Cite this article as: Sani, A-U. & Kaura, H. L. (2021). Daga Sassabe Zuwa Lauma: Tsokaci Game da Tasirin Zamani a Abincin Hausawa. Ɗanyamusa Journal of Curent Research in Hausa Studies, (1)1, p. 284-295.
Daga Sassabe Zuwa Yin Lauma: Taƙaitaccen Tsokaci Game da Tasirin Zamani a Kan Abincin Hausawa
Abu-Ubaida
Sani
Department
of Languages and Cultures
And
Habibu
Lawali Kaura
Federal
College of Education (Technical) Gusau
Abstract
Modernity has introduced a lot of inventions and new trends with regards to Hausa foods. This does not only concern the dietary habits of the Hausas but the totality of the process of food processing starting from land preparation through harvesting to cooking. The article investigates the influence of modernity on Hausa foods. The major objectives of the study are to examine the new inventions to the Hausa food processing and preparation processes as well as to ascertain the overall positive and negative impacts of such new trends. The research is based on Food Neophobia and Variety Seeking theory. It is hypothesized that the Hausas will accept modernization in their search for new tastes. The research learned that despite the numerous importance of modern inventions, they have many negative effects on personal health, ecosystem, as well as socioeconomic wellbeing of individuals, especially if not utilized properly. Finally, the paper suggested that there should be joint efforts by governments, resource persons, and media outlets as campaigns for educating and orienting the public extensively on proper utilization of the modern innovations, a strive which should be accompanied by well-planned programs to support the less privileged individuals harness the benefit.
Keywords: Modernity; Food; Farming; Cooking
Tsakure
Zamani ya zo da ƙirƙire-ƙirƙire da sauye-sauye da suka
shafi abincin Bahaushe. Wannan bai taƙaita ga cimaka ba kawai, ya haɗa har da dukkannin matakan samar da abinci (tun
daga gyaran gona har zuwa girbi) da kuma sarrafa shi. Takardar ta mayar da
hankali ne kan bincike game da tasirin zamani a kan abincin Hausawa. Maƙasudin
gudanar da binciken shi ne nazartar ƙirƙire-ƙirƙire da suka shafi samarwa da
sarrafa abincin Hausawa tare kuma da nazartar alfanu da komabayan da waɗannan
sauye-sauye suka zo da su. An ɗora nazarin a kan ra’in Food Neophobia and Variety Seeking (Ƙyamar
Abinci da Neman Nau’i).
Binciken na da hasashen cewa Hausawa za su karɓi abubuwan da zamani ya zo da su
yayin da suke ƙoƙarin neman sababbin nau’ukan abinci masu gamsarwa. Binciken ya
gano cewa, duk da ɗumbin alfanun da zamananci ya zo da su a wannan ɓangare,
suna ƙunshe da matsaloli da dama da suka shafi lafiya, yanayi, zamantakewa, da
kuma tattalin arziki – musamman idan ba yi amfani da su yadda ya kamata ba.
Daga ƙarshe takardar ta ba da shawarar cewa gwamnati da masana da kafafen
sadarwa su haɗa hannu wurin wayar da kan al’umma da faɗakarwa game da illolin
da ke tattare da abubuwan da zamani ya kawo tare da hanyoyin cin gajiyarsu da
kauce wa haɗurran da ke tattare da su.
Muhimman Kalmomi: Zamani; Abinci; Noma; Girki
1.0 Gabatarwa
Kamar yadda duniya ba a wuri ɗaya take tsaye ba, ta kasance tana zagayawa,
haka ma al’amuran duniya suke samun sauye-sauye. Sauye-sauye da ake samu sun
shafi dukkanin ɓangarorin rayuwar al’ummun duniya. Wato kamar ɓangaren harshe
da zamantakewa da gine-gine da tafiye-tafiye da sutura da abinci da sauran
abubuwan da suka shafi adabi da al’ada, tamkar dai yadda S/Tudu, (1987)
da Umar, (2007) da Abba, (2011) suka bayyana. Hausawa ma ba su kasance daban ba
ta fuskantar waɗannan sauye-sauye. Al’adun Hausawa a yau sun bambanta da yadda
suke baya. Irin wannan sauyi da aka samu kan al’adun Hausawa ya shafi abincinsu.[1]
A duk lokacin da aka samu cuɗanya tsakanin al’ummu guda biyu, dole ne a
samu tasirin al’adu da ɗabi’un wata al’umma a kan wata, ko
kuma a samu wannan tasiri daga ɓangarorin guda biyu. Sani da Maikwari, (2019:
241) sun rawaito Gordon, (1978) wanda ke da ra’ayin cewa yayin da aka samu cuɗanya
tsakanin al’ummu biyu, “al’adun al’ummu da suka kasance ƙalilan
sukan nashe su koma cikin al’adun
al’ummar
da suka fi yawa a wannan yanki.” Wannan ra’ayi ne na masu bin ra’in Unidirectional
Acculturation (Ra’in Nason Al’adu).[2]
Tasirin al’umma a kan wata al’umma na iya kasancewa ta fuskar harshe ko
sutura ko bukukuwa ko abinci da makamantansu.
Kamar haka ne, cuɗanyar da Hausawa suka yi da baƙin
al’ummu
kamar Turawa da Indiyawa da Larabawa da sauransu, suka samar da wasu
sauye-sauye ga abincin Hausawa. Wannan ya shafi yanayin samar da abincin
Hausawan da ma sababbin nau’o’in abincin da Hausawa suka kwaikwaya daga baƙin
al’ummu.
Yana da muhimmanci a nazarci waɗannan
sauye-sauye domin gano abubuwan da suka kasance masu alfanu tare da bin matakan
magance abubuwan da ke da illa.
Babban manufar wannan bincike ita ce ƙoƙarin bitar ire-iren sauye-sauye da aka
samu dangane da abincin Hausawa sakamakon tasirin zamani. Wannan kuwa bai tsaya
kan nau’ukan abincin ba kaɗai, har ma da hanyoyin samar da su da sinadaran
samar da su da kuma noma su. Kai tsaye takardar za ta mayar da hankali kan (i) nazartar
sauye-sauye da aka samu ga abincin Hausawa, (ii) nazartar alfanun da ke tattare
da sauye-sauye da aka samu ga abincin Hausawa, da (iii) nazartar illolin da ke
tattare da sauye-sauye da aka samu ga abincin Hausawa.
1.1 Ra’in Bincike
An ɗora wannan bincike a kan ra’in Food Neophobia and Variety Seeking.
Ba a ci karo da karɓaɓɓiyar fasssarar sunan ra’in ta gama-gari ba. Wannan
bincike ya fassara sunan ra’in da: “Ƙyamar Abinci da Neman Nau’i.” Wannan ra’i na da
fahimtar cewa, har kullum ɗan adam na fafutukar neman nau’ukan abinci mafiya daɗi
da biyan buƙata a gare shi. Sai dai yayin neman waɗannan abinci,
yana takatsantsan da guje wa wasu nau’ukan abinci musamman marasa daɗi ko masu
cutarwa. Tuorila et al., (2001) sun nuna cewa, tsofin mutane su ne suka fi taka
tsantsan wurin zaɓen abinci sannan su ne suka fi ƙyamar
sababbin nau’ukan abinci da ba su san da su ba.
Masana da dama sun yi rubuce-rubuce dangane da wannan ra’i. A cikin
rubuce-rubucen nasu, sun yi ƙoƙarin binciko dalilan da ke ja hankalin ɗan
adam zuwa amfani da nau’ukan abinci da kuma yadda yake ƙyamatar
wasu nau’uka
ko son wasu nau’uka.
Daga cikin masana da suka yi rubuce-rubuce a wannan fannin akwai Birch et al.,
(1987) da Van Trijp & Steenkamp, (1992) da Pliner, (1994) da Pelchat &
Pliner, (1995) da Koivisto and Sjoedean, (1996) da Pliner & Loewen, (1997)
da Koivisto-Hursti and Sjode (1997) da Loewen & Pliner, (2000) da Tuorila et
al., (2001) da Cooke et al., (2003) da Koester & Mojet, (2007).
Koester & Mojet, (2007: 100) sun goyi bayan Van Trijp & Steenkamp,
(1992) cewa mutane da ke da tsantseni da saurin gundura da nau’in abinci su ne suka fi karɓar sababbin
nau’ukan abinci cikin gaggwa. Mutanen da ba su wannan halayya kuwa yawanci
sukan ƙyamaci nau’ukan abincin da ba su saba da su ba. Sun
gwammaci su ci gaba da mu’amala
da nau’ukan
abincin da suka taso suka tarar kawai. A hasashen wannan bincike, Hausawa sun
rungumi nau’ukan abinci da kayayyakin sarrafa abinci da zamani ya zo da su
sakamakon son sauyin ɗanɗano da biyan buƙata. A ɓangare guda kuwa, tsofaffi daga
cikin Hausawa sun fi ƙin karɓar nau’ukan abincin da zamani ya zo
da su.
1.2 Dabarun Bincike
An bi muhimman hanyoyi guda biyu
domin tattara bayanai yayin gudanar da wannan bincike. Na farko shi ne lura. An
gwada yin amfani da kayayyakin zamani da suka shafi abinci kamar su gas kuka da
risho da firijin. An lura da bambanci da sauyi da suka samar tare da irin
tasirin da suke da shi. Misali, naman miya da zai ɓaci cikin kwana biyu idan ba
a yi amfani da shi ba, za a iya adana shi a cikin firijin na sama da wata guda
ba tare da wani abu ya same shi ba matuƙar akwai wadataciyar wutar lantarki.
Hanya ta biyu da aka bi domin tattara bayanan wannan bincike ita ce hira.
An tattauna da rukunin mutane daban-daban musamman mata da masu sana’ar abinci
da kuma manoma. Hirarrakin sun mayar da hankali wajen samun bayanai game da:
a. Bambancewa tsakanin abubuwan da suka kasance na gargajiya da na zamani
dangane da abincin Hausawa,
b. Ra’ayin Mutane game da sauye-sauyen zamani ga abincin Hausawa, da
c. Ilimi ko rashin ilimi dangane da alfanu ko illoli da ke tattare da wasu
abubuwan da zamani ya zo da su da suka shafi abincin Hausawa.
2.0 Ire-iren Tasirin Zamani a Kan Abincin Hausawa
Tasirin da zamani ya yi a kan abincin Hausawa bai kasance ta fuska ɗaya
kawai ba. A maimakon haka, tasirin ya samar da sauye-sauye ga wasu daga cikin
abincin Hausawa ta fuskar yanayin shuka su da kuma yanayin sarrafa su. A ɗaya ɓangaren
kuma, akwai nau’o’in abincin baƙin al’ummu da Bahaushe ya kwaikwaya kuma ya
mayar da su nasa ta hanyar yi musu kwaskwarima ko ma samar da su kamar yadda
suke ga al’ummar da ya ara. A ƙasa an tattauna nau’ukan sauye-sauyen da
abincin Hausawa na gargajiya ya samu a dalilin cuɗanyarsa da baƙin
al’ummu, da ma sababbin nau’ukan abinci da ya koya daga waɗannan
al’ummu.
2.1 Sauye-Sauye ga Abincin Gargajiya
Nau’o’in abincin Bahaushe na gargajiya da dama sun fuskanci sauye-sauye a
dalilin cuɗanyarsa da baƙin al’ummu da kuma tasirin zamani a jimlace. Wannan
ya shafi hanyoyin sarrafa abincin da kuma abubuwan da ake amfani da su yayin
samar da abincin. Idan aka ɗauki ɓangaren noma misali, za a tarar da ire-iren
waɗannan sauye-sauye. Noma dai fitacciyar hanya ce mai tsohon tarihi ta samar
da abinci ga Bahaushe.[3] A
da, Bahaushe yana amfani da hanyoyin noma ne na gargajiya domin samar da
abincinsa. Wato yakan yi amfani da kayan noma kamar su garma/galma, da kalme,
da gatari da lauje da sungumi da wuƙa da makamantansu. Sai ga shi zamani ya
samar wa Bahaushe kayan noma irin su tarakta (tantan) da habesta da ma wasu injimukka da suke taimakawa wajen gyaran gona, shuka iri, kula
da shukar, ban ruwa, da ciran shukar makamantansu duk a cikin sauƙi.
A ɓangaren noma har ila yau, Bahaushe ya wuce yin amfani da takin gargajiya
kaɗai. A maimakon haka, yanzu yakan yi amfani da takin zamani da kuma wasu
sinadarai ko magungunan kashe ƙwari da haki
iri-iri. Wannan ma za a iya kallon sa a matsayin sauyi ga hanyoyin samar da
abincin Bahaushe wanda zamani ya zo da shi.
A ɓangare guda kuma, yadda ake sarrafa amfanin gona da na lambu da duk wani
nau’in abincin da ake nomawa ya samu sauye-sauye a dalilin tasirin zamani.
Wannan ya samo asali ne daga irin sinadaran da ake amfani da su da kuma su
kansu hanyoyin sarrafawar. A yanzu wuraren adana abincin Bahaushe ba rumbu da
ruhewa ne kawai ba. Yakan sanya maganin ƙwari ga amfanin gonan da ya girbe sannan
ya adana cikin buhuna ko diro-diro ko jarkoki (ya danganta da nau’in amfanin),
cikin sito-sito na adana amfanin gona.
A ɓangaren dafa abincin kansa akwai sauye-sauye. Misali, a can da, Bahaushe
yana amfani da murhu kawai a matsayin abin
dafa abinci a gida. Za mu iya tunawa da kacici-kacicin Bahaushe da ke cewa: “Uku-uku
sun cika gari.”Amma a yau, Bahaushe ya samu ci gaban amfani da wasu hanyoyin
dafa abinci da suka maye gurbin
murhun duwatsu da itace kaɗai (kamar yadda yake a da). Tuni ya fara amfani da
kurho da gawayi da risho da elektirik kuka da gas kuka da makamantansu. Waɗannan
kuwa duk zamani ne ya zo da su.
Haka ma a ɓangaren kayan haɗin abincin Bahaushe, tuni aka samu sababbin
nau’o’in sinadarai daban-daban da suke da alaƙa
da ƙarin ƙamshi ko ɗanɗano. Sun haɗa da magi da
ajino moto da kori da dai sauransu.[4]
Jadawalin da ke ƙasa na ɗauke da misalan sababbin al’amura
da suka kasance a sha’anin abincin Bahaushe a yau:
Jadawalina 1: SababbinAbubuwa a HarkarSamarwa da SarrafaAbincinBahaushe
Kayan Aikin Noma Na
Zamani |
Sinadaran Noma Na
Zamani |
KayanDafaAbinci Na
Zamani |
SinadaranAbinci Na
Zamani |
Tarikita/tantan |
Takin zamani |
Risho |
Magi |
Janareta(injin ban-ruwa) |
Maganinƙwari |
Kurho |
Onga |
Habesta |
Maganinkasheciyawa |
Gas kuka |
Ajino moto |
Injimin feshi |
Maganin ƙara girman amfanin gona |
Elektirikkuka |
Kori |
Injin sussuka/casa |
Sinadarinajiyelema
(damshi) a gona |
Rayiskuka |
Madish |
Injimin shuka |
|
Elektirikketil |
Kirim salat |
|
|
Elektirik hita |
Tumaturin gwangwani |
|
|
Bilenda |
Koren wake |
|
|
Gireta |
|
Madogara: Hira
da Sani, (2020) da Pawa, (2021) da Sulaiman, (2021) da Abubakar, (2021) da Usman, (2021)
1.2 Sababbin Abinci
Akwai nau’o’in abinci daban-daban da Bahaushe ya samu sakamakon cuɗanyarsa
da baƙin al’ummu.
Saboda haka, za a iya kallon ire-iren waɗannan abinci a matsayin abincin zamani
ga Bahaushe. Nau’o’in abincin sun bambanta ta fuskar ɗanɗanonsu da kayan haɗinsu
da kuma siffofinsu da waɗanda Bahaushe ya saba amfani da su kafin cuɗanyarsa da
baƙin al’ummu.
Don haka, za a iya kasafta nau’o’in sababbin abincin
Bahaushe zuwa rukunai uku; wato abincin bukukuwa da na yau-da-kullum da kuma na
ƙwalama.
2.2.1 Sababbin Abinci na Bukukuwa
Cuɗanyar Bahaushe da baƙin al’ummu ya sanya nason al’adun waɗannan al’ummu
a cikin al’adun Bahaushe. Daga ciki har da al’adun da suka shafi bukukuwa kamar
na aure da haihuwa da makamantansu. Wannan kuwa ya yi taliyon da ya shafi
nau’o’in abincin da ake samarwa a lokacin waɗannan bukukuwa. Sababbin abincin
bukukuwan da Bahaushe ya samu sun haɗa da:
1.
Diɓila
2.
Fish-fayit
(fish-pie)
3.
Fof-fof/cincin
4.
Kek
5.
Mit-fayit
(meat-pie)
2.2.2 Sababbin Abinci Na Yau-da-Kullum
Bayan abincin bukukuwa, zamani ya kawo wa Bahaushe wasu sababbin nau’o’in
abincin da ake ci yau-da-kullum. Ire-iren waɗannan abinci sun haɗa da:
1.
Firayid
rayis
2.
Garin
tuwon samo
3.
Indomi
4.
Kuskus
5.
Makaroni
6.
Taliyar
kanti
2.2.3 Sababbin Abincin Maƙulashe
A ɓangaren ƙwalama ma, zamani ya kawo sauyi. Akwai nau’o’in abinci daban-daban
da zamani ya kawo, waɗanda kuma suna wannan rukuni na abincin ƙwalama.
Misalansu sun haɗa da:
1.
Gullisuwa
2.
Kek
3.
Liyafa
4.
Tawaita/tayota
5.
Tuwon
madara
2.2.4 Sababbin Ababen Sha
A ɓangaren ababen sha ma, zamani ya yi tasiri wajen samar da wasu sababbin
abubuwan sha da Bahaushe ba shi da su a da. Wasu daga cikin waɗannan sababbin
ababen sha da zamani ya kawo su ne:
1.
Jinja
2.
Kunun
dankali/kudaku
3.
Kunun
shinkafa
4.
Kwastad
5.
Tafiyota/kafiyota
6.
Jus
na kwakwa
7.
Zoɓo/soɓo
8.
Furutt salat
9.
Fosta
kilak
10.
Bebi
mis
11.
Tiyara
12.
Kunun
gyaɗa
13.
Kunun
aya
2.3 Dalilan Tasirin Abincin Zamani a Kan na Hausawa
Za a iya hasashen dalilan da suka ƙarfafa wannan tasiri na abincin zamani a
kan na gargajiyar Bahaushe kamar haka:
1. Nau’o’in abincin zamani sun zo da
mabambanta ɗanɗano da ƙamshi
idan aka kwatanta su da nau’o’in abincin Bahaushe na
gargajiya. Hakan na faruwa ne a dalilin nau’o’in kayan ƙamshi
daban-daban da kuma sauran kayan haɗin abinci da ake amfani da su yayin girka
abincin na zamani.
2. Haka kuma,ire-iren abincin na zamani sun
fito da wata kafa ta sabunta nau’o’in abincin Bahaushe na gargajiya da ya daɗe
da su, kuma ya gaji da su (suka gundure shi). Kamar yadda Koester & Mojet,
(2007: 100) suka nuna, a fahimtar Ra’in Ƙayamar Abinci da Neman Nau’i, mutane sukan
so samun sauyi a nau’ukan abincin da suka riga da suka gundure su.
3. Ire-iren abincin zamani sun zo da wani
sabon salo na musamman mai ƙayatarwa ta fuskar tsaftarsu da fasalin
jikinsu. Misali, garin tuwon samo yana zuwa ne a tsabtace cikin leda. Wannan ya
kasance koma bayan garin gero ko na masara ko na dawa wanda sai an gyara an niƙa
an tankaɗe kafin amfani da shi.
4. Nau’o’in abincin na zamani da yawansu suna
da sauƙin dafawa. Ma’ana akan dafa abincin cikin ƙanƙanin
lokaci ba tare da an sha dogon aiki ba. Misalan nau’ukan abincin zamani da ke
dahuwa da wuri sun haɗa da kuskus da indomi.
Haƙiƙa, waɗannan dalilai sun taka muhimmiyar
rawa wajen kawo tasirin abincin zamani kan na gargajiyar Bahaushe. A yanzu, ya
tabbata cewa, hatta abincin Bahaushe na gargajiya (misali kunun koko da kunun
tsamiya da tuwon dawa da makamantansu) akan bi hanyoyin zamani yayin dafa su.
Wannan na faruwa ta hanyar sanya musu wasu kayan haɗi na zamani, wato dangin
kayan ƙamshi da kuma kayan yaji.
2.4 Sakamakon Tasirin Zamani a Kan Abincin Hausawa
Tabbas, zamani ya yi tasiri a kan sha’anin abincin Hausawa ya haifar da
wasu sauye-sauye ga abincin na Hausawa. Mafi yawa daga cikin waɗannan
sauye-sauye ana kallonsu da mizanin ci gaba ga al’ada. Ko da yake, ba za a rasa ‘yan ƙalilan
da suka kasance koma baya ga rayuwar Bahaushe ba, musamman ta fuskar sanya
lalaci da kasala da sakalci yayin da aka samu hanya mafi sauƙi
na gudanar da lamura. Za a
kuma iya hasashen raguwar ingancin wasu daga cikin kayan amfanin gona da
Bahaushe ya saba samarwa a baya. A taƙaice, an kawo wasu daga cikin ci gaba da
zamani ya samar ga sha’anin
abincin Bahaushe. An kasafta wannan ci gaba zuwa fannin amfanin gona, da kuma ɓangaren
dafe-dafen abinci.
2.4.1 Ci Gaban da Zamani ya Samar wa Noman Bahaushe
i.
Injin
ban-ruwa na zamani, wato janareta yana taimakawa ƙwarai
wajen noman rani mai yawa ta hanyar sauƙaƙa bayi ga amfanin da ake nomawa.[5]
ii.
Samuwar
magungunan ƙwari na feshin amfanin gona sun kawo raguwar ɗumbin
hasarorin amfanin gonar da ake samu a dalilin ɓarnar ƙwari
a gonaki. Aktar, Sengupta, & Chowdhury, (2009: 1-2) sun zayyano wasu daga
cikin alfanun amfani da magungunan feshi a gona. Sun haɗa da (a) haɓaka amfanin
gona da (b) kare amfani daga ƙwari da (c) kare amfanin gona daga cututtuka.
iii.
Takin
zamani ya zo da bayyanannen sauyi ga haɓaka da girman amfanin gona cikin
gaggawa. Roberts, (2009: 15) ya bayyana cewa, ta hanyar amfani da takin zamani
ne kaɗai amfanin gona da ake samarwa zai iya wadatar ɗunbin al’ummar da ke
rayuwa a duniya.
iv.
Zamani
ya zo da injunan noma da ke sauƙaƙa aiki. Amfani da ire-iren waɗannan injuna
na bayar da damar yin aiki mai tarin yawa cikin ƙanƙanin
lokaci sannan cikin sauƙi. Daga cikin injunan noma da suka iso ƙasar
Hausa a yau akwai tarikita/tantan da injin sussuka. Magdoff, (2016) ya gudanar
da bincike game da amfani da injunan zamani domin inganta harkar noma. A shafi
na 33, ya nuna cewa, duk da cewa yawan amfani da ake samu ya dogora kan abubuwa
da dama kamar takin zamani da kyan ƙasa da sauransu, to injunan noma na zamani
ma na taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
v.
Zamani
ya zo da nau’o’in irin shuka da ke da saurin nuna. Sukan taimaka a samu amfanin
gona kafin ruwan damina ya ɗauke ko da a shekarar an samu ƙarancin
ruwan sama. Wasu daga cikinsu kuma na ba wa manoma damar shuka sau biyu a
damina guda a maimakon sau ɗaya.Oyekale, (2014: 345) ya bayyana cewa, amfani da
irin shuka mai inganci na ɗaya daga cikin abin da ke taimaka wa samar da abinci
a Nijeriya.
2.4.2 Naƙasu/Ƙalubalen Kayan Noman Zamani
i.
Amfani
da maganin feshin ƙwari na da buƙatar
ƙwarewa. Bayan haka, magungunan suna ɗauke da
illoli daban-daban. Aktar, Sengupta, & Chowdhury, (2009: 2-8) sun kawo wasu
daga cikin illolin magungunan feshi da suka haɗa da (a) illa ga lafiyar ɗan
adam kai tsaye ko ta cikin abinci da (b) gurɓata ƙasa
da (c) gurɓata ruwan rafuka da tekunan da ke kusa (d) kashe ƙwarin
cikin ƙasa da sauransu. Wilson, & Tisdell, (2001: 449-462) sun jaddada waɗannan illoli.
ii.
Tamkar
dai magungunan feshi, shi ma takin zamani na da matuƙar
illa ga lafiyar ɗan adam da sauran halittu na cikin ƙasa
da na ruwa. Chandini, Kumar, Kumar, & Prakash, (2019) sun gudanar da
bincike dangane da illolin takin zamani. Tsakanin shafi na 76 zuwa 80 sun
bayyana matsalolin amfani da takin zamni da suka haɗa da (i) gurɓata ruwa da
(ii) gurɓata iskar shaƙa da (iii) kashe halittun cikin ƙasa
da (iv) sanya wa amfani sinadarai masu illa ga lafiyar ɗan adam da sauransu.
Baya ga wannan, wasu ƙalubalen da ke tattare da takin zamani a ƙasar
Hausa sun haɗa da (a) ƙarancin ilimin amfani da takin zamanin da
kuma (b) tsadar takin zamanin wanda ke sanya manoma Hausawa da dama ba sa iya
mallakar sa.
iii.
Injunan
noma na da tsada, sannan akwai buƙatar ƙwarewa kafin a iya amfani da su. Saboda
haka, ba su kasance masu sauƙi ba ga talakawa, waɗanda kuma su ne kaso
mafi tsoka na manoman Hausawa. Ko bayan wannan, Magdoff, (2016: 42) ya kawo
wasu ƙalubalen da ke tattare da amfani da injunan noma
na zamani. Sun haɗa da rage ingancin amfanin gona da halin ko-in-kula da
gwamnatoci ke yi game da ingancin injunan yayin shigo da su daga ƙasashen
ƙetare. Bayan wannan kuma, samuwar injunan noma na
zamani ya janyo rashin aikin yi ga matasa da talakawa da dama. Wannan ya samu
ne kasancewar injin noma ɗaya zai iya yin aikin da sai matasa da dama sun taru
kafin su iya gudanarwa.
iv.
Jahilci
na hana manoma Hausawa musamman waɗanda ke karkara amfani da irin amfani gona
na zamani. Kafin su karɓi wannan sauyi, akan sha wahala ƙwarai
wajen wayar musu da kai tare da yi musu gwajin gani-da-ido. Bayan haka Oyekale,
(2014: 352-353) ya kawo wasu ƙalubale da ke tattare da shirin amfani da
iri na zamani. Sun haɗa da (a) samar da irin zamani da ingancinsu bai kai yadda
ake so ba da (b) rashin mayar da hankali kan shirin samar da irin zamani da (c)
rashin ingancin hanyoyi da matakan rarraba iri zuwa ga manoma da (d) rashin
isasshen horaswa da isar da bayanai ga manoma.
A ɗaya ɓangaren kuma, zamani
ya kawo sauye-sauye ga sha’anin dafa abincin Bahaushe. Wannan ma hanjin jimina
ne, akwai na ci akwai na zubarwa. A ƙasa an kawo alfanu da naƙasun
zamani ga sha’anin
dafa abincin Bahaushe a taƙaice:
2.4.3 Ci Gaban da Zamani ya Samar ga Dafa Abincin Bahaushe
i.
Zamani
ya samar da kayayyakin dafa abinci da suka wakilci itace da murhu. Daga cikin
waɗannan kayayyaki akwai risho da gas kuka da elektirik kuka da makamantansu.
Irin waɗannan kayan girki sun fi itace da murhu sauri, sannan ba sa baƙanta
tukunya (in ban da risho). Wani ci gaba da suka samar shi ne na rage saran
dazuka (domin neman itacen girki). Bayan haka, kauce wa amfani da itace da
murhu na rage adadin hayaƙi da ke tashi zuwa sararin samani (wanda
yake da illa ga yanayi). Stabridis & Gameren, (2018: 9) ya rawaito maganar
WHO, (2006) da ke jaddada illar amfani da itace a matsayin hanyar girki.
Itatuwan na fitar da sinadarin kabon monozayid wanda ke da illa yayin da
aka shaƙe shi.
ii.
Zamani
ya kawo ƙarin kayan haɗin abinci, dangin kayan ƙamshi
da ƙarin ɗanɗano (kamar yadda aka kawo misali cikin
jadawali na 1 da ke sama).
iii.
Zamani
ya zo da nau’ukan abinci da suke iya dahuwa cikin gaggawa (fast foods). Daga
cikinsu akwai indomi da kuskus da makamantansu. Dafa ire-iren waɗannan nau’ukan
abinci ba ya ɗaukar lokaci. A taƙaice ke nan, za a samu biyan buƙata
cikin ƙanƙanin lokaci.
iv.
Zamani
ya zo da nau’ukan abincin da ke iya ɗaukar tsawon lokaci ba tare da sun lalace
ba. Daga cikinsu akwai cincin da kek da dibila da sauran makamantansu.
v.
Samuwar
firijin ya ba da damar ajiye wasu nau’ukan abinci na tsawon lokaci ba tare da
sun lalace ba. A yau ana iya ajiye nau’ukan abinci a cikin firijin irin su
kayan marmari da na maƙulashe, har ma da tuwo da miya.
2.4.4 Naƙasun Tasirin Zamani Kan Abincin Bahaushe
i.
Gidajen
Hausawa masu ƙaramin ƙarfi
ba sa iya amfani da kayayyakin girki na zamani. Wannan na faruwa ko dai a
dalilin tsadar kayayyakin ko kuma saboda ƙarancin ilimi game da su da kuma yadda ake
amfani da su.
ii.
Kayayyakin
girki na zamani irin su gas kuka da elektirik kuwa suna da matuƙar
hatsari, musamman idan aka yi amfani da su ta hanyoyin da suka kauce wa ƙa’ida.[6]
iii.
Sinadaran
dafa abinci na zamani da ke ƙara ƙamshi da ɗanɗano suna da illa ga lafiyar ɗan
adam, musamman idan suka yi yawa ko aka yi amfani da su ba ta hanyoyin da suka
dace ba. Srinivasan, (2016) ya gudanar da bincike game da kayan girki na ƙarin
ɗanɗano da ƙamshi. Ya bayyana nau’ukan amfani da suke da shi.
A shafi na 103 ya bayyana cewa, amfani da su na iya cutar da fatar cikin ciki
da ake kira gastric mucosa.
iv.
Yawancin
nau’ukan abincin da ke dahuwa da wuri (fast foods) suna da illa ga lafiyar ɗan
adam. Dangane da yawan cin nau’ukan abinci masu dahuwa da wuri, Mohiuddin,
(2020: 8) na cewa:
The growing widespread use of fast food among
adolescents and young adults is of concern due to the high fat and energy
intake, which may cause obesity and subsequently obesity-related chronic
diseases.
Fassara
Ƙaruwar yawaitar amfani da nau’ukan abinci masu
dahuwa da wuri da matasa[7]
ke yi abu ne mai damarwa la’akari da yawan adadin maiƙo
da sauran sinadaren da ke cikinsu. Waɗannan sinadarai na iya haifar da ƙiba
ta rashin lafiya tare da wasu cututtuka masu tsanani da ke da dangantaka da ƙiba.
Major Md Serazul Islam, psc (2020) sun
gudanar da gagarumin bincike kan illolin amfani da nau’ukan abinci masu dahuwa
da wuri. A shafi na 22, sun zayyano wasu illolin amfani da ire-iren waɗannan
abinci. Daga cikin illolin akwai ciwon sukari da ƙiba
na rashin lafiya da hawan jini da makamantansu. Wani & Sarode, (2018: 82)
sun kawo jadawali da ke nuna mutane da dama na kamuwa da cututtuka sakamakon
amfani da nau’ukan abinci masu saurin dahuwa bisa jahiltar illolin waɗannan
nau’ukan abinci.
v.
Mafi
yawan nau’ukan abincin zamani da ke daɗewa ba tare da sun ɓaci ba kayan maƙulashe
ne waɗanda ke ɗauke da mai ko sukari da yawa. Ire-irensu kuwa na da illa ga
lafiyar ɗan adam. Mohiuddin, (2020: 8) ya tabbatar da samuwar ire-iren waɗannan
sinadarai a cikin nau’ukan abincin inda yake cewa: “The added fat, sugar, and
salt create a taste that makes people crave these foods.” Wato maiƙo
da ɗanɗanon (da ake samu cikin waɗannan nau’ukan abinci) shi ke sa mutane suna ƙara
kwaɗaituwa da su.Kaur, (2017: 492) ya tabbatar da cewa nau’ukan abincin maƙulashe
masu maiƙo ko sikari na janyo ƙiba
na rashin lafiya da ciwon sukari. Ashkirani & Deepthi, (2012: 10) sun
bayyana cewa nau’ukan maƙulashe da ake soyawa suna ɗauke da maiƙo
da sinadaren kolasteral waɗanda ke da illa ga zuciya da ƙoda.
3.0 Sakamakon Bincike da Shawarwari
Lallai an samu sauye-sauye masu ɗumbin yawa dangane da cimakar Bahaushe.
Wannan ya fara tun daga hanyoyin samar da abincin (noma) har zuwa yadda ake
sarrafa su (dafawa). A harkar noma an samu sauye-sauye tun daga ɓangaren kayan
noma na zamani (misali tarikita da habesta da injin shuka da sauransu), har
zuwa maganin feshi da na kashe ciyawa da kuma amfani da irin zamani mai jure wa
fari da tare da saurin nuna. A ɓangaren dafa abinci kuwa, akwai kayayyakin
girke-girke da aka samu a zamanance (kamar risho da gas kuka da rayis kuka). A ɓangare
guda kuwa, an kwaikwayi abincin baƙin al’ummu inda aka yi wa wasu daga
cikinsu kwaskwarima. Duka waɗannan sauye-sauye ba su zo da mamaki ba bisa
ra’ayin Ra’in Ƙyamar Abinci da Neman Nau’i. Dalili kuwa
shi ne, da ma ra’in ya tabbatar da ɗan adam a kullum na neman sauyi game da
cimakarsa domin sabuntawa daga abincin da ya gundure shi.
Ansamu ci
gabasosaisakamakonabubuwan da zamaniya zo da su da sukadangancisamarwa da
sarrafaabincinBahaushe. Injunannoma da magungunanfeshi da
nau’ukanirinazamaniduksamar da sauƙi da ci gaba ga al’amuran noman Bahaushe a
yau. A ɓangarn dafa abinci kuwa, amfani da kayan dafa abinci na zamani irin su
gas kuka ya taimaka wajen rage saran daji (wanda ke janyo gurgusowar hamada da
fari), sannan ya taimaka wajen rage gurɓatar iska sakamakon sinadarin da ke
cikin hayaƙin da itatuwa ke fitarwa. Bugu da ƙari,
samuwar sababbin nau’ukan abinci da kayan ɗanɗano da na ƙamshi
ci gaba ne.[8]
A ɗaya ɓangaren kuma, duk da ɗunbin amfanin abubuwan da zamani ya zo da su
da suka shafi samar da abinci da sarrafa shi, akwai illoli da dama tattare da
su. An ga ire-iren ƙalubalen da ke tattare da harkar noman
zamani a maganganun Oyekale, (2014: 352-353) da Magdoff, (2016: 42). Haka su
kansu kayayyakin girki na zamani na da nasu matsaloli kamar yadda suka zo a
maganganun Ashkirani & Deepthi, (2012: 10) da Srinivasan, (2016: 103) da
Wani & Sarode, (2018: 82) da Mohiuddin, (2020: 8).
Lura da duka waɗannan, wannan takarda na ba da shawarwari kamar haka:
i.
Gwamnati
ta zage damtse wajen samar da kyawawan shirye-shirye da za su ba wa manoma
horaswa da wayewan kai game da amfani da dabaru da kayayyakin noma na zamani.
Wannan yunƙuri ya kasance tare da haɗin guiwar malaman
jami’o’i da gidajen talabijin da na rediyo tare da kafafen intanet.
ii.
Gwamnati
ta ƙara ƙaimi wajen samar da shirye-shiryen tallafa
wa manoma da kayan noman zamani da suka shafi kayan aiki da iri da magungunan
feshi. A tabbatar da inganci da nasarar shirin ta hanyar bibiyar inda aka kwana
a-kai-a-kai.
iii.
A
samu huɓɓasa ta haɗaka tsakanin gwamnati da masana da gidajen talabijin da na
rediyo da jaridu da kafafen intanet wajen wayar da kai da ilimantar da al’umma
dangane da amfani da kayayyakin girki na zamani. Wannan ya shafi nuna wa
al’umma matakan da ya dace su ɗauka domin kaucewa illoli da ke tattare da
kayayyakin.
iv.
Mafi
yawancin takardu da littattafai da masana kiyon lafiya ke rubutawa dangane da
abinci da noma sun kasance cikin wasu harsuna na daban ba Hausa ba. A samu wani
ƙoƙari daga masana harshen Hausa na fassara
ire-iren waɗannan rubuce-rubuce zuwa harshen Hausa (wanda hakan zai kasance
tare da izinin masu asalin aikin).
4.0 Kammalawa
Haƙiƙa, kamar yadda zamani ya yi tasiri a ɓangarorin
rayuwar Bahaushe daban-daban, wannan tasiri ya shafi hanyoyin samarwa da
sarrafa abincin Bahaushe. Sai dai sauye-sauyen da aka samu sun kasance hanjin
jimina, wato akwai na ci akwai na zubarwa. Duk da haka, za a amfana da wannan
ci gaba na zamani sosai yayin da aka bi matakan da suka dace. Wannan ya shafi ƙoƙarin
gwamnatoci da masana da sauran rukunonin al’umma a matakai daban-daban domin
wayar da kai da ilimantarwa tare da ɗaukar matakai da suka kamata don ganin an
ci gajiyar abubuwan da ci gaban zamani ke zuwa da su, tare da kauce wa
illolinsu.
Manazarta
Abba, S.
(2011). “Nason Al’adun Turawa a Bukin Aure a Ƙasar Sakkwato. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen
Koyar Da Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Aktar, M. W., Sengupta, D. & Chowdhury, A.
(2009). Impact of pesticides use in agriculture: Their benefits and hazards. In
Slovak Toxicology Society SETOX, Vol. 2(1): Pp 1-12. doi: 10.2478/v10102-009-0001-7.
Ashkirani & Deepthi, R. (2012). Fast Foods and
their Impact on Health In Journal of Krishna Institute of Medical Sciences
University, Vol. 1, No. 2, July-Dec. 2012, Pp 7 - 15. Retrieved on 3rd March
2021 from: https://www.researchgate.net/publication/285169531.
Baba, F. A. (2009). Ɗanɗanon
Girki: Girke-girke a SauwaƘe. Kano: GAFA Books.
Birch, L. L, et al (1987). What kind of exposure
reduces children's food neophobia? Looking vs. tasting. Appetite. 1987
Dec;9(3): 171-8. doi: 10.1016/s0195-6663(87)80011-9. PMID: 3435134.
Bunza, A. M. (2014). Noma: Igiya Maɗura Kaya In An
Yi Ba Da Kai Ba Su Watse. Takardar da ake gabatar a taron ƙungiyar
Manoma ta tarayya, reshen Jihar Sakkwato (AFAN) a makarantar Ilmukan Ƙur’ani ta Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo Abubakar III, ranar Lahadi 31-05-2014 a bukin ƙaddamar
da kalandar manoma da karrama fitattun manoma da masu agaza wa aikin noma
Chandini, Kumar, R. Kumar, R. & Prakash, O.
(2019). The Impact of Chemical Fertilizers on our Environment and Ecosystem.
Pp. 69-86. Retrived on 8th March 2021 from: https://www.researchgate.net/publication/331132826.
Cooke, L,.Wardle, J. & Gibson, E, L. (2003),
`Relationship between parental report of food neophobia and everyday food
consumption in 2±6-year-old children', Appetite, 41, 205±206. Damasio A R
(1994), Descartes Error: Emotion, Reason and the Human Brain, New York, Avon.
Gordon, M. (1978). Human nature, clrass, and
ethnicity. New York: Oxford University Press.
Gummi, M. F. (2008). “Tsumagiyar Kan Hanya:
Nazarin Wasu WaƘoƘin Yunwa Na Baka A Sakkwato Da Zamfara Da
Kabi. Kundin Digiri Na Biyu Wanda Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan
Nijeriya, Sakkwato:Jami’ar
Usmanu Danfodiyo.
Kaur, R. (2017). Effect of Fast Food on Human
Health. A paper presented during a Two Days International Conference on Recent
Innovation in Engineering, Science, Humanities, and Management at Dev Ramaj
College for Women, Panjab, India.
Koester, E. P & Mojet, J. (2007). Theories of
Food Choice Development. Retrieved on 3rd March 2021 from: https://www.researchgate.net/publication/260365518.
Koivisto, U. K. & Sjoden, P. O. (1996).
Reasons for rejection of food items in Swedish families with children aged
2-17. Appetite. 1996 Feb;26(1):89-103. doi: 10.1006/appe.1996.0007. PMID:
8660035.
Koivisto-Hursti, U. K. & Sjoe, Dean, P. O.
(1997). Food and General Neophobia and their Relationship with Self-Reported
Food Choice: Familial Resemblance in Swedish Families with Children of ages
7±17 Years. In Appetite, 29, Pp. 89-103.
Loewen, R. & Pliner, P. (2000). The Food
Situations Questionnaire: a measure of children's willingness to try novel
foods in stimulating and non-stimulating situations. Appetite. 2000
Dec;35(3):239-50. doi: 10.1006/appe.2000.0353. PMID: 11073706.
Magdoff, F. (2016). Pros and Cons of Agricultural
Mechanization in the Third World. Retrieved on 8th March 2021 from: : https://www.researchgate.net/publication/275598898.
Major Md Serazul Islam, psc (2020). The Impact of
Fast Food on Our Life: A Study on Food Habits of Bangladeshi People. In Global
Journal of Medical Research: Volume 20 Issue 8 Version 1.0 Year 2020. Online
ISSN: 2249-4618 & Print ISSN: 0975-5888
Mohamed, E. (2012). Sizing optimisation of
stand-alone photovoltaic generators for irrigation water pumping systems. In
International Journal of Sustainable Energy, Volume 32,
10.1080/14786451.2012.697463.
Mohiuddin, A (2020). Fast Food Addiction: A Major
Public Health Issue. A Review. Arch Biomed Eng & Biotechnol. 3(4): 2020.
ABEB.MS.ID.000569. DOI: 10.33552/ABEB.2020.03.000569.
Muhammad, M. L. (2011). Mu Koyi Girki Mata. (Babu
maɗaba’a)
Mullaly, B. (2002). Challenging oppression: A
critical social work approach. Ontario: Oxford University Press.
Ngo, V. H. (2008). A critical examination of
acculturation theories. Retrieved on 1st June, 2019 from: http://www1.uwindsor.ca/criticalsocialwork/a-critical-examination-of-acculturation-theories.
Oyekale, K. O. (2014). Growing an Effective Seed
Management System: A Case Study of Nigeria. In Journal of Agriculture and
Environmental Sciences. Vol. 3, No. 2, pp. 345-354. ISSN: 2334-2404 (Print), 2334-2412
(Online).
Park, R. E. (1950). Race and Culture. Glencoe: The
Free Press.
Pelchat, M. & Pliner, P. (1995). “Try it,
you'll like it''. Effects of information on willingness to try novel foods. In Appetite,
24, Pp. 153-166.
Pliner, P. & Loewen, R. (1997). Temperament
and Food Neophobia in Children and their Mothers. In Appetite, 28, Pp.
239-254.
Pliner, P. (1994). Development of Measures of Food
Neophobia in Children. In Appetite, 23(2), Pp. 147-63. doi:
10.1006/appe.1994.1043. PMID: 7864609.
Roberts, T. L. (2009) The Role of Fertilizer in
Growing the World’s Food. In Better Crops, Volume 92, No 2. Pp 12-15. Retrieved
on 8th March 2021 from:
http://www.ipni.net/publication/bettercrops.nsf/0/D21DBC864569368D85257980006FC3DB/$FILE/Better%20Crops%202009-2%20p12.pdf.
S/Tudu, H. Z.
(1987). Tasirin Zamani A Kan Al’adun Aure A Ƙasar Sakkwato. Kundin Digiri Na Farko Wanda Aka Gabatar A Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Sani, A-U. & Maikwari, H.U. (2019). Cuɗanyar
Al’adu a Sabon Garin Kano: Wani Misali na “Mun zo Garinku Mun fi ku Rawa.” In
EAS Journal of Humanities and Cultural Studies, Volume-1, Issue-4. Pp 240-245.
ISSN: 2663-0958 (Print) & ISSN: 2663-6743 (Online) Available at: https://www.easpublisher.com/get-articles/359.
Scherer, T. F. (2017). Irrigation Water Pumps
(Revised). Retrieved on 8th March 2021 from: https://www.ag.ndsu.edu/publications/crops/irrigation-water-pumps.
Shehu, M. (2015). Sana'ar Noma a Ma'aunin Karin
Magana. Cikin https://www.amsoshi.com/2017/11/sanaar-noma-maaunin-karin-magana.html.
Srinivasan K. (2016) Spices and Flavoring Crops:
Uses and Health Effects. In: Caballero, B., Finglas, P., and Toldrá, F. (eds.)
The Encyclopedia of Food and Health vol. 5, pp. 98-105. Oxford: Academic Press.
Stabridis, O. & Gameren, E. V. (2018).
Exposure to Firewood: Consequences for Health and Labor Force Participation in
Mexico. Retrieved on 8th March 2021 from: https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S0305750X18300901?via%3Dihub.
Tuorila, H. et al L (2001). Food Neophobia
Among the Finns and Related Responses to Familiar and Unfamiliar Foods. In
Food Qual Pref 12, Pp. 29-37.
Umar, K. F.
(2007). Tasirin Zamani Kan Ire-iren Auren Hauswa. Kundin Digiri Na Farko Wanda Aka GabatarA
Sashen Koyar Da Kimiyyar Hausa Da Kimiyyar Harsuna, Maiduguri: Jami’ar Maiduguri.
Van Trijp, H. C. M. & Steenkamp, J. E. B. M.
(1992). Consumers's Variety Seeking Tendency with Respect to Foods: Measurement
and Managerial Implications. In Europ Rev Agricult Econ, 19, Pp.
181-195.
Wani, P. H. & Sarode, N. (2018). Impact of
Fast Food Consumtion on Health. In International Journal on Recent Trends in
Business and Tourism | Vol. 2 (3) JULY 2018. Pp 79 - 83. Retrieved on 3rd March
2021 from: https://www.researchgate.net/publication/341042503.
WHO, (2006). Fuel for life: household energy and
health. Geneva: World Health Organization.
Wilson, C. & Tisdell, C. (2001). Why Farmers
Continue to Use Pesticides Despite Environmental, Health and Sustainability
Costs. In Ecological Economics Volume 39, Pp. 449–462. DOI:
10.1016/S0921-8009(01)00238-5.
Yabo, B. A. (2006). “Kirarin Abincin Hausawa.”
Kundin Digiri Na Farko Wanda Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
[1] Muhimmancin
abinci ga rayuwar ɗan adam ya sa masana da ƙwararru a fannin al’ada da kiyon lafiya yin rubuce-rubuce
da dama dangane da wannan batu. Daga cikin rubuce-rubucen da aka ci karo da su
masu magana game da abinci akwai: Yabo, (2006) da Gummi, (2008) da Baba, (2009)
da Muhammad, (2011) da Ashkirani & Deepthi, (2012) da Kaur, (2017) da Wani
& Sarode, (2018) da Mohiuddin, (2020).
[2]Domin samun ƙarin bayani game da Ra’in Nason Al’adu
ana iya duba ayyukan Park, (1950) da
Gordon, (1978) da Mullaly, (2002) da Ngo, (2008) da Sani da Maikwari, (2019).
[3]Domin samun ƙarin bayani game da matsayin noma ga
rayuwar Bahaushe sai a duba Bunza, (2014) da Shehu, (2015).
[4]A hirar da aka yi da Malama Zainab Sani (2021), ta
bayyana cewa: “Ba sai an yi nisa sosai ba, ko shekaru hamsin baya aka duba za a
tarar da cewa Hausawa ba su san mafi yawan kayan ɗanɗanon da suke amfani da su
a girke-girkensu a yau ba.”
[5]Domin samun ƙarin bayani ana iya duba ayyukan
Mohamed, (2012) da Scherer, (2017).
[6]Bincike game da hanyoyin inganta amfani da waɗannan
kayayyaki na da matuƙar muhimmanci. A kafar intanet ta YouTube, akwai laccoci
da dama game da yadda ake amfani da kayayyakin girki na zamani (cikin
bidiyoyi).
[7]Maganar Mohiuddin, (2020) na nuna cewa matasa ne
suka fi amfani da nau’ukan abinci masu dahuwa da wuri. Wannan ya yi daidai da
tunanin ra’in Ƙyamar Abinci da Neman Nau’i, wato kamar yadda Tuorila et
al., (2001) ya nuna cewa tsofi su ne suka fi guje wa sababbin nau’ukan abinci.
[8]Za a iya samun ƙarin bayani game da
muhimmancin abubuwan da zamani ya zo da su da suka shafi noma da girki cikin
ayyukan WHO, (2006) da Roberts, (2009) da Aktar, Sengupta, & Chowdhury,
(2009) da Oyekale, (2014) da Magdoff, (2016) da Stabridis & Gameren, (2018).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.