Ticker

6/recent/ticker-posts

Matar Da Mijinta Ba Ya Ba Ta Haƙƙin Ciyarwa Mene Ya Kamata Ta Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam tambayata a nan ita ce mijina ba ya ba ni hakkina na aure komai ya bar min ci da Sha da duk wasu hidimomi da miji ya kamata ya yi wa matarsa, kuma sai lokacin bukata ya neme ni, ni kuma na ki, ina da laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, ‘yar uwa duk matar da mijinta bai iya kiyaye mata haƙƙin ciyarwa ba, to tana da zaɓi guda biyu da addinin Musulunci ya ba ta:

Tana da damar ta nemi saki daga wurin mijinta, kasancewar ba ya ba da haƙƙin ciyarwa na abinci, saboda haƙƙin ciyarwa haƙƙi ne na wajibi a kan miji. Ko kuma ta yarda ta yi haƙuri ta ci gaba da zama da shi a haka idan ta ga za ta iya.

Wannan su ne zaɓi biyu da shari'a ta ba wa matar da mijinta ya gaza ba ta haƙƙin ciyarwa. Amma shi Imam Albagwiy ya ce:

"Idan ta zaɓi ci gaba da zama da shi tare da ƙuncin ciyarwarsa, ikon ya ji daɗi da ita bai lizimce ta ba, tana da damar barin gidansa, domin iko a kanta yana yiwuwa ne ta ciyarwa..."

Duba Attahzeeb Fiy Fiƙhil Imamis Sháfi'iy (6/309).

Malam Albuhutiy ya ce: "Tana da damar ci gaba da zaman aure tare da shi, tare da hana shi kanta, kuma shugabancinsa da zama a gidansa bai lizimce ta ba, kuma ba shi da damar yi mata kulle, zai bar ta ta nemi abinci, ko da ta kasance mai wadata ce, saboda shi ɗin bai ba ta abin da ake canjin jin daɗin da shi ba."

Duba Kasshaful Ƙana'i An Matnil Iƙná'i (5/477).

Maganganun waɗannan malamai sun nuna cewa ba ki da laifin ƙin ba shi haɗin kai da kika yi na gazawarsa wurin ba ki haƙƙoƙinki na wajibi a kansa, musamman ma ciyarwa. To amma ni shawarar da nake ba ki shi ne; ko dai ki yi haƙuri ki ci gaba da zama da shi a haka, tare da ba shi haƙƙoƙinsa da ke kanki, ta yadda idan rashi ne ya sa hakan ke faruwa har Allah ya wadata shi, ko kuma idan ba haka ba ne mugunta ce ta sa shi haka, to ki nemi saki daga wurinsa kamar yadda Shari'a ta ba ki wannan damar a irin wannan matsalar.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments