Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Auren Da Ke Mu'amala Da Wasu Maza A Waje

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mene ne hukuncin Matar auren da take da aure amma take mu'amala da wasu mazan, sannan ya matsayin aurenta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. Mu'amalar matar aure da wasu mazan za a iya kallonsa ta fuskoki biyu, akwai na lallura akwai na haramci. Duk wata mu'ala ta lallura kamar kasuwanci ya haɗa ta da wasu maza, ko lallurar asibiti, ko wani al'amari makamacin haka, to ya wajaba a kanta ta ji tsoron Allah ta kiyaye huruminta na zamowa mace, kuma ta aure, dole muryarta ta zamo ƙasa-ƙasa, yana yin diresin ɗinta ya zama kammalalle ba tare da nuna alamar wani abu da zai iya haifar da fitinuwa da ita ga wasu mazan ba.

Mu'amala ta haramun kuwa ita ce idan tana mu'amala da wasu maza irin mu'amala ta aure da bai halasta ta yi wa kowa ba sai mijinta, to matuƙar tana yin haka, to lallai tana aikata babban zunubi ne, kuma ta ha'inci mijinta, sannan yana daga cikin alamomin munafuƙi idan aka amince masa ya yi ha'inci kamar yadda hadisi ya nuna, kuma Allah zai ɗanɗana mata azaba matuƙar ba ta ji tsoron Allah ta tuba ba. Sannan kuma aurenta yana nan, sai ta ji tsoron Allah ta tuba, irin tubar da ba tunanin komawa ga saɓon Allah a gaba.

Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments