𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
السلام عليكم
Malam menene hukuncin mutumin da
ya kashe kansa sakamakon ya shiga kunci? Kuma menene matsayin masu yi masa
addu'ar Allah ya jiƙan sa, Shin hakan ya halasta ne ko kuwa? Ina son a yi min ƙarin
bayani na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
وعليكم السلام
Mutumin da ya kashe kansa ya
aikata babban zunubi daga cikin manyan zunubai da malamai ke kira Kabá'iruz
Zhunuub. Babu wani dalili da zai sa mutum ya kashe kansa a yi masa uzuri a nan
duniya, kuma Allah ya ce:
"KADA KU KASHE KAWUNANKU,
LALLAI ALLAH YA KASANCE MAI JINƘAI NE A GARE KU". Suratun Nisá'i, aya ta
29.
Hadisi ya tabbata daga Annabi ﷺ
cewa: "Duk wanda ya kashe kansa da wani abu, za a dinga yi masa azaba da
wannan abun a ranar Alƙiyama" Duba Sahihu Muslim hadisi mai lamba 110.
Sai dai a aƙidarmu ta Ahlussunnah
waljamá'ah, duk wani saɓon Allah da mutum ya yi Allah zai iya yafe masa idan ya
so in banda shirka, kamar yadda aya ta 48 da ke Suratun Nisá'i ta tabbatar.
Wannan ya nuna kenan Allah zai
iya gafarta ma wanda ya kashe kansa idan ya ga dama, idan kuma ya ga dama zai
yi masa azaba, daga bisani a fitar da shi daga azaba zuwa rahama matuƙar ya
mutu a kan musulunci, saboda wanda ya kashe kansa ba kafiri ba ne. Allah ya
tsare mu da mugun ji da mugun gani. A taƙaice dai lamarinsa na wurin Allah
Ta'ala.
Haka nan kuma, game da yi ma
wanda ya kashe kansa addu'a, wannan shi ma ya halasta, matuƙar ya kashe kansa a
halin zamowarsa Musulmi.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.