Ticker

6/recent/ticker-posts

Musan Tauhidi 01: Ka Rantse Da Allah Ko Ka Yi Shiru

Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce: Idan ɗayanku zaiyi rantsuwa ya rantse da ALLAH ko ya yi shiru.

[Bukhari da Muslim]

Wato wannan hadisi yana mana nuni da cewa ba a rantsewa da kowa ko da wani abu inba ALLAH ba.

 ba a rantsuwa da Annabi {s.a.w}, haka kuma ba a rantsuwa da wani abin halitta komai girmansa komai darajarsa.

 ba a rantsuwa da ɗakin ka'abah ko masallaci ko mala'ika ko wani sahabi ko sammai ko ƙassai.

 Amma ana rantsuwa da Alƙur'ani domin shi Alƙur'ani zancen ALLAH ne.

 Haka kuma kana iya cewa na rantse da Ubangijin ka'abah wato ALLAH kenan.

 Haka kuma kana iya cewa na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai wato ALLAH kenan.

 Haka kuma kana iya cewa na rantse da wanda numfashina ke hannunsa wato ALLAH kenan.

 Haka kuma kana iya cewa na rantse da Ubangijin Mala'iku wato ALLAH kenan.

 Ammaba ya halatta mai rantsuwa ya ce na rantse da Manzon ALLAH {s.a.w} ko waninsa.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubannu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments