Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk Abin Da Mijina Ya Siyo Sai An Raba Daidai Da Nawa Da Nasa Da Na ‘Ya’yansa, Shin Hakan Ya Yi Daidai?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam Allah ya ƙara ilmi, tambayata a nan ita ce ina tare da mijina da yaransa biyu macce da namiji, amma komai ya siyo kamar nama, ko rake ko dai wani abun marmari ya fi son in raba shi daidai da nawa da nasa da nasu, shi ne nake son in san hakan daidai ne kuwa? Sannan dan Allah malam a taimaka min da addu'ar da ake yi idan an sace abu domin Allah ya bayyana shi ko ya tona wa wanda ya dauka asiri. Na gode Allah ya ƙara lafiya.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, babu laifi don miji ya siyo wani kayan abinci ya ce a raba daidai da daidai a tsakaninsa da ke matarsa da sauran ‘ya’yansa, ai ba kayan gado ba ne balle a ce an zalunci wani an ba shi rabonsa da na wani, wannan kawai kayan ih'sani ne yake siyo maku, kuma shi ra'ayin sa kenan a raba daidai da yara da manya, wannan ba wani laifi a ciki.

Sannan kuma ni ban san wata addu'a da ake yi idan an sace wani abu don Allah ya bayyana wannan abun ba, ko kuma addu'ar da Allah zai tona asirin wanda ya sace ba, ni a iya ɗan abin da na sani ban san wannan addu'a ba, kuma ban taɓa jin labarinta a wurin malamai ba. Saboda haka mafita kawai ki yi addu'a da duk harshen da kika iya a kan Allah ya bayyana maki wannan abu da aka sace maki, ko kuma Allah ya ba ki wanda ya fi shi alheri, wannan ita ce shawarata.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments