Ticker

6/recent/ticker-posts

Duk dai in mun lura gazawar da maza suke yi ne wurin ba da abin da ya dace a bayar na faranta zuciya. Wato buɗe baki a yi hira da iyali, da jinjina musu a inda ya dace, da sauraronsu a lokutan magana, da ƙaranta maida hankali wurin waya da komfuta, da ba su cikakken lokaci a sa'ilin da kake gida. Mace kam za ta yi babbar kuskure in ta ce za ta bar...
Kundin Ma'aurata - 7: Wata Matsalar
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Matan Ƙwarai


Waya tana daya daga cikin matsalolin mata a yau, da dai jarida ce, yanzu galibin maza ba sa karatu, sai talabijin ya zo ya ƙwace, yanzu kuma zamanin hanyoyin sadarwa ne, masamman Fesbuk da Watsap, in namiji ya dawo zai ci abinci mace takan so ta zo ta zauna kusa da shi tana kallonsa yana ci, tana sa rai da zai riƙa santi, yana yabon irin ƙoƙarin da ta yi wajen hada girkin, in ma hakan ba ta samu ba dai za su dan tattauna wasu abubuwan, duk ma abin da ya wakana a dan wannan tsakankanin ribar ƙafa ce wai kura ta taka kwado, wannan lokacin yana da mahimmanci ba dan ƙarami ba a wurin mace, wasu lokutan ma takan bar wasu batutuwan sai a waɗannan lokutan, masamman lokacin abincin safe da na dare, don galibin lokutan namiji bai da matsaloli da yawa a kansa.
.
Abubuwan da suke faruwa a wannan lokaci, in ta zo wurinsa lokacin ne zai dauko waya yana latse-latse yana cin abinci, hankalinsa kuma gaba daya yana kan wayar, ita mace kallonsa kawai take yi, ta zo don ta yi hira da shi, shi kuma ya juya mata baya, ƙila ma da wasu 'yammatan yake hirar, don wani sa'in har murmushi yake yi, har ya gama cin abincin ko ƙala ba zai ce ba bare ya yabi abincin, wani sa'in sai matar ta yi ƙoƙarin dawo da shi kan hanya "Abincin ya yi dadi kuwa?" Sai ya ce "Ƙwarai! Kin taba abinci ba dadi ne?" Sai kuma ya koma kan wayarsa, tana zaton ta samo hankalinsa amma kuma ya koma, wata takan yi ƙoƙarin jawo hankalinsa da cewa "Ka san miyar me kake ci?" Sai ya amsa "Ba alayyaho ba ne?".
.
Ta ce "Rai-dore ne, wani ganye ne da ake maganin typhoid da shi" sai ya ce "Mhnn!" Shi kenan, in ta ce "Kana son shi na ci gaba da yi maka?" Sai ya ce "Ƙwarai kuwa" in ta ji haushi sai ta kama gabanta ta ƙyale shi, irin waɗannan dabi'un suke sa mace ta ajiye wa namiji abincinsa a inda ya saba zama, in ya dawo sai ta leƙo ta yi masa sannu da zuwa kawai ta koma, don tana tunanin zuwanta wurin baida amfani, wata idan ta leƙo ta ga ya dora wayar a kan tebur yana cin abinci sai ka ji ta zaulaye shi "A miƙo maka wayar ne?" Da zai amsa za ta miƙo masa ɗin ta koma wurin yaranta, tanan kam sai mun yi yaƙi ba ƙarami ba wurin kawar da wannan dabi'ar.
.
Wani abin da zai ba ka mamaki akan sami mata da irin wannan halin, amma gaskiya kadan ne, na girma na sami uwayenmu sukan tarbi mazansu in har suka dawo gida, su karbi abin dake hannunsu, su shigar musu da shi ɗaki, wasu kuwa matar sai dai ta fadi a ciki "Barka da dawowa" ko matsawa a wurin ba za ta yi ba, kamar ba ma maigidanta ba ne, abinci ta riga ta gama yana turakansa, ta yi masa shimfida kuma ta kai masa ruwa don haka ta gama nata, irin wannan dabi'ar ba ta rasa nasaba da yadda mazansu suke, mazan ba su ba su fuskar da za su zauna kusa da su ba bare su tattauna wasu abubuwan da suka shafi cikin gida.
.
Na sani da wuya, amma akan sami macen da ita haka Allah ya yi ta, ba ta da lokacin da za ta zauna da namiji su yi hira, za ta kawo masa abinci, ta zauna a gabansa, amma ba ta da wani abin da za ta tattauna da shi, in ma shi ne ya bijiro mata da magana sai dai ta amsa daya biyu ta yi shuru, har shi ma a ƙarshe ya gaji ya dena ma yi mata magana gaba daya, irin wannan zarafin akwai shi amma ba kowani lokaci ba, kuma ya fi hatsari a tarbiyar 'ya'ya mata, domin za ka taras mu'amalolinsu na ƙauna a cikin gida ba su da yawa ko kadan, namiji dama tarairayarsa ake yi, ana zaulayarsa da sanya shi hira, da haka duk buƙatun da ake nema suke cika, in ya kasance wace za ta yi haka ita ma ba ta da lokacinsa shi kenan kowa ya iya allonsa ya wanke, kusan zamantakewar ta koma yadda wasu suke yi kenan a baya, sai ya zama za ta yi magana da shi ne in tana da buƙatarsa, in kuma ba haka ba kowa ya yi harkarsa, maganin wannan shi ne, ita macen ta fahimci girman wannan abu a nan gaba ta yi wa tukkan hanci.
.
Anan in an sami irin wannan rashin daidaituwan akwai wasu abubuwa da suke shugowa tsakiya, wato mace takan mai da martani, kasancewar ranta ya baci, kamar ta ce "Kai sai mutum ya gama zamanshi ko kallonsa ma ba za ka yi ba, bare ka yaba wa kwalliyar da ya yi" anan ba ma maganar abinci take yi ba, lokacin ne zai daga ido ya ce "Kin yi kyau mana, ba ki ga ina ta kallonki ba?" Ta ce "Wannan lallen ya ba ka sha'awa?" "I mana ai ina son lalle" "Don ma da rana na yi, ga shi ina ta aiki da ruwa, da a ce da daddare na yi na kwana da shi da ya fi haka ja" tana yi tana kallon yatsun hannunta da ƙasar ƙafafunta, in ta dago kai sai ta ga kallon wayarsa kawai yake yi ba abin da take ƙoƙarin nuna masa ba, sai cewa yake yi "Ya yi kyau ai" wasu lokutan wannan ya kansa mace ta fara tambayar kanta "Wai me yake gani a wayannan?" Ƙila daganan ta fara zarginsa.
.
Wato Ita Mace...
Mace tana ganin ko kana kallon abu a matsayin ya ba ka sha'awa dole ka fadi kuma da baki, kamar kwalliyarta da yadda take ƙoƙari wajen gyarar gidanta gami da tarbiyyar yara, haka in ta yi ma abinci, ko ka yi santi dole dai ka ce ya yi dadi, in so samu ne ma ku tattauna kowanne, wannan ne zai nuna ka yaba, shi kuma namiji yana ganin haba ai an wuce nan, ƙila ma akwai yara a wurin, kamar zubar da girma ne kadan, ita kuma ƙara mata kwarjini zai yi ka fadi a gaban yaranta, sai ta ji ka fasa mata kai, wata macen in 'yan uwanta mata sun yi mata maganar yadda take shiga, da ba ta shawara wajen gyaran kai, ko gyaran gida, sai ka ji ta ce "Abin da ko ka yi ba yaba miki za a yi ba?" In ta bari kuma an sami wani babban gibi mai wuyar toshewa.
.
Duk dai in mun lura gazawar da maza suke yi ne wurin ba da abin da ya dace a bayar na faranta zuciya. Wato buɗe baki a yi hira da iyali, da jinjina musu a inda ya dace, da sauraronsu a lokutan magana, da ƙaranta maida hankali wurin waya da komfuta, da ba su cikakken lokaci a sa'ilin da kake gida. Mace kam za ta yi babbar kuskure in ta ce za ta bar ado ko gyara abinci don ba a yabawa, maigida zai dauka ba ta iya ba ne, a maimakon ya fahimci cewa matsalar daga wurinsa ne.
.
Ya zama dole a wurin uwargida ta fara bin duk hanyoyin da suka dace wurin ganin ta dora maigidanta a kan turbar da take so don gyaran gidanta, ta koyi haƙuri, sannan ta fahimci cewa namiji ya dan bambanta da mace a wurin rayuwa, ta yi masa hanzari kasancewar ya dawo gida don ya huta ne, ta taimaka masa a wasu abubuwan da suka zama wajibi, ta gane cewa zaman da take yinnan don ta faranta masa rai ne, in ta ci nasara a lokacin ne ita ma nata ran zai yi haske, ta bi a hankali har ya fahimci yadda take, ta koya masa yadda zai riƙa yaba mata, kar ta tafi a kan cewa ya iya ya ƙi ne don muganci, in ta yi haka duk za su ji dadin rayuwarsu.

Post a Comment

0 Comments