Citation: Bakura, A.R. & Sani, A-U. (2022). Kishi A Bakin Makaɗan Baka. In South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature (SARJALL), Vol. 4, Issue 02, Pp 45-57. ISSN 2664-8067 (Print) & ISSN 2706-5782 (Online). DOI: www.doi.org/10.36346/sarjall.2022.v04i02.002.
Kishi A Bakin Makaɗan Baka
Dr. Adamu Rabi’u Bakura1
Abu Ubaida Sani2
1 & 2 Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau
Tsakure
Manufar wannan maƙala ita ce bitar ma’anar kishi da yanaye-yanayensa, musamman a tunanin Bahaushe. Maƙalar ta bi matakin nazartar waƙoƙin makaɗan baka a matsayin hanyar gudanar da bincike. A cikin waƙoƙin ne ta zaƙule yanaye-yanayen kishi a farfajiyar tunanin Bahaushe. An ɗora akalar nazarin kan tunanin Bahaushe cewa “So so ne, amma son kai ya fi.” A bisa wannan ra’ayin Bahaushe ne takardar ke da hasashen cewa, kowane mutum na da zummar samun ɗaukaka da fice sama da dukkannin tsaransa. Sakamakon binciken ya nuna cewa, ba kamar yadda mutanen da dama ke tunani ba, al’amarin kishi bai taƙaita ga abin da ake samu tsakanin masoya ba kawai. Ya shafi dukkannin ɓangarorin rayuwa. Sannan dalilai da dama na sa a bayyana kishi. Daga ƙarshe takardar ta ba da shawarar bin matakan da za su tabbatar da giyar kishi ba ta kai ga janyo aikata abin da ya saɓa wa hankali da kyakkyawar al’ada da zamantakewar lumana ba.
Fitilun Kalmomi: Kishi; Waƙa; Makaɗa; Bahaushe; Hausa
1.1 Gabatarwa
Kishi kalma ce ta Hausa da ke cikin jinsin kalmomin da masana harshe suka saka a ɓangaren sunaye na maza. Wannan kalma tana a matsayin “suna” (noun). Bayan haka, takan ɗauki ɗafa-ƙeya. Ire-iren waɗannan ƙare-ƙare su suka wanzar da samuwar kashe-kashen kishi zuwa nau’uka daban-daban. Da zarar an ambaci kalmar “kishi” kurum ba tare da an ambaci kishin kaza ba, to a fahimtar mazauna ƙasar Hausa abin da zai faɗo musu a zuciya shi ne kishin da ke aukuwa a tsakanin mata da maza. A haƙiƙanin gaskiya kuwa, kishi bai taƙaita a wannan bagire ba kawai. A maimakon haka, ya shafi kusan dukkannin rayuwar ɗan Adam. Kai ba ɗan Adam ba kawai, kusan dukkannin halittu masu rai da aka yi bincike a kansu, sai an tarar da cewa suna da kishi.
Ganin cewa lamarin kishi abu ne da ya yi fice da shige a sha’anin rayuwar ɗan Adam, musamman ma Bahaushe, shi ya sa wannan maƙala ta karkato da akalarta wajen nazari a waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, domin a fito da sigar kishin da ke cikinsu. Hakan zai taimaka wajen fito da nau’ukan kishi fili. Sai dai wannan nazari zai keɓanta ne ga waƙoƙin fada da na maza da kuma waƙoƙin jama’a. Duk da haka an share wannan fagen ta hanyar bayyana ma’anar tubalan ginin wannan maƙalar. Tubalan kuwa su ne kishi da waƙa.
1.2 Dabarun Gudanar Da Bincike
Wannan bincike ya tattaro dukkannin bayanansa ne daga tushe. A cikin takardar, an ɗauki waƙoƙin baka a matsayin tushen bayani a matakin farko. A cikin waƙoƙin bakan ma, wannan takarda ta ware nau’uka uku domin taƙaita nazarin a kansu, wato:
i. Waƙoƙin Fada[1]
ii. Waƙoƙin Maza[2]
iii. Waƙoƙin Jama’a[3]
Bayanan da aka samu daga rubuce-rubucen masana da manazarta su suke daidaita alƙiblar nazarin. An ɗora binciken kan ma’aunin ra’ayin Bahaushe da ke cewa: “So so ne, amma son kai ya fi.” A bisa wannan ra’ayi, binciken na da hasashen cewa, waƙoƙon fada da na maza da na jama’a na ɗauke da tsattsafin burin son fice tare da zarra a cikin tsara. A taƙaice ke nan, hasashen binciken ya tafi kan cewa, kowane mutum na kishin kansa a matakin farko kafin waninsa.
2.1 Ma’anar Kishi A Luggace
Kalmar kishi ta ja hankalin masana da dama. Abraham (1962: 526) a ƙamusunsa ya bayyana ma’anar kishi ta hanyoyi daban-daban. Daga cikinsu akwai inda ya kira shi da “Ganin ƙyashi” (Jealousy). Akwai kuma ma’anar “Gasa” ko “rigengento” (rige-rige). Shi kuwa Bargery (1934: 613) a ƙamusunsa ya bayyana ma’anar kishi da cewa: “Kishi shi ne ganin ƙyashi da ke tsakanin kishiyoyi.” A cigaba da bayanin kishi, ya kawo kashe-kashen kishi kamar haka: “Kishin birni, kishin kai, kishin sauri a Karin harshen Kananci ko kishin samri a Katsinanci, da kuma kishin zuci.”
Yayin fassara ma’anar kalmar Larabci ta algirah wadda ke ɗauke da ma’anar kishi, Talata Mafara (2020) ya rawaito Nasif na cewa: “... canjawar zuciya da motsawar jini domin nufin ramuwa, saboda dalilin tarayyar wani abu da ba ya karɓar tarayya.” A cigaba da bayaninsa, ya ce: “Mafi tsananin kishi shi ne wanda ake samu a tsakanin ma’aurata.”
Yayin da muka dubi waɗannan ma’anonin kalmar kishi da masana suka bayar, za mu iya cewa, kishi wani yanayi ne da zuciya ke shiga na son ganin an samu ɗaukaka sama da sauran tsara tare da yin hamayya da duk wani mai yunƙurin kamo ta ko tarayya da ita a farfajiyar ɗaukaka ko jin daɗinta. Kishi na iya kasancewa hanya ta gwagwarmaya da ke tattare da zargi da tuhuma da saɓani da rashin jituwa da husuma da mugun nufi, domin ƙoƙarin kare keɓantacciyar ƙauna ga abin so ba tare da yin tarayya da wani ba. Duk da haka, addini na taka rawa wajen ganin kishi bai ɗauki alƙiblar mugun nufi na ƙyashi da hassada da nufin sharri ba.
2.2 Ma’anar Kishi A Ɗabi’ance
Bayan ma’anar kishi ta lugga, akwai kuma ma’anarta ta fuskar ɗabi’a, wato ma’ana ta sarari (fili). Ita wannan ma’ana, da zarar an faɗe ta kowa zai fahimta, ba tare da wani dogon tunani ba. A nan ma manazarta da dama sun tofa albarkacin bakinsu ta hanyar bayyana ra’ayoyinsu dangane da ita wannan ma’anar. Ingawa (1989: 3) ta bayyana ma’anar kishi da cewa: “... a Hausa na nufin wata hanya ta tsokana don nuna fifiko ko kare abin so dangane da irin matuƙar son da ake yi wa wannan abu.”
A ra’ayin Gobir kuwa, “kishi shi ne nuna damuwa a kan wata ni’ima ko baiwa da Allah ya yi ma wani mutun, tare da fatar ni’imar nan ta gushe (ƙare) ko kuma ta dawo gare shi, ko jin cewa, ni’imar ba ta dace da kowa ba sai shi kaɗai.”[4]
A taƙaice ke nan, a ɗabi’ance kishi ɗabi’a ce ga ɗan Adam da ke tattare da gwagwarmayar rashin son yin tarayya ga keɓantacciyar soyayya da ke aukuwa a tsakanin jinsin namiji da mace. Yayin da aka kalli lamarin kishi ta wata fuskar kuwa, za a iya bayyana shi da cewa, nau’i ne na ƙauna da fatar alheri ga wani abu da ke haddasa wa ɗan Adam aiwatar da gwagwarmayar da za ta taimaka masa wajen kare mutuncinsa da kansa da martabarsa da ɗaukakar darajarsa, da ɗorewar wanzuwar abin da yake so da ƙauna.
Irin wannan ma’ana ce ta wanzar da samuwar kishin zuci, da kishin addini, da kishin ƙasa, da kishin harshe, da kishin al’ada da dai makamantansu. Abin la’akari a nan shi ne, a sakamakon ɗafa-ƙeyar da ake yi wa kalmar kishin, shi ya haifar da nau’o’in kishi da ke ƙunshe da ma’anoni kala-kala kamar kishin samri ko kishin sauri da kishin birni da kishin uwar miji da kishin ƙanin miji da kishin banza da dai sauransu.
A bisa wannan fahimta, kishi wata halittacciyar ɗabi’a ce da Allah ya halicci bayinsa da ita, sai dai yadda halittun kan gabatar da kishin ne ya bambanta. Hakan kuma ya yi daidai da ra’ayin Bahaushe da aka ɗora wannan bincike kansa. A sassauƙar fahimtar ra’ayin, duk da mutum na iya kishin ƙasarsa ko garinsa da sauransu, to a farko yana kishin kansa ne kafin komai.
2.3 Ma’anar Waƙa
Waƙa a bisa ma’anarta a luggace tana nufin furta abin da ke cikin ƙwalwa. Domin tabbatar da haka, sau da yawa akan ji Bahaushe na furta nau’ukan kalamai da ke ƙasa:
a. Na waƙa yi masa dukan tsiya.
b. Na sha waƙa zuwa aikin Hajji.
c. Na waƙa masa farashin kayan.
d. To, Allah ya sa ba waƙa ba ce.
A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali Bahaushe kan ce:
i. Ai na zaci waƙa ce.
ii. Ya matse sauti kamar mai waƙa.
iii. Zaƙin murya sai ka ce zabaya.
Kalmar waƙa ba baƙuwa ba ce a cikin rubuce-rubucen masana da manazarta. Masana da dama sun kawo ma’anar waƙa a rubuce-rubucensu mabambanta. Daga cikinsu akwai Garba, (1990) da Gusau, (1984) da Umar, (1987) da Usman & Sani, (2020) da Gobir & Sani, (2021) da sauransu. Babban abin lura shi ne, dukkannin ma’anonin waƙa da masana ke bayarwa sun ginu ne kan muhimman kalmomi da suka haɗa da:
- a. Hikima da fasaha da zalaƙa
- b. Rerawa
- c. Tsari na musamman
- d. Ɗango/Shaɗara
- e. Baiti/Ɗiya
- f. Amo
- g. Ƙafiya
A taƙaice, waƙa ita ce duk wata tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da hikima da ake rera ta, gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman. Idan aka ce waƙar baka kuwa, waƙa ce da ba rubutacciya ba. Waƙoƙin baka na makaɗa, wasu muhimman tubala ne da ake ginawa domin ilmantarwa ko sadarwa ko nishaɗantarwa ko bayar da wata gagarumar gudunmawa a tsakanin al’umma. Hasali ma a iya cewa, waƙa kusan ta yi ruwa ta yi tsaki, ta dulmuya sosai a cikin rayuwar Bahaushe.
3.0 Yanayin Kishi A cikin Waƙoƙin Baka Na Makaɗa
Kalmar yanayi tana ƙunshe da ma’anar kamannu ko siga, ko ɗabi’u, ko halayya. Saboda haka, yanayin kishi a cikin waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, yakan ɗauki matakai daban-daban domin irin yadda kishin ya karkasu zuwa rukuni-rukun. Kuma kowane nau’i da sigarsa ta musamman da ake gabatar da shi. Don haka, abu ne mai matuƙar wuya a fito farar-ɗaya a bayyana wata bayyananniyar siffar da za a ce ta keɓanta ga kishi, musamman in ba an fito fili ƙarara aka bayyana takamaiman kishin da ake magana a kansa ba.
Kishi yakan bayyana a cikin waƙoƙin baka na Hausa ta fannin gargaɗi da faɗakarwa tare da wayar da kan al’umma don su kauce wa abin da ake hangen zai cutar da su, ko su aikata wani abu da ake sa ran zai amfane su. Wani zubin yakan zo ta hanyar shammatar abokin hamayya don a huce haushi. Kishi yakan bayyana ne ta hanyar nuna ƙyama da rashin jituwa tare da ƙoƙarin nuna wasu munanan ɗabi’un wanda ake hamayya da shi domin sauran al’umma su ƙyamace shi tare da guje masa. Akan nuna yadda al’umma kan duƙufa wajen gwagwarmayar mallakar wani abin duniya ko ƙoƙarin kare abin da aka keɓanta da sonsa kamar sarauta da mata. Wani zubin akan nuna fifiko tare da kasawar abokin hamayya. Yakan sauya kama ya zama zambo ko habaici ko nuna rashin damuwa a kan wani aibin da ya samu abokin hamayya.
Saboda haka, kishi ba ya da takamaiman yanayi, domin yakan ɗauki tubalai daban-daban a cikin waƙoƙin baka na Hausa domin gina wani jigo. Sai dai abin cewa a nan shi ne, lamarin ya dogara ne ga manazarci da kuma irin yadda yake ganin al’amarin kishi.
3.1 Kishi A Waƙoƙin Fada
Waƙoƙin fada su ne waƙoƙin da ake aiwatarwa ga mutanen da ke riƙe da sarauta ko wani mutum da ke da dangantaka da sarki ko wata sarauta. Masu aiwatar da ire-iren waɗannan waƙoƙin ana yi musu laƙabi da suna Makaɗan Fada. Su makaɗan fada, sukan zauna, a ƙarƙashin wani sarki, ya zama ubangidansu. Shi za su dinga yi wa waƙa, amma duk da haka sukan fita yawon kiɗi, su yi wa wani sarki waƙa da izinin ubangidansu. Irin wannan al’ada ta yawon kiɗi, takan sa a sami wani mawaƙi ya nuna kishinsa a kan wani, har ya kai ga yi masa zambo ko habaici, musamman in ya fahimci sarki yana son makaɗinsa. Irin wannan ne ya auku tsakanin Gurso makaɗin sarkin Mafara Barmo da Jankiɗi Sarkin Kiɗan Sarkin Katsinan Gusau Muhammadu Mai’akwai, a inda Gurso ya yi wa Jankiɗi habaici saboda tsananin kishi. Yake cewa:
Mai wuyar karo, toron giwa,
Ɗan Nagwamatse ba a Ja ma.
Rigo faɗa ma sarki, ai ta biɗam mani,
Gida Gusau, in dawo nan.
Zakara da kai da Jatau ku bar faɗa,
Taku sussuka ta yo tsaba,
Mun taho mu sam bakin shiƙa,
Don an ci daɓuri sai ba ta zo (Gusau, 1980: 56).
Wannan zambo da aka yi wa Jankiɗi, ya sa yaransa suka tunzura suka mayar da martani, saboda tsananin kishin ubangidansu, a ƙarƙashin jagorancin Dangaladimansa, Labo. Kishi ya rufe musu ido, wanda hakan ya sa suka saɓa wa al’ada ta hanyar yin zagi a cikin waƙar sarauta. Ga kaɗan daga cikin martanin da suka mayar masa a cikin waƙar:
Gagara gasa tsayayyen zaki,
Kurman giwa ratsa maharba.
Ka san Gurso shi a kare,
Ta shi da ɗiya nai mata guda,
Tana nan ko sai ban sha su kai,
In Gurso ya zo shi da swahe,
‘Ya’yan Gurso sai da marece,
Ba ɗamri aure suke yi ba,
Kowa shi zo shi haye ta,
Ga ta da su ci babu iyaka,
Wayyo Gurso za su kashe ni.
Bala’i sunan tsohon Gurso,
Uwa tai ko fatara ta hi duƙe,
Mai jan haure watse gidaje.
Burar Gurso ta isa bura,
Ta watse dogo da sakwati,
Ga jirgi nan ba shi wuce wa,
Ga ƙaura nan sai a yi hange,
Gurso baƙin jaki, bura ta kashe ka,
Gurso baƙin jaki, bura ta kashe ka,
Mai wa Allah duk shi yi taɓi,
Ba taɓin ƙwallo ba, na bura,
Baƙin jaki, bura ta kashe ka.
Na roƙi Rabbu Allah Sarki,
Allah ka isamman ga matsaci,
Abubakar, Umar, Usman, Aliyu,
Albarkar nan tasu na roƙa,
Allah sa Gurso shi makance (Gusau, 1980: 57-58).
Idan muka kalli waɗannan ɗiyoyin za mu tarar cewa, kishi ya sa yaran Jan-kiɗi su fito fili ƙarara ba tare da wata fargaba, ko kunya ba, suka ci wa Gurso mutunci, tamkar yadda mace kan yi, a yayin da wutar kishi ta ruru a zuciyarta.[5]
Makaɗan fada ba kanwar lasa ba ne wajen bayyana ksihinsu, sai dai suna da hanyoyi dama da suke amfani da su wajen nuna kishin. Wani zubin idan kishin ya motsa, sukan fito fili ƙarara, ba kunya ba tsoro, su nuna cewa duk a cikin sarakuna babu kamar sarkinsu (ubangidansu), kuma a tsakanin mawaƙa, ba kamarsu. Misali Narambaɗa ya faɗi irin wannan, a inda yake cewa:
Bana Ahmadu Hausa ka yi rinjaye, ni na yi,
In an ce Isa, ba ka jin an ce wani sarki,
Ni ko duk Hausa ba ka jin waƙa bayan tau
(Shinkafi, 1998: 65).
Idan muka dubi wannan ɗango za mu tarar, Narambaɗa na ƙoƙarin ya bayyana wa jama’a cewa, Sarkin Gobir Ahmadu ya fi duk sauran sarakunan ƙasar Hausa ɗaukaka da alheri da daraja. Haka shi ma makaɗinsa, ya fi duk sauran mawaƙan Hausa iya waƙa. Duk ya yi hakan ne a sakamakon kishin da yake yi wa sarkinsa.[6]
Har ila yau za mu ga cewa, kishi kan sa makaɗan fada su fito fili su nuna kasawar sauran mawaƙa, musamman abokan hamayyarsu. Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya yi irin haka a cikin waƙar ‘Yandoton Tsahe, a inda yake cewa:
Duk makaɗin da at Tsahe nai jam’i
Har baƙi har ‘yan gidan su duka,
Babu mai ƙulla waƙa kamat tawa,
Ga makaɗi ya ƙulla waƙa tai,
Sai a amsa mashi, ba a ƙara mai,
In na ƙulla waƙa a ƙara man,
Mu huɗu duk azanci gare mu,
Shin ƙaƙa mutum guda za ya radde mu?
(Alhaji Musa Ɗanƙairo: ‘Yan Doton Tsahe)
Dubi irin yadda kishi ya sa Ɗanƙwairo koɗa kansu ta hanyar nuna cewa duk makaɗan da ke ƙasar Tsahe da baƙi da ‘yan gidan ba wanda ya kai shi iya waƙa, balle ma ya fi shi. Ba nan kaɗai ya tsaya ba, domin har ya yabi ‘yan amshinsa da azancin ƙari da kulla waƙa. Daga nan kuma sai ya nuna kasawar abokan hamayyarsa na rashin irin wannan azanci nasa.
A wasu lokutan kuwa makaɗan fada kan nuna kishinsu ne a yayin da suka fahimci wani na ƙasa da su yana son ya yi jayayya da su. A cikin irin wannan yanayi ne sukan fito ɓaro-ɓaro su bayyana ma duniya cewa lallai wannan bai kama ƙafarsu ba. Misali Narambaɗa ya yi irin wannan a cikin waƙarsa, a inda yake cewa:
Zamfara ba makaɗin da ka ja min,
Baya ga Jankiɗi, sai ko Ɗandawo,
Sai Ɗandodo Alu mai tabshi,
Amma ba makaɗin gayya ba,
Ai ba a gama ni da yaro,
Na san yaro bai yi muƙamina ba,
Kar ku gama ni da yaro,
Na san yaro bai yi zalaƙata ba,
Kar ku gama ni da yaro,
Na san yaro bai yi fusahata ba,
Ƙaryar banza yaro bai kai,
Inda Narambaɗa mai tabarniƙun sarki
(Shinkafi, 1998:6).
Haƙiƙa kishi ne ya sa Narambaɗa ya fito yana jayayya da wani matsashin mawaƙi, a inda yake bayyana wa jama’a da’awarsa ta fin sa muƙami da zalaƙa da fasaha. Hasali ma har ya kai ga yi wa al’umma hannunka mai sanda da cewa idan har za su yi kamance, to kar su kamanta shi da mai kiɗin gayya, kuma dai shi yaro ne. Idan har kamance za a yi, to sai a kamanta shi da irin su Jankiɗi, da Ɗandawo da kuma Ɗandodo Alu, mai tabshi. A ganin Narambaɗa, da waɗannan mawaƙan kaɗai za a iya kwatanta shi.
A ɓangaren kishin kai, mawaƙan fada ba a bar su a baya ba, domin yana ɗaya daga cikin abin da ke sa mawaƙi ya yi wa kansa kirari wanda zai jawo masa ƙwarjini tare da yin barazana a idon jama’a, domin kowa ya kasance yana son shi, kuma ya rinƙa sha’awar sauraren waƙoƙinsa. Misali Salihu Jankidi ya nuna haka a cikin waƙarsa, a inda yake cewa:
Azka takwas da girken sulaƙi,
Wandon doma da jabba ta ƙawa,
Na sa tsala na yi naɗi,
Na kammala nai haske,
Da ni duk da ɗiyana,
Kowa gane mu sai ya ce,
hala Jankiɗi ya zo,
Shi na (Gusau, 1980: 48).
Babu shakka wannan ɗango ya nuna mana yadda mawaƙin ke kishin kansa. Hakan ne ya sa har ya fito fili yana barazana da yadda shi da yaransa ke cika fuska, har jama’a su rinƙa sha’awar zuwa kallon su a yayin da suke aiwatar da sana’arsu ta waƙa.
Makaɗan fada sun fi yawancin jama’a amfani da tufafin gargajiya, in ka cire sarakuna da malaman addini. Domin a kullum za ka same su sanye da manyan riguna da wandunan buje, da taguwoyi masu manyan hannaye, da kuma hulunan dara, ko dogayen huluna, irin na gargajiya. Haka kuma za a same su a mafi yawan lokuta da naɗin rawani a kansu. Sun dai riƙe wannan al’ada ta sanya suturar gargajiya ne a sakamakon irin kishi da suke yi wa al’adun, hasali ma irin waɗannan tufafi ne sarakuna kan ba su. Wannan shi ya sa kishinsu bai ta’allaka kan amfani da suturar ba sai da ya kai su ga bayyana su a cikin waƙoƙinsu. Misali Ɗanƙwairo a cikin waƙarsa ta gargajiya yana cewa:
‘Yan Arewa da an nan,
Waɗanda aɗ ɗiyan Musulmi,
Ƙwairo na gargaɗin ku,
Ku zan azumi da sallah,
Ku zan kono da zakka,
Ku matan ƙasarmu,
Waɗanda aɗ ɗiyan Musulmi,
Ku zan ka yin lulluɓi,
Ban da sayen suket da ‘yak kanti,
Kuna yawo rariya-rariya,
Abin ga ya ba da kunya,
Abin ga da ban takaici,
Sai ka ga ɗan Musulmi,
Ya sa wando yadi guda,
Ga ‘yar shat ya sanya,
Ya sa ‘yas suwaita,
Ba hula ga kai nai,
Aljihu nai ba tasbaha,
Sai ƙwalin sigari (Ibrahim, 1983: 24).
Idan muka dubi wannan ɗango za mu ga irin yadda Ɗanƙwairo ya bayyana kishinsa ta fuskar addininsa wato Musulunci, a inda ya nemi Musulmi da tsayar da rukunan nan na Musulunci ta hanyar kula da salla da zakka da azumi, har ma da zakkar fid-da-kai. Daga nan sai ya gangaro a kan matan Musulmi, a inda ya nemi su rinƙa yin lulluɓi, kamar yadda Musulunci ya yi umurni. Sannan kuma ya ja musu kunne a kan su daina kwaikwayon al’adun Turawa ta hanyar sa ƙananan tufafi waɗanda ke bayyanar da tsiraici. Hasali ma da ya zo kan maza, ya nuna ƙyamarsa a kan masu ɗabi’ar nan ta amfani da guntuwar sutura, wadda ta saɓa wa al’adun ƙasar Hausa, hasali ma irin wannan sutura takan muzanta wanda ya ƙaƙaba wa kansa ita. Sannan ya jawo hankalin matasa da su watsar da ɗabi’ar shan sigari.
Makaɗan sarauta ba kawai sun tsaya a kan kishin amfani da suturar gargajiya ba ne kawai, domin kuwa sukan hankaltar da al’umma don su kula da sana’o’in gargajiya. Misali Sarkin Taushin Katsina ya nuna irin wannan kishi a cikin waƙarsa ta Al’adun Gargajiya, a inda yake cewa:
‘Yan yara ‘yan makaranta,
Manya da ƙanananku ku ɗau zancena,
Ku kama al’adu na iyayenku,
Kar ku yarda da aikin banza,
Kai ji zakkuwar Turawa,
Sun tarar da mu muna da sana’ar hannu,
Muna da al’adunmu na gargajiya,
Da za mu gadara mu ma,
Akwai maƙera namu,
Na gargajiya suna da sana’ar hannu,
Akwai magina namu,
Kuma muna da dukawanmu,
Kuma muna da wanzamanmu,
Kuma muna da mata masu zare,
Nan ƙasarmu ga marina, ga baba,
Akwai masaƙa namu na gargajiya,
Da ke mana saƙa tun can
(Sarkin Taushin Katsina: Waƙar Al’adun Gargajiya)
Babu shakka, duk wani da ya nazarci wannan ɗiya, zai tabbatar cewa lallai wannan mawaƙi ya tabbata mai kishin al’adunsa, har ma da ƙasar Hausa baki ɗaya. Mawaƙin ya yi matashiya ne game da riƙe sana’o’inmu na gargajiya da muka gada kaka-da-kakanni, kamar ƙira, gini, jima, dukanci, wanzanci da zare da saƙa tufafi da rini da kayan da ake aiwatar da su, kamar baba, waɗanda mu muke noma abinmu, ba sai an sayo daga wata ƙasa ba. Lallai ke nan waƙar ba ta tsaya kan kishi al’ada kawai ba, har ya haɗa da kishin ƙasa.
3.2 Kishi A Waƙoƙin Maza
Waƙoƙin maza, su ne waƙoƙin da ake yi wa jarumai wato masu nuna bajinta. Wannan rukuni ya ƙunshi ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan farauta da ɓarayi da ‘yan kokawa, domin tun can asali, jarumai ne aka sani ke aiwatar da su. A cikin irin waɗannan waƙoƙin, za a tarar cewa suna ƙunshe da kishi. Hasali ma idan aka yi nazari, za a fahimci cewa, sai wanda ake kishi za a tsaya a rera masa waƙa, irin wannan.
Waƙoƙin maza sun bambanta, kamar yadda mazan suka bambanta. Hasali ma Hausawa kan ce kowane allazi da nasa amanu. To irin haka ya haifar da bambancin makaɗan maza da kuma irin yadda sukan bayyana kishinsu. Misali mawaƙan ɓarayi kan haɗa da yin ‘yan tsafe-tsafe, domin su tabbatar da sun cimma muradinsu. Don kuwa a wurin waɗannan mawaƙan, babu abin kunyar da ya fi makaɗi ya takali namiji, shi kuma namijin ya kasa yin motsi. Don haka tilas sai an shirya. Misali an yi wani namijin kuturu, mai asiri wanda, ya tara malamai ya ce ya daina tsafi da farauta da fashi, don haka a roƙa masa Allah, ya shirye shi. Yayin da Barau (makaɗi ne) ya samu labari, sai ya kwashi kayan kiɗansa, sai can, ya fara kiɗa, yana cewa:
Biyo ka sha ruwa ta ƙare,
Tunda babu ranka a kundi,
Ni kam da duniya tana yarda ma,
Da ta yarda ni cikin tsummana,
Da kowane kuturu kamarka ya watse,
Da duniyag ga ta yi kushewa,
Amma lokacin kana tsaye daidai,
Ban ƙi uban kowa ya guggule ba[7]
A cigaban ruwayar, wannan ziga da Kassu Zurmi ya yi ta tunzura wannan jarumi har ya riƙa kirari, yana cewa:
Ku tashi malamai tun cikin girmanku,
Ku tashi tun kuna da rawunna,
Wallahi kun ci ragon banza,
Tuba babu razana, kuma babu,
Na dawo gare ka, mai buga kawo,
Sake man kiɗa, ka sa mini rana,
Sai na ba ka kan mutum tara daidai.
Wannan ya nuna mana irin yadda makaɗa kan ratse hanya domin tsananin kishi da suke nunawa idan wani daga cikin mazajensu ya dawo wa hanya. Hasali ma kishinsu ne ya haifar da wannan kuturun ya tunzura har ya dawo yana yin wasu kalamai ga malaman da ya tara.
Wasu mawaƙan sukan nuna kishinsu ne ta hanyar ƙara wa gwarzayensu ƙaimi. Hasali ma sukan kwatanta su da abubuwan ban tsoro, ta yadda abokan hamayyarsu za su razana domin su samu galaba a kansu. Misali, Ɗan’anace ya yi irin haka a cikin waƙar da ya yi wa Shago, a inda yake cewa:
‘Yan maza kun ji kiɗin kututturu, na Bakura
Duna mahaukaci na Yamma da Rimi,
Rigima Aradu mai ɗume kurma,
Mutuwa ina ruwanki da tsoho,
Kai shi lahira gidan ɗan gangu,
Burundumi abin zuba shara,
Samji irin hakin da ka ramno,
Lahira a kai miki gawa,
Yaro gafarakka ga sababi nan
Kada aradu ta farma,
Halan ba ka san halin ƙanin ajali ba,
Sannu da ɗibar sheɗa,
Mutuwa kin daɗe kina kashe bayi,
In da lahira ana buga dambe,
Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai (Tukur, 2001: 30).
Makaɗin ya zuga gwarzonsa, wato Shago ta hanyar amfani da kalmomi kamar, mahaukaci, rigima, aradu, barundumi, mutuwa, lahira, sababi, ƙanin ajali, mai ɗibar sheɗa, mai kashe bayi - duk ya siffanta shi ne da waɗannan abubuwa domin abokan adawarsa su razana, har lakar jikinsu ta mutu, su kasa taɓuka komai, idan sun yi ido biyu da Shago a fagen dambe.
A wasu lokutan kuwa, irin waɗannan makaɗan sukan yi wa gwarzayensu hannunka mai sanda ne, saboda tsananin kishinsu da suke yi. A irin wannan hali ne sukan lurar da su cewa, su kula kada su bi zugar da suke yi musu, domin tana iya kai su ga halaka. Ɗan’anace ya bayyana irin wannan kishin, a inda yake cewa:
Wallah in kana biyat ta kiɗina,
Walle ina halaka ka,
Sai na sa ka inda ba ka hitowa,
Sai mu rage kiɗi, mu sassauta mai,
Don kai ya haukace baki ɗai (Tukur, 2002: 58).[8]
Wani lokacin, makaɗan maza kan bayyana kishinsu ta hanyar yi wa gwarzonsu kyakkyawar fata. Wannan shi ya sa Ɗan’anace ya yi wa Ɗandunawa addu’a ta neman tsari, a inda yake cewa:
Allah agaza mana,
Kada shaggu su cim muna (Gusau, 1984: 56)
Wannan ya ƙara nuna mana cewa kishin da mawaƙan ke nuna wa gwarzayensu, na ƙauna ne, ba na hamayya da ƙyama ba.
3.3 Kishi A Waƙoƙin Jama’a
Waƙoƙin jama’a, waƙoƙi ne da ake rera wa sauran mutane, ba tare da ƙeɓancewa ga wani rukuni na jama’a ba. Masu aiwatar da ire-ien waɗannan waƙoƙin, su ake yi wa laƙabi da makaɗan jama’a. Hasali ma ba su ta’allaƙa ga kowa ba. Sukan yi wa kowa da kowa kiɗa da waƙa, muddin dai aka yi musu hasafi ko kuma suka ga alamar za su sami abin masarufi. Don haka ba su da takamaiman wani rukuni da suke yi wa waƙa, balle su yi takatsantsan ko su nuna jin kunya ko sanin ya kamata, domin kare martabar wani. Wannan shi ya sa suka bambanta da sauran rukunonin mawaƙa, kuma shi ya haifar aka samu bambancin yadda suke gabatar da kishinsu a yayin da suke aiwatar da sana’arsu.
Mawaƙan jama’a kan bayyana kishinsu ta hanyoyi da dama. Wasu kan bayyana kishin nan da ke tsakanin mata da miji, musamman inda aka samu rabuwar aure a tsakanin ma’auratan. Idan kuwa an samu faruwar haka, mawaƙi ya samu labarin wani na neman matar da ya saki, to a cikin irin wannan hali mawaƙin kan fito fili ya bayyana kishinsa ta hanyar yi wa wancan zambo ko ma ya fito fili ya zage shi. Za a iya ganin irin wannan a cikin waƙar Alƙali Maɗanɗani ta Mamman Shata. Hasali ma bincike ya tabbatar da cewa an gina tulabin wannan waƙar ne a sakamakon kishin matarsa mai suna Yelwa, wadda alƙali ya raba shi da ita. Daga baya kuma sai alƙalin ya koma yana neman ta tare da wani mai kuɗi (Rafukka, 1999: 58). Shata na cewa:
Ni an fi ni,
An ƙwace man matata da na so
Wannan shi ya ƙwace
Matar Shata ya tai ya ci.
(Mamman Shata: Waƙar Alƙali Maɗanɗani)
Idan muka dubi wannan baitin za mu iya fahimtar cewa, an aiwatar da waƙar ne domin a huce haushi. Hasali ma Shata ba ya tsaya kawai a kan bayanin an yi masa ƙwacen mata ba, har ya kai ga zagin wanda ya ƙwace masa matar, a inda yake cewa:
Wai na ji kahurin kirari ranar yake mata,
Ga ta baƙa gajeruwa.
Ya ga gajeruwa ‘yar baƙa,
Shegen Tudun-Wada.
Shegen ya yi gida a Zariya,
Tudun-Wada.
Yau ga kafiri,
Marar kunya ɗan baƙar uwa.
Ku kore shi Zariya,
Nan dai zuwa ya yi.
Allah tsine ma,
Allah watse maka.
Ka kau ji sau biyu,
Tun da ka hau,
Ruwan cikin matata gajeruwa.
(Mamman Shata: Waƙar Alƙali Maɗanɗani)
Waɗannan ɗangaye sun nuna yadda tsananin kishi ya sa Shata fitowa ƙarara, ba tare da shakka ko tsoro ba, ya ambaci abokin hamayyarsa da cewa shi kafiri ne. A wani gun kuma ya ce masa shege. Hasali ya yi wa jama’a hannunka mai sanda, domin a gane abokin hamayyar tasa ta hanyar nuna mazauninsa tare da bayyana wa jama’a cewa baƙo ne, don haka a kore shi. Daga ƙarshe dai ya tsine wa abokin hamayyar tasa, kuma ya ce ya yi haka ne a kan kishin ya sadu da matarsa.
Mawaƙan jama’a ba su tsaya kawai wajen yi wa waɗanda suka raba su da matan aurensu zambo ba, har sukan yi wa wanda ya yi yunƙurin raba su da karuwarsu zambo. Wannan za a iya ganin sa a cikin waƙar Sani Sabulu mai take: Waƙar Mai Dadiro. An gina waƙar kan irin wannan kishi ne. Ya aiwatar da ita ne a dalilin dukan da wani mai dadiro ya yi wa wata karuwa a garin Dingyaɗi, wadda ake yi wa laƙabi da ‘Yaryakanaye. An doke ta ne saboda Sani Sabulu ya sauka gunta. Hasali ma ya tafi da ita wurin wasa. Wannan shi ya sa kishi ya yunƙuro wa Sani, ya rufe masa ido, ya yi wannan waƙa. Dubi yadda yake siffanta mai dadiro da abubuwan ƙyama, a inda yake cewa:
Mai dadiro kana kayan yunwa,
Mai dadiro kana da baƙar dauɗa,
Mai dadiro kana kayan tsumma,
Mai dadiro kana da kinibibi,
Mai dadiro kana da baƙin kishi,
Mai dadiro kana da baƙar fitina,
Mai dadiro kana da ƙoshin baƙin rai.
(Sani Sabulu: Waƙar Mai Dadiro).
A wannan ɗiya, ya bayyan mai dadiro a matsayin mayunwaci, mai zunubi, kuma huntu, wato marar sutura, kuma munafuki, mai tsananin kishi da faɗa da kuma baƙin rai. Sani Sabulu ya yi haka ne domin ya huce haushinsa. Bugu da ƙari, shi Alhaji Sanin ya yi ishara da haka a inda yake cewa:
Ga yanzu wannan kiɗa na mai dadiro ne,
Ku masu dadiro kak ku gune,
Mai dadiro guda yat taɓo ni,
Saboda Nana,
Kai wace Nana,
Shugaba Nana ‘Yaryakanare,
(Sani Sabulu: Waƙar Mai Dadiro).
A wannan ɗiyar waƙa, ya bayyana dalilin waƙar, wanda shi ne kishi, don haka ne yake nuna wa sauran masu irin wannan hali cewa wani ne ya tsokane shi don kawai ya sauka a gun farkarsa.
Mawaƙan jama’a ba su tsaya a kan bayyana kishin da ke da alaƙa da mace ba, har ma akan sami lokutan da sukan nuna kushe ga junansa, saboda tsananin kishi. A irin wannan yanayi ne akan sami mawaƙi na nuna kishin kansa ta ƙoƙarin kare mutunci da kuma irilinsa a tsakanin al’umma. Za a iya samu kyakkyawan misali a cikin waƙar Mamman Shata ta Bakandamiya. A cikin wannan waƙar, Shata ya nuna kishin kansa ta hanyar barazana domin ya jawo hankalin jama’a wajen sauraren waƙarsa, wanda hakan zai sa ya sami abin duniya, a inda yake cewa:
Matsoraci ba shi zama gwani ko wane ne,
Ya zama kamar ni hilin waƙa,
Saranin waƙa ban san tsoro ba.
In na fito Shata ne,
Kun san ni na san ku,
Sai ƙaƙa?
(Mamman Shata: Waƙar Bakandamiya)
Kishin kai ya sa Shata koɗa kansa da kansa, a inda ya ke nuna cewa shi gwanin waƙa ne, wanda ba ya tsoro ko nuna fargaba a duk lokacin da aka nemi ya shirya waƙa nan take. Hasali ma saboda kishi, Shata yake ɗaukar wasu rukunonin mawaƙa ba bakin komai ba, waɗanda ba su kai matsayin su yi jayayya da shi ba. Don haka ne yake cewa a cikin waƙar:
Na ƙyale banjo da kukuma,
Wargin yara ne.
(Mamman Shata: Waƙar Bakandamiya)
Mawaƙan baka na jama’a sukan gina waƙoƙinsu ta amfani da tubalan kishin kai. Sukan yi haka ne domin kare martaba da zubewar mutunci a idon jama’a. Ɗaya daga cikin halaye mafiya muni a ƙasar Hausa shi ne a ce Musulmi yana tsafi. Hasali ma ko da yana yi ba zai so a bayyana shi a matsayin matsafi ba. Don haka ne Shata ya fito yana ƙalubalantar masu zargin sa da cewa yana amfani da iskoki wajen yin waƙoƙinsa, a inda yake cewa:
Ba malamai ba ne,
Ba bori, ba na tsafi,
Ni haka Allah yai ni,
Da yai ni kau ya tsare ni.
(Mamman Shata: Waƙar Bakandamiya)
Mawaƙin bai tsaya nan ba, sai da kishi ya sa ya fito fili ya faɗakar da masu wannan da’awar, ta hanyar nuna musu irin halayyar nan ta ɗan Adam ta son kai da babakere ga duk wata harka da ta shafi mallakar abin duniya da kuma jin daɗi, inda koyaushe mutum zai fi son komai daga shi sai ‘ya’yansa, musamman abubuwa da suka shafi dukiya, kamar kuɗi da gidaje da motoci da kuma kyawawan mata. Wannan ya yi daidai da tunanin Bahaushe da takardar ta ginu a kansa. Misali Shata na cewa:
In malami ne ya fara shirya ‘ya’yanshi,
Su samo, su kawo mashi,
Koko su ba sa son samu sai dai ni?
Da tsohona?
A’a, da sakel,
Ku bincika dai, samu fa!
In bori ne, su fara girka ‘ya’yansu,
Su samo, su kawo masu,
Ko ko su ba sa son samu sai dai ni da tsohona?
Nairori, gidaje da motoci ga sutura,
Ga mata, zumdum-zumdum,
Kai ta nemo ma ɗan wani, kai ga naka?
(Mamman Shata: Waƙar Bakandamiya)
A ɓangare guda kuwa, mawaƙan jama’a kan gina waƙoƙinsu domin kishin sana’arsu, musamman a cikin yanayi na siyasa, wanda aka hana kiɗa da waƙa. Hakan na faru musamman idan da mawaƙan ne aka yi fafutikar yaƙin neman zaɓe, har haƙa ta cimma ruwa, to amma sai aka wayi gari aka kafa dokar hana roƙo. A yanayi makamancin wannan, waɗannan mawaƙan duk lokacin da suka tunkari ‘yan siyasa, sai su kada baki su ce ai an hana roƙo, saboda shari’a ake. Wannan al’amari shi ya yunƙuro da kishin sana’arsu, a inda Bello Ɗanshabiyu yake cewa:
Ba mu tura ta, kuma mu ba mu ce ku tura ba,
In dai motar siyasa ce, dab bana ba ni tura ta.
Motag ga da ac cikin turɗa,
Mun zaka munka tura ta,
Don mu makaɗa ka waƙarta,
‘Yan yara su kama kuwwatta,
Karuwai na zauwa zaɓe,
Motar ta kai saman kwalta,
Daɗa ko lib ba a ɗaukar mu.
Suka rantse kiɗi haramun ne,
Suka ce roƙo haramun ne.
(Bello Ɗanshabiyu: Waƙar Motar Siyasa)
Idan aka yi la’akari da waɗannan ɗiyan waƙar, za a fahimci cewa mawaƙin yana gangami ne a kan a ƙaurace wa ‘yan siyasa, saboda sun sami nasara, amma sun yi watsi da su. A ciki ya bayyana wa al’umma cewa ba za su sake taimakon duk wani ɗan siyasa ba, domin ko ya sami nasara ba wani amfani da za su samu. A wani ɓangaren kuma mawaƙin ya fito sarari ya nuna kishinsa a kan malaman addini, waɗanda yake zargin su ne suka bayar da fatawar hana kiɗa da waƙa. Don haka ne Bello Ɗanshabiyu ya fito ƙarara yana cewa:
Da ‘yan mata,
Da ‘yan yara,
Da mu makaɗa na turaye,
Kuma ba mu ce ku tura ba,
Bari mai wa’azi ya tura ta,
Shi ya san da Allah ne,
Don Allah ba a ɓoye mai
(Bello Ɗanshabiyu: Waƙar Motar Siyasa)
Ta fuskar kishin ƙasa kuwa, za mu tarar cewa, mawaƙan baka sun yi ƙoƙarin cusa wa al’umma kishin ƙasarsu, ko kuma na wani ɓangaren da suka fito. Mawaƙan kan yi amfani da tubala daban-daban domin gina wannan yanayi. Ire-iren waɗannan tubalan sun haɗa da gargaɗi, faɗakarwa, wayar da kai da dai sauran su. Misali Alhaji Mamman Shata ya rera wata waƙa mai suna Yan Arewa Ku Bab Bacci, a inda yake gargaɗin ‘yan Arewa kamar haka:
‘Yan Arewa ku bab bacci,
Nijeriyarmu akwai daɗi,
Ƙasar Afirka baƙar fata,
In ka yi yawo ciki nata duk,
Ba kamar Nijeriya gidan daɗi,
Balle Arewa uwad daɗi.
(Mamman Shata: Waƙar Yan Arewa Ku Bab Bacci)
Shi kuwa Ali Ɗansaraki saboda tsananin kishin da yake yi wa sashen da ya fito, sai ya ɓuge yana yabon sashen, wato Arewa, a inda yake cewa:
Idan ana dara fid da uwa ake,
in ana maganar Nijeriya,
to ai ta Arewa tana gaba,
don ƙasar albarka tamu ce,
tabbata tutar Shehu tana nan.
(Ali Ɗansaraki: Waƙar Arewa)
Shi kuma Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai, saboda kishin da yake yi wa ƙasarsa, a tasa waƙar, kira yake ga ‘yan Nijeriya gaba ɗaya da su haɗa kansu, domin ta haka ne kaɗai ƙasar za ta ci gaba. Yana cewa:
Ina Yarbawa, Nufawa,
Ina jama’ar Ibo,
Da ku jama’ar Tibi,
Duk ku taru, mu je gaba ɗai,
Mu koma ‘yan uwa.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar Haɗa Kai)
4.0 Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya fahimci cewa, kishi na zuwa cikin sigogi mabambanta. Daga cikin nau’ukan kishi akwai kishin kai. Narambaɗa ya nuna kishin kansa kamar yadda ya fito a Waƙar Sarkin Gobir Ahmadu da aka kawo a ƙarƙashin 3.1 da ke sama inda ya ce “Ni ko duk Hausa ba ka jin waƙa bayan tau.” A nan ya nuna kishinsa ga sauran makaɗa tare da kore duk wata tarayya da aka yi da shi a fagen fice a duniyar waƙa. A ƙarƙashin 3.3 ma an nuna yadda Mamman Shata ya bayyana kishin kansa a cikin waƙarsa ta Bakandamiya. Duk waɗannan sun yi daidai da tunanin Bahaushe da takardar ta ginu a kansu game da son kai ko kishin kai.
A ɓangare guda kuwa, akwai kishin ubangida. Dangane da irin wannan yanayi, an ga yadda yaran Jankiɗi suka nuna kishin ubangidansu yayin da Gurso ya taɓa shi cikin waƙa. A misali wani irin wannan, an ga yadda Narambaɗa ya nuna cewa ubangidansa wato Sargin Gobir Ahmadu ya shafe kowa, shi kaɗai ne sarki a Isa. A waɗansu lokutan kuwa, mawaƙa na nuna kishin al’ada ko addini. An ga irin wannan a cikin waƙar Alhaji Musa Ɗanƙwairo ta gargajiya. A ciki ya nuna kishin tufafin gargajiya na Hausawa. Sarkin Taushin Katsina ma ya nuna irin wannan kishi a waƙarsa ta Al’adun Gargajiya.
Bayan haka, akan samu yanayi da ubangidan makaɗi ya yi sanyi, ma’ana ya ɗan ja baya ga jarumtar da yake da shi, ko kuma ma ya kauce hanyarta gaba ɗaya. A irin wannan yanayi makaɗi na iya nuna kishinsa tare da yin duk abin da zai yi domin ganin jarumta da fifikon ubangidansa ta ɗore. An ga irin haka cikin misalin da aka kawo na Kassu Zurmi a ƙarƙashin 3.2 da ke sama. Duk da haka, akan samu makaɗa da ke faɗakar da waɗanda suke kambawa ta hanyar nuna musu su yi takatsantsan domin kada su takalo abin da ya fi ƙarfinsu. Wannan yana nuni ga soyayya da kishin da suke musu. A ƙarƙashin 3.2 da ke sama, an ga yadda Ɗan’anace ya yi irin wannan inda ya faɗakar da Shago cewa ya lura kada kambawa ta kai shi ta baro shi.
Nau’in kishi mafi sanuwa shi ne wanda ya shafi al’amarin soyayya. Shi ma yakan fito a cikin waƙoƙin makaɗan baka na Hausa. An ga misalin irin wannan a cikin waƙar Mamman Shata ta Alƙali Maɗanɗani wanda aka kawo a ƙarƙashin 3.3 da ke sama. Sani Sabulu ma ya yi abu makamancin wannan a cikin waƙarsa ta Mai Dadiro.
A ɓangare guda kuwa, kishin ƙasa ko yanki na sa makaɗan baka kasa danne abin da ke zukatansu. A ƙarƙashin 3.3 da ke sama an ga misalai makamantan wannan da suka haɗa da waƙar Arewa ta Ali Ɗansarki da kuma Waƙar Yan Arewa Ku Bab Bacci ta Mamman Shata. Shi ma Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ba a bar shi a baya ba wajen nuna irin wannan kishi a inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su taru su yi kishin cigaban ƙasarsu.
5.0 Kammalawa
Lallai kishi abu ne da ke tare da kowace irin halitta, musamman ma bani Adam. Don haka, ba abu ne wanda zai keɓanta da wani jinsi ba. Idan aka yi la’akari da misalai da ke ƙunshe cikin ɗiyoyin waƙoƙin da aka nazarta, za a iya fahimtar cewa, kishi ya zama ruwan dare game duniya. Ya yi shige da fice a cikin kowane irin al’amari na zaman rayuwar duniya. Za ma a iya cewa, ba za a iya taɓuka komai ba a rayuwa idan babu kishi. Haka kuma, duk al’ummar da ta rasa shi, za ta ga taskun duniya. Abin da ya fi kyau shi ne, a bi matakan tabbatar da cewa giyar kishi ba ta kai ga ingiza mutane zuwa aikata ayyukan da suka saɓa wa zamantakewar lumana ba. A bi matakan tabbatar da cewa sahihin koyarwar addini da kyawawan al’adu sun yi jagorancin zukata game da abin da ya shafi kishi, domin tabbatar da zamantakewa kyakkyawuya. Malaman addini da shuwagabanni da mawaƙa da marubuta duk na da rawar takawa a wannan fage.
Manazarta
Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari Kan Waƙar Baka TaHausa, Zariya : Gaskiya Corpora-Tion limited.
Abraham, R.C. (1960). Dictionary of The Hausa Language, London: University Press.
Bakura, A.R. (2003). Gurbin Kishi A Adabin Hausa: Tsokaci Kan Zube Da Waƙoƙin Baka. Kundin digiri na biyu (M.A. Hausa) Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Bakura, A.R. (2014). Kishi A Ƙasar Hausa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English Dictionary and Enlish-Hausa Vocabulary, Zariya: Bugu Na biyu, Ahmadu Bello University Press Limited.
Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa, Lagos:Ibrashi Islamic Publications Centre Limited.
Garba C. Y. (1990). Ƙamus Na Harshen Hausa, Nigeria: Evan Brothers Publishers Limited.
Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing Press. ISBN: 978-978-59094-0-01.
Gusau, S.M. (1984). Nazarin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka Na Hausa, Littafi Na Ɗaya. Kaduna: Barakar Publishers Ltd.
Gusau, S.M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa, Kaduna: Fisbas Media Services.
Gusau, S.M. (2002). Salihu JankiɗI Da Waƙoƙinsa. Kano: Kaduna: Barakar Publishers Ltd.
Gusau, S.M. (2014). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka Na Hausa. Na ɗaya da Na biyu, Kano: Century Research and Publishing Limited.
Ibrahim, M.S. (1983). Kowa Ya Sha Kiɗa, Nigeriya: Longman Limited.
Ikara, A.T. (1988). Gudummawar Waƙoƙin Makaɗa Wajen Wayar Da Kan Jama’a, takardar da Aka gabatar a Jami’ar Bayero, Kano.
Ingawa, Z. S. (1989). Kishi A Ƙasar Hausa: Yanayi Da Amfani Da Illolinsa, Maƙalar da aka Gabatar a makon Hausa na sha-tara, Jami’ar Bayero, Kano.
Inuwa, A. da wasu, (1993). Alhaji Sani Sabulu Na Kanoma Da Waƙoƙinsa, Kundin Digiri Na ɗaya (B.A. Hausa) , Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Jinju, M. H. (1981). Rayayyen Nahawun Hausa, Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.
Rafukka, B.S. (1999). Zambon Shata: Nazari Da Sharhi Na Wasu Daga Ciki Waƙoƙin Alhaji Mamman Shata. Kundin Digiri Na Farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Shinkafi, S.I. (1998). Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali (1875-1960). Kundin Digiri Na Farko (B.A. Hausa). Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
Talata Mafara, M.I. (2000). Kishi Da Zamantakewar Ma’aurata A Musulunci, Kaduna: Bamoya Printing Press.
Tsahe, S. M. (2000). Nazari A Kan Waƙar Motar Siyasa Ta Alhaji Bello Ɗanshabiyu. Kundin Neman takardar shaidar EN-SI-I a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sakkwato.
Tukur, I. (2001). MakaɗI Aka Fi Mu Ba Dambe Ba: Damalmalar Salon Kambamawa A Cikin Waƙar Shago Ta Ɗan’anace, Kundin Digiri Na Farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Umar, M.B. (1987). Dangantakar Adabi Da Al’adun Gargajiya, Kano: Maɗaba’ar Kamfanin Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.
Usman, B.B. & Sani, A-U. (2019). Gargaɗi ga Kyautata Zamantakewa: Faɗakarwa Daga Alƙalamin Isan Kware Ɗan Shehu. In East African Scholars Journal of Education, Humanities and Literature, Volume-2, Issue-10, Pp 621 - 632. ISSN 2617-443X (Print) | ISSN 2617-7250 (Online). Available at: https://www.easpublisher.com/get-articles/950.
[1] Kamar yadda Bahaushe ke cewa “burin kowane ɗan sarki shi ne ya zama sarki,” haƙiƙa dole a tsammanci cin karo da kishi a cikin fada. Idan kuwa haka ne, to lallai za a ci karo da tsattsafin kishi a cikin waƙoƙin makaɗan faɗa. Wannan kuwa shi ne dalilin da ya sa aka zaɓi “waƙoƙin fada” a cikin ɗaya daga cikin nau’ukan waƙoƙi uku da nazarin zai mayar da hankali kansu.
[2] A duk inda aka samu wata gasa, musamman ta nuna jarumta da bajinta, kowane ɗan takara so yake ya kasance zakara. A bisa wannan dalili ne binciken ke hasashen cewa, dole za a samu tsattsafin kishi cikin waƙoƙin maza. Idan kuwa akwai, to yaya siga ko sigogin kishin suke?
[3] A rayuwar jama’a ta yau da kullum akwai kishi. Tsinto baituka kan kishi daga bakin makaɗa zai taimakawa wajen fahimtar yadda al’amarin yake dalla-dalla.
[4] An karɓi wannan bayani daga bakin Dr. Y.A. Gobir a hira da aka yi da shi baki da baki.
[5] Hasali ma, mai da martanin ya sa har Gurso ya kai ƙara gaban Alƙali Yahaya na Sakkwato, daga ƙarshe aka gane shi ne ba shi da gaskiya, don shi ne ya fara. Sai Alƙali Yahaya ya yi wa Gurso faɗa. Hasali ma Sarkin Musulmi Abubakar ya tara su, ya yi musu gargaɗi daga ƙarshe, ya shirya su (Gusau, 1980: 59).
[6] Hasali ma za a iya ganin wannan a zahiri, domin kuwa Narambaɗa ba ya yi wa duk wani ɗan sarki ko basaraken da ba ya ga maciji da ubangidansa waƙa. Ana iya cewa, saboda irin wannan hamayyar ce ya sa har ya bar gidan duniya bai yi wa Sardaunan Sakkwato waƙa ba.
[7] An samu waɗannan bayanai daga bakin Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza (2001). Mawaƙin shi ne Kassu Zurmi.
[8] Wannan ɗiyar waƙa ta bayyana mana irin cikakkiyar ƙaunar da ke tsakanin Shago da Ɗan’anacen ke kishinsa.
author/Rabi'u, A.R. & Sani, A-U.
journal/South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature
pdf-https://www.researchgate.net/publication/359773848_Kabilu_a_Tunanin_Bahaushe_Duba_Cikin_Labaran_Barkwanci
paper-https://www.researchgate.net/publication/359773848_Kabilu_a_Tunanin_Bahaushe_Duba_Cikin_Labaran_Barkwanci
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.