Hukuncin Yin Azumi Ranar Juma'ah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam ya gida ya iyali ya kokari da jama,a Allah yataimaka Allah yasaka da Alkhairi Allah yajikan iyaye

    Malam Dan Allah inaneman karin bayani game da azumi ranar Juma,a ance ba'ayin ko wani azumi ranar jumaa indai ba watan Ramadan ko da naramuwane ance bai halattaba ayishi ranar Juma,a shi ne nake neman karin bayani Allah yasaka da Alkhairi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Gaskiya ba haka Maganar take ba. Shi Annabi ﷺ ya hana mutum ya keɓance ranar Juma'a kaɗai ne don yin Azumi, ko kuma sallolin dare. Domin ita Juma'a ranar Eedin Mako ne ga dukkan Musulmai baki ɗaya.

    Mafiya rinjayen Malaman Musulunci sun ce wannan hanin da akayi, hani ne na karhanci ba wai haramci ba. Wato Keɓantar Juma'a da Azumi ba wai Haramun ba ne. Makruhi ne.

    Sai dai idan mutum ya azumci alhamis zai iya haɗawa da juma'ar. Ko kuma ya azumci asabar bayan ya azumci juma'ar. To idan mutum ya yi haka babu komai a kansa.

    Imamu Ahmad da Imamun Nisa'iy sun ruwaito wani hadisi ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-As (ra) tare da isnadi Ingantacce cewa:

    "Manzon Allah ﷺ ya shigo wajen Sayyidah Juwairiyyah bintul Harith (ra) -wato Matarsa- alhali tana azumi aranar wata Juma'a. Sai ya ce mata "SHIN KIN YI AZUMI JIYA NE?" Sai ta ce "A'a". Sai ya ce "KINA NUFIN YIN AZUMI GOBE NE?". Sai ta ce "A'a". Sai ya ce "TO TUNDA HAKA NE KI AJIYE AZUMIN".

    Wato ya umurceta ta ajiye azumin ne tunda ba ta Azumci Alhamis ba, kuma ba ta ɗauki niyyar azumtar Asabar ba. Don haka kar ta azumci juma'a kaɗai. Kamar yadda Sayyiduna 'Aamir Al-Ash'ariy (ra) ya ce "Naji Manzon Allah ﷺ yana cewa "HAKIKA RANAR JUMA'A RANAR EEDINKU CE, DON HAKA KAR KU AZUMCETA SAI DAI IDAN KUN YI AZUMI GABANTA KO BAYANTA".

    (Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi da Kyakkyawan Isnadi).

    Bukhariy da Muslim ma sun ruwaito shigen irinsa ta hanyar Sayyiduna Jabir bn Abdillahil Ansariy (ra).

    Amma Malamai sun ce idan kina azumtar Kwanaki uku ɗin nan akowanne Wata, kuma sai azumin ya haɗa har da Juma'a a ciki, to babu laifi ki azumceta. Ko kuma azumin ramuko ko Bakance, duk za ki iya azumtar Juma'a ɗin ba tare da Karhanci ba.

    Haka ma azumin Sittu Shawwal idan kina jerawa ne, za ki iya haɗawa da juma'a ɗin. Hakanan masu yin irin azumin Annabi Dawud ko azumin Kaffara, suma zasu iya haɗawa da ita. Kuma babu laifi.

    WALLAHU A'ALAM.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.