𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mutane da yawa musamman 'yan boko
akida suna ta tambaya suna cewa: "Babu wani hadisi ingantacce da Annabi ﷺ
ya kashe wanda ya zage shi, hasalima akwai waɗanda suka aibata Annabi a
gabansa, suka zage shi amma bai kashe su, bai Kuma Yi umarni da kashe su ba,
don Allah malam Ya abin yake, kuma sahabbai ba su far musu ba"?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam, Allah Yana cewa
a cikin suratul Ahzaab aya ta (57): "Tabbas waɗanda suke cutar da Allah da
mazonsa ﷺ Allah Ya la'ance su a duniya da lahira Kuma ya tanazar musu da azaba
wula kantacciya"
Ka'ab dan Al'ashraf ya kasance Yana
cutar da Annabi ﷺ sai Manzon tsira ya shelanta cewa wa zai isar masa game da wannan
cutarwar da ake masa?, sai Muhammad dan Maslama Ya ce ya Manzon Allah ﷺ kana so
na kashe shi? sai ya ce na'am, sai ya tafi gidansa shi da tawagarsa, suka aika
shi lahira, bayan ya Yi sabuwar Amarya daga babban gida, Kamar yadda Bukhari ya
rawaito a hadisi Mai lamba ta (3811).
Annabi ﷺ ya samu labarin wani
Makaho da ya kashe baiwarsa cikin dare, sai ya tambaye shi me ya sa ka Yi
haka?, sai ya ce ta kasance mai tausasawa gare ni, Kuma Ina da kyawawan Yara da
ta haifa mi ni, amma Kuma tana aibanta ka, na kan hana ta, amma sai ta ki
hanuwa, jiya da daddare na ji ta tana aibanta ka sai na samo Adda sai na
dankara a cikinta, na danna har ta mutu, ɗan da yake cikinta ya bulluko, sai
Annabi ﷺ ya ce: "Ku shaida tabbas jininta ya ta fi a banza", Abu
dawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a hadisi Mai lamba ta ; (4361).
Ire-iren waɗannan hadisan suna da
yawa, suna tabbatar da aika duk Wanda ya zagi Annabi ﷺ zuwa Lahira .
Tabbas akwai munafukan da suke
aibanta Annabi ﷺ a zamaninsa Kamar yadda ya zo a suratu Attauba da kuma suratu
Almunafikun, amma bai kashe su ba, saboda mutanen da suke gefe za su ce
Muhammad ﷺ Yana kashe sahabbansa, saboda ba za su bambance tsakanin Wanda Ya
shiga Musulunci da wasa ba da kuma Wanda ya shiga da gaske, saboda wannan
maslahar Annabi ﷺ ya kyale su, don toshe barnar da za ta iya hana wasu shiga
Musulunci.
Idan mutum ya ga Wanda ya zagi
Annabi ﷺ bai iya jurewa ba har jami'an tsaro su karaso, ya aika shi Barzahu
saboda fusata da kuma sonsa ga manzon tsira ﷺ jinin arnen ya tafi a banza, Babu
kisasi, mutukar zagin da ya yi
da gangan ne, ba shi da tawili ko shubuhar da ta kasa warwaruwa, in kuma ya
bayyana ba zaginsa ya yi ba, to sai ya biya rabin diyyar Musulmi, amma ba za a kashe
shi ba.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.