Nazarin Waƙar Sakaryar Mace Daga Bakin Barmani Coge Da Mamman Duka

    In Kadaura Journal of Hausa Multi-Disciplinary Studies, Vol. 1, No 1, Department of Nigerian Languages and Linguistics Kaduna State University, Kaduna. Pp 108-119/ISSN 2536-7609.

    Barmani Coge

    Nazarin Waƙar Sakaryar Mace Daga Bakin Barmani  Coge  Da Mamman  Duka 

    Rabi Mohammed
    Jami’ar Jihar Kaduna, Nijeriya
    E-mail:rabimohammeddatti@gmail.com
    Phone No: 08060771666

    Tsakure

    Wannan takarda za ta yi tsokaci ne game da mummunarɗ abi’ar da aka ambata “Sakarci” ta fuskkar adabin Hausa. Wato za a waiwaya ne ga wasu makaɗan Hausa da aka ambaci sunansu a saman wannan takarda, a ga yadda suka auna wannanɗ abi’a. Ganin cewa waɗannan mawaƙa mabambanta jinsi ne, kuma sun kalli mace suka yi waƙa mai turke iri ɗaya, kai har ma salon,  za a so a gane shin wane tasiri waɗannan waƙoƙi ke da shi a cikin al’umma, musamman ma ga waɗanda waƙoƙin suka jiɓinta, wato mata. 

     

    1.0 Gabatarwa

      A bisa al’ada dai Bahaushe bai yarda da sakarci ba tun farko har zuwa lokacin da ya tsinci kansa a musulunci, ya kasance ya ƙara masa ƙaimi wajen tabbatar da cewa sakarci ba ɗabi’a ce mai kyau ba. Wannan shi ya ba wasu makaɗan Hausa damar yin waƙa da nufin ankarar da masu wannan ɗabi’a, su daina. Domin haka za a bayyana ma’anar wannanɗ abi’a, sannan a bi sawunta a bakin Marigayiya Barmani Coge mai Amada da kuma Mamman Duka mai goge, a ga yadda suka kalle ta da kuma irin salon da suka yi amfani da shi don isar da saƙonsu. Amma kafin nan fa?  

    2.0 Wace ce Barmani Coge, Wane ne Mamman Duka?

        Barmani Coge tana daga cikin fitattun mawaƙan baka waɗanda suke yi wa jama’a waƙa cikin harshen Hausa. An haife ta a wajen shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da arba’in da biyar (1945), a garin Funtuwa ta Jihar Katsina. Sunanta na yanka shi ne Sa’adatu. Bisa al’ada ta sami laƙabin ‘Barmani ne’ a sakamakon an haife ta ne bayan an ta yin wabi, ita ta kasance ta farko wadda ta rayu. Sunan Coge kuma ta same shi ne saboda yanayin waƙar da ta fara yi, tana faɗin, “Ku sauya kiɗa sannu-sannu zan coccoga”. A gaba kuma ta ƙara faɗin, “In ban taɓo cagewa ba, ban ji nai waƙa ba.” Ta fara kiɗan Amada wato kiɗan ƙwarya inda take waƙa tana ambaton waliyyai musamman na ɗarikar Tijjaniyya ko Ƙadiriyya, domin kuwa `yar gidan Malamai ce. Da haka ta ci gaba har ta shahara (tare da `yan amshinta)  wajen yin waƙoƙin da suka shafi lamuran zaman duniya daban-daban waɗanda suka haɗa da na yabo da faɗakarwa musamman ga mata. Wasu daga cikin kanun waƙoƙinta Shahararru akwai:

    ●Waƙar Coge

    ●Waƙar Sama Ruwa

    Waƙar Kishiya

    Waƙar Gwarne

    ●Waƙar Alherin Allah

    ●Waƙar Mai Abin Daɗi

    ●Waƙar Lalle-lalle

    ●Waƙar Ɗuwaiwai

    ●Waƙar Lale-lale Maraba Da Ke Zinariya

    ●Waƙar A Zage Zogala

    ●Waƙar Sakarai     (Gusau 1996:210).

       Hajiya Barmani Coge dai bisa taƙaitawa, ta yi kyakkyawar rayuwa gwargwado tunda ta yi karatun addini a gidansu kuma an yi mata aure har ta haifi `ya`ya tara. Kuma ba ta fara waƙa ba sai bayan ta yi aure tare da goyon baya daga mijinta da kuma mahaifinta. A halin yanzu ba ta raye. Ta rasu ranar Lahadi, 03/03/2013 Miladiyya, daidai da 21/Jimadathani/1434, Hijirar Annabi Muhammad (SAW), kamar yadda aka ji daga bakin iyalinta ranar 16/09/2014.           

        Shi kuma Mamman Duka ɗan asalin garin Kwanar Ɗangora ne da ke jihar Kano. An haife shi a wajen shekarar 1934 bisa ƙiyasi. Shi Mamman Duka bai yi karatun boko ba, sai dai bisa yadda aka sani a ƙasar Hausa, duk ɗan musulmi ana sa shi a makarantar allo, to shi ma ya yi. Ya shahara ne a kiɗan Goge inda ya fara waƙa a zamanin NEPU. Bai gaji waƙa ba, amma ya yi waƙoƙi da dama. An bayyana cewa da alama ya fi son wannan waƙa da ya yi ta ‘Sakarai’. A halin yanzu ba ya raye. Ya rasu da jimawa tunda ya kai shekara ashirin da biyar zuwa talatin da rasuwa. Ke nan ya rayu a duniya cikin shekaru hamsin. (An sami wannan bayani ne ranar 29/09/2014 daga bakin Hajiya Amina da wani Dattijo Usama Abdullahi, waɗanda suke zaune a Na’ibawa, cikin garin Kano). Sun kuma nuna cewa su abokan wasan Mamman Duka ne a Sabon garin Kano.

         Amma kuma da aka je garin Kwanar Ɗangora ranar 30/09/2014 don ƙara binciko tarihin Mamman Duka sai aka sami saɓanin asalinsa inda wani da ake kira Audu Ƙwaryama (Sai godiya) ya bayyana cewa, shi Mamman Duka ɗan asalin Nijar ne wanda ya yi rayuwa a cikin garin Kano. Yakan je Kwanar Ɗangora ne don yin sana’a. Dangane da iyali kuma ya ce babu wani nasa ko ɗaya a nan garin. Shi dai Audu Ƙwairama ya ce tare suke kiɗan goge da Babba mai goge wanda kuma a shirye yake ya bayar da tarihinsa da wasu waƙoƙinsa da ka.  

        Za a iya samun cikakken tarihin Hajiya Barmani Coge kasancewar an yi rubuce-rubuce a kanta da kuma hirarraki a kafar wasu gidajen rediyo na ciki da wajen ƙasar nan. Sai dai shi Mamman Duka, ba a yi karo da wani rubutu a kansa ba, ko da a gan shi cikin sahun mawaƙan baka da aka ambata a rubuce.

    3.0 Ma’anar Sakarci

           Bagery G.P (1934), ya bayyana ma’anar ‘Sakarci’ da cewa “Siffofi ko ɗabi’u na sakaran mutum”. Ya kuma bayyana cewa “Sakarai ko Sakare shi ne mutum mara amfani wanda ke da ƙarancin hankali, wato Shashasha.”

            Shi ma Skinner N. (1965), da Ƙamusun CSNL (1977) duk sun tafi a kan cewa Sakarai na nufin ‘mutum mara amfani’.

         Ke nan, Wannan kalma ta ‘Sakarci’  tana ɗaukar ma’ana ta ‘ɗabi’a wadda ta saɓa wa hankalin ɗan Adam.’ Wannan ɗabi’a ta dunƙule wasu munanan ɗabi’u ne waɗanda da zarar an ga mutum yana aikatawa, za a kira shi ‘Sakarai’ mace kuma ‘Sakarya’. Munanan ɗabi’un kuwa sun haɗa da kwaɗayi da rashin tattali da ƙazanta da rashin iya magana da yawon banza da rashin wayo da sauransu. Babu shakka idan da za a ga wani ko wata bai damu ko ba ta damu da neman ɗari da kwabo wanda zai tallabi rayuwarsa ko rayuwarta ba, to za a tsince shi/ta a wani hali na sata ko maula, wato roƙo da kwaɗayin abin hannun  wanda bai zama sakarai irinsa ko irinta ba.    

    4.0  Sakaryar Mace A Bakin Barmani Coge Mai Amada

        Bisa yadda aka fahimci ma’anar sakarci, a iya cewa lallai akwai ƙanshin gaskiya, domin Kamar yadda aka sani Allah Maɗaukakin Sarki ya rarrabe halittar ɗan Adam da dabbobi ta fuskar hankali inda aka fifita ɗan Adam bisa dabbobin. Don haka ana sa ran a ga mutum yana aikata abin da zai amfani rayuwarsa kodayaushe. Idan kuwa aka sami akasin haka, to ana ɗaukar mutum  Sakarai ko Wawa ko Banza ko Wofi, duk a matsayin rashin wayo ko ma rashin hankali. 

         Bari mu fara jin ta bakin shahararriyar mawaƙiyar jama’a wato Barmani Coge, wadda kasancewarta mace bai hana ta ta zayyana irin wannan mummunar ɗabi’a da wasu mata ke da ita ba. A bakin Barmani dai lallai babu sakaryar mace da ta fi wadda ta tsinci kanta cikin kishiyoyi, amma ita sam ba ta neman ɗari da kwabo, sai dai ta ci ta kwanta. Wannan yana nuna rashin tattali wanda kan jefa mutum a ɗabi’a ta kwaɗayi da ƙazanta da rashin karsashi da kuma rashin natsuwa.

        A cikin waƙar da ta kira waƙar Sana’a, ta bayar, su kuma `yan amshinta na faɗin ‘sakarai ba ta da wayo.’

    Ga abin da take cewa:

    Da ban da sakaren mace sauna,

     

    Wadda tana wurin miji su ukku.

     

    Duk saura suna ta sana’a.

     

    Ita ko sai idan gari ya waye,

    Ta tashi noƙai- noƙai,

    Ta leƙa wancan ɗaki,

    Yaya ina kwananku?

     

    Mun kwana lafiya mun tashi,

     

    To yaya da sauran tsaba?

     

    Sai su ce ki duba falo,

    Akwai ragowar dawa.

     

    Ta ci gaba da siffanta ɗabi’ar sakarcin mace tana cewa:

     

    Ko za ki itace yaya?

     

    Da ai kowa yana ta sana’a,

    Kin san ba ma yi tuwo ba.

     

    To yaya da sauran dawa?

     

    Da sai su ce ki duba falo,

    Akwai ragowar dawa,

    Ballagaza bazaar - bazar ta ɓarza,

    Kana kan ta tausa har ta talga,

    Kana kan ta ɓarka har ta tuƙa,

    Yaran gida ku kawo kwano,

    Ke uwar miji ga naki,

    Na gano abin mamaki,

    Ta Audu mai roƙo,

    Da an yi haihuwa a garinsu,

    Ana ta gayyar barka,

    Ta je ta ɗebi ruwa,

    Sai ta je ta rangaɗa wanka,

    Sai ta ɗauro leshi.

     

    Ɗaya kuma sai ta je ta ɗauro supa,

    Sai ta kusa da su ta je ta ɗauro Joji,

    Kuma ga ili gwaggwaronsu ga murjani,

    Kuma sannan ga agogo ga takalma,

    O! yaya ni na bi ku?

     

    To yaya ina  gyauton  nan ,

    Wanda kike yin cin-cin,

    In tsantsame shi in bi ku?

     

    Ballagaza ta bi su noƙai-noƙai.

     

    Kuma an je wurin barka,

    Ga uwargida bisa wundi,

    Ɗayar a kan `yar kanti,

    Ballagaza Bankaura,

    Da wadda ba ta sana’a,

    Ta ɗauki guntun keso,

    Ta kakkaɓe shi ta zauna.

     

    Ana ta ga tuwo `yan barka,

    Uwargida ta ce Allah raya,

    Ita ma ɗayar ta ce mun ƙoshi,

    Yaya a ƙi ci a ƙyale?

    Wannan tuwo abin Allah raya?

    Ai abun buki na buki ne,

    Kai yaya a miƙo yaji,

    Sai ta kama kantara loma,

    Hadda ta tada gyangyaɗassu na gado,

    Kai za a gida ko a’a?

    Kai ko a bari sai azahar?

    Kai rana ko ta take.

     

        Barmani Coge ta gina wannan waƙa tata ce kan sana’a, tana jawo hankalin mata da su kama sana’a ban da zaman banza. To a wannan waƙa da ta yi sai take nuna cewa duk macen da ba ta sana’a kuwa sakarya ce, kuma ta kira ta Ballagaza da kuma Bankaura,wani ƙarin sunan mace sakarya, kamar yadda aka gani.

        Barmani Coge ta yi ƙoƙarin bayyana ire-iren halayen macen da ba ta sana’a a cikin kishiyoyinta. Kishiyoyin na sakaryar macen suna ta sana’a amma ita ba ta sana’ar komai sai dai ta ci ta kwanta. Barmani Coge ta ba da misali da ballagazancin sakaryar mace inda ta nuna cewa ba ta ma iya abinci ba, saboda rashin natsuwa, domin in za ta yi tuwo kafin tukunya ta tausa take yin talge, kuma ba za ta bari talgen ya nuna ba, sai ta tuƙa. A taƙaice dai ɗanyen tuwo za a ci.

        Wani kuma abin da ya ba Barmani Coge mamaki game da sakaryar mace shi ne, inda aka yi haihuwa an saba a je a yi barka. To su kishiyoyin sakaren macen nan da za su tafi barka kowacce ta caɓa ado da kayayyaki daban-daban, to amma ita Ballagaza, saboda rashin sana’ar nan ya sa ma ba ta da wani ƙwaƙƙwaran zanin da za ta fita zuwa anguwa. Don haka sai ta buƙaci ɗaya kishiyar tata da  ta ba ta aron gyauton da take yin sana’ar cin-cin, ta  ‘tsantsame’ ta bi su. Tsantsamewa na nufin wanki sama-sama ba wanda zai fita tas ba. A haka nan dai ta bi su zuwa barka. A can gidan barkan ma sai da ta nuna sakarcin, inda aka yi masu tayin abinci, kowa ya yi kawaici ya nuna ya ƙoshi, amma ita sai ta ce za ta ci. Nan ta yi ta ‘kantara loma’, daga ƙarshe sai ta hau gyangyaɗi, kana ta farga ta ce da kishiyoyinta ko za a gida? koko a bari sai  azahar?

    5.0 Sakaryar Mace a bakin Mamman Duka Mai Goge

        Yayin da Barmani ke nuna rashin sana’ar mace a matsayin sakarci, sai wani mawaƙi wato, Mamman Duka ya nuna kwaɗayi a matsayin sakarci. Wannan ya bayyana tun a gindin waƙar inda `yan amshi ke maimaita faɗin: “Sakarai ta ci tsire kullum ba ta ɗaura zani ba mai kyawo.  Burinta sinima kullum ba batunta zani ba mai kyawo.” 

        A cikin waƙar, da ke tafiya cikin salon hira, an nuna irin wannan ɗabi’a ne a yayin da mace mara tattali kan jefa kanta a kwaɗayi (irin na ƙwalam da maƙulashe), inda kullum in har ba ta ci tsire ba , to fa babu zaman lafiya. Hakan ta faru a lokacin da mai atamfofi (Alh. Jigili) ya kawo talla ta ɗauki guda biyu alhali ba ta da ko sisi. Ta yi kuma alƙawarin zuwa kwana bakwai za ta biya kuɗin, amma hakan ba ta samu ba.

    Ga yadda ta kasance nan:

    Salamu alaikum

                Ah! Alhaji Jigili sannu da zuwa

    Hajiya barkanku da hutawa

    Yawwa sannu da zuwa

    Ahm! Na dawo ne kan alƙawarinmu da ke

    To Alhaji Jigili yau ko ni kam ba ni da ko ɗari

    Ba ki da ko ɗari?

    Wallahi ba ni da ko ɗari

    Me tsire kawo

    Me tsire!

    Na’am

    Ga shi ya kawo

    To nawa-nawa?

    Dala-dala

    To zare min na naira biyu

    To ga shi

    To ga naira biyunka

    To madalla sai anjima

    To wato ni kuma da na zo nan kika ce min ba ki da ko ɗari,….

    Ah! Alhaji Jigili me i fi raina, ba zan ci nama ba don kana bi na bashi?

    Wato ni nawa kuɗin ba za ki ba ni ba ke nan ko?

    Ah! Zan ba ka mana

    To shi ke nan, ni na gaba sa karɓa mani

    To je ka

    To shi ke nan

     

         An dai fahimci lallai kwaɗayi ya fi ga mata wanda kuma yakan jefa su a wani hali kamar yadda akan ce ‘ Kwaɗayi mabuɗin wahala’ ko kuma ‘Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutu.’ To babu shakka mawaƙin nan bai gushe ba har sai da ya nuna abin da ya biyo baya sakamakon ƙin cika alƙawarin biyan bashin atamfa da  wannan mata ta yi.

          Ga ta bakin nasa:

    Salamu alaikum!

    Yawwa Alhaji Jigili!

    Ah! Ranka ya daɗe Sa

    Lafiya na gan ka a nan duk ka haɗa gumi?

    Ina fa lafiya, idan ka ga na zauna ai da dalili

    To meye dalili?

    Wata yarinya ce ta karɓi turamena guda biyu na naira arba’in da huɗu.

    To kuma da na je na tambaye ta ma , sai ta ce ba ta san kuɗin ba.

    Ba ta ba ka kuɗin ba yanzu?

    Ba ta ba ni ba ai.

    Kofur Tanko!

    Na’am - na’am!

    Ku tafi da Alhaji Jigili ku je ku taho da yarinyar nan da ta karɓi turamensa.

    To Sa! To shi ke nan mu tahi.

       

        Duk da cewa mawaƙin bai ƙara komai ba a kan wannan ɗiya, amma ya ba mu haske cewa dai Alhaji Jigili ya kai ƙarar matar nan da ta hana masa kuɗinsa na atamfofi ofishin `yansanda. Kuma har an aika a taho da ita. An kuma san lallai dole a matsa mata ta biya wanda kuma zai iya kai ta ga wani mawuyacin hali, tunda da wuya ne ma in tana da wata halartacciyar  sana’a. Don haka sai dai ta je ta yi wata zambar don ta fita a wannan hali.

     

    6.0 Dangantakar waƙoƙin a faifan nazari

        Waɗannan waƙoƙi guda biyu za a iya kallon su ta fuskar turke da yadda aka warware shi da kuma irin salon da mawaƙan suka yi amfani da shi wanda lallai hakan ta sa hankali ya karkata ga wannan nazari.

    6.1 Turke

        Kamar yadda Gusau (2008:370 ), ya yi bayani, “Turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo kuma ana magana ne akan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba.” Har wa yau, ya nuna cewa, akwai ƙananan matakai da za su iya taimaka wa mai nazarin waƙar baka fitar da turken waƙar da yake yi wa sharhi cikin sauƙi. Waɗannan kuwa su ne, muhallin Turke da taƙaita Turke da Warwara da Tsettsefewar Turke da kuma Tubalan Ginin Turke. Dangane da nau’o’in Turke kuwa a waƙar baka, Gusau (2008:376-390), ya nuna akwai na Yabo zalla da na Zuga zalla da na Yabo surke da Zuga da na Ta’aziyya da na Zambo da na Tarihi da na Siyasa da na Soyayya da na Faɗakarwa da na Jaruntaka da na Koɗa kai da na Ban-dariya da na Addini da kuma na Ɗarsashi ko Rinjayen Zuciya.

        Yanzu za a iya bugun ƙirji a ce waƙar da Barmani Coge ta yi da wadda Mamman Duka ya yi, waɗanda aka ce wani abu a sama kaɗan, dukkansu Turke ne na faɗakarwa domin kuwa suna tunasarwa da yin hannunka mai  sanda ne ga duk wata mace da ta siffantu da wannan ɗabi’a ta sakarci, ta gane ba zai haifar mata ɗa mai ido ba. Za a iya tabbatarwa tun a gindunan waƙoƙin, yayin da a waƙar Barmani Coge ake faɗin, “Sakarai ba ta da wayo”, a waƙar Mamman Duka kuma sai ake cewa, “Sakarai ta ci tsire kullum ba ta ɗaura zani ba mai kyawo. Burinta sinima, kullum ba batunta zani ba mai kyawo.” A lokacin da mai sauraro  ya ji haka, to take zai fara hararo wasu siffofin da za a iya alaƙanta sakaryar mace da su, ko da kuwa mawaƙin bai Ambato su ba.

        Mawaƙan nan guda biyu sun taka rawa iri ɗaya wajen warware turke, kowannensu ya nuna rashin tattali a matsayin abin da ke mayar da mace sakarya a idon alumma. Duk da cewa a zahiri waƙar da Barmani ta yi, ta fi fitowa ɓaro-ɓaro a wajen nuna rashin neman na kai a matsayin sakarcin mace. Shi kuma Mamman Duka a tasa waƙar, hakan bai bayyana ɓaro-ɓaro ba. Sai dai a bisa fahimta za a iya cewa akwai ɗarsashin hakan musamman idan muka duba yadda Alhaji Jigili ya nemi kuɗinsa, wannan mata dai ta gaza biya. Wannan ya nuna cewa da tana da ƙwaƙƙwarar sana’a da ta iya biya. Bugu da ƙari, ko da ta ci tsire da kuɗinta, ta sayi zanin da take so ta ɗaura, da wataƙila ba ta kasance sakarya ba. Idan aka alaƙanta wannan da waƙar Barmani, za a ga cewa ta nuna kishiyoyin Ballagaza ko sakarya a sakamakon sana’arsu, suna sayen zannuwa na yayi, su ɗaura su kuma kece raini a tsakanin mata. Suna kuma cin abin da ransu yake so da kuɗinsu. Kamar a inda Barmani ta ce:

    Da ai kowa yana ta sana’a,

    Kin san ba ma yi tuwo ba.

     

    Da an yi haihuwa a garinsu,

    Ana ta gayyar barka,

    Ta je ta ɗebi ruwa,

    Sai ta je ta rangaɗa wanka,

    Sai ta ɗauro leshi.

     

    Ɗaya kuma sai ta je ta ɗauro supa,

    Sai ta kusa da su ta je ta ɗauro Joji,

    Kuma ga ili gwaggwaronsu ga murjani,

    Kuma sannan ga agogo ga takalma,

     

    Amma ga wadda ba ta sana’a sai gani sai hange. Idan ta gaza kuwa ta zama maroƙiya kuma makwaɗaiciya ko ta shiga rigima iri-iri don tana so ta mallaki abin da masu hankali suka mallaka. Kamar yadda Barmani ta misalta:

    O! yaya ni na bi ku?

     

    To yaya ina  gyauton  nan ,

    Wanda kike yin cin-cin,

    In tsantsame shi in bi ku?

     

    Ballagaza ta bi su noƙai-noƙai.

     

    Kuma an je wurin barka,

    Ga uwargida bisa wundi,

    Ɗayar a kan `yar kanti,

    Ballagaza bankaura,

    Da wadda ba ta sana’a,

    Ta ɗauki guntun keso,

    Ta kakkaɓe shi ta zauna.

     

    Ana ta ga tuwo `yan barka,

    Uwargida ta ce Allah raya,

    Ita ma ɗayar ta ce mun ƙoshi,

    Yaya a ƙi ci a ƙyale?

    Wannan tuwo abin Allah raya?

    Ai abun buki na buki ne,

     

    6.2 Salo

           An dai san cewa ma’nar salo ba baƙuwa ba ce ga manazarta fannin Adabi. Don haka ba za a zurfafa ba, za a tafi kai tsaye ne a nuna cewa lallai waƙar da Barmani Coge ta yi da wadda Mamman Duka ya yi, game da sakaryar mace, duka sun taka ƙafar salon hira ne na daga jikin tsanin salon da masu aikin Adabi ke hawa har zuwa ƙololi don kai saƙonsu inda ake buƙata. Ko da yake, waƙar da Mamman Duka ya yi, idan an saurare ta, za a gane cewa ta kasance `yar ƙwarya-ƙwayar wasan kwaikwayo ce a bisa ta Barmani Coge.

         Domin tabbatar da hakan ga misalin yadda waƙar ta zamo wasan kwaikwayo:

    Alhaji: Salamu alaikum

    Hajiya: Ah! Alhaji Jigili sannu da zuwa

    Alhaji: Hajiya barka da hutawa

    Hajiya: yawwa sannu da zuwa. Kai atamfofi ka ɗebo haka masu kyau?

    Alhaji: Ga atamfofi fa masu kyau

    Hajiya: To ka ba ni turmi biyu mana

    Alhaji: Turmi biyu? Kowane turmi ɗaya naira ahirin da ɗaya ne, turmi biyu naira arba’in da biyu ke nan.

    Hajiya: To ka bani na saya.

    Alhaji: To ga su, me za a samu yanzu wurinki?

    Hajiya: Wallahi ko kwabo yau ba za ka samu ba Alhaji.

    Alhaji: Ba ko kwabo, to sai yauhe?

    Hajiya: Sai rana i ta yau.

    Alhaji: To hi ke nan Allah ya kai mu.

             Daga wannan ɗiya ne sai aka ƙulla da ɗiyoyin da aka gani can baya waɗanda in an lura za a ga wasu `yan wasan cikin waƙar sun bayyana, kamar su  mai tsire da Sa (ɗansanda) da kuma kofur Tanko.

    Ita kuwa Barmani Coge, da kanta take sassauya murya musamman ma dai in ta zo nuna hoton sakaryar mace. Misali:

     Ita ko sai idan gari ya waye,

    Ta tashi noƙai- noƙai,

    Ta leƙa wancan ɗaki,

    Yaya ina kwananku?

     

    Mun kwana lafiya mun tashi,

     

    To yaya da sauran tsaba?

    Da kuma inda ta ce:

    O! yaya ni na bi ku?

     

    To yaya ina  gyauton  nan ,

    Wanda kike yin cin-cin,

    In tsantsame shi in bi ku?

     

    Ballagaza ta bi su noƙai-noƙai.

     

    Ana ta ga tuwo `yan barka,

    Uwargida ta ce, “Allah raya”,

    Ita ma ɗayar ta ce, “mun ƙoshi”,

    “Yaya a ƙi ci a ƙyale?”

    “Wannan tuwo abin Allah raya?”

    “Ai abun buki na buki ne”,

    “Kai yaya a miƙo yaji!”

    Sai ta kama kantara loma,

    Hadda ta tada gyangyaɗassu na gado,

    “Kai za a gida ko a’a?”

    “Kai ko a bari sai azahar?”

    “Kai rana ko ta take.”

     

        Yanayin muryar da Barmani take yi a matsayin sakaryar mace kai da ji za ka gane murya ce mai nuni da rashin wayo tamkar dai yadda bahaushe ke kallon ɗan fari. Tunda ɗan fari a wajen bahaushe, an san maganarsa ta sha bamban da ta sauran ƙannensa wataƙila saboda kawaici da uwa take yi a kansa, sai ya dinga shirme da rashin wayo idan yana magana.

    7.0 Tasirin waƙoƙin Ga Al’ummar Hausawa

        Lantana (2004) ta nuna cewa, a Nijeriya, masu fasahar baka suna taka rawar gani a tsakanin al’ummar Hausawa. Su waɗannan masu fasaha, sun kasu biyu, maroƙan Fada da maroƙan jama’a waɗanda kowanne akwai irin rukunan jama’ar da suka fi yi wa waƙa. Nazarin na Lantana (2004) ya kawo misalin Barmani Coge a matsayin maroƙiyar baka ko mawaƙiyar baka ta jama’a da take a matsayin `yan sahun gaba-gaba daga cikin ire - iren mawaƙan da ke kawo canji a cikin al’umma musamman a kan waƙar nan ta ‘Sana’a’ wadda ke ƙarfafawa mata su nemi `yancinsu daga ƙangi na tunani da fin ƙarfi da tattalin arziki.   Sannan kuma a cikin waƙar, Barmani ta yi kira ga mata da su nemi ilimi. Bayan nazarin ya yi sharer fage ne fa, sai ya yi sharhi a kan waƙar ta sana’a daki-daki.

        Asabe (2006), ita ma ta yi bayani game da yadda matan Hausawa na gargajiya ke amfani da nau’o’in hikimomin al’umma a hankalce a matsayinsu na iyaye mata, domin su gwada wa yara hanyoyin rayuwa ta duniya. Ta nuna cewa, mata Hausawa, tun farko sukan yi ‘yan waƙe-waƙe na aiki da na raino da sauransu. A cikin ire-iren waƙoƙin suna tarbiyyar yara game da ɗabi’a ta ƙwarai tare da tsoratarwa a kan mummunar ɗabi’a. Ta kawo misali daga  wata waƙar aiki na mata mai cewa:

    Ayye nanaye, iye yaraye aye manya sa lalle,

    Lantu sauna, Lantu shegiya, Lantu sauna,

    Lantu ta bi masu bugun kwano,

    Sun yi mata ciki sun koro ta,

    Ta tuna babu sarki sai Allah,

    Aye nanaye, iye yaraye aye manya sa lalle

     

    Da in yi cikin shege,

    Gara ruwan kwara su ɗauke ni,

    Su kai ni rijiya da macizanta,

    Su kai ni inda ɗan baƙi mai sari ya saran

     

        Sai ta bayyana cewa, wannan waƙa da sauran makamantanta, suna da  ma’ana a irin muhallan da aka yi amfani da su. Suna sa `yanmata bisa ɗabi’a ta gari, su iya haƙuri  har sai lokacin da aka halatta masu mazansu da za su kwanta da su. Domin duk yarinyar da ta rashi budurcinta kafin aure, to ana ɗaukarta banza ce a tsakanin  tsararrakinta da zuri’arta da sauran al’umma. Kuma wannan al’amari ne da har yanzu Hausawa ke riƙo da shi, a cewar Asabe (2006).

        Daga ƙarshe, ta kwaɗaitar da mata a kan su kasance masu sha’awar tarbiyyartar da yaransu ta irin waɗannan yane–yanen zantukan na al’adun gargajiya domin suna da tasiri ga zuciyar yaro fiye da magana ta yau da kullum. Yane-yanen  zantukan hikiman al’umma sun shafi waƙar ibada da hikayar mafari da tarihihi da tatsuniya da ba’a da karin magana da sauransu.

        Babu shakka za a iya yarda da hasashen waɗannan manazarta, domin waƙar da Barmani ta yi ta ‘Sana’a, matan Hausawa suna jin daɗinta kuma suna cin gajiyarta. Wannan nazari ya gano hakan a yayin da ya tuntuɓi Asiya Muhammad mai kimanin shekara arba’in da biyar,`yar asalin garin Kubau (ta ƙasar Zazzau) ce, wadda ta ce:

    “Na daɗe da jin wannan waƙa, kuma wallahi ta yi waƙarta a kan hanya. Faɗakarwa ne wannan waƙa, a tashi a nemi kwabo ( a nemi kuɗi ), a kashe su ta hanya mai kyau. A gaskiya wannan waƙa ta yi min daɗi kuma ta yi min amfani don ta ba ni ƙarfin gwiwa wajen neman abin kaina ta fuskar sana’a. Lallai sana’a kan sa zaman aure ya ɗore tunda na ga misali a kaina da ma wasu matan, yadda sana’a kan taimaka wa mace yin alheri da kuma zumunci. Sau da dama idan muna tsaka da sana’ar saƙa, kafin a ankara, sai a ji muna rero waƙar Barmani musamman inda takan ce, “ Ku kama sana’a mata, ayye macen da ba ta sana’a aura ce. A yi ƙuli-ƙuli ko ai ƙosai ko da dakau aka samu ma a yi.” 

     

    Ta ci gaba da cewa:

     “Shi ma Mamman Duka tasa waƙar faɗakarwa ce a gare mu mata mu daina cin bashi, amma mu nemi halallinmu ko da miji bai ba mu ba, mu nemi na kanmu mu sayi sutura mai kyau mu ɗaura mu ji daɗi. sai dai a gaskiya waƙar Barmani ta fi tsokalo zuciyata.”

     

        Babu shakka ashe wasu mawaƙan Hausa sun taimaka wajen ɗora zukatan mata bisa hanya mai kyau wanda zai kai rayuwarsu ga Tudun ‘mun tsira’.

    8.0 Kammalawa

        A taƙaice, daga abin da aka fahimta tun a farko na ma’anar sakarci, za a iya cewa lallai Barmani Coge da kuma Mamman Duka sun auna wannan kalma kuma sun nuna cewa wasu halayya da mutum ke wanzarwa tsakanin al’umma, kan tabbatar da a kira mutum ɗin sakarai. Domin ɗan Adam Allah  ya ba shi hankalin da har zai san abin da zai amfana da wanda zai cutu daga gare shi. Misali, rashin natsuwar macen , yana cutar da al’umma musamman ma a tsarin zaman Hausawa da ake yin karɓa-karɓa na girki tsakanin kishiyoyi inda  hakan ya haifar da rashin iya abincin da `yan gida za su iya ci. Sai kuma cin bashi ba tare da ƙwaƙƙwarar sana’a ba,  ballantana mace ta sami damar biya, wanda har zai kai ga hukuma inda za a hukunta ta. Wannan kuwa, zubar da mutuncin sauran mata ne.

        Daga ƙarshe, wani abin lura a wannan nazari shi ne, ashe idan mata suka kama sana’a ƙaƙƙwara domin samun abin biyan buƙatunsu na yau da kullum, zai yi wuya a sami sakaren mace ko Ballagaza ko Bankaura mara zuciyar neman abin kanta. Da fatan saƙon da ke cikin wannan nazari zai amfanar da mata a duk inda suke.                  

     

    MANAZARTA

    Tuntuɓi mai takarda.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.