Feɗe Waƙar Jarumar Mata Ta Makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) Bisa Gadon Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya

     Da wuya a ce akwai wani Bahaushe kuma mazaunin ƙasar Hausa da bai taɓa jin ko da ɗuriyar waƙar Jaruma ta Makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) ba. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya feɗe wannan waƙa domin manazarta.

    Jaruma - Yusuf Breaker

    Feɗe Waƙar Jarumar Mata Ta Makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) Bisa Gadon Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya 

    Daga

    Sa’idu Muhammad Gusau
    Jami’ar Bayero, Kano 

    1.0  Gabatarwa  a kan Salsalar Waƙa

    Wannan waƙa, makaɗi Hamisu Yusuf Sa’id (Breaker) shi ne ya yi ta kuma ya yi wannan waƙa ne kamar yadda ya saba yin waƙoƙinsa na soyayya. Har wa yau kuma Hamisu Breaker makaɗi ne wanda yake amfani da Kiɗan Sitidiyo[1] kuma yakan yi waƙoƙi ne a ƙungiya ko kuma a kaɗaita.

    Hamisu Yusuf Sa’id wani matashi ne wanda Allah ya hore masa shirya waƙar Hausa bisa lokacinsa da yake a cikinsa. Ana yi masa laƙabi da Breaker domin ya iya taka rawa gwarwado da zamanin da yake a ciki. Bisa dukkan alamu Hamisu Breaker bai yi aure ba illa yana a gaɓar samartaka ne. Domin haka, ba a bin mamaki ne ba idan ya tsara kuma ya rera wannan waƙa ta Jarumar Mata.

    A nazarin nan kuma an sami wannan waƙa wadda aka turo mini ita cikin wayata daga mutane daban-daban waɗanda suka haɗa da Malam Kamilu Ɗahiru Gwammaja da Kubra Muhammad Abba da Malam Ibrahim Ali KEZ, abokin Abdullahi Buba Gashuwa. Daga bisani ni kuma na saurari waƙar, sannan na juya ta a takarda[2].

    Makaɗi Hamisu Breaker ya yi wannan waƙa ta Jarumar Mata ba da jimawa ba aka yi salla ƙarama, Idil Fitri ta wannan shekara 2020 miladiyya (Lahadi 24/5/2020). Kuma ya yi waƙar ne a cikin ganiyar rani ko zafi daidai kuma da lokacin da ake hana mutane fita, ana kulle su a gidajensu saboda Corona Ɓirus (Coɓid 19) duk da kuma ga watan Ramalan da azumin da ake yi a cikinsa.

    Har wa yau kuma waƙar Jarumar Mata tana da yawan ɗiya aƙalla guda goma sha biyar (15).

    Haƙiƙa, waƙar Jarumar Mata ta zama ruwan dare game duniya a tsakanin mutane tun ma ba Hausawa ba. Hamisu Breaker ya yi wannan waƙa ne da harshen Hausa bisa kari na Kananci. Domin haka,mutane tun ma ba matasa ba sun yi hidimar haddace ta, tare da sassauya ta gwargwadon ƙauna da bukatar kowannensu. Wata matar aure ce da take nuna son mijinta, wani don son kuɗi wani don ƙaunar dabbobi kamar akuya, wani don bukatar ya samu gida ko mota da sauransu. Ta haka suke maming waƙar, suna juya ta, ta amfani da kalmominsu amma bisa amo da yanayin rerawarta da kuma raujinta.

    Kamar yadda aka bayyana a baya, sunan yanka na wannan makaɗi shi ne Muhammadu Hamisu, mahaifinsa kuma shi ne Sa’idu, sannan kakansa shi ne Yusufu. Unguwar Hamisu Breaker ita ce Ɗorayi Ƙarama a sashen Unguwar Bello, a Ƙaramar Hukumar Gwale, Jihar Kano.Huku An haifi Hamisu a shekarar 1992. Ya yi makarantar Firamare ta Gwamnati a Ɗorayi Ƙarama, ya kuma yi makarantar sakandare ta Gwamnati, Ƙarama da Babba duka a Ɗorayi Babba a Jihar Kano. Haka kuma shi mutum ne mai riƙe abubuwa, mai kaifin hadda, mai mayar da maganganu kamar yadda ya ji su. 

    Hamisu Breaker ya fara waƙa ne a sa’ilin da yake a Makarantar Ƙaramar Sakandare ta Dorayi Babba, a Jihar Kano, kuma har yau yana a kai. Allah ya ƙara masa basira da ɗaukaka. Duk da yake Hamisu Breaker ya tashi da shirya waƙoƙi tun yana a makarantar allo, musamman waɗanda ya yi a tsakanin ‘yan’uwansa ‘yan makaranta na wasu Ƙasidu, amma ‘yan shekaru kaɗan ya zama mawaƙi ko makaɗi kuma ya fara fitar da album nasa na farko a ƙarshen shekara ta 2016. Lokacin nan ne ya fitar da album mai ɗauke da waƙoƙi aƙalla guda shida, yawancinsu kuma na soyayya ne[3].

    Hamisu Breaker makaɗi ne wanda Allah ya ba mutane da yawa. Mawaƙi ne wanda ya yi shuhura a harkokin sadarwa na zamantakewar jama’a[4] . A Youtube kaɗai yana da mabiya fiye da dubu arba’in (40,000) ga kuma Facebook ga Instagram da makamantansu.

     

    2.0 Saƙo ko Tarken Waƙar

    2.1 Gundarin Turke

    Babban saƙon da wannan waƙa take ƙunshe da shi, shi ne nuna tsantsar soyayya irin wadda take wanzuwa tsakanin masoyi da masoyiyarsa, wadda kuma bisa yawanci takan zama mutu ka raba ne. Soyayyar masoyi zuwa ga masoyiyarsa ya ratsa wannan waƙa tun daga ɗanta na farko har kuwa zuwa ƙarewarta a ɗa na 15. Wannan waƙa tana ɗauke da kalmomi masu fizgar zuciya, kuma masu sakaya zance bisa hikima da adonta masoyiya. Kuma waɗannan kalmomi da aka zaɓo masu bayyana soyayyar masoyi ga masoyiyarsa ne waɗanda suke tafiya tamkar sautin jirgin ƙasa a yayin da ya darkako hanya.

    2.2 Muhallan Turke na waƙar:

    A wasu misalai na muhallan turke na wannan waƙa su ne inda ɗa na 4 da ɗa na 5 suke faɗin:

    Jagora: Tilas ganin mu tilas barinmu,

      : Ƙaunarki tun da nai nisa,

      : Sam ba batun na fasa ko za a ce mun in ba da rai fansa.

     

    Jagora: Tsarin zubin ki daidai ne,

    : Ya kama zuciyata ne,

    : Ina ji kamar mafarki ne,

    : Ina son ki so mataki ne.

        (Breaker, Waƙar Jarumar Mata, ɗa na 4-5)

    Akwai kuma wani misali inda yake cewa a ɗa na 6:

     

    Jagora: Ni ban da damuwa in har zan buɗe ‘yan idanuna,

     : In kalle ki ga ki dab da ni,

     : To me za ya dami ƙalbina.

        (Breaker, Waƙar Jarumar Mata, ɗa na 6)

     

    2.3 Taƙaita Turke Waƙar

    Saƙonnin da wannan waƙa ta ƙunsa a gunduwa-gunduwa ta ma’ana sun haɗa da:

    Ɗa na 1-2: Suna nuna ƙarfin son masoyi ga masoyiyarsa domin ko ana ha maza ha mata sai ya sami masoyiyarsa kuma daga nan ba zai sake tanka wa kowa ba. Wato buri ya cika.

    Ɗa na 3:  Masoyi ba zai kula kowa ba sai kawai masoyiyarsa

    Ɗa na 4-5: Waɗannan ɗiya sun shafi muhallin tarke a inda masoyi ya yi ta kwatanta masoyiyarsa. A nan ne kuma masoyi ya nuna ba zai daina nuna soyayyarsa ga masoyiyarsa ba ko da ko zai mutu ne.

    Ɗa na 6: Shi ma wannan ɗa wani muhallin turke ne a inda shi masoyi yake sauwara yana tare da masoyiyarsa. Domin haka babu wani abu da zai dami zuciyarsa ko ya ɗauke masa hankali.

    Ɗa na 7-10: Suna nuna masoyi ya fahimci masoyiyarsa mai ƙaunarsa ce, mai cika masa muradinsa, mai kuma ceto nasa bisa kowane hali na rayuwa.

    Ɗa na 11: Duk da ƙarfin son da wannan masoyiya take nunawa, masoyin yana ganin a duniyar nan ba wanda zai iya ɗaukar tunaninsa sai kawai ita masoyiyarsa.

    Ɗa na 12: Masoyi yana ba da shawara a kan soyayya ga duk wanda ya sarƙu da ita sai ya yi hanƙuri, musamman dangane da sauye-sauyen halayenta.

    Ɗa na 14: Ɗan waƙar yana gargaɗin samari da ‘yanmata a kan su dinga tafiya a sese a soyayya, kuma su yi hakuri da ita, sannan a daina gaugawa.

    Ɗa na 15: Wannan ɗa na 15 shi ne wanda ya rufe wannan waƙar. Da ne da yake yin faɗakarwa a kan masoyi yana taka tasa sa’a, haka kuma shi ma yana da rana ta shanya garinsa.

     

    3.0   Awon Baka na wannan waƙa

    Yawan layuka na ɗa

    Zubin ɗiya a waƙar – An buɗe waƙar ne da yanayin kiɗa na gangunan Turawa, sannan aka ci gaba kai tsaye da zuba ɗiyan waƙar.

    Tsarin ɗa ko ɗiya a waƙar

    Tsarin Rerawa

    Takidi a ɗiyan waƙar

    Karin murya da amsa amon waƙar

    4.0  Adonta Harshe a Waƙar

    Alamtarwa = Kalmar Masoyi (ɗa na 15)

    Kamantawa = ɗa na 5, da ɗa na 12, da ɗa na 13.

    Siffantawa = ɗa na 2, da ɗa na 10.

    5.0  Aiwatar da harshen Waƙa

    Yawan Kalmomi = 372 Kalmomi

    Zaɓen Kalmomi = Misali rai, zuciyata, ruwa, iska, kewa, jure, jira, ɗau fansa, jimirin jiranki, sirrin rayuwa, gani, bari, maƙiya kalamaina, da sauransu.

    Maganganun Hikima

    Karin Magana: gani nan bari nan: ɗa na 4.

    Wanda ya mutu ba ya jin kira: ɗa na 3.

    Karin Harshe na Waƙar = Kananci

    Ginin Jumla a Waƙar = Akwai nau’o’i daban-dabam, kamar:

    Jumla Sassauƙa: ɗa na 6, ɗa na 14.

    Jumla Tsattsaura: ɗa na 2, ɗa na 12.

    Jumla Korau: ɗa na 1, ɗa na 4.

    Jumla Ƙanga Dogarau: ɗa na 11, ɗa na 8, ɗa na 10.

    Jumlar Aikatau: ɗa na 8, ɗa na 10.

    Yankunan Jumla: ɗa na 4, ɗa na 5, ɗa na 10.

     

    6.0  Tasirin Waƙar ga Al’ummar Hausawa

    Waƙar jarumar Mata  ta yi tashe sosai musamman ma a wajen matasa Hausawa, maza da mata, ma’aurata da marasa aure. Waƙar ta shiga zukatan matasa Hausawa ka’in-da-na’in, musamman a lokacin bikin Salla Ƙarama ta wannan shekara ta Lahadi 24/5/2020 Miladiyya. Waɗannan matasa sun haddace waƙar, sun kuma yi maming nata dangane da soyayya da ƙauna da son rai daban-daban da suke nunawa.

    Ina iya tunawa a tarƙe ko a nazarin waƙar baka akwai abubuwa biyu da za a yi la’akari da su a kowace waƙa da za a yi nazari kuma a ƙarfafa wa mutane su saurare ta. Akwai waƙar da za a yi wa nazari wadda ta dace da al’adu kyawawa na al’ummar Hausawa kuma ta bi sharuɗɗa da dokokin addinin Musulunci da Hausawa suka yi imani da shi kuma suke biya. Sannan akwai waƙa Ballagazazziyar waƙa wato ita ce wadda ta saɓa wa al’adun al’ummar Hausawa da addininsu. Su kansu kuma zukatan masu sauraron waƙoƙin baka kashi biyu ne. Akwai zukata masu kyau waɗanda suke bin kyawawan dokokin al’adu da ƙa’idojin addinin al’ummarsu. Akwai kuma wasu zukatan waɗanda babu ruwansu da dacewar al’adu bisa godabu managarta ko kuma abubuwan da addininsu suka zo musu da su na shiriya. Har wa yau kuma wannan ya zama wani nuni ne na abin da zukata suke so kuma ko suke sha’awa.

    A ma’ana ta lugga an bayyana Kalmar Zuciya da (i) ‘wata curarriyar tsoka da take cikin ƙirjin mutuum ko dabba ko tsuntsu wadda ke aika jini zuwa sauran sassan jiki. (ii) Fusata ko saurin fushi. (iii) Sa zuciya, watau zaton aukuwar abin kirki. (iɓ) Ƙarfin Zuciya, watau jarunta. (ɓ) Zuciyar maraya, watau wata irin saƙa mai fari da baƙi. (ɓi) ya hau dokin zuciya, watau ya fusata. (ɓii) ajiyar zuciya, watau numfasawa. (ɓiii) Ƙawa-zuciya, watau tsananin son abu. (iɗ) wadatar zuci, watau dangana’ (CNHN, Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero: sh 495). Dangane da ma’anar zuciya ta fannin ilimin addinin Musulunci kuwa ita ce yadda Annabin Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ambata a cikin Hadisinsa na shida na littafin Al-Arba’una al-Nawawiyya yana cewa: Tabbas akwai wata tsoka a jikin ɗan’adam, idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta ɓaci dukkan jiki ya ɓaci. Lallai ita ce: Zuciya. Buhari da Muslim suka ruwaito shi (Ƙaura, Salihu Abubakar, 2017: 38-40).

    Haka ne kamar yadda ya gabata, an sami matasa a wasu sassa na ƙasar Hausa, maza da mata, waɗanda suka shisshirya ɓideo, suna maming na wannan waƙa, wasu mata ne waɗanda suke caɓa rawa a gaban mazajensu, wasu sun sanya abubuwan ƙaunarsu a gabansu suna bin wannan waƙa, suna kuma sassaka nasu ƙare-ƙare gare ta da sauran makamantan waɗannan abubuwa. Wannan wani nau’i ne na rage zafin zaman gida, wataƙila ko ba komi sai don su kashe kwarkwatan zaman kulle na gida da aka saka su domin Corona Ɓirus (Coɓid 19).

    Bisa al’adu na Hausawa da na addinin Musulunci da suka samu daga bisani, Hausawa dukkansu, maza da mata, an san su da jin kunya da sirranta abubuwa, tun ma ba mata nasu ba. Namiji yake cewa mace yana son ta da aure amman ba ita macen ba. Zai yi wuya mace ta dubi idanun namiji, ta yi ido arba da shi, kuma ta gaya masa tana son sa ko tana ƙaunar sa ko tana begen sa. Amma a yau, an sami tasire-tasire na zamani da haɗuwar Hausawa da wasu baƙin al’adu na jinsunan mutane daban-daban tun ma ba Turawa ba, sai wasu Hausawan suka kwaikwayi wasu baƙin al’adu har suka ƙanƙame su, suka dinga aiki da su. Yau ga shi an cim ma wani lokaci matan aure na Hausawa wai su ne suke yi wa mazajensu waƙa, suna nuna soyayyarsu gare su, ba su bari mazajen su gaya musu waɗannan kalamai ba.

    Wannan abun da ya faru ya haddasa ka-ce-na-ce da ƙalubale a tsakanin wasu Hausawa, musamman ma Malamai[5] waɗanda suke ganin wannan wata hanya ce ta cin zarafin addinin Musulunci da ko-in-kula da shi. Waɗannan Malamai suna ganin ba a nuna:

    -         Tsoron Allah ba, ko

    -         Kunya ko

    -         Kishin iyali

    -         Kuma ba ƙauna ce ba

    -         Kuma ba mawadda ce ba domin ba a nuna sirri ba, kamar yadda al’adun Hausawa suka amince. Kuma addinin Musulunci ya yarda a dinga sirrintawa a kan aiwatar da abubuwa.

    Dubi misali a Alƙur’ani, mai girma Suratu al-A’araf, aya ta 33. Sannan kuma akwai maganar Halifa Sayyadina Umar ibn Haɗɗaɓi inda ya yi wa wani mutum wanda yake magana da matasa a ƙofar gidansa kandarko har ya zungure shi da sanda yana faɗin: A fa ƙofar gida kake’. Shi ko mutumen ya gaya masa, ai yana bisa dokin ƙofar gidansa ne, kuma yana magana ne da matarsa. Sai Sayyadina Umar ya nuna masa, ‘Ashe babu sirri a magana, kowa yana jin ka, yana kuma ganin ka, kuma Allah ya umurci a yi sirri a tsakanin iyali’.

    Amma idan aka dubi wannan waƙa ta Jarumar Mata da nutsuwa, za a ga haƙiƙa ta dace da a yi nazarinta kuma a iya sauraronta, kuma mai nazari ya yi bugun gaba da ita. Waƙa ce wadda ba ta saɓa ƙa’idojin fiɗar waƙa ba, kuma ba ta taɓa al’adun al’ummar Hausawa ko dokokin addininsu na Musulunci ba.

    Wasu mutane ne suka ɗauke ta suka jujjuyata ta yadda zukatansu da sha’awace-sha’awacensu suke so[6]. Kuma su masu son waɗannan al’adu waɗanda za a iya kira munana ne, sun yi gamon katar da wannan waƙa ta Jarumar Mata, makaɗin ya sake ta ko ya fitar da ita. Daga nan suka ɗauke ta suka dinga jujjuya ta, ta yadda suke bukata, kowane rukuni bisa gwargwadon abin da zuciyarsa take ƙauna, kamar dai yadda aka bayyana a baya.

     Hasali ma dai waƙar tana ƙarfafa soyayya da mawadda a tsakanin mutane. Ta haka ne Kamilu Dahiru Gwammaja yake tofa albarkacin bakinsa a kan waƙar yake faɗar, ‘waƙa ce mai taɓa zuciya, mai sakaya zance kuma ta ƙunshi wasu maganganu na hikima, ga ta mai adonta harshe (Ganawa da Gwammaja, K.Ɗ., ranar Talata 9/6/2020 da ƙarfe 9:30 na dare).

    Domin haka, a fahimta ta, wannan waƙa ta Jarumar Mata ta cancanci nazari.

     

    MANAZARTA

    CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

    Gusau, S. M. (2002) SarkinTaushi Salihu Jankiɗi. Kaduna: Baraka Press and Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2008a) Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2008b) Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

    Gusau, S. M. (2016a) Makaɗa da Mawaƙan Hausa na Biyar. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Gusau, S. M. (2016b) Ƙamusun Kayan Kiɗan Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Ƙaura, S. A. (2017) Ma’anonin Hadisan Ma’aiki. Zaria: Ahlul-Lahi for Printing and Distribution.



    [1] Kiɗan Sitidiyo, kiɗa ne wanda ake yi a wani ɗaki da ake kira Sitidiyo wanda aka zuba wa kayan kiɗa iri-iri kama daga fiyano da ganguna (irin na Turawa) da miksa da makirifon (Amsa-amo) da na’urar sauti (lasifika) da hedifon da maɗaukan fiyano da sauransu. Shi wannan ɗaki na Sitidiyo yana da makaɗa masu tafiyar da harkokin kiɗa a cikinsa kuma ana iya saka masa kowane irin nau’in sauti, tun ma ba na kiɗa ba (Gusau, 2016: 27-29). Da alama wannan ne ma ya sa aka buɗe wannan waƙa ta Jarumar Mata da wani amo na kiɗa mai karsashi da jan hankali.

    [2] An kawo juyin matanin wannan waƙa a ɓangaren rataye na wannan takarda.

    [3] Ga waɗannan waƙoƙi kamar haka (1) So na Gaskiya (2) Hamra (3) Shimfiɗar Fuska (4) K.T. (5) Hauwa (6) Bikin Saƙon Amarya.

    [4] Wato Social Media.

    [5] Daga cikin waɗannan Malamai akwai Malam Mu’azzam Ibrahim na Sashen Musulunci a Jami’ar Bayero, Kano da Malam Dr. Abdullahi Usman Umar Gadon Ƙaya, Kano da Malam Muhammadu Rabi’u Rijiyar Lema, Kano da Dr. Sanusi Ramadhan da sauransu.

    [6] Su kansu wasu Hausawa da suka ɗauki wannan waƙa ta Jarumar Mata,  suka aiwatar da ita bisa waɗannan abubuwa kuma a zahiri, sun ari wani shiri ne na [E] wanda DSTƁ take gudanarwa wanda ake yin tsare-tsare iri-iri kamar tsari na Kardashians wanda ake nunawa, wato wanda ake haska shi a talabijin nasu.

    A wannan shiri na Kardashians mazauwa gidan sukan bayyana sirri na gidan ne ta kowane gefe nasa ba tare da sayawa ba, kuma tufafin da matan gidan suke sanyawa na ainihin tsiraici ne na inna naha, ga yin kalamai sasakai babu wata kunya ko nutsuwa ko kishin kai. Haƙiƙa, waɗannan al’adu sun saɓa wa shiriya ta addinin Musulunci.

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.