𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamou aleikoum, malam ina tambaya, ni ce na kasance na haihu wata daya kafin Ramadan, da Ramadan ya zo ban yi azumi ba, ban ma gwada ba ballantana in ga zan iya ko kuwa, kawai sai na fake da ciyarwa ban yi azumin ba, to malam ramkaci zan yi ko chiyarwa zan yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, Game da
hukuncin mace mai ciki da mai shayarwar da suka sha azumi, malaman Musulunci
sun yi saɓani game da abin da ke kansu na hukunci, shin ciyarwa za su yi kaɗai,
ko ramawa kawai, ko kuma ciyarwa da ramawa?
Waɗannan zantuttuka guda uku, wanda
ya fi rinjaye a cikinsu shi ne:
Mai ciki da mai shayarwa idan suka
sha azumi saboda kasawa ko tsoron kada su jigata, ko saboda tsoron kada abin da
ke cikin nasu ya jigata, to abin da ke kansu shi ne za su rama wannan azumin ne
da suka sha a lokacin da suka sami dama, ko da an sami jinkirin ramuwar saboda
wata lallura.
Saboda mai ciki da mai shayarwa ana
riskar da su ne a cikin marasa lafiya da matafiyan da suka sha azumi.
Sheikh Abdul'aziz Bn Baaz ya ce:
"Mai ciki da mai shayarwa hukuncinsu ɗaya da maras lafiya, idan azumi ya
tsananta a gare su an shar'anta masu karyawa, ramuwa ta tabbata a kansu a
lokacin da suka sami damar hakan, su kamar marasa lafiya ne, wasu daga cikin
malamai sun tafi a kan cewa abin da ke kansu shi ne ciyar da miskini a kowace
rana, sai dai wannan magana ce mai rauni wadda aka rinjaya. Abin da yake daidai
a kansu shi ne za su rama ne kamar hukuncin matafiyi da maras lafiya , saboda
faɗin Allah mai girma da buwaya da ya ce:
"Wanda ya kasance maras lafiya
a cikinku, ko a halin tafiya, to sai ya rama a wasu ranaku na
daban""Suratul Baƙara, aya ta 184.
Duba Majmú'u Fataawá na Ibn Baaz
(15/225).
Wannan ita ce fahimtar Fataawal Lajna
a mujallad na 10 shafi na 220, kuma ita ce fahimtar da ta fi rinjaye a wurin
mafi yawan malamai.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.