Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Shaye-Shaye A Garin
Gusau (3)
NA
BASHAR ISYAKA
BABI NA BIYU
TARIHIN SHAYE-SHAYE
2.0 GABATARWA
Wannan babi
zai tattauna ne a kan tarihin shaye-shaye, ma’anar shaye-shaye a garin Gusau.
Abubuwan da ke sa maye, dalilin shan abubuwan da ke sa maye masu shan abubuwan
da ke sa maye, wuraren da ake shan abubuwa masu sa maye da sauransu.
2.1 MA’ANAR
SHAYE-SHAYE
Kalmar
shaye-shaye kalma ce wadda take ba da ma’anar shan wasu ababe masu haifar da
maye. Shaye- shaye wani abu ne da ke sa maye ya kuma fitar da mai shan daga
hankalinsa.
Bala
(1994:46) ya ce; shaye-shaye wata kazamar ɗabi’a ce
wadda matasanmu ke fama da ita, wadda sanadiyyarta mutuncinsu ke zubewa. Domin
da zarar ka ga mutum yana shaye-shaye komi kimarsa a idon jama’a mutuncinsa zai
zube a gurinu.
Umar (1993)
ya ce, shaye-shaye abu ne wanda ya ƙunshi wasu
nau’o’i na rashin mutunci. Cin zarafi, zubar da girma, wulaƙantar
da kai, da kuma rashin sanin darajar da ke ga ɗan Adam.
A Tawa
Fahimta Shaye-Shaye: Yana haifar da lalaci ga matasa da rashin
kunya, da rashin ganin girman ‘ya’ye da kuma rashin tausayi, haka da hana su
neman na kansu. Haka kuma shaye-shaye yana cutatar da matasa ta hanyar
lafiyarsu inda yake kawo ciwon hanta, da koda, da kunburin huhu da ciwon kansa
dasauransu.
2.2
SHAYE-SHAYE A GARIN GUSAU
Kamar yadda
muka gani a sama, kasancewar shaye-shaye yanayi ne na shiga wani hali na
lalacewa; wanda wasu mutane kan yi domin biyan wata buƙata. Wannan
kan faru ta sanadiyyar shan, miyagun ƙwayoyi ko,
shaƙawa, ko kuma gunɗawa da
sauransu.
Matsalar
shaye-shaye ruwan dare ce game duniya, wadda wannan zamani babu wata al’umma
wadda ba ta fama da wannan matsala a cikin rukunin mutanenta. Garin Gusau gari
ne da Allah ya albarkata da rukunin mutane mabanbanta, daga cikinsu har da masu
shaye-shaye. Wannan bincike ya shiga sassa ko unguwanni daban-daban- dangane da
binciko yadda al’amarin shaye-shaye yake gudana a garin Gusau. Daga cikin
wuraren akwai:
1. Gusau ta
gabas
2. Gusau ta
yamma
1. Gusau ta
gabas ta ƙunshi
a. Unguwar Gwaza
b. Fira da ƙwaɗi
c. Filin Jirgi
d. Unguwar Kara
e. Unguwar
matazu
f.
Samaru
g. Damɓa
h. Hayin Malam
Sani
i.
Kwango
j.
Sami naka
k. Sha’iskawa da
sauransu
2. Gusau ta
yamma ta ƙunshi
a. Sabon Gari
b. Birnin Ruwa
c. Sabon Fegi
d. Gada Biyu
e. Hayin Ɗan
Hausa
f.
Bakin Gulbi
g. Gangaren
Kwata
h. Tulluƙawa
i.
Ƙofar Mani da
Sauransu
Matsalar
shaye-shaye ta bunƙasa ne a garin Gusau
ta sanadiyar yawaitar masu sayarwa da tu’ammali da kayan shaye-shaye. Haka kuma
akwai matsalar rashin ɗaukar nauyi ko haƙƙin da Allah
ya azawa uwaye kan yaransu. Musamman rashin sa ido ga abokan ‘ya’yansu da kuma
rashin tsawata ‘ya’yansu ga zuwa wuraren da ake miyagun ɗabi’un
shaye-shaye.
2.3 ABUBUWAN
DA KE SA MAYE
Akwai
nau’o’in abubuwa daban-daban waɗanda mashaya kan yi amfani da su domin
yin wannan ɗabi’ar ta
shaye-shaye. Waɗannan abubuwa
sun haɗa da:
a. Giya
b. Ƙwaya
c. Shalisho
d. Wiwi (Tabar
Ibilis)
e. Babba Jiji
f.
Kwata
g. Shaƙen
Fetur
h. Shan bula
i.
Madarar Sukuday
j.
Cin ashana
k. Benelin/Totalin,
da sauransu
1. Ma’anar
Giya: Wasu sarrafaffen ruwa ne da ake amfani da su domin ɓatar da
hankalin mutum.
Ra’ayin
Masana Game da giya.
1. Imamu
Buhari ya ruwaito (Hatdisi na 6778) cewa Annabi Muhammad (SAW) yana bugun wanda
ya sha giya da hannu ko da takalmi saboda haramcinta ga musulunci.
2. Allah
Subhanahu Wata’ala ya haramta ma Musulmi su sha giya saboda tana fitar da su
cikin hankalinsu suna aikata laifuka masu zunubai: Suratul Nisa’i, aya ta (Ƙ3:25)
3. Hikimar
hana mutum ya sha giya shi ne dan ya kiyaye lafiyar jikinsa da kuma hankalinsa
da guje ma almubazzaranci da dukiyarsa (Kawahihi Fighiyya Ibn Zaji P: 310).
Kuma ita
wannan giya ta kasu gida uku kamar haka:
a. Ta Kamfani
b. Ta
gargajiya
c. Bammi
Ta Kamfani: Ita wannan
giya safarar ta ake yi daga wasu kamfanoni. Ita wannan giyar ana amfani da
na’ura domin yin ta, sannan a zuba ta cikin kwalabe a riƙa sayar wa
jama’a (mashaya).
Ta gargajiya:
Irin
wannan ita ce wadda ake kira burkutu. Ita wannan giyar da hatsi ake yin ta,
wato dawa ko gero ake jiƙawa su yi
tsawon sati guda cikin ruwa har sai ta yi tsiro da wari sannan a ciro ta a
sarrafa ta a mayar da ita giya.
Bammi: (Itama wata
nau’in giya ce ta gargajiya wadda masu shaye-shaye ke amfani da ita domin sanya
su maye. Ita wannan giya ana tatsota ne da itacen kwakwa inda ake fasa wannan
kwakwa ruwan da ke cikinta su riƙa yoyo cikin
gora su ne ake sarrafawa da sunan giya (Bommi).
Wasu matasa
na shan giya domin ganin abokansu na sha, kamar yadda masu iya magana ke cewa
“zama da maɗaukin kanwa
na sa farin kai”. Haka zalika wasu na ganin har in ba ka shaye-shaye to kai ba
ka waye ba. Haka nan wasu na shan giya domin jin daɗin rayuwarsu,
wani kuma saboda sabo yake shan ta ko yana son ya bari, bai iyawa saboda
jikinsa ya saba da ita, watau shan giya ta zama al’adarsa.
2. Ƙwaya:
Ma’anar
ƙwaya: Ƙwaya na nufin
duk wani nau’i na magani wanda ba na ruwa ba ko kafso ana kiransa ƙwaya.
To a cikin irin waɗannan magunguna ne masu wannan ɗabi’a suka zaɓo wasu suke
amfani da su a matsayin abubuwa masu sa maye domin suna shan su har su wuce
iyaka. Daga cikin waɗannan ƙwayoyi akwai:
a. (Diazepam
D5 ) : Ita wannan kwaya ta D5 an yo ta ne saboda maganin barci domin waɗanda ba su da
lafiya su yi amfani da ita domin su samu yin barci.
b. (Rohupnal
RCD): Ita ma wannan ƙwayar, musamman an yo
ta ne domin maganin gajiya, to shi ne mashaya suka ɗauki waɗannan ƙwayoyi
suna taunawa fiye da yadda ya kamata. Don suna hada guda ɗari (100) su
tauna lokaci guda, to sai kwakwalwarsu ta juye su shiga maye. Kuma ita wannan ƙwaya
suna taunawa ne idan za su yi wani ta’addanci da dai sauransu.
c. Tiramol:
Shi ma wannan maganin gajiya ne ga majinyata, amma mashaya sun mayar da ita
abun shaye-shaye wadda wani lokaci wani ko wasu idan har ba su yi amfani da ita
ba, ba su iya ɓarkata
(aiwatarda) komai.
3. Shalisho:
Shi shalisho wani gam ne da ake amfani da shi wajen yin faci na tib da dai
sauran gyaran duk abin da masu faci ke yi da shi. Shalisho yana cutar da
mashayansa ainun a huhunsu, domin illarsa ta fi ta giya. Domin ɗan shalisho
da zarar ya sha shalisho tana nuna masa babu mai ganin shi. Don haka yana iya ɗaukar komai
gabanka. Babbar illar shalisho ita ce yana gwada ma mashayansa su saci abubuwan
mutane don ba su ganinsu.
Haka kuma da
mai shan shalisho da mai madarar sukudaye kamar ɗan juma ne da
ɗan jumai’,
domin kowane na jawo abubuwa na fitar da hankali a lokacin da suke shan wannan
shalisho. Domin shalisho ba abinci ba ne rashin hankali ne kawai ga matasa su
riƙa shan shi don neman biyan wata buƙata
tasu.
4. Wiwi
(Tabar Iblis): Wannan wani haki ne da ake shukawa idan ya yi ganye sai a cire
ganyen a shanya ya bushe, ko kuma idan an ciro shi danyanshi sai a sa cikin
tasa a soya shi har sai ya bushe, shi ke nan ya zama wiwi, daga nan sai a fara
sayar da shi ga waɗanda ke shan shi. Ita wannan taba ta iblis
ana amfani da ita ana naɗa ta da farar takarda a murɗa ta kamar
taba a sa mata wuta kamar yadda ake yi ma taba ana ja a hankali har sai ta ƙare.
Haka kuma, ana amfani da ɗiyanta a riƙa tauna su,
kuma su waɗannan ɗiyan suna da
wasu ruwa cikinsu to duk da ruwan suke tattaunawa saboda su ma suna sa maye
sosai.
Akasari ita
wannan tabar iblis (Wiwi) ana saka ta ne wani keɓantaccen
bagire domin kaucewa idon mutane da jami’an tsaro. Idan ta fito ta yi girma sai
a cire ta a yi amfani da ita. Kuma ba ko ina ake samun irinta ba sai a wajen
masu sayar da ita.
Waɗansu mutane
na shan wiwi domin kore damuwar da ke tare da su ga rayuwarsu. Sannan wasu na
shan wiwi su kori aljannun da ke kanunsu. Sayar da wiwi sana’a ce ga wasu
mutane, amma wannan sana’a tana da dokoki waɗanda ake
hukunta duk mutumen da aka kama da ita. A wasu wurare har hukuncin kisa ake
yanke wa duk wanda aka kama ya karya dokar.
5. Babba
Jijji: Wannan
wani haki ne wanda ke fitowa a bola, kuma ainahi ya samo sunansa ne daga
fitowar da yake yi a bola. Shi wannan haki ba shuka shi ake yi ba, Allah cikin
hikimarsa yake fitar da shi ba don amfanin mutane ko dabbobi ba. Ubangiji kawai
ya san abin da yake nufi da shi. Duk tsiron da ubangiji ya fito da shi daga
cikin ƙasa yana da nashi amfani na daban. Ko dai ya
zama maganin wata cutar ko kuma ya zama cutar. Idan waɗanda ba
magani ba ne a gare su suka riƙe shi magani to
zai zama mai cutar da su.
Haka wasu ɓara-gurbin
mutane suka riƙa wannan ganyen amatsayin abin shan su. Kuma
shi wannan ganyen yana cutar da su ƙwarai da
gaske, dan sanadiyar shan shi yana kawar masu da hankali ƙwarai, kai
har ma da rasa rayuwa. Haka kuma idan suka sha shi duk duniya ba su ganin kowa
da kima ko mutunci domin duk lokacin da mashayi ya yi shaye-shayensa ba mai ɗaukarsa da
mutunci. Haka babba jijji yana yin ɗiya kamar na yalo, kuma ɗiyan ne ake
fashewa a sha don a sami maye (yan bori).
6. Shan Ruwan
Kwata: Kwata
wata mummunar ƙazanta ce da ke faruwa bayan kowane gida da
duk magudanun ruwan unguwanni. Ita ce mashaya suka ɗauka suna sha
domin ta canza kwakwalwarsu nan take, sannan ta
sa su cikin munanan halaye. Wani babban abin ban haushi a nan shi ne ba
wai ainahin ruwan kwatar suka sha ba; a a dagwalgwalon kwatar na ƙasa
suke sawa a tsumma suna shaƙar warin.
Kuma shi wannan wari shi ke sa su wannan mayen.
7. Shaken
Fetur: Man fetur wani mai ne da ake zuba wa injin mota da sauran injuna da
ke amfani da shi a yayin da ake aiki da shi. Shi wannan fetur mashaya suna shaƙan
sa domin ya kawar da hankalinsu, domin shi ma yana haifar da maye. To idan suna
da wata manufa ta yin rashin kunya kuma suka ga suna cikin hankalinsu to ba za
su iya aikata rashin kunyar ba. Sai su tura kansu cikin tankin man fetur ko
tankin mota ko na mashin su yi ta shaƙar fetur ɗin har sai ya
ji ya yi caji, ya fito da kansa. To daga nan komi yana iya aikatawa don a
wannan lokacin ba cikin hankalinsa yake ba.
8. Bula: Wannan wata
hoda ce bulu da ake amfani da ita wajen rinin kaya, ko kuma a sa ta a wasu
kuraje da ake ce ma ‘yan luɓus domin tana maganinsu. Abin mamaki
wasu mashaya sun mayar da bula abin da za su sha su sami maye. Wannan bula wasu
mashaya na shanta ba don komai ba sai don tana ɓatar da
hankalinsu su aikata rashin kunya ga wasu mutane.
9. Madarar
Sukudaye: Madarar
sukudaye haka take kamar madara gari fara, mashaya suna amfani da ita lokacin
da suke son su ji sun fita daga hayyacinsu, haka kuma lokacin da suke so su sa
kansu cikin mummunan hali; domin ita ma wannan madarar tana sa maye ainun tare
da fitar da mutum daga cikin hankalinsa. Haka kuma ita wannan madarar ta
sukudaye tana sa mutum ya ɗauki kansa kamar ya fi kowa a lokacin
da yake shan wannan madarar. Bugu da ƙari zai ɗauki mutane
ba su ganinsa. Madarar sukudaye tana haifar da wata cuta a huhun mai shanta,
zai ji kirjinsa na bugawa da ƙarfi, kuma ta
haifar da ciwon anta da dai sauran miyagun cututtuka. Sannan tana sa ƙeƙashewar
zuciya da rashin tausayi.
10. Cin
Ashana: Ashana
wata abu ce da ake amfani da ita wajen kunna wuta da duk wani abu da za a sa
mashi wuta kamar irin su bindiga. Ita ashana guba ce, amma mashaya sun mayar da
ita kayan shaye-shaye. Suna amfani da kan ashana, domin suna cire kan na sama
su cinye shi, kuma shi ne gubar. Daganan sai hankalinsu ya gushe su aikata duk
abin da suke so na ɓatanci ko na cin mutunci.
2.4 DALILIN
SHAN ABUBUWAN DA KE SA MAYE
Dalilin da ya
sa wasu mashaya suke amfani da abubuwa masu sa maye a lokacin shaye-shayensu
sun haɗa da:
1.
Wasu mashaya suna shan kayan maye ne saboda
rashin aikin yi. Saoda idan mutum ya zama ba ya da aikin yi sai zaman kashe
wando, to a nan ne ya ke fara tunanin abin yi a zuciyarsa. Daga ƙarshe
sai ya abka cikin wannan mummunar tabi’a ta shaye-shaye.
2.
Sannan wasu mashaya suna amfani da waɗannan miyagun
ƙwayoyin da sauran abubuwan sa maye ne saboda
su nuna wa jama’a sun waye wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum.
3.
Ɓacin rai yana
ɗaya daga
cikin abubuwan da ke sa mutane abkawa cikin wannan mummunar ɗabi’a ta
shaye-shaye. Wani idan gidansu akwai kuɗi in mamarsa ba ta
gidan kuma ana muzguna ma shi a gidan hakan kan jefa shi cikin wannan halayyar
ta shaye-shaye. Sau da yawa yaran da uwayensu mata ba su a gidan ubansu suna fuskantar
azabtarwa da za ta kai su shiga wannan halayya.
4.
Gata, nuna wa yaro gata yana jawo ya lalace
har ta kai ba a iya tankwara shi. Irin wannan yana jawo ya ƙulla
hulɗa da ɓata gari yara
masu shaye-shaye, waɗanda za su koya ma shi wannan ɗabi’a.
5.
Wasu mashaya suna shan wannan abubuwan da aka
faɗi a can baya,
saboda gurinsu ya cika; watau in suna so su cimma wani ko wata mutunci, to akan
haka sai su riƙa shaye-shaye saboda idan suna cikin
hankalinsu ba za su iya aikatawa ba.
2.5 MASU SHAN
ABUBUWAN DA KE SA MAYE
Akwai
nau’o’in mutane masu amfani da abubuwa masu sa maye. Irin waɗannan mutane
sun haɗa da:
1.
Maza
2.
Mata
3.
Yara masu kimanin shekara tara zuwa goma
4.
Akwai samari ko matasa
5.
Sannan kuma akwai dattijai da kuma tsofaffi
6.
Matan aure
7.
Yan ƙwadago ko
lebarori
Waɗannan su ne
mutane da ke shan abubuwan da ke haifar da maye.
2.6 WURAREN
DA AKE SHAN ABUBUWAN DA KE SA MAYE
Yanayin wajen
shaye-shaye ya banbanta daga wuri zuwa wuri, tun daga kalolin kayan
shaye-shaye. Ma’ana dai kowane abun shaye-shaye akwai keɓantaccen
wurin da ake shan shi. Misali masu shan giya akwai gidajen giya da aka tanada
na musamman dan shan ta, da zarar mashayi ya je gidan giyar zai ishe ana yin
shaye-shaye. Inda ake shan ta kwalba daban, inda ake shan burkutu daban. Sannan
kuma an tanadi wurin zama musamman dan mashayan. Akasari irin waɗannan gidaje
za ka iske maza da mata ne ke taruwa suna gwangwajewa wanda da zaran ka ga irin
waɗannan gidajen
ka san gidaje ne na mutanen banza (‘yan giya).
Haka kuma a
bagiren da ake shan taba wiwi da shalisho wani bagire ne wanda suke aikata
wannan mummunan halin. Abin nufi a nan ba su fitowa fili su sha wiwi da
shalisho, suna ɓoye kansu a
cikin jejji ko cikin wani kwazazzaɓen rami ko gefen gari inda dai mutane
ba su ganinsu da kuma kangayen gidaje. Ita tabar wiwi da shalisho ana samun
dilolinsu a waɗannan wuraren
da mashaya suke sayen wiwi ɗin su sha. Su kuma sauran kayan
shaye-shaye irin su kwata, babba jiji, ashana, sukudaye da sauransu ba su da
wani takamammen wurin shansu. Domin za ka ga ‘yan kabu-kabu idan suna tukin
mashin suna iya amfani da su, ko wasu masu aikin ƙarfi. Haka
nan ashana a gaban kowa suna iya cin ta.
A taƙaice
dai shi yanayin wajen shaye-shaye da zarar ka gan shi za ka gane wurin banza
ne. Saboda yadda suke tafiyar da harkarsu ta yau da kullum. Misali a wata
ziyarar da na kai a wata mashaya da ke Unguwar Gwaza Gusau mai suna; “Mami
Market” domin in gane wa idona, na ga yadda ake tu’ammali da giya da masu
shanta kwalba da masu shan ta gargajiya wato burkutu da bammi.
Haka kuma ita
wiwi, na tafi dabobin da ake shanta na ga yadda ake mu’amalarta na saye da
sayarwa da shanta. Daga cikin dabbobin da na ziyarta sun haɗa da:
-
Dutsin tsafi
-
Yar Rufewa
-
Farna
-
Filin Ali Silif
-
Fira da kwaɗi
-
Cocin kwano
Duk dabobin
da na tafi na ga yadda ake tu’ammali da kayan shaye-shaye kala-kala.
Kasancewar na
ziyarci guraren da ake yin shaye-shaye na yi hira da wani matashi mai wannan ɗabi’ar ta
shaye-shaye inda na tambayesa sunansa; sai yace:
Suna: Iro Dawa
Shekara 25, lokaci karfe 2:30 na marce,
20/6/2019
Unguwa: Sabon Fegi
Tambaya: Me ya sa ka ke shaye-shaye?.
Amsa: Na fara shaye-shaye ne a sanadiyar
abokaina domin abokaina su ne nake rakiya suna yin shaye-shaye suna ba ni. Tun
ba na sha har na kai na fara sha, kai tun ba na jin daɗi har na
saba. Tun ba na saye da kuɗɗina har nakai ina ba da kuɗɗina ina saye.
Tambaya: Me kake ji idan ka sha?
Amsa: Idan na sha ina ganin duniya ta
zauna daidai
Tambaya: Wane kalar kayan shaye-shaye kake sha?
Ansa: Ina shan Daga (Wiwi) da ƙwaya
Haka kuma na
kai ziyara a wata mashaya mai suna (Mami Market) da ke shiyar unguwar gwaza
Gusau, inda na iske ana shaye-shayen giya a nan ma na yi hira da wani mutum
inda na tambayi sunanshi sai ya ce.
Suna: Baba Alaske
Shekara 40 lokaci karfe 4:30 na marce, 21/6/2019
Unguwa Tudun Wada Labin-Labin
Tambaya Baba wagga kwalba fa?
Amsa: Yaro giya ce
Baba Kana shan giya ne?
Amsa: Yaro ina shan giya?
Tambaya: Baba yaushe ka fara shan giya
Amsa: Yaro na kai shekara 20
Tambaya Baba me ya sa ka shan giya?
Amsa: Yaro wata rana ina saurayi, muna
soyayya da wata Budurwata sai aka yi mata aure ba da ni ba. Wannan ɓacin rai shi
ne ya sa ni wannan shan giya domin ita ɗai nake sha in ji na
rage wannan ɓacin ran. Tun
tana sa ni maye ina faɗuwa har nakai na saba ko da na sha ta yanzu
ba na jin komai.
Haka kuma na
ziyarci wata mashaya da ke fira da kwaɗi, Tudun Wada Gusau
inda na sami matasa maza da mata suna ta shaye-shaye nan ma na yi fira da wata
matashiyar kamar haka:
Suna Laure
Unguwa Fira da Kwaɗi
Shekara 21, lokaci karfe 11:00, 22/7/2019
Tambaya: Me kike yi a nan?
Amsa: Muna bajewa
Tambaya: Wannan kwalbar fa?
Amsa: Totolin ne
Tambaya: Tun yaushe kika fara shaye-shaye?
Amsa: Na daɗe
Tambaya: Da me dame kike sha?
Amsa: Ina shan totolin da ƙwaya
Tambaya: Me ya sa ki shaye-shaye?
Amsa: Na fara shaye-shaye ne a Sanadiyar
Maraici, saboda mamata ta rasu ina hannun kishiyar mamata. To tana azabtar da
ni shi yas sa na bar gidanmu na dawo gurin saurayina wanda shi kaɗai ne ka sona.
Idan raina ya ɓaci to idan
na sha sai inji komi ya wuce.
Bisa ga
bayanan da suka gabata, an fahimci cewa yawancin masu ɗabi’ar
shaye-shayen kayan abubuwan maye suna yin haka ne saboda rashin gatanci da
maraici da kuma hulɗa da miyagun abokanai. Waɗannan dalilai
da waɗanda na yi
hira da su suka kawo ba lalle ne su zama mafarin shaye-shaye ba, sai dai idan
akwai niyyar yin haka.
2.7 KAMMALAWA
A cikin
wannan babi na biyu an kawo tarihin shaye-shaye, ma’anar shaye-shaye a garin
Gusau, abubuwan da ke sa maye, dalilin shan abubuwa masu sa maye, wuraren da
ake shan abubuwan da ke sa maye, da kuma su kansu masu shan abubuwan sa maye ɗin.
Great!
ReplyDeleteMunajin Dadi Allah ya Kara basira
ReplyDelete