi da bori.

2.     Rayuwar Hausawa: Ta fannin sana’oin gargajiya misali farauta, noma kiwo.

3.     Tsarin zaman jam’a : Zamantakewa iyali na gidan yawa, tun daga kakanni da iyaye da  tattaɓa kunne.

4.     Shugabanci: Tun daga gida, Maigida, shi ne shugaba mai tsawatarwa har zuwa uwargida, sai a unguwa akwai mai unguwa da sauransu.

5.     Tattalin Arziki : Inda ake tanadi da adana hatsi (abinci) a rumbu don gaba da kuma asusu a ɗaki domin ajiye kuɗi.

6.     Bukukuwa da wasanni: Wanda ya shafi tun daga suna na haihuwa da aure, da mutuwa da sarauta da wasanni da ake yi a wannan lokaci.

7.     Magungunna: Na gargaji na magori na cututtuka iri-iri da na yan bori.

3.2 TARIHIN RAYUWAR ALHAJI MUSA ƊANƘWAIRO

     A wannan babi za a yi magana game da wasu muhimman rukunai na tarihin rayuwar Alhaji Musa Ɗanƙwairo tun daga bayanin haihuwarsa da ƙurciyarsa da yanayin kiɗansa da sauransu.

 

Alhaji Musa Ɗanƙwairo

                              Alh Musa Ɗanƙwairo Maradun (1909-1991)

3.2.1 SUNAN MAKAƊI DA LAƘABINSA

Sunan wannan makaɗi na yanka shi ne Musa wanda mahaifinsa ya zana masa lokacin da sati ya zagayo da haihuwarsa a ka yanka bisar suna aka raɗa masa suna da “Musa”.

Makaɗa Musa ya sami laƙabin “Danƙwairo” a sanadiyar sunan wani ƙanen mahaifinsa wanda ya yi tafiyarsa yawon duniya da ake kira “ƙwairo” shi ne dai ƙwairo yaron usman ne, kuma yana da zaƙin murya,amma daga baya sai ya bar kiɗa. To bayan da Musa ya kai kimanin shekara bakwai, sai ya soma karƃi  tare da mahaifin nasa, saboda yana da zaƙin murya kamar ƙwairo, sai makaɗa usman ya ce “ Ga Ɗanƙwairo kuma an mayas. Shi ken an sai sunan Ɗanƙwairo ya bi makaɗa  Musa ( Gusau,2005:104)

3.2.2  ASALIN IYAYE DA MAHAIFAN MUSA ƊANƘWAIRO

         Sunan mahaifin musa Ɗanƙwairo shi ne Usman Dan kwanda, mahaifiyarsa kuma ana kiranta ‘yarnunu wadda ta fito daga ƙauyen goran namaye a cikin karamar hukumar mulki ta maradun a cikin jahar Zamfara.

          Mahaifinsa kuma, wato usman dan kwanda mutumin dankado ne a cikin yankin karamar hukumar mulki ta Bakura, a jihar Zamfara.makaɗi Usman Dan kwanda yana kiɗan noma da na Saraki, sai sarkin ƙayan Maradun Ibrahim I (1903-1923) ya taso ya koma ƙasar Maradun ya zama makaɗin sa. Anyi wannan hijira ne lokacin da Ɗanƙwairo yake da shekara biyar da haihuwa watau shekarar 1914. (Gusau, 2015). 

3..2.3  SHEKARUN HAIHUWARSA

        Makaɗi Musa Ɗanƙwairo a bisa zance mafi rinjaye sahihin bincike dangane da inda aka hai fe shi  da kuma shekarar da aka haife shi ya nuna cewa shi makadi Musa Danƙwairo an haife shi ne a shekarar 1909 a ƙauyen ɗan kado cikin ƙasar Bakura ƙaramar hukumar mulki ta Bakura a cikin jihar Zamfara a halin yanzu.(Gusau, 2005).

3.2.4 ILIMINSA

       Dangane da iliminsa makaɗi Alhaji Musa Ɗanƙwairo a iya cewa Allah ne ya yi wa Danƙwairo gamon katar da fahimtar hanyoyin fasaha da hikima , amma bai sami damar shiga makarantar allo ba , haka ma kuma bai yi boko ba. Allah yakan ba mutun baiwar wani abu ba sai an koya masa ba. Sannan kuma yana da saurin fahimta da kuma ɗauke duk wani tarihin abubuwan da yake ji ga manya.

Wata ƙila wannan shi ne yake ba shi haske ga fahimtar madafar al,amuran da ke afkuwa yau da kullun.

          Ɗanƙwairo dai a taƙaice bai sami karatun allo ba balantana na zamani sai dai makarantar kiɗa kawai.(Gusau,2005:105).

3.3.5 RAYUWAR AURE DA IYALIN MUSA ƊANKWAIRO

(Gusau,2005:115) yace Alhaji Musa Ɗankwairo Allah ya albarkace shi da yin aure. yana da matar aure guda uku da ‘ya’ya goma sha bakwai (17), goma maza, bakwai mata. ‘ya’yansa maza su ne:

Alhaji Muhammadu (daudun kiɗa) – ya rasu

Alhaji Abubakar (daudun kiƙa -yanzu sarkin kiɗa)

Alhaji Abdu wakilin kida

Alhaji Sani marafan kida – ya rasu

Garba Ciroman kida

Umaru

Muhammad balarabe

Musa

Ibrahim

Umaru – ya rasu

           Huɗu daga cikin su watau, Umaru Muhammad Balarabe ,Musa Ibrahim  kidan noma suka yi:

  ‘Ya ‘yan mata kuwa sune:

Hauwa

Zalihatu

Habiba

Amina

Aishayu                                    

Sa’adatu da

Aminatu

Bayan haka da jikoki maza da mata dari da hudu (104).

3.2.6 FARA KIƊA DA WAƘA

Musa Ɗanƙwairo ya gaji kiɗa gaba da baya kuma ya buɗa ido a cikin sa. Ya fara koyon kiɗa a gurin ,mahaifinsa Usman tun yana ɗan shekara bakwai wato wajejen 1916.  A lokacin ya soma da kiɗan kanzagi har ya zo ya karbu kamar dai yadda ake koyon kiɗa.

Bayan mahaifinsa ya bar kiɗa sai ya hannuntashi ga wansa makaɗa kurna. Awurin Abdu Kurna ya naƙanci kiɗa sosai ya dinga binsa zuwa wajajen kiɗa daban-daban. Saboda hazaƙar Ɗanƙwairo sai Abdu Kurna ya bashi muƙamin Daudun kiɗa watau Ɗangaladimansa. Tun yana Dangaladiman kiɗa aka ga alamar taimaka wa Kurna bayar da waƙa da kuma ƙari gareta. (Gusau,2005:107)

  Mawaƙin ya yi wata waƙa   ta sarkin Maradun, “

Gindin waƙa:      Bubakar baban Baraya

                          Ya riƙa bai san sake ba

 

  Jagora           : Hawanai lafiya

  Y/Amshi        :Dattijo hawa nai lafiya sauka da girma.

A nan mawaƙin ya nuna mana cewa shi yana ƙari kuma yana yin amshi ga ɗiyan waƙa.

Musa Ɗanƙwairo duk lokacin da ya sami sauli ba a zuwa wani rangadin kiɗa ko zuwa yammaci, sai ya dinga waƙoƙin noma tare da yara yan’uwansa.Amma duk lokacin daya dawo yawon gayauna yana nuna duk abun da ya samo.

Yana cikin wannan hali, sai makaɗa Kurna ya ba shi izini ya fara yi wa ya’yan sarakuna waƙa don ya saba da kiɗan sarakuna. Waƙar da ya fara yi ta ya’yan sarakuna ita ce wadda ya tafi tare da uwargidansa Zemo tana yi masa amshi. Ga waƙar:

Gindin Waƙa: Dan sarki a gode maka

                       Jikan dodo ɗan gwamma

 

 Jagora:       Ya tafi daji ba shi komawa

  Y/Amshi:     Kullum daga duƙe sai duƙe

                      Gyado mai ƙoƙarin gaske

 

Jagora:          Mijin diya jikan Nomau

                     Gwarzon Ango karsanin Ali

                     Gungaman Iro ɗan jatau

  Y/Amshi:    Kullum daga duƙe sai duƙe

                      cayaɗo mai ƙoƙarin gabce

                      (Gusau,2005:107-108)

3.2.7 KAYAN KIƊANSA

Makaɗa musa Ɗanƙwairo tun lokacin da ya fara koyon kiɗa yana amfani da Kotso ne a matsayin abin kiɗansa. Ɗanƙwairo mahaifinsa makaɗin fada ne tun asali kuma kayan kiɗansa shi ne kotso. Hakama wansa watau Abdu kurna da mahaifinsu ya ba izinin yin kiɗa shi ma da kotso yake yin kiɗansa.

Haka kuma lokacin da Ɗanƙwairo ya yi kiɗan noma ya yi amfani kayan kidan da ake kira farar “ganga” da ita ce ya yi amfani a wajen kiɗan noma.

 Makaɗa Usman mahaifin Ɗanƙwairo shahararren makaɗi ne na noma a Bakura tun kafin ya koma ƙayan Maradun.

 Kuma yana haɗawa da kiɗan saraki. Sannan yana amfani ne da kayan kiɗan da ake kira farar “ganga” da “kotso” shi ma waɗannan ya gaje su ne tun daga nasa mahaifin watau Makaɗa kaka wanda ya yi kiɗan yaƙi da na noma. Saboda haka kayan kiɗan da Ɗanƙwairo ya yi amfani da su a wajen sana’arsa ta kiɗa da waƙa su ne farar ganga a wajen kiɗan noma, sai kuma kotso a wajen kiɗan saraki wanda da

shi aka san shi har ya barkiɗa ya koma ga Allah mahaliccinsa.

(Gusau,2005) 

3.2.8 IRE-IREN WAƘOƘINSA

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo yayi waƙoƙi da dama ta fanni iri-iri, ya kuma yi waƙoƙi masu ɗinbin yawa waɗanda shi kansa ya tabbata bai iya ƙiyasta adadin yawansu. Amma a dunƙule dai ire-iren waƙoƙin daya yi su ne.

 

                   :Waƙoƙin noma

                   :Waƙoƙin ta’aziyya

                   :Waƙoƙin siyasa  

                   :Waƙoƙin gargaɗi da faɗakarwa

                   :Waƙoƙin jama’a

                   :Waƙoƙin fada na sarakuna.

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙoƙin noma wanda muna iya cewa su ne ya fara yi tun lokacin wata waƙa da ya yi ta noma mai Gindin waƙar.

Gindi:       :Dan sarki a gode maka

       :Jikan dodo ɗan gwamma

 

    Y/Amshi:        :Ya tafi daji bashi komawa

       :Kullun daga duƙe sai duƙe

       :Mijin diya jikan nomau

                                      :Gwarzon ango karsanin Ali

Ga kuma misali wata waƙa mai suna waƙar noma.

            Jagora:         Noma babba sana’a

            Y/Amshi:      Koway yi ta ya bar rasawa

 

 

Jagora :           Ku zan aje noma daidai ne

             Kowa aje gero da dawa

            Kuzan tsare noma daidai ne

       Y/Amshi :       Kowa aje gero da dawa

          Wannan ya debe takaici

Waƙar ta’aziyya: makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi waƙar ta’aziyya inda ya yi wa Sir Ahmadu Sardaunan Sakkwato waƙa, yana cewa:

 

Jagora:Ya wuce reni ba a yi mai shi

 Amadu jikan Garba Sadauki

Daudu:Farimiyan jihar Arewa Ahmadu

 Abin da kai ma Nijeriya

Har ƙasa ta naɗe, ana tuna ka

Ahmadu jikan

Y/Amshi: Bawan Allah Gamji ɗan ƙwarai

     Gohe Allah

    Malam Gohe, Allah gafarta ma.

Waƙoƙin siyasa: Ɗanƙwairo ya yi waƙoƙin siyasa. Ga misali wata waƙa da ya yi ta siyasar N.P.N sunan waƙar jam’iyar siyarsa N.P.N mawaƙin na cewa:

Gindin waƙa: Jamiyar N.P.N

  Aminci dai N.P.N

Y/Amshi:    Ku ya da karya

 

Jagora :        Ku kamma gaskiya X2

Y/Amshi:    ku ya da karya,

Ku kamma gaskiya X2

Karku sake don Allah

Mutane kar ku sake don Allah.

                               Waƙoƙin Gargaɗi da faɗakarwa:

Mawaƙin ya yi waƙoƙi da damna gargaɗi da faɗakarwa zuwa ga jama’a ga misalin wata waƙa da ya yi inda yake cewa:

Gindin waƙa:             Mu bi al’adunmu na gargajiya

  Kar mu sake mu mance

Mu bi al’adunmu na gargajiya

Kasan arewa Babbar riga

Ga rawani da taggo

Mu bi al’adunmu na gargajiya

Waƙoƙin jama’a: makaɗa Ɗanƙwairo ya yi wa jama’a da yawa waƙoƙi. Ga misalin ɗaya daga ciki. Waƙar Alhaji Bello maitama Yusufu.

Gindin Waƙa: Minista na ciniki

          :Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf

 

Jagora :                   :Kai minista na ciniki

Y/Amshi :               :Allah ya isam ma Bello maitama yusuf

 

Jagora :                 :Taho ga ka ga maza

Y/Amshi:                : Wandara uban Akke Ado sarkin fada

:Minista na ciniki

:Allah ya isam ma Bello maitama yusuf                      

          Sai kuma waƙoƙin fada na sarakuna inda a nan ne ya shahara kuma a cikin wannan kashi aka saka shi. Watau makaɗin sarakuna, a cikin rabe-raben mawakan Hausa ya yi waƙoƙin sarauta da dama. Ga misalin daya daga ciki. Waƙar Aliyu yandato II.

Gindi waƙa :Bida arna bai yarda a kai mai wargiba

          Mai wuyya gaba ya hana karya yandoto

 

Jagora:        Dansabagadi na jekada ya nike maza

Y/Amshi:   Waddara sun lakkwata,duk sun yaushi

       Dansabagadi na jekada ya hada maza

      Waddara sun lakkwata,duk sun yaushi

      (Gusau,2005:108)

3.2.9 MATSAYIN KIƊA A WAJENSA

  Hausawa na cewa: “Gado malan” Musa Ɗanƙwairo ya dauki kiɗa da waƙa a matsayin gado. Saboda ya gaji kiɗa a wajen mahaifinsa.

  Haka kuma waƙa a wajen Musa Ɗanƙwairo ya nuna cewa sana’a ce a wajensa. Saboda ciki ya ke ci kuma ciki yake sha.

3.2.10 TAFIYE- TAFIYENSA.

   Tafiya mabuɗin ilimi inji Hausawa. A sanadiya sana’ar kiɗa makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi tafiye-tafiye da dama. A wannan dalili ne na kiɗa da waƙa Ɗanƙwairo ya riƙa bin sardauna Ahmadu har Kaduna yana yi masa waƙoƙi.

Don haka anan gida Nijeriya Ɗankwairo ya yawata garuruwa da birane da dama tun a garinsu Maradun da Tsahe, da Sakkwato, da Daura, da Kano, da Jalingo, da Gwambe, da Bauchi, da Barno, da Muri, da dai sauransu.

3.3 NAƊEWA

Mun gabatar da shimfiɗa munyi ma’anar Al’ada da ra’ayoyin masana da ire-iren al’ada da kuma naɗewa duk acikin babi na uku.

 

 

 

BABI NA HUƊU

 LALUBEN AL’ADUN HAUSAWA A CIKIN WASU WAƘOƘIN ƊANƘWAIRO

4.0 SHIMFIƊA

 Babin yana magana ne a kan Al’adun Hausawa da kuma lalubo wasu waƙoƙi a cikin waƙoƙin Musa Danƙwairo sai dai Al’adun suna da yawa an lalubo kaɗan daga ciki.

4.1 AL’ADUN HAUSAWA         

Kamar yadda bayani ya gabata, duk abubuwan da akasarin jama’a na kowace al’umma su ka amince da yin su, ko yin amfani da su ko suka yarda da su, sune al’adunsu. Idan waɗannan abubuwa sun yi zaune da gindinsu, bayan sun samo asali tun daga kaka da kakanni, shi kenan sun zama al’adun gargajiya. Da zarar al’ada ta kafu, ta zama ta gargajiya, yana da wuya a tumɓuke ta farat daya.wannan ya sa da yawa, akan yi ta ɗauki-ba-ɗadi kafin a sami damar kasha wata al’ada ta gadon-gado Alal misali, duk da girman tasirin zuwan turawa ƙasar Hausa da yawa daga cikin al’adun Hausawa na gargajiya, ba su yi wata sakewa ta a zo a gani ba.

          Al’ummar Hausawa mutane ne masu tsananin riƙo da Al’adunsu na gargajiya, sai dai kuma al’ada aba ce mai rai wadda take tafiya tare da lokaci ko zamani. Don haka tana iya samun gauraya da wasu baƙin al’adun har su ka ga karƃuwa ga wannan al’umma, kusan wannan dalili ne ya haifar da karkasuwar ko rarrabuwar al’adun har zuwa gida uku, wato al’adun gargajiya da gaurayayyin al’adu da kuma baƙin al’adu a tsakanin al’ummar Hausawa da kuma cikin ƙasar Hausa. (Mu’azu,2013:2)

4.2 LALUBEN AL’ADUN HAUSAWA A CIKIN WASU WAƘOƘIN ƊANƘWAIRO

   A wannan babi za a lalubi wasu Al’adun Hausawa waɗanda Musa Ɗanƙwairo ya faɗi a cikin wasu waƙoƙinsa tare da yin taƙaitaccen sharhi na manufar da ta ke ƙunshe a ciki. Hakan ce za ta bamu hasken gane cewa Ɗanƙwairo makaɗin baka na Hausa ne da ya taimaka wajen raya da taskece wasu al’adun al’ummarsa.

4.2 WASU AL’ADUN HAUSAWA

          Al’adun Hausawa suna da yawa ga kaɗan daga cikin su.

v Neman Aure- kayan toshi, kayan zance, dukiyar aure, kayan lefe, Daurin  Aure, Sa rana , garar Aure sa lalle, kamu, wankan Amarya tarewa da sauransu.

v Haihuwa- akwai Al’ada kamar haka goyon ciki,kayan kauri, zanen suna, gara, reno, yaye, kaciya, wankan biki da sauransu.

v Mutuwa- zaman makoki,itama wannan Al’ada ce tana ɗauke da wasu al’adu da ake yi sun hada da zaman makoki ta’aziya takaba, wankan gawa, sutura da sauran su.

v Addini : Bangaren addini kuwa akwai addinin gargajiyar Hausawa suna da abubuwan bauta kamar iskoki,magiro, gajimare, tsinburbura da sauransu.

v Abinci : Hausawa suna da abincinsu na gargajiya wadan suke amfani da shi a rayuwar su tayau da kullum kamar irinsu tuwu,hura, danbu, wake, danwake wasa wasa da sauransu.

v Bukukuwa : Suna daya daga cikin ire-iren Al’adun da Hausawa suke gudanar wa a rayuwar su ta yau da kullum sun hada da Bukin budar kai, bukin budar daji, kalan kuwa, bukin kaciya, bukin aure, haihuwa da sauransu.

v Wasanni : suna daga cikin Al’adar da Hausawa suke gudanarwa a rayuwar su, sun hada da wasannin da yara suke a tsakanin su na kwaikwayon abubuwan  da manya

sukeyi kamar wasar yar tsana, wasan kalan kuwa, dabo dabo, dan akuyana daku aya, da sauransu.

v Sana’o’i : itama sana’a wata al’ada ce da Bahaushe yake gudanar wa domin samun abun masarufi a rayuwar sa ta yau da kullum. Akwai sana’ar noma,farauta, kiyo, kira, saka, dukanci, jima, fawa, kadi,dilanci da sauransu

v Mulki: shi ne shugabanci na jan ragamar al’uma. Wannan wata al’ada ce da Hausawa suke yi ta hanyar naɗa wani daga cikin su don ya zama shugabansu, tun daga maigida da iyalan sa. Akwai shugaban gida wato, mai gida da kuma shugaban al’umma, wato sarki da kuma shugaban wasu ƙungiyoyi, da kuma shugaban masu wata sana’a da kuma shugabannin siyasa, da sauransu.

v  Taimako: Taimako wata dabiace ta Bahaushe, taimako na nufin ka agaza ko ka      taya wani yin wani aiki Bahaushe yakan agazawa gajiyayye ko kasasshe ko mabukaci.

v  Atakaice waɗannan su ne kadan daga cikin ire-iren Al’ada Bahaushe, wadda yake gudanarwa a rayuwarsa ta yau da kullun.

 

4.2.1 AL’ADUN HAUSAWA A CIKIN WASU WAƘOƘIN MUSA ƊANKWAIRO

          Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya ambaci wasu Al’adun Hausawa a cikin, wasu waƙoƙinsa. Akwai inda yake ambatar wata sana’a babba ta Bahaushe wato noma.

4.2.2 Noma : Noma na ɗaya daga cikin al’adar Bahaushe wadda ta shafi sana’arsa da ya fara yi a doron ƙasa lokacin da  ya gama yawonsa na farauta.

To idan muka duba makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya nuna wannan Al’ada ta sana’ar noma a cikin waƙar da ya fara yi ta ya’yan sarakuna. Mawaƙin na cewa.

Gindin waƙar

Ɗan sarki a gode maka

Jikan Dodo ɗangwamma

 

Jagora:         Ya tafi daji bashi komowa

Y/Amshi :    Kullun daga duƙe sai duƙe

Gyaɗo mai ƙoƙarin gaske. ( Gusau,2019 :54)        

A nan makaɗin ya nuna mana cewa Bahaushe yana da wata Al’ada ta yin noma a matsayin wata sana’a da zai yi domin samun abincin rayuwa. Kalmar duƙe tana nufin noma,Kamar yadda Bahaushe yake cewa

“Na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar.”

Har a ciki ya ƙara cewa:

Jagora :        Jikan Namadi kullum ango

Y/Amshi:      Karsanin Ali

Gungaman Iro dan Jatau

Kullun daga duƙe sai duƙe

Gyaɗo mai ƙoƙarin gabce.

Dan sarki a gode maka

Jikan Dodo ɗan Gwamma. ( Gusau 2019:54)

Abincin Hausawa shi ma wani nau’i ne na al’adun Hausawa. A cikin waƙar Aliyu na II  wato ‘Yandoton Tsafe mawaƙin na cewa:

Gindin Waka : Bi da arna bia yarda

                             : A kai mai wargi

                             : mai wuyan gaba

                             :Ya hana karya “Yandoto”

 

          Jagora :                 :Wani ya barkace

                             : Yana shawagi biɗak kaɗe

                             : Aljihu twake da kashin bauna

 

Jagora:                  Iko ya yi

Y/Amshi               : Gardama, ɗan sarki na bisa kaiwa kullum

 

Jagora         :         : Ina abu !

                             : Bi da arna bai yarda

                             : A kai mai wargi ba

                             : Mai wuyya gaba

                             : Ya hana karya ‘ Yandoto

          A nan kaɗe da kaiwa duk wani nau’in abinci ne na Hausawa,  A cikin ƙamusun Hausa,(Hausa. (2006 : 223) an kawo ma’anar kade da (1) Kadanya (ii) ko mai wanda ake samu daga ‘ya’yan kadanya ‘ Kaiwa’ kuma tana nufin ‘ya’yan kanya. (ƙamusun Hausa 2006 : 226).

Jagora : Naɗe mani sarkin kiɗi

Y/Amashi                       : Na jekada, mui ta duniya

                                      ; Kurna naga sarkin ƙaya

                                      : Danƙwairo makaɗin ‘yandoto’

                                      ; Bi da arna bai yarda

                                      : A kai mai wargi ba

                                      : Mai wuyag gaba

                                      : Ya hana ƙarya ‘yandoto.

 4.2.3 Ubangida: Wannan wata al’ada ce da aka san mawaƙan Hausawa suna da iyayen  gida. Waɗanda su ke ɗauke da nauyinsu. Wannan al’ada ta fito a cikin wata waƙa da Musa Ɗanƙwairo ya yi wa Alhaji ‘Yandoton Tsafe.

          A nan munga cewa shi Kurna mawaƙin sarkin ƙayan Maradun ne, shi kuma ƙanensa watau Musa Ɗanƙwairo makaɗin ‘Yandoton Tsafe ne, Aliyu ‘Yandoto na II. Idan mun duba wannan al’ada ce ta ta galibin sarakunan  ƙasar Hausa.

4.2.4 TA’AZIYYA: Al’ada ce ta Hausawa idan mutum ya ƙaura, ko kuma ya rasu to ana yin ta’aziyya, ko gaisuwa da nuna alhini na rashinsa.To an samu haka a cikin waƙar ta’aziyya ta marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Mawaƙin na cewa:

Gindin waƙa:

Gindin waka:   Ya wuce raini ba a yi mai shi,

Amadu Jikan Garba Sadauki,

 

Jagora :           Firimiyan jihar Arewa Amadu

Abin da kai ma Nijeriya,

Hak ƙasa ta naɗe, ana tuna ka

Y/Amshi :       Amadu Jikan bawon Allah

Gamji ɗan ƙwarai

Gohe Allah,

Malam Gohe, Allah gafarta ma.

Jagora :           Malam

Y/Amshi :         :Amadu Allah dai ya jikai nai

 

Jagora :            :Gaba ta wuce,

:Yanzu a samo wani kamatai

:Ya wuce rani ba a yi mai shi

:Amadu jikan Garba Sadauki

          To mun ga makadin yayi addu’a irin ta ta’aziyya haka ya fito a cikin wannan ɗiyan waƙa guda 2 da ya yi wa Sardaunan Sakkwato, Ahmadu Bello.

4.2.5 GADO: Wannan shi ma wata Al’ada ce ta Hausawa idan magabaci ya rasu sai ya samu wanda zai gaje shi. To haka ta samu a cikin wata waƙa da Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi wa ‘Yandoton Tsafe. Mawaƙin na cewa:

Jagora             :Batun kiɗi ko ba ku nan yi mu kai,

:Kun karantar da mu,

:Mun yi kiɗan baki,

:Mun yi wasulla, mun yi tayi

:Yanzu ilmi mukai tun da mun sabka

:In hwa waƙa ce,

:Duk mun san yadda za mu ƙulla ta,

:In ance mutum mai tujara ne,

:Sai ya haihuwa da mai tujaran nan,

:In Allah ya ba mutum kwazo,

:Ya bar haihuwa da nai ya lalace

:Tun da gado ne

:Mun gani tun ga diyan masara,

:Abun goye kowa da gemu nai.

          To anan mun ga Kalmar gado ta fito a cikin wannan waƙa. Gado kamar yadda aka bayyana a ƙamusun Hausa (2006: 149) yana nufin, dukiyar da mamaci ya bari ko muƙami ko hali ko sifa ko kaya da mutum ya gada. Don haka anan za mu ce Musa Dankwairo yana nuna wannan sana’a ta kiɗa gadar ta suka yi sun kuma ƙware a cikinta, sun gaji muƙamin yi wa sarakuna waƙa, sun gaji kiɗan kotso da yanayin aiwatar da waƙar gaba ɗaya.

Idan ba a manta ba a can baya an yi bayanin yadda ya gaji kiɗan daga kakanni da iyaye har ma da wansa Kurna. Wannan Al’ada ta gado, Al’adar Hausawa ce tun kafin musulunci sai dai da musulunci ya zo ta tsara yadda gado yake saƃanin yadda yake a al’ada.

Gindin waƙa:

    :Kar mu sake mu mance

    :Ku bi al’adunmu na gargajiya

    :Mu bi al’adunmu na gargajiya.

 

          Jagora :   Kyawon Dan arewa  Babbar Riga

   :Ga rawani da taggo

  :Mubi al’adunmu na garagajiya.

Anan mun ga cewa riga da taggo da rawani duk sutura ce ta Bahaushe. Wanda kuma sutura na ɗaya daga cikin kayan Al’ada na Hausawa, mun ga yadda suka fito a cikin wannan waƙa ta Alhaji Musa Ɗanƙwairo.

          Bangaren addinin musulinci kuma an san Bahaushe da al’adar riƙa tasbaha (carbi) domin roƙon Allah. Ɗanƙwairo ya ambaci cewa a riƙa amfani da tasbaha a cikin wannan waƙa tasa ta al’adun gargajiya. Inda yake cewa:

 

Jagora:                  :Kai abun ga ya ban takaici

:Abun ga ya ban takaici

:Sai ka ga ɗan Musulmi

:Da wandon yadi guda

:Ga‘yar shat ya sa ga wuyanai

:Ba hulla ga kai nai

:Aljihu nai ba tasbaha

Y/Amshi :              :  Sai kwalin sigari.

Idan mun dubi wannan ɗan waƙar Ɗanƙwairo ya Ambato kayan Al’ada na Hausawa kamar Hulla, da kuma tasbaha.

4.2.6 LULLUƁI: Shi ma ɗaya ne daga cikin al’adar Hausawa musamman ga matan Hausawa, idan za su fita.To haka ya fito a cikin wannan waƙar ta Al’adun gargajiya.    Inda mawaƙin ke cewa:

Jagora :                :Ku ko matan ƙasarmu

:Waɗanda suke ɗiyan musulmi

:Ku zanka yin lulluɓi

:Ban da, sayen ‘yakkanti

:Banda sayen ‘yakkant

:Kuna ta yawo rariya-rariya

 

Jagora                  :Abin ga ya bada kunya.

 

4.2.7 ABINCI: Duk a cikin waƙar ya ƙara kawo abincin Hausawa na Al’ada. Inda yake cewa:

 

Jagora :                Inda haka gaskiya ne

:Ku mance hura da nono

:Sannan ku mance Tuwo da nama

Y/Amshi :                 Mu bi al’adunmu na gargajiya,

:Kar  mu sake mu mance,

:Mu bi al’dunmu na gargajiya.

  Tuwu da miya abincin Hausawa ne wanda suke ci suke sha hura da nono ma haka abincin Hausawa ne da suke sha domin maganin yunwa wadannan sune abincin Hausawa na Al’ada.

4.2.8 SANA’A: Sana’a Sa’a inji Hausawa, wata babbar al’ada da Alhaji Musa Daƙwairo ya ambata a cikin wata waƙa da ya yi mai suna “Noma babbar Sana’a” mawaƙin na cewa:

Gindin waƙar:

:Noma babbas sana’a

:Kaway yi ta ya bar rasawa X 2

Jagora :                Ku zan aje noma daidai ne

:Kowa aje gero da dawa

:Ku zan tsare noma daidai ne

Y/Amshi :              :Kowa aje gero da dawa

:Wannan ya ɗebe takaici.

:Noma babas sana’a

 

Jagora ;                :Taimaki bayin ka Allah

:Allah kai a mai iyawa.

:Noma babbas sana’a

4.2.9 ROƘO: Roƙo shi ma wata al’ada ce musamman ga mawaƙanmu na Hausa. Mun ga haka a cikin  waƙar  “Alhaji Shehu Shagari, Tsohon Shugaban ƙasa”.

Gindin waƙar:

Shugaban ƙasa jikan Sule,

Wada duk aka so ya kai,

 

Jagora:                 Sarkin Gwaram

Y/Amshi:               Waziri ban rena mai ba,

 

Jagora :                :Alhaji Baba Umar

                             :Ya rabbana ya kara wadata ka

Jagora                  :Umaru jikan mamman

Y/Amshi:              Ya rabbana ya ƙara wadata ka

 

Jagora :                Na zo ka ba ni mota,

Albarkacin girman mai girma,

Na zo ka bani mota ta hawa,

Darajar girman maigirma.

To anan munga cewa duk wata ɗabia ce mawaƙan Hausa, idan suna waƙa sukan roƙi abu ga waɗanda suke yi wa waƙa. Ko a bayyane ko a boye. To wannan ita ma wata Al’ada ce ga Hausawa.

Gindin waƙar:

Na Alhaji Abba mijin maza

Na yadda da Ado Ɗandawaki

Jagora                  Kai ne mulki ne ilmi

Ba a hika taimako ba Addo

Alhaji Ado ka yi komi

 

Jagora :                Dan dattijo

Y/Amshi:               Ni Alhaji Ado ka yi komi

 

Jagora                  Taimaki gazajje

                             Taimaki maraya

Y/Amshi:               Alhaji Ado Ɗandawaki

 

Jagora :                Ya bai wa gazajje

Ya bai wa maraya

Y/Amshi:               Alhaji Ado Ɗandawaki

 

Jagora                   Ka ba kuturu

Ka ba makaho

Y/Amshi                Alhaji Ado Ɗandawaki.

 

          Gazajje da maraya da kuturu da makoho duk masu neman taimako ne, don haka Danƙwairo ya nuna Alhaji Ado Dandawaki yana taimaka musu, ya kuma yabe shi saboda wannan al’ada ta taimako.

     A taƙaice waɗannan al’adu da muka tsakuro  muka lalubo a cikin wasu daga waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, Sun isa zama hujja waƙoƙin makaɗin cike suke da Al’adun Hausawa waɗanda za a yi alfari da su a kuma nunawa duniya.

 

4.3 NAƊEWA

Mun gabatar da shimfiɗa a babi na huɗu Al’adun Hausawa da ire-iren al’ada da laluben wasu al’adu a cikin wasu waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Maradun duk a cikin babi na huɗu.

 

 

 

 

 BABI NA BIYAR

                                                SAKAMAKON BINCIKE

5.0 SHIMFIƊA

          A cikin wannan babi za a kawo bayanai ne waɗanda suka ƙunshi taƙaitaccen bayani dangane da wannan bincike da aka gabatar, sai kuma sakamakon da binciken ya gano.

          Wannan bincike ne mai suna laluben wasu Al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Danƙwairo Maradun. A wannan aikin an yi gabatarwa dangane da muhimman matakai masu nuna alƙiblar da aikin ya dosa kamar taƙaitaccen bayani akan waƙoƙin baka na Hausa da nuna cewa suna cikin ƃangaren adabi. Haka kuma an kawo muhimmancin kiɗa da waƙa a ƙasar Hausa. Wannan aiki kuma ya kawo laluben wasu al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo.

          A babi na ɗaya haka kuma an kawo dalilin bincike da manufar bincike da iyakancewar bincike da hanyoyin da muhimmancin bincike sai matsalolin bincike da kuma naɗewa.

   A babi na biyu daga nan sai aka yi bitar ayyukan da suka gabaci, wannan binciken a matakan ilimi mabambanta kamar rubutattun littafai da muƙalu da kuma kundayen bincike.

   A babi na uku daga nan kuma sai aka bibiyi ma’anar Al’ada da ire-iren al’ada da tarihin rayuwar Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun. Kamar sunansa da laƙabinsa da asalin iyayensa da shekarun haihuwarsa da iliminsa da kuma bayanin rayuwarsa ta aure watau, iyalansa da lokacin daya fara kiɗa da waƙa. Haka kuma an kawo nau’in kayan kiɗansa da ire-iren waƙoƙinsa tare da nuna matsayin kiɗa a wajensa da kuma bayanin tafiye-tafiyen da ya yi a lokacin da yake gudanar da wannan sana’a ta kiɗa da waƙa.

   A cikin babi na huɗu a wannan bincike an kawo bayani akan al’adun Hausawa, da ma’anar al’ada da kuma ire-iren al’adun Hausawa haɗi da kawo laluben wasu al’adu a cikin wasu daga waƙoƙin makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun.

          Daga nan sai wannan bincike ya zo da jawabin kammalawa, sai kuma taƙaita bayanin bincike da sakamakon abin da binciken ya gano sai manazarta.

5.1 SAKAMAKON BINCIKE:

1.     Angano makaɗa Ɗanƙwairo mutum ne mai iya fito da Al’adun Hausawa a cikin waƙoƙin sa

2.     Makaɗa Ɗankwairo yana nuni da ƙyawawan Al’adun Hausawa da nufin zaburarwa.

3.     Waƙoƙin na sa ma’adani ne na ƙunshe Al’adun Hausawa musamman na gargajiya.

4.     Waƙoƙin nasa tamkar madubi ne ga masu son sanin Al’adun Hausawa.

 

5.2 SHAWARWARI

     A sakamakon binciken da aka gudanar a kan laluben al’adun a wasu waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Maradun da irin tasirin da suke da shi ga rayuwar al’adun Hausawa. Binciken na ba da shawarwari kamar haka:

-         Dalibai manazarta waƙoƙin Hausa su dage wurin gudanar da bincike kan waƙoƙin Hausa da ake da su domin fito da irin gudunmuwar da suka bayar wa da jawo hankalin matasa don kulawa da al’adun gargajiya.

-         Shawara ga makarantun sakandare har zuwa na manyan makarantu na jami’oi da su rika taskace ire-iren waɗannan waƙoƙin domin saƙonnin da suke ciki na bunƙasa al’adu.

5.3 NADEWA

    A ƙarshen wannan babi na biyar anyi taƙaitaccen bayani dangane da binciken da aka gabatar sai sakamakon bincike, wannan bincike mai suna Laluben Al’adu a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun anyi shimfiɗa,an kawo mahimmancin kiɗa, ankawo dalilan bincike sai bitar ayyukan da suka gabata, tarihin makaɗi da laƙabinsa duk a cikin babi na biyar.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

                                                    MANAZARTA

Adamu Aisha Ismail (2002) “ Salo da Sarrafa  Harshe a cikin Wasu Waƙoƙin       Jam’iyyun A.N.P.P da P.D.P a Jihohin kano da jigawa kundin digiri na Biyu. Sashen koyar da harsunan Nijeriya. Kano Jami’ar Bayero.

Ammani, M. (2009) Nazarin Maganganun Hikima a Waƙoƙin Aliyu Ɗandawo kundin digiri na biyu sashen koyarda harsunan Nijeriya. Kano. Jami’ar Bayero.

Auta, A.L (2017) Fadarkarwa a Rubuttattun Waƙoƙin Hausa. Kano. Jami’ar    Bayero.

Bello A. M da Bashir I. (2004) Harshe da al’adun Hausawa, sashen koyar da  Harsunan Nigeria.Kano : FCE

Bunza, M.A (2006) Gadon Fede Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeriya limited

Bunza, M.A. (2009) Narambada. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre    Limited.

Dangambo, A. (1984) Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar       Hausawa. Kano:  Triumph Gidan sa’adu zungur.

Dangambo, A. (2007) Daurayar Gadon Fede waƙa. Kano: Amana Publishers.

Dangambo, A. (2011) Rabe-Raben Adabin Hausa (Salon Tsari) Zaria; Amana Publishers.

 

Garba, M. (1998 “ Azancin Magana a Waƙoƙin Makadan Baka. Kundin Digiri na    Biyu. Sashen koyar da Harsunan Nijeriya Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M (2002) Salihu Jankidi Sarkin Taushi. Kaduna: Baraka press and     Publishers.

Gusau, S.M (2005) Makada da Mawakan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, U.G. (2012) Bukukuwan Hausawa Gusau. Ol-faith Prints.

Gusau, S.M (2013) Dangantakar Waƙoƙin Baka da Al’adun Hausawa: Bunƙasa ko Koma-baya Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzi’i na Biyu. Kano: Century Research and Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2015) Abdu Karen Gusau. Kano: Century Research and Publishers   Limited.

Ibrahim M.S (1985) Dangantakar Al’ada da Addini; Tasirin Musulunci kan Rayuwar  Hausawa ta Gargajiya” Kundin Digiri na Biyu. Kano Jami’ar Bayero.

Magaji, A. (Babu shekara) Wasu Al’adun Hausa: Yanaye-Yanayensu a Ƙasar Katsina. Kundin Digiri na uku. Kano, Jami’ar Bayero.

Ma’azu, A. (2013) Bakin Al’adu a Kagaggun Littafan Soyayya Na Hausa. Zariya. Ahmadu Bello University Press Limited.

Sankalawa, I.B (1994) Nazarin Rayuwar Makaɗa Sani Sabulu Kanoma da Falsafar Waƙoƙinsa. Kundin Digiri na Ɗaya. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Umar, M.B. (1987) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph.

Yahaya, I.Y da Dangambo, A (1986) Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publishers Company Limited.

Yakasai, A.S (2003) “Sadarwa Tsakanin Maza da Mata: Nazarin Dangantakar Harshe da Daidaituwar Jinsi” Mukala day a gabatar a taron kara wa Juna Sani, Sakkwato. A sashin koyar da harsunan Nigeria Jami’ar Usman Danfodiya.

Yakubu, G (2012) Adon Harshe a Waƙoƙin Mamman Shata na Masu Sarauta Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya. Kano: Jami’ar Bayero

Yahaya A. D, (1980) The Authority System in Northern Nigeria (1950 – 70) Zaria, Ahmadu Bello University Press Yohanna, S. (1988) the Colonial State.

Yaro, S. A. (1997) Development of Pressrout For The Beneficial of Mallam Ayuba Manganese deposit to penomanganese feedcwado. PHD thesisi ABU Zaria Unpublished.

                          

 

 

 

 

 

                                  RATAYE NA 1

                             Waƙar al’adun gargajiya.

Gindin waka:          : Karmu sake mu mance

                               :Mu bi al’adunmu na gargajiya X2    

Jagora                   :Mu bi al’adunmu na gargajiya

Y/Amshi                :Kar ku sake ku mance,

 Mu bi al'adunmu na gargajiya. X2

 

Jagora :                 :Niyyah kai !

Y/Amshi               :Karmu sake mu mance

                             :Mu bi al’adunmu na gargajiya X2 

 

Jagora :                 :Kyawon Ɗan 'arewa babbar riga,

:Ga rawani da taggo,

Y/Amshi :              :Mu bi al’adunmu na gargajiya.

 

Jagora :                 :Kyawon Ɗan arewa babbar riga,

Y/Amshi :             :Ga rawani da taggo.

 

Jagora :                 :Ko ranar suna,

:Ko Jumu’a ka ɗauka,

:Mu bi al’adunmu na gargajiya.

Y/Amshi :             :Mu bi al'adunmu na gargajiya,

:Kar mu Sake mu mance,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

 

Jagora:                  :Yan'arewa da an nan,

:Waɗanda ad ɗiyan Musulmi,

:Ƙwairo na gargaɗinmu,

:Ku zan azumi da sallah,

:Ku zan kono da zakka,

:A zan azumi da sallah.

Y/Amshi :             :Ku bi al'adunmu na gargajiya,

:Kar mu sake mu mance,                                  

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

 

Jagora:                  :Ku ko matan kasarmu,

:Waɗanda suke ɗiyan Musulmi,

:Ku zanka yin lulluɓi,

:Ban da sayan yarkanti,

:Kuna ta  yawo rariya-rariya,

:Abin ga              

Y/Amshi:              :Ya ba da kunya,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

:Kar mu sake mu mance,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

:Ku ko matanmu Arewa,          

:Waɗanda ad ɗiyar Musulmi,

Jagora                   :Ban da sayan siket da "yarkanti,

:Kuna yawo rariya-rariya, abin ga ya ba,

Y/Amshi :             ;Mu kunya,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

:Kar mu sake mu mance,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya. x2

 

Jagora :                 :Abin ga da ban takaici, x2

:Sai ka ga ɗan Musulmi,

:ga wandon yadi guda,

:Ga 'yar shat ya sa ga wuyana,

:Ba hula ga kai nai,

:Aljihu nai ba tasbaha sai,

Y/Amshi:              :Sai kwalin sigari.

 

 

Jagora:                  :Aljihu nai ba tasbaha,

Y/Amshi:              :Sai kwalin sigari,

:Mu bi al adunmu na gargajiya.

 

Jagora :                 :"Yan'arewa Musulmi,

:Kun ce ba ku son babbar riga,

:Ina ganin ku,

:Kun ce ba ku son babbat taggo,

:Ina ganin ku,

:Kun ce ba ku son babban wando,

:Ina ganin ku,

:To, in haka gaskiya ne,

Y/Amshi :             :Ku mance hura da nono,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya,

:Kar mu sake mu mance,

:Mu bi al’adunmu na gargajilya.

 

Jagora                   :In haka gaskiya ne,

YAmshi:               :Mu mance hura da nono,

 

Jagora                   :Sannan a mance tuwo,

Y/Amshi:              :Tuwo da nama,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya,

:Kar mu sake mu mance.

 

Jagora                  :Ko da kana da mota,

Y/Amshi :             :Ka sai dokinka ka ɗaure,

 

Jagora                   :Ko da kana da mota,

Y/Amshi               :Ka sai dokinka ka ɗaure,

 

 

 

Jagora                   :Wurin mota daban ne,

:Kuma,

Y/Amshi:              :Wurin doki daban ne,

 

Jagora                   :Wurin mota daban na,

:Kuma,

Y/Amshi               :Wurin doki daban ne,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

 

Jagora                  : In ka tashi hawan doki,

:Ka hau ka yo,

Y/Amshi :             : Kilisa,

:Ka dawo gida ka daure,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya,

:Kar mu sake mu mance,

:Mu bi al'adunmu na gargajiya.

                             RATAYE NA 2

Makaɗi :               :Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Waƙar                   : Nona

G/Waka                 :Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora                     :Noma babbas sana'a,

Y/Amshi :              :Koway yi ta ya bar rasawa, x2

 

Jagora:                 :Ku zan aje noma daidai ne,

Kowa aje gero da dawa,

 :Ku zan tsare noma daidai ne,

Y/Amshi               : Kowa aje gero da dawa,

 :Wannan ya ɗebe takaici,

: Noma babbas sana'a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora:                 : Taimaki bayin ka Allah,

Y/Amshi :              Allah kai an mai iyawa,

: Noma babbas sana’a.

 

 

Jagora                   :Taimaki bayin ka Allah,

Y/Amshi :              :Taimaki bayin ka Allah,

: Allah kai am mai Iyawa,

                              : Noma babbas sana'a,

 

Jagora         :Can dauri Nijeriya ƙasarmu,

:Allah ya ba ta arzikin noma kasan nan,

:Mu noma gero mu noma dawa,

:Ga shinkafa ga gyaɗa,

:Ga auduga muna noma,

:Ga masara kuma ga shinkafa,

:Ga acca kuma ga maiwa,

:Ga alkama muna noma,

:Arkikin man fetur ya motso,

:kasuwar man fetur tat tashi,

:Duk munka watsar da noma,

:Munka koma a kan kwangiloli,

:To ga shi arzikin fetur,

:Yanzu ya kare kasar nan,

:Can kasan da muke kaiwa,

:Can Kasashen da muke kaiwa,

:Kassuwan mai ta kare ,

:To ku 'yan Nijeriya,

:Yanzu me za mu komawa,

:Gara mu koma kan noma,

:Gara mu koma gun noma,

:Mu tara abinci ƙasarmu,

:Mu samu abinnci da za mu ci,

:Mu yi sutura ƙasammu,

:Mu sami abin yin sutura,

:Kana sannan mu neme kuɗɗi,

:Mu kare mutunci na kanmu,

 

Y/Amshi :     :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

Jagora         : Mu kare mutunci na kanmu,

Y/Amshi :   :Mu kare mutuncin ƙasar ga,

 

Jagora         : Kun san gero da dawa,

:Da sauran abin za mu ci,

:Shi muka ci a Nijeriya,

:Amma auduga da gyaɗa,

:To ita ce za mu ɗauka,

:Mu kai ta can kasashen waje,

:Mu sayar mu samo kuɗɗi,

:In dai munka samo kuɗɗi,

:Mu gina asibiti,

:Domin kiyon lafiyammu,

:Mu kare mutunci na kanmu,

Y/Amshi     :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

 

 

Jagora:         :In mun samo kuɗɗi mun tara,

:Kana mu gina godabe,

:Masu zagaya Nijeya,

:Kayan unhwanin gona,

:Ko ina aje a kai,

:Mu kare mutuncin ƙasag ga,

Y/Amshi :    :Mu kare mutunci na kanmu,

 

Jagora         : Mu kare mutunci na Kammu,

Y/Amshi     :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

 

Jagora         :In dai mun sami kuɗɗi da yawa,

:Sannan mu gine makarantu,

:Gara mu je mu nemi ilmi,

:Mu kai ‘ya ‘yanmu Su sami ilmi,

:Mu kare mutunci na kanmu,

Y/Amshi :   :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

 

Jagora           :Kowa ya kare mutunci na kainai,

Y/Amshi      :Yakare mutinci ƙasag ga,

:Noma Babbas sana'a.

 

Jagora         :Wada duk muka so Nijeriya,

:Mutane dun na hore ku,

:Manyan garuruwanmu,

:Kowane gari kazzo,

          :Ka hangi dala ta gyaɗa,

:Ka hangi dala ta auduga,

:Kowane dum mun tara,

:In dai mun mike mun yi kwazo,

:Mun kare mutunci na kannmu,

Y/Amshi :   :Mun kare mutuncin ƙasag ga,

 

Jagora :        :Mun kare mutunci na kanmu,

Y/Amshi :   :Mun kare mutuncin ƙasag ga,

 

Jagora :        :Darajar Nairammu da tah faɗi,

:To kuma sannan,

Y/Amshi     :Za ta dauwa,

 

Jagora         :Darajar Nairammu da taf faɗi,

Y/Amshi :   :To kuma sannan za ta dauwa,

 

Jagora         :To ku ma'aikatan Nijeriya,

:To ku tsaya kan gaskiya,

 :Kowa ya yi aiki don Allah,

:Kai ka tsaya ga naka aiki,

:Nima in tsaya ga nawa aiki,

                      : ln muyi haka nan mun taimaki kanmu,

 : In muyi haka nan mun yi daidai,

 :Kar mu tsaya muna yin ƙeta,

:Muna cutar kanmu da kanmu,

:Kai babba ka shirga ɓanna,

:Sannan ka ce yaronka bai yi,

:Kowa duk ya tsaya ya dage,

:Mu kare mutuncinmu zak kyau,

Y/Amshi :    :Mu kare mutuncn ƙasag ga,

 

Jagora         :Mu kare mutuncinmu zak kyau,

Y/Amshi     :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

:Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

Jagora:        :Ku jama'an Nijeriya,

:Talakkawa da Sarakuna,

:Da ku ma'aikatan Gwamnati,

:Alhaji Musa Ɗanƙwairo,

:Shi ma ya yi horon jama’a,

:Kowa ya kama noma da gaske,

:Nima Alhaji Ɗanƙwairo

:Bayan na aje kotsannina,

:Na je Sakkwato can gidana,

:Ni ma zan koma gona,

:In kama noma kwarai da gaske,

:In tara gero in tara dawa,

:In nemi abinci na kaina,

Y/Amshi :   : In nemi abinci na kaima, x2

 

Jagora :        :Na kare mutunci na kaina, X2

Y/Amshi :   :Na kare mutuncin ƙasag ga, X2

:Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

 

Jagora :                   :Kowa ya tsaya ya yi aiki,

:Yawon banza,

Y/Amshi `             : Ba a so nai,

 

Jagora :                 :Kowa ya tsaya ya yi aiki,

Y/Amshi :             :Yawon banza ba a so nai,

:Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora :                 :Da ku ma'aikatan government,

:‘Yan kasuwa da talakkawa,

:Da manya-manyan Sarakunanmu,

:Kowa ya ba da goyon baya, X2

Y/Amshi               : Mu taru mu ceto ƙasag ga, X2

 

Jagora                  :Jama’a,

YIAmshi :             :Mu taru  mu ceto ƙasag ga,

                               :Noma babbas sana'a,

                              :Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora                     :Kowa ya kama aikin daji,

: Kowa nas san bai da aiki,

:Gwamma ya je ka ya dau fartanya,

:Ya zo ya kama aikin daji,

:In yai haka nan, x2

Y/Amshi:              :Yayi daidai, x2

 

Jagora :                 :Kowa naz zan bai da aiki,

:Yana yawo ga titi banza,

Y/Amshi :             :Irinsu ka ‘yan sace-sace,

.                            : Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa

Jagora:                  :Taimaki bayin ka Allah, x2

Y/Amshi :             :Allah kai am mai iyawa, x2

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora                   :Manyan Sojojin Nijeriya,

:Kowa ya kama noma ƙwairo,

Y/Amshi :             :In kui haka nan kun yi daidai,

 

 

Jagora :                 :Manyan ‘Yansandan Nijeriya,

:                            :Kowa ya kama noma ƙwairo,

Y/Amshi :             :In kui hakan nan kun yi daidai,

 

Jagora :                 :Manyan Kwastanmu na Nijeriya,

:Kowa ya kama noma Kwairo,

Y/Amshi :             :In kui haka nan kun yi daidai,

 

Jagora                   :Imagireshan da N.S.O.,

:Kowa ya kama noma Kwairo,

Y/Amshi :             :In kui haka nan kun yi daidai,

 

Jagora :                 :Sarakunammu na Najeriya,

:Kowa ya kama noma ƙwairo,

Y/Amshi               :In kui haka nan kun yi daidai,

 

Jagora                  ‘Yan Kasuwa na Nijeriya,

:Kowa ya kama noma Musa,

YIAmshi               :In kuyi haka nan kun yi daidai,

:Noma babbas sana’a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora                   :Sai mun aje gero mun aje dawa,

:Ga masara ga alkama,

:Ga shinkafa ga masara,

:Idan abinci yat taru,

Y/Amshi :             :In yai haka nan ya yi daidai,

 

Jagora                   :Darajar noma,

Y/Amshi :             :Za ta ƙaru,

 

Jagora                  :Domin isan nan,

Y/Amshi:              :Darajar Naira za ta dauwa,

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora:                 : Mun shirya mun tara aiki,

:Ga ya nan a gabanmu jibge,

:To ku 'yan Nijeriya,

:Kara mu motsa mu miƙe,

:Mu kare mutuncinmu ya fi,

Y/Amshi :             :Mu kare mutuncin ƙasag ga,

Jagora                   :Muna da abin yi ƙasanmu,

:Kun san mun sami komai,

:Allah ya albarkato ƙasar Nijeriya,

:Da arziƙi,

:Sai In mun ƙi yin biɗa,

:ln mun ƙi yin biɗa,

:In min miƙe mun nemi na kanmu,

:Allah za ya taimake mu,

:Kowa nan nemi taimako gun Allah,

:Sai ya yi mai,

:Diba min faɗin Nijeriya,

:Ko'ina akwai magurzayye,

:Na gurza auduga,

:Ko ina sannan Nijeriya akwai dala ta gyaɗa,

:Sannan akwai dalan auduga,

:To diba yanzu babu ko ɗai,

:Gara mu tashi mu kama aiki.

:Mu kare mutunci na kanmu,

 

Y/Amshi :    :Mu kare mutuncin ƙasarmu.

 

 

Jagora         :In munyi haka nan,

Y/Amshi      :Mun yi daidai,

 

Jagora         :Yawon banza,

Y/Amshi :   :Ba a so nai,

 

Jagora         :Yawon,

Y/Amshi :    :Banza ba a so nai,

 

Jagora         :Aiki a yi domin Allah,

:Barna a bari kuma domin Allah, x2

Y/Amshi :             :In mui haka nan mun yi daidai, x2

 

Jagora                  :A Kama hanyoyin shara'a,

:Sannan shara’a a kan gaskiya,

:in dai mutum na nashi aiki,

:To, bas shi da nashi aiki,

:Shi ma shi bari in yi nawa,

Y/Amshi               :Kat ma ka bari 1n yi nawa,

:In munyi haka nan mun yi daidai,

 

 

Jagora                   :Ai in mui haka nan,

Y/Amshi :            :Mun yi daidai,

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora                   :Abin da ak kyawu gare mu,

:Mu daina sha'awar kayan waɗansu,

: Mu daina shawar kayan waɗansu,

: Mu kuma shawar kayan kasarmu,

: In mui haka nan, x2

Y/Amshi               : Mun yi daidai, x2

 

Jagora                  :Jama'a,

Y/Amshi               :In mui haka nan mun yi daidai,

::Noma babbas sana’a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.

jagora          :         Malam ka ce gyara kakai,

:Wai kai don kana da mulki,

:Ko ko don kana da arziki,

:Kaje ka sawo kayan ƙasashen waje,

:Don ka sanya, ka ƙi sayen na gidanka,

:Ka ɗau kuɗɗi ka kai su can waje,

:Ka bar gida ba komai,

:To wai kai wai don ka waye,

:To su ko talakkawa,

:Don sun zo sun yi sawo can,

:To su ko sai ku ce sun yi laifi,

:Sai in kun kare mutuncinku,

:Sannan su ma su yi koyi,

 

Y/Amshi              :Su kare mutuncin ƙasag ga,

 

Jagora         :         Su kare,

Y/Amshi :             :Mutuncin ƙasag ga,

;Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

 

Jagora :                 :Ko can gyara ya banna,

:Gwamnati na foron Jama'a,

:Kowa ya kama aiki da gaske,

:kowa na zan bai da aiki,

:wannan ya cuci kansa,

:Sannan

Y/Amshi               :Ya cuci  kainai, x2

 

Jagora                  :Sannan kuma,

Y/Amshi               :Ya cuci kainai,

:Noma Babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

Jagora                  :Ɗanƙwairo na sha dariya,

:Na iske Bahillacen daji,

:Yana ta kiwon shanunai,

:An ba shi furag gero yas sha,

:Da nan sai yac ce miyatti,

Y/Amshi :             :Gardi ne yar ratsi kainai,

 

 

 

Jagora :                 :Gardi ne,

Y/Amshi :             :Yar ratsa kainai,

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

 

Jagora:                 :Taimaki bayinka Allah, x2

Y/Amshi :             :Allah kai am mai iyawa, X2

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora :                 :Ku dai manyan Nijeriya,

:Tun farko na ga laifinku,

:Kun kwashe arzikin Nijeriya,

:Wasu masu mugun hali,

:Waɗanda ad da kishin ƙasa,

:nan sun tara kuɗɗinsu,

:Cikin NIjeriyarmu daidai,

:Amma wasu ga shi sun kwashe,

:Sun kai su can wa' yansu ƙasa,

:Kai mai boyon wuta bonu,

:Ran da duk wutan nan tak kama,

:Kai ka san,

Y/Amshi :              :Ta bab barinka,

 

Jagora         :Ran da duk wutan nan tak kama,

Y/Amshi     :Kai ka san ta bab barinka,

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora         :Kai ku zan riƙa noma daidai ne,

:Kowa aje gero da dawa,

Y/Amshi     :Ka san ya ɗebe takaici,

:Noma babbas sana' a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

 

 

Jagora:        :Tsohon aiki noma na duƙe,

:Tsohon aiki,

Y/Amslhi    :Noma na duƙe,

 

Jagora :        :Tsohon aiki,

Y/Amshi     :Noma na duƙe,

:Koway yi ka,

:Ya bar rasawa,

 

Jagora         :Tsohon aiki,

Y/Amshi :    :Noma na duƙe,

 

Jagora :        :Koway yi ka,

Y/Amshi     :Ya bar rasawa,

                      :Noma babbas sana'a,

                     :Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora:        : Ga mai abinci yana jin daɗi,

:Ga raggo yana Kallo,

:In lokacin damina ta kama,

: Da lokacin damina ta kama,

: Da Allah ya yi ruwan sama,

:Kowa ya ɗauki kwashe,

:Ya je gona ya kama aiki,

:Shi ko raggo yana kwancinai,

:Ga lokacin ɗiba abinci,

:Ya zo kowa yana ɗiba abinci,

:Raggo yana kallon su,

:                            :Domin ba ya da komi Ɗanƙwairo,

:Domin Ka cuci Kanka,

:Ka ƙi aiki na daji,

:Kuma ba ka da aiki birni raggo,

:Amman Ka cuci,

 

Y/Amshi               :Kanka,

 

Jagora         :         Raggo,

Y/Amshi :             :Amman ka cuci kanka,

: Noma babbas sana’a,

: Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora :                 :Noma tsohon aiki, x2

Y/Amshi               :Koway yi ka ya bar rasawa, x

 

Jagora                  : Muna da arziki nan ƙasarmu,

:Allah Sarki ya bar ga,

: Allah Sarki ya albarkace mu,

: Da alhairin hatsi da auduga,

:Had da gyaɗa Allah ya ba mu,

:Kowak kag ga yana wahala,

Wannan bai yarda da Allah ba,

Ya ki biɗar aiki da kyawo,

:Ya ki tsare aiki da kyawo,

Y/Amshi               :Yawon banza yake yi,

 

Jagora                  :Wannan,

Y/Amshi :             :Yawon banza yake yi,

 

Jagora                  Yawon banza, X2

Y/Amshi :             :Ba a so nai, x2

 

Jagora                   :Daga yawo Sai,

Y/Amshi:              :‘Yan sace-sace,

:Noma babbas sana'a,

:Koway yi ta ya bar rasawa.

 

Jagora:                  :Taimaki bayin ka Allah,

Y/Amshi               :Allah shi am mai iyawa.

:Makaɗi Alhaji Musa Ɗanƙwairo

:Wakar Gargaɗin jama'a

 

 G/Waƙa               :A yi aiki na gaksiya,

:Kam mu ɓatad da kanmu.

 

Jagora :                 :Kowa nab bi gaskiya,

:Ya kyauta,

Y/Amshi               :Ma kai nai,

 

Jagora                  :Kowa nab bi gaskiya,

Y/Amsai:              :Kowa nab bi gaskiya,

:Ya kyauta ma kai nai,

:A yi aiki na gaksiya,

:Kam mu ɓatad da kanmu.

 

Jagora :                 :In dai nik kama waƙa,

Y/Amshi :             :Ni kai ba, x2

 

Jagora :                 :Kai ban his sad da kai ba,

:Ni ban,

Y/Amshi:              : His sad da kai na.

 

Jagora                  :Ban his sad da kai ba,

Y/Amshi               :Ban his sad da kaina,

Jagora                  :Ke ban his sad da ke ba,

Y/Amshi :             :Ni ban his sad da kaina,

 

                                     RATAYE NA 3

Makadi                : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Wakar                 :  'Yandoton Tsahe Alhaji Aliyu 1l (1960-1991)

G/Waka               : Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi da,      

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘yandoto.

 

Jagora        :         Bi da arna bai yarda,

Y/Amshi               : Bai yarda a kai mar wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai Wargı ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Dan Sabon Gari na Jekada,

: Ka nike maza,

Y/Amshi     : Waddare sun lakkwala duk sun yaushi,

 

Jagora        : Dan sabon Gadi na Jakada,

: Ya haye maza,

Y/Amshi     : Waddare sun lakkwata duk sun yaushi,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai ma wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Wani ya barkace,

Y/Amshi     : Yana shawagin bidak kade

: Aljihu twake da kashin bauna,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba

: Ya hana Karya ‘Yandoto.

Daudu        : Iko ya yi,

Y/Amshi     : Gardama, dan Sarki na bisa kaiwa kullum,

 

Jagora        :         Ina abu!

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi ba

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana Karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Ko can samu ka Jan sarauta,

Y/Amshi     : Bakumbushi da za a nadi

: Ta ce masu sai kun dawo,

: Bi da arma bai yarda,

: Kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana Karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Ya hau da lahiya,

Amshi         : Sabka lahiya, uban Sarkin Kofa ci maraya,

: Dodo wandara gwarzon Sani,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Jagora         : Hawan da kay yi,

: Kai je Bilbis ran Talata,

: Ali dan Muhammadu,

Y/Amshi     : Ka dibge daji da doki,

: Sai ta jin nai kai,

: Bayanai gami da barwa

: Sai hattara su kai,

: Kotsanni da masu gangumma duka suna hwadin,

: Ga bajimin Garewa ya darzazo,

: Dimau na Amadu,

: Dan Shehu tarnaki hanani,

: Ka bige Kangara,

: Ya koro makiya duk sun bi,

: Bi da ama bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Daudu        : Ko can wargi.

Y/Amshi     : Wuri garai,

: Mussar Jibda aka garkewa,

:Har ai mata iko,

: Kwa ishe damisa hay yai izgilin da yag dwagas,

: Sai ya ci wuyatai danya,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba.

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Nada mani Sarkin Kidi, x2

Y/Amshi     : Na Jekada, mui ta duniya,

: Kurna na ga Sarkin Kaya,

: Dankwairo makadin ‘Yandoto,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mar wargi Da,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto. x2

 

Jagora        : Hadari kashe kaifin rana,

: Ci gari Ali gandon Gura-Guri

: Hadari,

Y/Amshi     : Kashe karfin rana,

: Ci gari Ali gandon fashin tama,

: Bi da arna bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

 

Jagora        : Tsahe gidan mai Kano ya yi kyau,

‘Y/Amshi    : Ali ya dada shi bai rage masu,

: Alu ya rika karfi da masu,

: 'Yan jira dole sai kui ta hankuri.

 

Jagora        : Cigari Ali,

‘Y/Amshi    : Dutsin fashin tama,

 

Jagora        : Zakı hadari kashe kaifin rana,

‘Y/Amshi    : Ci gari Ali dutsin tashin tama,

: Bi da arna bai yarda.

: kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: Ya hana karya ‘Yandoto.

Jagora        : Wajen yaki Ali ka dauki girma,

: An san da Yandoton Tsahe,

: Tun da fa Ali shi,

Y/Amshi     : Bai fada su,

: Ya kari gaba na Bubakar,

: Bai dauki reni ba mai masa,

: ‘Yandoto ka gaji kokari,

: Ya kori gaba na Bubakar

: Bai dauki reni ba mai masa,

: Yandotso ka gaji kokari,

: Bi da ama bai yarda,

: A kai mai wargi ba,

: Mai wuyag gaba,

: ‘Ya hana karya ‘Yandoto,

 

                                  RATAYE NA 4

Makadi       : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Wakar        : Alhaji Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwaio

G/Waka      :Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki,

 

Daudu        : Ya wuce raini,

Y/Amshi     : Baa yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

 

Jagora        : Gungurun,

Y/Amshi     : Kashin giwa na Alu ba ka haduwa,

: Kowac ci ka sai ya cake makoshi,

 

Jagora        : Gabas da yamma, kudu da arewa,

: An san kai ne Sardauna mai kwana kyauta,

Y/Amshi     : Saboda baiwa, Amadu saboda hairi aka sakanı ma,

: Yawuce raini ba ayi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

Daudu        : Firimiyan Jihar Arewa Amadu,

: Abin da kai ma Nijeriya,

: Hak kasa ta nade ana tuna ka,

: Amadu jikan,

 

Y/Amshi     : Bawan Allah, gamji dan kwarai,

: Gamji na kwarai, gohe Allah,

: Malam Gohe Allah gafarta ma,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

Zwali          :Firimiya mai halin waliyyai,

: Sui maka shairi ka mai da hairi,

: Sui maka hairi ka rama hain,

Y/Amshi     : Wanga halin Shehu ya gado,

: Mahassada dai ka ta jidali,

: Amadu dan Iro ba ruwanai,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

Daudu        : Malam,

Y/Amshi     : Amadu, Allah dai ya jikai nai,

 

Daudu        : Gaba ta wuce,

Y/Amshi     : Baya ad da saura,

: Yanzu a samo wani kamatai,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

Daudu        : Gaba ta wuce,

Y/Amshi     : Baya ad da saura,

: Yanzu a samo wani kamatai,

 

 

Jagora        : Gaba ta wuce,

Y/Amshi     : Baya ad da saura,

: Yanzu Ku nemo wani Kamatal,

: Ba tsoro ba kariyaz zucci,

: Ya gwada Jikan Shehu,

: Amadu ya gwada jIKan Shehu na shi.

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

 

Jagora        : Shi Amadu ya samu duniya,

: Ya kau gwada ya samu duniya,

: Yai alheri ya rika kanne,

: Ya rika 'ya'ya, ya rIka barwa,

: Ya rika bayi da,

Y/Amshi     : Talakkawa,

: Ran Juma'a da karhe biyu,

: Rannan yaki yac ci Amadu,

:Niy kuka niy bakin rai,

: Nit tuna Allah, nim mashi muna,

: Da walakanci gara shahada ga Musulmi,

: Don ba illa ne ba,

: Da walakanci gara shahada ga Musulmi,

: Don ba illa ne Da,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba Sadauki.

 

           : Bangon tama mai wuya iza,

: Bajimin Sir Kashim,

: Uban Zagi Bello dan Hassan,

: Mai martabar Danhodiyo,

: Mai martabar Mamman Bello,

: Mai martabar Abdulalhi,

: Mai martabar Attahiru,

: Mai martabar Moyi da Alto

‘Yan/Amshi : Da uwar Daje,

: Mai martabar Isan Kware Autan Shehu,

: Mai martabar Ibrahimu mai kahon kero,

: Sadauki dan Sadauki,

: Kakaninka waliyan Allah ne,

: Ba ba’a ba ko can,

: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Garba sadauki.

 

                                        RATAYE NA 5

Makadi       : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Wakar        : Alhaji Bello Maitama Yusufu, Sardaunan Dutse

 

G/Waka      : Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusut.

Jagora        : Minista na ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusufu,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Minista na ciniki,

: Allah ya 1sam ma Bello Maitama Yusulu,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf

 

Jagora        : Kai Minista na ciniki,

Y/Amshi     : Alah ya isam ma Bello Maitama Yusufu,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya 1sam ma Bello Maitama Yusut.

 

Jagora        : Taho ga ka ga maza,

Y/Amshi     : Wandara uban Akka Ado Sarkin Fada,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora         : Dutsin fashin tama,

Y/Amshi     : Sardauna uban Akka Ado Sarkin Fada,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Dutsin fashin tama,

Y/Amshi     : Sardauna uban Akka Ado Sarkin Fada,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Gagarau sa maza gudu,

Y/Amshi     : Ba a jan ka ranar yaki,

 

Jagora        : Ki sake sa maza gudu,

: Ba a jan ka ranar fada,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya Sam ma Bello Maitama Yusuf.

Jagora        :        Wataranaa Alhaji Ɗankwairo,

: Ina can Sakkwato na shiga mota,

: Na dora kewayar Dirmi,

: Sai nih hangi jam mota,

: Da nig ga lambar sano gare la,

: Sai nij ja birki Ɗankwairo,

: Da nil leka,

: Han na yi zaton Maitama Bello ne,

: Ba Maitama Bello ne ba,

: Ashe Yusufu Matama nc,

: Da yaj je Sakkwato yad dawo0,

: Ya isko ni gidana,

: Sai yad debo kuddi da yawa yab ban,

Y/Amshi     : Don Bello Maitama yab ba ni,

 

Jagora        :        Yac ce mani,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

Y/Amshi     : Don Bello Maitama yab ba ni,

 

Jagora        : Yas sake debo kuddi,

: yac ce amshi Ɗankwairo,

: Wannan kuddin, kuddin, kudin mata ne,

: Yac ce wannan kuddin,

Y/Amshi     : Kudin mata ne,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Ranar Karamar Sallah da anka yi,

: Ina Sakkwato Ɗankwairo,

: Muhammadu Bello ya je Gwaram,

: Rannan ka yi hawan yaki,

: Ni ban je ba nij ji labari,

: In ji 'yan birnin Kano,

Y/Amshi     : Duk sun je Gwaram,

: Wurin kallonka,

: Duk sun tafi Gwaram,

: wurin kallonka,

 

 

Jagora        : Zaki,

Y/Amshi     : Duk sun tafi Gwaram,

: Wurin kallon ka,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Da nid dade ban ga Bello ba,

: Sai nid dauko mouata,

: Naj je ano wurin nemanshi,

: Gurgura duisi wargi gare ka,

: An san manya suna cikin gimansu,

: Gurgura dutsi wargi gare ka,

: An san manya suna cikin gimansu,

: Ko can an san,

Y/Amshi     : Manya suna cikin girmansu,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Alhaji uban Alhaji Sadauki,

Y/Amshi     : Alhaji uban Alhaji Sadauki,

 

Jagora        : Alhaji uban Alhaji Sadauki,

Y/Amshi     : Alhaji uban Alhaji Sadauki Mamman,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Gagarau mai ban tsoro,

: Ki sake ba a jan ka,

Y/Amshi     : Ranar yakl,

Jagora        : Zaki

Y/Amshi     : Ki sake ba a jan ka yakı,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Giwa ba ta Kaho,

: Kowac ce ta yi Kaho,

Y/Amshi     : Karya ne, x2

 

Jagora        : Giwa,

Y/Amshi     : Kowac ce ta yi Kaho,

: Karya ne,

 

Jagora        : Dutsin fashin tama,

: Sardauna uban Akka Ado Sarkin Fada,

: Taho ga ka ga maza

Y/Amshi     : Sardauna uban Akka Ado Sarkin Fada,

 

Jagora        : Dutsin tashin tama,

                   : Ci fansa

Y/Amshi     : Uban Akka Ado Sarkin Fada,

 

Jagora        : Taho ga ka ga maza,

Y/Amshi     : Sardauna uban Akka Ado Sarkin Fada,

 

Jagora        : Mamman Bello,

Y/Amshi     : Uban AKka Ado Sarkin Fada,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Da nid dade ban ga Bello ba,

: Sai nid dauko motata,

                   : Niz zo Kano

Y/Amshi     : Wurin nemansa,

 

Jagora        : A niz zo Kano,

Y/Amshi     : Wurin nemansa,

 

Jagora        : Sai Sarkin Gida yac ce min ai Sardauna,

Y/Amshi     : Ba ya nan ya tashi,

 

 

Jagora        : Ai Sardauna ba ya,

Y/Amshi     : Nan ya tashi,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Muhammadu ya shiga jirgin Lagos,

: Ko ko ya shiga jirgin yawo,

: ko ko ya shiga jirgi Lagos

Y/Amshi     : Ko ko ya shiga jirgin yawo,

 

 

Jagora:       : Da nij je Lagos Dankwairo,

: Na tambayi Shehu Shagari,

: Yac ce manı wa kake nema,

: Nac ce Sardauna Muhaamdu Bello,

: Yac ce Alhaji Dankwairo,

: Ka ga dubu biyar ka koma,

: Sardauna ya zo ya kwana,

Y/Amshi     : Amma ba shi gida ya zarce,

 

Jagora        : Amma ba shi,

Y/Amshi     : Gida ya zarce,

: Minista na ciniki

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Yaje Amirka da London,

: Dac can zai wuce Birnin Makka,

: Domin ya yo ziyara,

: Sai nit ta rokon Allah, Allah,

Y/Amshi     : Kawo Bello gida laliya,

 

Jagora        : Mamman,

Y/Amshi     : Allah kawo ka gida lafiya,

 

Jagora        : Shugaban bikin Filanin Yola,

‘Yan/Amshi : Had da Barebari sun san shi,

 

Jagora        : Muhammadu

Y/Amshi     : Had da Barebari sun san shi,

                   : Minista na ciniki

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        :Kaji irin kidin,

Y/Amshi     : Kidin da kan fi karifin yaro,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

Jagora        : Kun ji irin kidin da kan fi karfin yaro,

Y/Amshi     : Karfin yaro,

 

Jagora        : in dai kaj ji tambura,

: Kotsanni suna kara,

Y/Amshi     : To wanga nan kidi,

: Na dan Sarki ne,

: To wanga nan kidi,

: Na Dankwairo ne,

 

Jagora        : Duk in da kaj ji tambura na kara,

: Sannan kidi na Kotso ne,

Y/Amshi     : To wanga nan kidi na Dankwairo ne,

 

Jagora        :         Ta tabbata,

Y/Amshi     : Wanga nan kidi na Dankwairo ne,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf

 

Jagora        : Ranar karamar sallah ta bana,

: Muhammadu ka yi hawan yaki,

: Ni ban je ba nij ji labari,

: Da kaj je can birin Gwaram,

: ‘Yan birnin Kano sun je,

Yan/Amshi : Gwaram wurin kallonka,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Yan birnin Kano gaba ɗaya,

Y/Amshi     : Duk Sun je Gwaram wurin kallonka,

 

Jagora        : Ga bindiga tana hannunka,

: Ga zagaigai suna a gabanka,

: Baya gare ka bayin Sarki,

: Baya gare ka bayin Sarki,

: Ga makada nan sun jera,

: In ji tsoffin Kano suna faɗin,

: Kamad dai Sule Sarkin Yaki,

: Irin Hausan,

Y/Amshi     : Kamad dai Sule Sarkin Yaki,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Yadda ka ba ni mamaki,

: Muhammadu da kat taho Kan0,

: Ka shiga mota za ka Argungu,

: Tun da kaf fito Kano,

: Da kaj je cikin garin Gwarzo,

: Duka sun zo wurin taron dattijo,

Y/Amshi     : Sun zo wurin taron dattijo,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusuf.

 

Jagora        : Yad da kaf fito gidanka lafiya,

: Ka dawo gidanka lafiya,

: Da yaj je can birnin Dayi,

: Duk sun je wurin taron dattijo,

: Yadda kaf fito gidanka lafiya,

Y/Amshi     : Allah mai she ka gida lafiya,

 

Jagora        : Da kaj je gidanka laliya,

: Yadda kaj je gidanka laiiya,

: Ka dawo gidan,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusut.

Jagora        : Da yaj je cikin garin Funtuwa,

: Duk sun fito taron dattijo,

Y/Amshi     : Yadda kat ito gidanka lafiya,

: Ka dawo gidanka lafiya,

: Minista na Ciniki,

: Allah ya isam ma Bello Maitama Yusufu.

 

 

                                        RATAYE NA 6

Makadi       : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Wakar        : Alhaji Ado Ɗandawaki

G/Waka      : Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Ɗandawaki.

 

Jagora        : Na yadda da Ado Ɗandawaki,

Y/Amshi     : Na Alhaji Abba Mijin Maza,

 

Jagora        : Mai yabo gun Allah,

‘Y/Amshi    : Na Alhaji Musa Da'u ka huce hushi,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Ɗandawaki.

 

Jagora        : Ado mahassadanka sun yi ga banza,

Y/Amshi     : Don na ce masu sun yi ƙarya,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Dandawaki.

 

Jagora        : Allah,

Y/Amshi     : Don na ce musu sun yi karya,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Dandawaki.

 

Jagora        : Kai ne mulki kai ne ilmi,

: Ba a hi ka taimako ba Ado, x

Y/Amshi     : Alhaji Ado ka yi komi, x

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Dandawaki.

 

Jagora        : Dan dattijo,

Y/Amshı     : Ni Alhaji Ado ka yi komi,

 

 

Jagora        : Taimąki gazajje,

: Taimaki maraya,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Ɗandawaki,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Ɗandawaki.

 

Jagora        : Ya bai wa gazajje,

: Ya bai wa maraya,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Ka ba kuturu,

: Ka ba makaho,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Ɗandawaki,

: Na Yadda da Ado Ɗandawaki.

 

Jagora        : Dattijo,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Ɗandawaki

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Ɗandawaki.

 

Jagora        : Can Sakkwato garin Shehu,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Can da nij je Jihar Neja,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Na zo Jihar Kaduna,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado 1Dandawaki,

 

Jagora        : Sai nil leka Jihar Benuwai,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Dandawaki

 

Jagora        : Sai nit tali Jihar Kwara,

Y/Amshi     : Suna da Ado zad dama,

: Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Jihar Plateau na duba,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Jihar Bauchi na duba,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

Jagora        : Jihar Gongola nid duba,

: Suna da ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Kar Nijeriyag ga na duba,

: Kowace Jiha na je,

: Suna da Ado zad dama,

Y/Amshi     : Ba su da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Sai da nit taho Jihar Kano,

: Kano akwai dubun komai,

Y/Amshi     : Nan anka yi Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Da Allah yay yi Annabi Adamu,

: Allah yay yi Ado Bayero,

Y/Amshi     Yay yi Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Sai Haliku,

Y/Amshi     : Yay yi Ado Dandawaki,

: Na Alhaji Abba Mijin Maza,

: Na Yadda da Ado Dandawaki.

 

Jagora        : Wani kyandir dai hitilab banza,

: Ko da ba lhitila gidana,

: Ka san ba ni sayen kyandir,

: Sai in sai hitila in kunna,

: Sharrin kyandir in ka saya,

: In ka kwanta ka yi bacci,

: In dai kyandir yaf fadi,

Y/Amshi     : Yanzu ya kone ma gida,

: Na Yadda da Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Yanzu ya jawo gobara gida,

: Mijin Hajiya Ni'ima,

YAmshi      : Alhaji Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Mijin Hajiya Ni'ima,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Dandawaki,

 

Jagora        : Mijin Alhajiya Jabba,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Dandawaki,

 

Jagora        :         Mijin Alhajiya Jabba,

Y/Amshi     : Alhaji Ado Dandawaki,

: Na Alhaji Abba mijin maza,

: Na yadda da Ado Dandawaki.

 

                               RATAYE NA 7

Makadi      : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Wakar        : Jam'iyyar siyasa ta N.P.N

G/Waka      : Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

Jagora        : Ku ya da karya.

Y/Amshi     : Ku kamma gaskiya,

 

Y/Amshi     : Ku kamma gaskiya,

Jagora        : Ku ya da karya,

Y/Amshi     : Ku kamma gaskiya,

: Kar ku sake don Allah,

: Mutane kar ku sake don Allah,

: Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Ki yini lafiya,

: Ki kwana lafiya,

Y/Amshi     : Ki tashi lafiya N.P.N.

 

 

Jagora        :  Kowash shiga,

Y/Amshi     : Ya sha dadi,

: Daki da masara N.P.N.,

Jagora        : Kui ta tunani,

: kui ta hankali,

: kai dun,

Y/Amshi     : Mutumin N.P.N.,

: Bai zan mutumin banza ba,

Jagora        :         Wannan,

Y/Amshi     : Bai ya da hwadin karya ba.

: Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Ko ni makadin N.P.N,

Y/Amshi     : Ban san sukak kowa ba,

 

Jagora        : Sannan ban san,

Y/Amshi     : Zagin kowa ba,

 

Jagora        : Sai dai wanda yab bace hanya,

: Dankwairo in mashi roko,

Y/Amshi     : Ya Allah mai so shi,

: Shi taho ya bi babbar hanya.

 

Jagora        : To kun ji tamburan N.P.N,

Y/Amshi     : Haji Dankvairo ya shirya,

 

Jagora        : Ita Jamiyag ga ta N.P. N.,

: Duk inda taj je kafa reshe,

Y/Amshi     : Ko da birmi ko da daji,

: Magana ta gaskiya take fadi

: Ba ta ya da fadin karya ba,

 

Jagora        : Ita hay yau,

Y/Amshi     : Ba ta ya da fadin karya ba,

 

Jagora        : Kabiru Direba na gode,

Y/Amshi     : Domin dai ban ram mai ba,

: Domin darajar N.P.N,

 

Jagora        :Ya ban,

Y/Amshi     : Domin darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Sarkin Gwaram Muhammadu Sani,

Y/Amshi     : Ya ban domin darajar N.P.N.

: Jam iyyar N.P.N.

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Alhaji,

‘Y/Amshi    : Sarkin Gwaram Muhammadu Sani,

: Ya ban don darajar N.P.N.,

 

Jagora        :        Na gode ya ban,

Y/Amshi     : Don darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Kabiru,

Y/Amshi     : Dircba na gode maka,

: Ya ban don darajar N.P.N.

 

Jagora        : Na gode wa Damburan na Katagun,

Y/Amshi     : Ya ban don darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Haji Babani ya ban,

Y/Amshi     : Don darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Dan Waziri,

Y/Amshi     : Jikan Waziri uban Batulu,

 

Jagora         : Ban ram mai ba,

                    : Dan Waziri baban Waziri,

Y/Amshi      Jikan Waziri baban Batulu,

: Ban ram mai ba,

'Y/Amshi    : Jikan Waziri baban Batulu,

 

Jagora          : Ban ram mai ba.

: Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

Jagora        : Ita Jam iyag ga ta N.P.N.,

: Duk inda taj je Kala reshe,

: Ko da birni,

Y/Amshi     : Ko da daj

: Magana ta gaskiya taka ladi,

: Ba ta ya da fadin,

 

Jagora        : ita hay yau,

Y/Amshi     : Ba ta ya da fadin karya ba,

 

Jagora        : Ya ba ni Naira dari gaba dai,

Y/Amshi     : Ya ni Damburan,

: Domin darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Na gode ma Shugaban N.P.N.,

Y/Amshi     : Allah ya rika ma,

 

Jagora        : Lawali

‘Y/Amshi    : Allah ya rikama

                   : Jam’iyyar N.P.N

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Dan Buran,

Y/Amshi     : Babani Allah ya rika,

 

Jagora        : Ku mutane yan Nijeriya,

: Dankwairo na horon ku,

: Kak Ku sai da mutuncinku,

: Kak ku sai da mutuncin,

Y/Amshi     :’Ya’yanku, ku yi hankali don Allah,

 

Jagora        : Na ce ku,

Y/Amshi     : Mutane "yan Njeriya,

: Dankwairo nai maku horo,

: Kak ku sal da mutuncinku,

: Kak ku Sai da mutuncin ‘ya’yanku,

: Ku yi hankali,

 

Jagora        : Na ce,

Y/Amshi     : Ku yi hankalı don Allah,

 

Jagora        : Kowa na son ya rika gaskiya,

‘Y/Amshi    : Komi yac ce zai yi da kai,

: To ban ce mai a a.

Jagora        : Shi President mu na N.P.N.,

: Alhaji Shehu Shagari,

: Yaro ne ba tsoho ba ne,

: Ga shi da arziki da ilmi,

Y/Amshi     : Sannan da sanin dattako,

: One Nation One Destinty,

: Kasa daya ce a gu daya,

: Nigerian National Party,

: Akwai farin jini gare ta,

: Jam'iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Ba Nijeriya kadai ba,

: Kai duk Afurka baki daya,

: Sunai mana latan alheri,

: Wajen jama'an N.P.N.,

: Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Amma,

Y/Amshi     : Wajjan jama'an N.P.N.,

 

Jagora        : Ni Alhaji Musa Dankwairo,

: Da ni da magoyd,

Y/Amshi     : Bayana duka muna cikin N.P.N.,

 

Jagora        : Siyasa ba gaba ba ta,

: Kai ku ji domin siyasa,

Y/Amshi     : Ku dubi haramun danbil’amu,

:Wai shi ka gamin mai waka,

Jagora        : Ka je ka bayyana halina,

Y/Amshi     : In dora fadin halinka,

 

Jagora        : Ni kau,

Y/Amshi     : In dora fadin halinka,

: Ka dora fadin ina waka,

: In dora fadin kai sata.

: Jam'iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Shi kalwani ba dan goyo ba ne,

Y/Amshi     : Kwag goye ka kana yasshe shi,

 

Jagora        : Alhaji Adamu Mohamnmed,

: Ya ban,

Y/Amshi     : Don darajar N.P.N.,

 

Jagora        : Kayan da amale yad dauka,

: In yat tafi yak kai zang0,

: In dai an aza wa jakı,

Y/Amshi     : Ba zai iya dagawa,

Jagora         : Ka san,

Y/Amshi     : Ba zai iya dagawa nan ba,

 

Jagora        : Da kare da biri,

Y/Amshi     : Da bakar mussa,

: Barnar da kukai an gane,

 

Jagora        : Tun da,

'Y/Amshi    : Duniya tag gane,

: Gobe ba biya sai duka

: Jam'iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N.

 

Jagora        : Ai ga giwa tai ruri,

Y/Amshi     : Sai zaki yab boye,

 

Jagora        : Kuma ga zaki ya yi babbaki,

Y/Amshi     : Sai kura tab boye,

 

Jagora        : Kuma ga kura ta nisa,

Y/Amshi     : Awaki duk sun boye,

: Tumaki duk sun ruga,

 

Jagora        : Jihar Sakkwato na leka,

Y/Amshi     : Masu hankali masu ilmi,

: Duka suna cikin NP.N.,

 

Jagora        : Jahar Kaduna da nit leka,

Y/Amshi     : Masu hankali masu ilmi,

: Duka suna cikin N.P.N.,

 

Jagora        : Jihar Kano da nid diba,

Y/Amshi     : Masu hankali masu ilmi,

: Duka suna cikin N.P.N.,

Jagora        : Jihar Bauchi da nid dira,

Y/Amshi     : Masu hankali masu ilmi,

: Duka suna cikin N.P.N.,

 

Jagora        : Jihar Gongola da ail Ieka,

Y/Amshi     : Maşu hankali masu ilmi,

: Duka suna cikin N.P.N.

: Jam iyyar N.P.N,

: Aminci dai N.P.N,

 

                         RATAYE NA 8

Makadi      : Alhaji Musa Ɗankwairo Maradun

Waƙar        : Alhaji Shehu Shagari, Tsohon Shugaban Kasa,

: Turakin Sakkwato

G/Waƙa      : Shugaban Kasa jikan Sule,

: Wada duk aka so ya kai.

Jagora        : Shugaba mai cikakken iko,

Y/Amshi     : Shugaba mai cikkaken iko,

 

Jagora         : Shugaba mai cikakken iko,

Y/Amshi      :Wada duk aka so ka kai,

: Shugaban Kasa jikan Sule.

 

Jagora        : Dadin da ny Jiya Haji Dankwairo,

: Tutaru wadda a kasar Makka,

: Da Alhaji Musa kwance take,

: An tasshe ta ta koma tsaye,

Y/Amshi     : A wajcn fuskar Musulunci,

: Yau Nijeriya ita ta daya,

 

Jagora        : Ranad dai ga watan goma,

: Cikin wata Oktoba,

: Cikin 1979,

: Rad da Shehu yaz zamo,

: Shugaban kasa mai cikakken iko,

: Duk Afurka ga baki daya,

: Duk inda Shugaban kasa yake,

: Wasu sun aiko da takardu,

: Wasu sun turo wakilansu,

: Wasu sun yo wayat tangaraho,

: Wasu sun aiko da takardu,

: Wasu sun shigo cikin Nijeriya,

Y/Amshi     : Su yi ma murnar samun girma,

 

Jagora          : Sun zo,

Y/Amshi     : Su yi ma murnar samun girma,

 

Jagora        : Hadarin kasa maganin mai kabido,

: Yaki mai yada gidan gona,

: Kauce yaro kauce giwa,

‘Y/Amshi    : In ka kiya tana tattaka ka,

: Shugaban Kasa Jikan Sule,

                   : Wada duk aka so ya ka

Jagora        : Sarkin Musulmi na murna,

: Na Sardauna ka goge makiyansa,

Y/Amshi     : Sun taru Ssun koma baya,

: Shugaban Kasa Jikan Sule,

: Wada duk aka so ka kai.

 

Jagora        : Yawo yana kara ilim,

: Yawo yana kara hankali,

: Yawo yana kara tunani,

:To ko ban yi karatu ba,

: Na ji dadin nau yawo,

: Amma ga Wani yat yawon banza,

Y/Amshi     : Bai yiy haske ba Kara duhu yay yi,

: Shugaban kasa jikan Salc,

: Wanda duk aka so Ka Kai.

Jagora        : Adamu AIiyu ban raina mai ba,

: Na yi godiya dan AIkali, x*

: Alhaji Danburan Na Katagun,

Y/Amshi     : Jikan Waziri ban rena mai ba,

 

Jagora        : Dan Waziri,

Y/Amshi     : Ban rena mai ba,

 

Jagora        : Dan Muhammadu jikan Mamman,

: Sarkin Gwaram,

Y/Amshi     : Waziri ban rena mai ba,

 

Jagora        : Sarkin Gwaram,

Y/Amshi     : Waziri ban rena mai ba,

 

Jagora        Sarkin Gwaram,

Y/Amshi     : Ban rena mai ba,

Jagora        Alhaji Baba Umar,

Y/Amshi     : Ya Rabbana ya kara wadata ka, x2

 

Jagora        : Ummaru jikan Mamman,

Y/Amshi     : Ya Rabbana ya kara wadata ka,

 

Jagora        : Na zo ka ba ni mota,

Y/Amshi     : Albarkacin girman mai girma,

 

Jagora        : Na zo ka ba ni mota ta hawa,

Y/Amshi     : Darajar girman mai girma,

Shugaban Kasa jikan Sule,

Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora        :Abin da nis sani,

:Ni nawa sani,

:Yawo yana kara ilmi,

:Yawo yana kara hankali,

:Yawo yana kara tunani,

Y/Amshi :   :Kai ko ban yi karatu ba, x2

 

Jagora :      :Na ji dadin nai yawo,

Y/Amshi :   :Amma ga wani yay yawon banza,

 

Jagora        :        Shi bai y1 haske ba,

YIAmshi :  :         Kara duhu yay yi,

 

Jagora          :Ni ai wuya ta da duniya,

:Ga wani don tsananin mulki,

: In yak kwanta sai an tassal,

:1o mulkin nashi ya kare,

Y/Amshi :   Yayi kwance ya rasa mai tassai,

 

 

Jagora

Y/Amshi:    :Yayi kwance,

:Yanzu,

                   :A riasa mai tassa1,

:Agora Ko kuwakka tai kyawu zaki,

:kuwakka tai ky

:Kada maza dal 2aki,

:ga wani na ei adi,

 

Jagora:        :Sai yana tadin ban yarda ba,

YAmshi        : Sai a sake sabuwar kokuwa,

 

Jagora:       :Shi ba kab bs wa,

Y/Amshi :  : Ya Rabbana ya kara wadata ka,

                    :Bai bakinai,

 

Jagora        :Shugaba mai cikakken iko,

Jagora :      :Uban Bala uban dan na Hude,

YAmshi :       :Alhaji Shehu giwa sha masu,

 

Jagora        :Alhamdu Lillahi sai Hamdala,                   

:Nasara tare da adalci aminci,

:Sun Koma wguda,

Y/Amshi :   : Shehu Shagari ka sa su aljihu

,

Jagora        :Maganar tsari na Nijeriya,

:Abin da kal fadi tilas aka dauka,

Y/Amshi :    :Yanzu ina wani ba kai ba,

 

Jagora        :Shehu Aliyu,

Y/Amshi     :Ina wani ba kai ba,

 

Jagora        :Duka Shugaban da anka yi Nijeriya,

:In bayan Prime Minister Tafawa,

:Sai Shugaban "Northern Nigeria,

:Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato,

:Ba wani shugaba mai cikakken Iko,

Y/Amshi :  :  Sai kai Alhaji Shehu amintacce,

 

Jagora"      :Field Marshal namu na Nijeriya,

:Shi ne shugaban "National Party,

:Bawan Allah dan bawan Allan,

Y/Amshi :   :Jikan bawan Allah ne shi,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora:       :Shehu,

Y/Amshi     :Jikan bawan Allah ne shi,

:Jagora Gaskiya kak ku hada ta da karya,

:Kowas samu tuwan masara,

:Idan dai yac ci ya Koshi,

Y/Amshi :   :To kun san bai cin kwakwa danya, x

Jagora        :Sar am sami gida na shiga,

:ldan dai an shiga an gine,

:Sannan za a nemi makulli,

:Idan dai babu gida na shiga,

Y/Amshi :   : Makullin ka ya zan,

 

Jagora        : Kai kan Malam,

Y/Amshi :   :Makullinka ya zan kam banz4,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora        : Ga zaki nan,

Y/Amshi :   : Yai tsaye gun mashigi,

 

Jagora:       : Wani wawa ya gitta mai,

Y/Amshi :    : Shi kau zaki yat tattaka shi,

:Jagora Na ci dariya Dankwairo,

:Wasu sun yi butulcCi gun Allah,

Y/Amshi     :Murnarsu ta koma kuka,

 

Jagora :      :Sabgar kwarai,

Y/Amshi :   :Ad da dadi, x2

 

Jagora :      :Ai gwanin tainyar kura,

Y/Amshi :   :Yana gaba ya koma baya,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora :      :Haji Baba Umar,

Y/Amshi :   :Ya Rabbana ya kara wadata ka,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora :                :Na zo ka ba ni mota,

: Dalilin Gwamna Tatari Al,

Y/Amshi :             :Dalilin girman mai girma,

 

Jagora :                : Na zo ka ba ni mota,

                              :Darajar Tatari Ali,

Y/Amshi :             Darajar girman mai girma,

 

Jagora :                :Darajar,

Y/Amshi :             :Girman mai girma,

:Shugaban Kasa jikan Sule

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora :                :Sai ya ba ka mota,

:Sai ka ba ni mota 504,

:Station Wagon,

Y/Amshi :             :Duk in shige,

:Ina ta bugun tur,

Jagora :                :Kuma ka ba ni mai tanhwal,

Y/Amshi              : Ta dauki kaya,

:Ta dau 'yan yarana,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora :               : Dattijo dan dattijo,

:Ran da yah hau mulkin Nijeriya,

:Ya taho Jihar Sakkwato,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

:Jagora Ya tati Jihar Kaduna,

 

Y/Amshi:              :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

Jagora                  :Ya tafi Jihar Kano,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoy anai,

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Kano,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Bauchi,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoyanal,

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Borno,

Y/Amshi:              :Can domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                 :Ya tali Jihar Gongola,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora:                :Ya tali Jihar Benuwe,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanal,

 

Jagora                   :Ya tali Jihar Rivers,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

:Shugaban Kasa jikan Sule

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Bendel,

Y/Amshi              :Can domin ya duba mutanenai,

:annan ya gal da masoyana,

:Shugaban Kasa Jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

Jagora:                :Jihar Imo ya zo ya duba,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                 Ya tafi Jihar lmo,

Y/Amshi:             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                 : Jihar Ogun ya zo ya duba,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da nasoyanal,

 

Jagora:                :Jihar Ondo ya zo ya leka,

:mutanenai.

YAmshi                :Domin ya duba mutanenai,

:yanai,

 

Jagora                 :Jaay y ya icha,

Y/Amshi               :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da ma

:Sannan ya gar da masoyanai,

 

Jagora                  :Ya tati Jihar Lagos,

Y/Amshi :             :Can domn ya duba mutanenai,

:Sannan ya gal da masoyanai,

:JagoraYa tali Jahar Kwara,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                  :Ya tati Jihar Lagos,

Y/Amshi:             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyana,

 

 

Jagora                  :Ya tali Jihar Bendei,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora                 :Jihar mo ya zo ya duba,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gat da nasoyanai,

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Imo yanai,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,

: Sannan ya gar da masoyanai,

 

Jagora                 :Jinar Ogun ya zo ya duba,

Y/Amshi:             :Domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

Jagora                  :Jihar Ondo ya z0 ya leka,

Y/Amshi                :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora:                :Jihar Oyo ya zo ya duba,

Y/Amshi :             :Domin ya duba mutanena,

:Sannan ya gai da masoyanai,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

 

Jagora:                :Ya tafi Jihar Lagos,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenal,

:Sannan ya gai da masoyanal,

 

Jagora                  :Ya tafi Jihar Kwara,

Y/Amshi:             :Can domin ya duba mutanenai,

:Sannan ya gai da masoyanai,

Jagora                  :Ya tafi Jihar Lagos,

Y/Amshi :             :Can domin ya duba mutanenai,,

:Sannan ya gai da masoyanai,

 

Jagora :                :Nijeriyag ga ta zama taka,

:Kai ko Shehu ka zama nasu,

Y/Amshi :             :Kowa ba ya gudun Shenu,

:Kuma Shehu ba ya gudun Kowa,

:Kowa ba ya gudun shehu,

:Kuma Shehu ba ya gudun kowa,

 

Jagora                 : Dan Aliyu ban,

Y/Amshi               :Rena mai ba,

 

Jagora                  :Adamu Aliyu,

Y/Amshi :             :Ban rena mai ba,

Jagora:                :Ina ta godiya dan Alkali,

: Muna ta godiya,

 

Y/Amshi                  :Dan Alkali,

:Shugaban Kasa jikan Sule,

:Wada duk aka so ya kai.

Jagora :                :Babban Manajan Airport,

:Muhammadu Yola na Hadeja,

Y/Amshi :             :Ya Rabban ya kara wadata ka,

 

Jagora                  :Babban Manajan Airport,

:Muhammadu Yola Hadeja,

:Dan Malam Muhammadu,

Y/Amshi:              :Ya Rabbana ya kara,

Jagora                  :Mijin Uwani,

YIAmshi:             :Ya Rabbana ya kara,

 

Jagora:                 :Mijin Uwani,

Y/Amshi:              :Ya Rabbana ya kara,

 

Jagora:                :Baban A'i,

Y/Amshi:              :Ya Rabbana ya kara wadata ka,

:Shugaban kasa Jikan Sule,

:Wada duk aka so ka kai.

Post a Comment

0 Comments