𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamou Alaikum, Malam ina kwana
da fatan kun tashi lafiya, Malam ina da tambaya shin ya halasta yin Addu'a a
sujada na sallar farillah da Hausa dan na ji wani malami yana cewa bai halastaba,
Malam mine ne bayani?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám, ‘yar uwa
malaman Fiƙhu sun yi saɓanin fahimta a kan yin addu'a da harshen da ba Larabci
ba a cikin sallah, akwai fahimtar da ta ce:
1. Ya halasta ga wanda ba ya iya
yin Larabci ya yi addu'a da wani harshe a cikin sallah, amma bai halasta ga
wanda ya iya kyautata Larabci ba, idan kuma har ya yi da harshensa alhali ya
iya kyautata Larabci, to sallarsa ta ɓaci.
2. Sai kuma fahimtar da ta ce Ya
halasta ga wanda ya iya kyautata Larabcin da wanda ma bai iya Larabcin ba su yi
adddu'a a cikin sallah da harshensu.
3. Fahimta ta uku kuma suka ce; bai
halasta ga wanda ya iya kyautata Larabci da wanda bai iya ɗin ba ma su yi
addu'a da wani harshen da ba Larabci ba a cikin Sallah.
Duba Almausú'atul Fiƙhiyya
Alkuwaitiyya (11/172, 173).
Amma fahimtar da ta fi zama daidai
ita ce ta farko, wato wanda bai iya Larabci ba, ko ba ya iya kyautata shi, to
ya halasta ya yi addu'ar da harshensa ko da a cikin Sallah ne, saboda Allah ya
san ma'anar abin da kowane harshe yake nufi, kuma ba ya ɗora wa rai face sai
abin da za ta iya.
Shaikhul Islam ya ce: "Addu'a
ta halasta a yi ta da Larabci ko ba da Larabci ba, Allah Mai Tsarki ya san
nufin mai roƙonsa da abin da yake nema, ko da harshensa bai tsayu ba, lallai
Allah ya san abin da amon sautuka ya ƙunsa duk da saɓanin harsuna, duk da
mabambantan buƙatu".
Dubi Majmu'ul Fataawá (22/489).
Saboda haka, ‘yar uwa ba laifi ga
wanda bai iya Larabci ba ko bai iya kyautata shi ba ya yi addu'a da harshen da
ba Larabci ba a cikin sujjada, amma makaruhi ne ga wanda ya iya Larabci sosai
ya yi addu'a da wani harahe a cikin sallah.
Allah S.W.T ne mafi sani
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
HUKUNCIN YIN ADDU’A DA HAUSA A
CIKIN SALLAH
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Malam, wani ne
ya ce wai malamai sun bayar da fatawar cewa ya halatta mutum ya yi addu’a da
Hausa a cikin sallah. Ni kuma na ce, gaskiya ban taɓa ji ba! Shi ne nake tambaya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Ba abin mamaki ba ne a samu
bambancin fatawa a kan mas’alolin fiqhu, saboda bambancin mahangar da malamai
suke duban mas’ala ta cikinsu.
Muhimmin abu dai shi ne:
Kowannensu ya ji tsoron Allaah, kuma ya gina bincikensa da maganganunsa a kan
tubali ƙaƙƙarfa
na ilimi, ba son-zuciya ko bin sha’awar-rai
ko shaci-faɗi ba.
Babu wani malami guda a bayan
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya zama tsararre daga
yin kuskure, ko mantuwa, ko zamiya a cikin maganganunsa na ilimi.
Don haka, dole ne duk malami
na-Allaah ya zama cikin shirin karɓar
gyara daga duk inda ta fito, matuƙar dai kuskurensa a cikin maganganunsa da
fatawoyinsa sun bayyana.
Nau’ukan addu’a a cikin Sallah
iri biyu ne: Akwai Du’aa’ul Mas’alah da kuma Du’aa’ul Ibaadah.
1. Na-farkon shi ne wanda a
cikinsa akwai nema da roƙon Allaah a fili cewa ya biya wata buƙata, ko dai ta hanyar
tunkuɗe wani sharri,
ko kuma ta hanyar janyo wani amfani ga mai yin addu’ar. Alal misali: Addu’ar Buɗe Sallah mai lafazin
اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ
الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنْ خَطَايَايَ ؛ كَمَا يُنَقَّى
الثَّوْبُ الْأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ ، اللَّهُمَّ اغْسِلْنِي مِنْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ
وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدِ
Ya Allaah! Ka nisantar da abin da
ke tsakanina da kura-kuraina, kamar yadda ka nisanta a tsakanin Gabas da Yamma!
Ya Allaah! Ka tsaftace ni daga kura-kuraina, kamar yadda ka tsaftace farar tufa
daga datti! Ya Allaah! Ka wanke ni daga kura-kuraina da ruwa da ƙanƙara
manya da ƙanana.
Amma Du’aa’ul Ibaadah kuwa ita
ce, wadda a cikinta babu roƙo ko neman wata buƙata a fili daga Allaah Maɗaukakin Sarki, sai dai
kawai karanta kalmomin girmamawa da kambama Ubangiji Ta’aala, kamar wani
lafazin na addu’ar Buɗe
Sallaah, cewa
سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ ، وَتَعَالَى
جَدُّكَ ، وَلَآ إِلَهَ غَيْرُكَ
Ya Allaah! Tsarki ya tabbata gare
ka haɗe da godiyarka;
kuma Sunanka ya yi albarka; kuma martabarka ta ɗaukaka;
kuma babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai kai!
Sannan yawancin wuraren da ake
yin karatu a cikin sallah sanannu ne, kuma kafaffu ne, waɗanda mutum ba shi da ikon
sauya su, ya zo da waɗanda
ba su ba, kamar haka
1. Bayan kabbara kafin a fara
karatu: Addu’o’in Buɗe
Sallah. Kafaffu ne.
2. A tsaye kafin Ruku’u: Karatun
Fatihah da Surah. Kafaffu ne.
3. A bayan Fatihah: Ameen.
Kafaffe ne.
4. Addu’a don kawar da waswasi:
Isti’azah. Kafaffiya ce.
5. A cikin ruku’u: Zikirori da
Addu’o’i. Kafaffu ne.
6. Dagowa daga ruku’u: Zikiri ne
kafaffe.
7. A cikin Sujada: Zikirori da
Addu’o’i. Kafaffu ne.
8. A zama tsakanin sujada-biyu: Zikirori da
Addu’o’i. Kafaffu ne.
9. Kafin ruku’un raka’ar ƙarshe:
Qunuut na Wutri , kafaffe ne.
10. Bayan ruku’un raka’ar ƙarshe:
Qunuut na Naazilah , ba kafaffe ne. Amma yana dacewa da yanayi ne.
11. Zaman Tahiya: KaratunTahiya,
kafaffe ne. Addu’ar neman tsari daga sharrin abubuwa huɗu, kafaffe ne. Sauran addu’o’i da zikirori
kafin sallama, kafaffu ne.
Daga nan an fahimci cewa
1. Yawancin wuraren yin addu’o’i
a sallah kafaffu ne, mutum ba ya iya zuwa da wata addu’arsa ta musamman a tare
da su, ko a maimakonsu.
2. Addu’o’in Al-Qunuut da aka ce
ana iya ƙarawa,
ana ƙarawa
da abin da ya dace da yanayin da ake ciki ne. Kuma da Larabci ake yi, ba da
wani yare kamar Hausa ba.
3. Ko a cikin Sujada da aka
riwaito cewa: Ku yawaita yin addu’a a cikinsa, da kuma Zaman Tahiya da aka
riwaito cewa: Sannan sai ya zaɓi
addu’ar da ya fi so ya yi , manyan malamai irinsu Al-Imaam Ahmad sun zaɓi cewa: Ma’anarsa ita ce:
Ku zaɓo daga cikin waɗanda suka inganta daga
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Kuma duk mun san cewa: Ba da
Hausa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi addu’o’insa ba.
Sannan kuma ga Sahabi Mu’awiyah
Bn Al-Hakam (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya gai da mai atishawa a cikin sallah a
masallaci. Daga baya kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
kira shi, ya gaya masa cewa: Wannan
sallar, babu wani abu na maganar mutane da ke gyara ta. Ita dai tilawar
Alqur’ani ce da zikirin Allaah kawai.
Idan kuwa har yin maganar Sahabi
da harshen Larabci a cikin sallah za a nuna cewa ba ya gyara sallah, to ina
kuma ga wanda ya yi da wani yaren da ba Larabcin ba, kamar Hausa?!!
Kuma idan muka yarda da cewa, ya
halatta a yi addu’a a cikin sallah da Hausa saboda hujjar wai mai yin addu'ar
bai iya Larabci ba, to ranar da wani ya zo da cewa, ya halatta a yi karatun
Fatihah ko Surah a cikin sallar da harshen Hausa ko Fulatanci ko wani harshen
da ba Larabcin ba, saboda irin wannan dalilin cewa bai iya Larabci ba, me za mu
ce masa?!
Tun da akwai sauran wuraren da
Shari’a ta bayyana cewa ana karɓar
addu’a a cikinsu, waɗanda
ba cikin sallah su ke ba, kamar: A tsakanin kiran sallah da iqamah; da ƙarshen
dare; da lokacin saukan ruwan sama; da lokacin da musulmi ke cikin tafiya; da
ranar Jumma’a,
musamman daga bayan la’asar
kafin faɗuwar rana, da
sauransu. Meyasa musulmi ba zai yi addu’a a waɗannan
lokutan da yarensa ba? Meyasa zai nace sai ya yi addu’a da yarensa a cikin
sallah, ta yadda zai iya samun matsala dangane da sallarsa?
A ƙarshe: Kar mu manta: Wanda ya bayar da
fatawa a kan halaccin hakan, ba fa wata aya ko hadisi ya janyo a fili ƙarara
mai nuna halaccin hakan ba, a iya saninmu. Illa dai kawai a fahimtarsa da
addini ne yake ganin babu matsala idan musulmi ya yi addu’a da yarensa a cikin
sallah! Shi ne muke cewa: Idan aka tafi Lahira kuma ya zama an samu matsala
fa?!
Don gudun hakan gara dai mutum ya
nisanci saka kalmomin da ba daga harshen Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) suka fito ba, a cikin sallarsa.
Wannan fahimtarmu kenan a kan
wannan mas’alar a yanzu. Wanda ya zo da hujjar da ta fi wannan a shirye mu ke,
mu karɓa daga gare
shi, kuma mu sauya matsayinmu, in shaa’al Laah.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah
Assalafiy
08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.