𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
Alaikum, Malam dan Allah ya hukuncin auren da miji yake kira da Auren kaddara?
Kuma ya halasta mace ta ci gaba da zama da mijin al'halin bai kiyaye hamsu
salawat?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, baiwar Allah don miji ya kira aurensa da matarsa a matsayin auren ƙaddara
wannan bai ɓata auren
ba, sai dai kawai wata ƙila yana yi ne don ya ɓata
wa matar rai, kuma kuskure ne mutum ya aikata wani aiki don ya ba wani Musulmi
haushi ba tare da cancantar yin hakan ba, amma hakan bai ɓata aure ba a magana ta
gaskiya.
A dangane da
zaman aure da mijin da ba ya yin salloli biyar na kowace rana kuwa, to da farko
dai matar ya wajaba ta yi masa nasiha a kan hakan, ta kuma nuna masa ƙin yin
sallah kaɗai yana iya
mayar da mutum kafiri, idan an yi an yi da shi ya gyara, kuma an kai shi ƙara
wajen duk waɗanda ake
ganin zai ji maganarsu amma ya ƙi gyarawa, to daga nan sai ta kai shi ƙara
wurin hukuma ta raba wannan aure, saboda ba ya halasta mace Musulma ta yi zaman
aure da kafiri, duk da wasu malaman suna da fahimtar wanda ba ya sallah, kuma
bai yi inkarin wajabcinta ba, bai kafirta ba, amma fahimtar da ta fi dacewa da
ayoyin Alƙur'ani
da Hadisan Manzon Allah ﷺ,
da kuma fahimtar Sahabbai ita ce duk wanda kwata-kwata ba ya sallah to ya
kafirta, saboda faɗin
Annabi ﷺ cewa:
"Alƙawarin
da ke tsakaninmu da su (kafirai) shi ne sallah, duk wanda ya bar ta ya
kafirta".
Musnadul Imami
Ahmad (22937), Tirmizhiy (2621), Ibn Majah (1079).
Domin meman ƙarin
bayani duba Majmu'u Fatáwá na Ibn Uthaimeen (21/46 - 51). Ko a duba: Hukmu
Tárikis-Salati shi ma na Ibn Uthaimeen. Ko a duba Hukmu Tárikis-Salati na Almuhaddis
Nasirud-Deen Albániy.
Allah ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.