𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Warahmatullahi, malam ya aiki? Tambaya ita ce, ina da makociya wacce shekarunta sun ja sai ta zo ta tambaye ni a kan cewa shekaru 25 zuwa 27 a lokacin da ta haifi 'yar autar ta da wacce take binta ta sha azumi a dalilin haihuwa a Ramadana kuma ba ta ranka shi ba sai dagaba ya aka fada mata sai ta ranka, sai tazo guna ni kuma sai na tambaya mata malaminmu a kan matsayin ta sai ya ce ba sai ta ranka ba kuma ba za ta ciyar ba sai dai ta yi istigfari na fada mata. Amma yanzu haka ba ta da lafiya sosai, shi ne nake son in kara sani shin waccan fatawa daidai ce ko kuwa saboda azumin da aka lissafa ya kai azumi 40? Shin ya zan yi dan a halin yanzu da wuya in za ta iya azumi saboda rashin lafiyar, dan ta kai wata hudu komai sai an mata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám. 'yar uwa an
amsa makamanciyar wannan tambaya aba ya da dama, malaman Musulunci sun yi
maganganu kusan guda huɗu a kan matar da ta sha azumi saboda ciki ko shayarwa,
amma maganar da ta fi rinjaye, kuma wadda ita ce mafi yawan malamai suke tafiya
a kai ita ce:
Duk matar da ta sha azumi saboda
ciki ko shayarwa, to hukuncinta shi ne za ta rama (ranka) wannan azumin ne, ba
ciyarwa za ta yi ba, kuma wannan ita ce fahimta mafi rinjaye a wurin malamai.
Idan kuma rashin lafiya ya hana ta
rankawa, to za a duba ciwon da take fama da shi ne, idan likitoci ne suka
tabbatar da ciwon da take fama da shi ba wanda a kan warke ba ne a iliminsu, to
wannan ita ce za ta ciyar ba sai ta rama ba, amma idan har ciwon da take fama
da shi ana iya warkewa, to wannan ba ciyarwa za ta yi ba ranka azumin za ta yi.
Saboda haka, waccan fatawar da aka
ba ta na cewa ba sai ta rama azumin ba, kuma ba sai ta ciyar ba istigfari kawai
za ta yi, wannan kuskure ne babu ko shakka, istigfarin zai yi mata amfani ne a
kan jinkirin ramawa da ta yi, amma bai wadatar wurin biyan mata bashin wancan
azumin da ake bin ta ba.
Sai dai idan ya kasance ta tsufa da
yawa ne, ta yadda ba za ta iya yin azumi ba saboda wannan gajiyawar ta tsufa,
to a nan shi ne za ta iya ciyarwa, amma asali abin da ke kanta shi ne rankawa
ba ciyarwa ko istigfari ba, lallurar tsufar da zai hana ta ramawa ne ya sa aka
ce za ta ciyar ba rankawa (ramawa) ba.
Domin ƙarin bayani a duba Assharhul
Mumti'u Ala Zaadil Mustaƙni'i (6/347-350).
Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.