Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin azuminta ya inganta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mace taji dumin jini amma jinin bai fito kafin magariba ba, ko kuma taji radadi na ciwon al’ada Amma kuma jinin bai zo ba to shin Azuminta na wannan ranar ya inganta ko kuma ya wajaba ta Rama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan mace taji dumi na haila kuma tana azumi Amma kuma Jinin hailan bai fito ba sai bayan sallar Magriba, ko Kuma taji radadi na haila Amma kuma jinin bai zoba sai bayan sallar Magriba bayan faɗuwar rana, to Azuminta na wannan rana ingantacce ne kuma ba za ta Rama wannan Azumin ba in na farilla ne kuma ladan Azumin bai ɓaci ba idan azumin ya kasance na nafila ne. 

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments