Alamomin Son Manzon Allah ﷺ ❤️

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Malam an ce mutum ya so Manzon Allah fiye da iyayesa, dan Allah ta ya mutum zai nuna haka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salám, 'yar uwa lallai babu shakka Manzon Allah ﷺ ya ce: "Imanin ɗayanku ba ya cika har sai ya zama ya fi so na fiye da ɗansa da iyayensa, da ma mutane baki ɗaya". Albukhariy (15), Muslim (44).

    Alƙali Iyadh ya faɗa cewa: "Lallai duk wanda ke son wani abu yakan fifita wannan abin, yakan kuma fifita dacewar lamurransa da wannan abin, idan kuwa ba haka ba, to bai zamo mai gaskiya a cikin soyayyar nan tasa ba, ya zama iƙrari ne kawai yake yi, masoyin Manzon Allah ﷺ na gaskiya shi ne wanda alamomin hakan ke bayyana daga gare shi, na farkonsu ya haɗa da:

    1. Yin koyi da SHI, da neman yin aiki da SunnarSA, da bibiyar maganganunSA da ayyukanSA, da kwatanta aiki da abubuwan umurninSA, da nisantar abubuwan haninSA, da tarbiyantuwa da ladubbanSA, mai wahalarsa da mai sauƙinsa da abin nishaɗinsa da kuma abin ƙinsa. Sheda a kan wannan magana ita ce faɗin Allah Ta'ala:

    "Ka faɗa masu ya Manzon Allah: In har kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah ya so ku". Ali Imran (31).

    Duba Asshifa'u Bita'areefi Huƙuƙil Musɗafa (2/24).

    2. Daga cikin alamar son Annabi ﷺ akwai yawan tunawa da SHI, duk mai son wani abu yakan yawan tunawa da shi, da kuma yawan fatan haɗuwa da SHI, saboda kowane masoyi yana son haɗuwa da abin soyayyarsa.

    3. Na daga cikin alamar son Manzon Allah ﷺ girmama SHI da daraja SHI idan aka ambace SHI, da kuma yin ƙanƙan da kai a dai-dai lokacin kiran sunanSA.

    4. Na daga cikin alamar Son Manzon Allah ﷺ yawaita yabonSA da abin da ya dace a yabe SHI da shi, mafi tuƙewar abin da za a yabi Annabi ﷺ da shi shi ne yaba masa da abin da Allah Ta'ala yake yaba masa kuma abin da SHI kanSA yake yaba wa kanSA da shi, Mafificinsa shi ne yin salati da tasleemi a gare SHI, saboda umarnin da Allah Ta'ála ya yi cewa:

    "Lallai Allah da Ma'ikunsa suna yi wa Annabi salati, ya ku waɗanda suka yi imani ku yi salati ga Annabi kuma ku yi tasleemi iya tasleemi" Ahzab (56).

    A cikin wannan ayar akwai umurnin yi maSA salati, don haka ne ma Manzon Allah ﷺ ya ce: "Marowaci ne wansa duk aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba" Attirmizhiy (3546).

    5. Yana daga cikin alamar soyayya ga Annabi ﷺ mutum ya so abin da Annabin yake so, waɗanda suka haɗa da Iyalan gidanSA, da SahabbanSA na Muhajirai da Ansar, da yin adawa ga duk wanda yake adawa da su, da ƙin waɗanda suke ƙiyayya da su kuma suke zaginsu, da bayar da kariya ga waɗanda Annabi ﷺ yake so ɗin can, da neman shiriya da shiryarwarsu, da kuma yin koyi da sunnarsu.

    6. Yana daga cikin alamar son Annabi ﷺ mutum ya yi ladabi wurin kiran sunanSA, kada mutum ya kira sunansa kaɗai ba tare da haɗa shi da wata kalma ta girmamawa ba, mutum ya siffanta shi da Annabci ko Manzanci wato ya ce; Annabin Allah, ko Manzon Allah, da makamancin haka.

    7. Na daga ciki akwai yaɗa sunnarSA, da isar da ita da koyar da ita ga mutane. Tabbas Annabi ﷺ ya ce: "Ku isar da saƙona ko da aya guda ce...". Albukhariy (3461).

    8. Yana daga cikin alamar son Manzon Allah ﷺ ba da kariya ga sunnarSA ﷺ, wato kare ta daga ɓarnar maɓarnata, da kare ta daga jirkitarwar masu guluwwi, da kare ta daga tawilin jahilai, da kuma kare ta ta hanyar yin raddi ga shubhohin zindiƙai da masu guluwwi, da bayyana ƙarerayinsu.

    Duba littafin can ASSHIFÁ'U (2/24 zuwa 28) domin ƙarin bayani.

    'yar uwa waɗannan su ne ginshiƙai da idan har aka samu sun tabbata a rayuwar mutum, to alama ce da ke tabbatar da wannan mutum masoyin Manzon Allah ﷺ ne na haƙiƙa kamar yadda malamai suka tabbatar. Wato kenan, iƙrarin son Manzon Allah ﷺ a baki kaɗai, ba tare da samun waɗancan alamomi a ayyukan mutum ba, to wannan bai sami kamala ta soyayyar Annabi ﷺ ba. Muna roƙon Allah da sunayenSA kyawawa da siffofinSA maɗaukaka da ya ƙara mana son Annabi ﷺ.

    Allah Ta'ála ne mafi sanin dai-dai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    Alamomin Son Manzon Allah

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Malam an ce mutum ya so Manzon Allah fiye da iyayesa, dan Allah ta ya mutum zai nuna haka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salám, 'yar uwa lallai babu shakka Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Imanin ɗayanku ba ya cika har sai ya zama ya fi so na fiye da ɗansa da iyayensa, da ma mutane baki ɗaya". Albukhariy (15), Muslim (44).

    Alqali Iyadh ya faɗa cewa: "Lallai duk wanda ke son wani abu yakan fifita wannan abin, yakan kuma fifita dacewar lamurransa da wannan abin, idan kuwa ba haka ba, to bai zamo mai gaskiya a cikin soyayyar nan tasa ba, ya zama iqrari ne kawai yake yi, masoyin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam na gaskiya shi ne wanda alamomin hakan ke bayyana daga gare shi, na farkonsu ya haɗa da

    1. Yin koyi da shi da neman yin aiki da Sunnarsa, da bibiyar maganganunsa da ayyukansa, da kwatanta aiki da abubuwan umurninsa, da nisantar abubuwan haninsa da tarbiyantuwa da ladubbansa, mai wahalarsa da mai sauqinsa da abin nishaɗinsa da kuma abin qinsa. Sheda a kan wannan magana ita ce faɗin Allah Ta'ala

    قُلْ إِن كُنتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

    "Ka ce: '' Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.'' (suratul Ali Imran Aya ta 31).

    Duba Asshifa'u Bita'areefi Huquqil Musɗafa (2/24).

    2. Daga cikin alamar son Annabi Sallallahu alaihi Wasallam akwai yawan tunawa da shi, duk mai son wani abu yakan yawan tunawa da shi, da kuma yawan fatan haɗuwa da shi, saboda kowane masoyi yana son haɗuwa da abin soyayyarsa.

    3. Na daga cikin alamar son Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam girmama shi da daraja shi idan aka ambace shi, da kuma yin qanqan da kai a dai-dai lokacin kiran sunansa.

    4. Na daga cikin alamar Son Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yawaita yabonsa da abin da ya dace a yabe shi da shi, mafi tuqewar abin da za a yabi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da shi shi ne yaba masa da abin da Allah Ta'ala yake yaba masa kuma abinda shi kansa yake yaba wa kansa da shi, Mafificinsa shi ne yin salati da tasleemi a gare shi, saboda umarnin da Allah Ta'ála ya yi cewa:

    إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا

    "Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi." (Suratul Ahzab Aya ta 56)

    A cikin wannan ayar akwai umurnin yi masa salati, don haka ne ma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Marowaci ne wansa duk aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba" Attirmizhiy (3546).

    5. Yana daga cikin alamar soyayya ga Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mutum ya so abin da Annabin yake so, waɗanda suka haɗa da Iyalan gidansa, da Sahabbansa na Muhajirai da Ansar, da yin adawa ga duk wanda yake adawa da su, da qin waɗanda suke qiyayya da su kuma suke zaginsu, da bayar da kariya ga waɗanda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake so ɗin can, da neman shiriya da shiryarwarsu, da kuma yin koyi da sunnarsu.

    6. Yana daga cikin alamar son Annabi Sallallahu alaihi Wasallam mutum ya yi ladabi wurin kiran sunansa, kada mutum ya kira sunansa kaɗai ba tare da haɗa shi da wata kalma ta girmamawa ba, mutum ya siffanta shi da Annabci ko Manzanci wato ya ce; Annabin Allah, ko Manzon Allah, da makamancin haka.

    7. Na daga ciki akwai yaɗa sunnarsa, da isar da ita da koyar da ita ga mutane. Tabbas Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Ku isar da saqona ko da aya guda ce...". Albukhariy (3461).

    8. Yana daga cikin alamar son Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ba da kariya ga sunnarsa, wato kare ta daga ɓarnar maɓarnata, da kare ta daga jirkitarwar masu guluwwi, da kare ta daga tawilin jahilai, da kuma kare ta ta hanyar yin raddi ga shubhohin zindiqai da masu guluwwi, da bayyana qarerayinsu.

    Duba littafin can ASSHIFÁ'U (2/24 zuwa 28) domin qarin bayani.

    'Yar uwa waɗannan su ne ginshiqai da idan har aka samu sun tabbata a rayuwar mutum, to alama ce da ke tabbatar da wannan mutum masoyin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ne na haqiqa kamar yadda malamai suka tabbatar. Wato kenan, iqrarin son Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam a baki kaɗai, ba tare da samun waɗancan alamomi a ayyukan mutum ba, to wannan bai sami kamala ta soyayyar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ba.

    Muna roqon Allah da sunayensa kyawawa da siffofinsa maɗaukaka da ya qara mana son Annabi Sallallahu alaihi Wasallam.

    Allah Ta'ála ne mafi sanin dai-dai.

    Jamilu Ibrahim, Zaria.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Questions and Answers

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.