Ticker

6/recent/ticker-posts

Shaye-Shaye A Garin Gusau (2)

 

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Shaye-Shaye A Garin Gusau (2)

NA

BASHAR ISYAKA

 

Shaye-shaye

BABI NA ƊAYA

1.0 GABATARWA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Maɗaukakin sarki, mahaliccin kowa da komai. Tsira da amincin allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa da Alayensa da waɗanda suka bi shi da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

 

Bisa ga binciken da nake son in gudanar a kan shaye-shaye a garin Gusau ya sa na ɗauki wannan dama don in yi aikina a kan abin da ya shafi rayuwar matasa na wannan zamani irin su, ‘yan wasan tsallake- tsallake da guje-guje da ‘yan aikin ƙwadago da direbobi masu yin doguwar tafiya; kai har ma da makiyaya waɗanda ke tafiye-tafiye zuwa wurare daban-daban da dai sauransu. Dukkan waɗannan rukunin al’umma suna amfani da ƙwaya ko abubuwa masu sa maye domin nishaɗi ko akasin haka.

 

Shaye-shaye ba karamin tasiri ya yi ba wajen gurɓata taribiyar matasa a garin Gusau, domin kuwa matasa masu shaye-shaye su ne ke aiwatar da abubuwa kamar irin su bangar siyasa, da faɗace-gaɗace tsakaninsu da sace-sace, da rashin ganin darajar mutane da rashin kyakkyawar manufa cikin rayuwarsu ta yau da kullum.

 

Saboda haka ɗabi’ar shaye-shaye ɗabi’a ce wadda ta kawo matsaloli masu ɗinbin yawa, da kuma taɓarɓarewar tarbiyar matasa ta kowane fanni; kamar yadda za’a gani a wannan bincike nawa.

 

1.1 MANUFAR BINCIKE

Kundin bincike na ɗaya daga cikin abubuwa waɗanda ake buƙata ga kowane ɗalibi kafin ya kammala karatunsa a jami’i. Wannan shi ne zai bai wa ɗalibi damar mallakar takardar shaidar kammala karatunsa. Wannan yana ɗaya daga cikin manufar wannan bincike.

 

Haka zalika, irin la’akarin da na yi da yadda rayuwar ɗabi’ar shaye-shaye ta zama ruwan dare ga matasanmu ya sa na yi sha’awar gudanar da bincike a wannan fanni na ilimi.

 

Saboda haka, ganin yadda shaye-shaye ke ƙara ƙamari ga rayuwar matasa ya ƙara mani ƙaimi in yi bincike a kan wannan matsala, domin in ba da tawa gudummawa wajen magance ko rage wannan mummunar halayyar ta shaye- shaye a zukatan matasa maza da mata. Wannan mummunar ɗabi’a ta taimaka wajen ruguza tarbiyar wasu daga cikin matasa, kasancewar yanzu halin da ake ciki kashi sittin na matasa suna aiwatar da wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye.

 

Har wa yau, wannan bincike zai taimaka wajen jawo hankalin hukuma, musmaman wadda ke kula da wannan ɓangaren na Shari’ar Musulunci, da ta sa ido ga masu aiwatar da wannan ɗabi’a domin ta ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin kawar da ita a cikin matasa.

 

A ƙarshe wannan bincike zai taimaka ainun wajen magance wannan mummunar ɗabi’a mai tarin illoli barkatai. Kuma zai nuna ma matasa ilolin da ke cikin wannan mummunar aƙidar da suka ɗauka gadan-gadan, wadda idan ba su bari ba, daga bisani za su yi da na sani. Ita kuwa “da-na-sani ƙeyace, a baya ake barin ta”. Da fatan wannan bincike zai yi tasiri ga rayuwar matasa da kuma al’umma baki ɗaya

 

1.2 DALILIN BINCIKE

Kamar kowane irin bincike da akan gudanar ana yin sa domin zaƙulo wasu muhimman abubuwa da kila a da ba a san su ba, ko kuma an sani amma ba a kula da su ba. Ko kuma ba a taskace su ba domin amfanin masu nazari. Hausawa na cewa “kowa ya yi da kyau zai ga da kyau” . Wannan magana ta yi dai dai da dalilina na yin wannan bincike. Dalili ke nan da ya sa na ja ɗamara na kuma zage damtse domin in yi nazari a kan wannan matani mai taken “shaye-shaye a garin Gusau”. Ga dukkan alamu wannan bincike shi ne irinsa na farko da aka aiwatar a kan abin da ya shafi illolin shaye-shaye a tsakanin matasa a garin Gusau. Don haka wannan shi ne babban dalilin da ya sa na zaɓi wannan batu in yi nazari a kansa domin in zaƙulo illolin da shaye-shaye ke haifarwa ga rayuwar matasa. Da fatar Allah ya ba ni ikon aiwatar da wannan bincike cikin nasara.

 

1.3 MUHALLIN BINCIKE

Wannan bincike da zan gudanar a kan shaye-shaye a garin Gusau, bincike ne da ya shafi rayuwa ta yau da kullum da matasa ke ciki. To da haka ne na ga ya kamata in yi rubutu a wannan fanni, domin in ba da tawa gudummawa a wannan ɓangare, haka kuma binciken zai taƙaita ne a garin Gusau domin nan ne matattarar matasa masu irin wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye ta yanke cibi.

 

1.4 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

Kowane al’amari akwai hanyoyi da dabarun da ake bi domin gudanar da shi. Haka ne ya sa wannan aikin zan bi wasu hanyoyi wurin aiwatar da shi, domin samun nasarar kamala shi cikin sauƙi.

 

Hanya ta farko da za ni yi amfani da ita, ita ce ta yin amfani da kundayen bincike da kuma wasu littafai da aka wallafa masu alaƙa da wannan bincike. Haka kuma zan ziyarci ɗakunan karatu daban-daban, domin duba ayyuka musamman waɗanda suka jibinci tarbiya da ɗa’a a makaratu domin samun ƙarin bayani a kan nawa aikin.

 

Wata hanya da zan yi amfani da ita ta huɗu itace ta amfani da ƙasidu da mujallu da jaridu masu bayani a kan ilolin shaye-shaye. Haka kuma wata hanya da zan yi amfani da ita wurin tattara bayanai ta haɗa da tuntuɓar wasu malaman addini domin jin ra’ayoyinsu dangane da wannan ɗabi’a ta shaye-shaye. Bugu da ƙari zan tuntubi wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa wato matasan da wannan ɗabi’ar ta shaye-shaye ta zama masu alaƙaƙai a zukatansu. Har wa yau bincike zai gana da jami’an hukumar yaki da safara da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ta ƙasa domin samun ƙarin bayani dangane da illolin wannan ɗabi’a a tsakanin al’umma musamman matasa.

 

1.5 HUJJAR CI GABA DA BINCKE

Akwai ayyuka da dama da aka riga aka gudanar a wannan fage, waɗanda sun suka rawar gani wajen faɗakarwa da tunatarwa ga al’umma, da kuma nuna masu illar shaye-shaye.

 

Waɗannan rubuce-rubuce sun nuna wa jama’a muhimmancin kyakkyawar tarbiyya ga matasa ta yadda za su kasance ‘yan ƙasa na gari. A sakamakon ayukkan da suka gabata an samu nasarar rage wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye. Haka kuma an samu rage gurɓatar tarbiya. Amma duk da haka za a iya cewa “akwai sauran rina a kaba”, watau akwai buƙatar a sake mai da hankali a waɗannan fannoni domin ganin cewa an ci nasara ɗari bisa ɗari, wajen kawar da wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye a cikin al’umma.

 

Saboda haka ne na ga ya kamata in cigaba da bayar da gudummawa, watau in yi iyakar abin da nake iya yi na ci gaba da bincike a wannan fanni. Domin a samu nasarar kawar da wannan mummunar ɗabi’a ta shaye-shaye a garin Gusau.

 

1.6 BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce a wannan fanni na ilimi, saboda haka ya zama dole in bayyana inda nawa binciken ya dosa. Sannan kuma in faɗi wasu daga cikin rubuce-rubucen da aka aiwatar a wannan farfajiya ta fannin ilimi.

 

A cikin wani sharhi da wani shehin malami ya yi watau (Narahatsi) watau mai nazari a kan ƙwayoyi, wanda ya fito daga arewa maso yamma a wata babbar asibiti da ke chicago. Cewa ya yi ‘nikotin’ yana haifar da yawan mutuwa kuma yana rage wa mai shakensa karfin nazari a kwakwalwarsa. Sannan kuma ya ce “giya da Nikolin  (koken) suna da tasiri ga mai amfani da su, amma a lokacin da ya mai da hankalinsa gare su suna illata shi ainun.

 

Bisa ga maganar kambri (1993) cewa ya yi ‘ƙwaya wadda ita ce mataimakiyar rayuwa, amma yanzu ta koma shaye-shaye, ta kuma haifar da ruɗani ga jama’a. To ita wannan ƙwaya kamata ya yi a yi hani daga shanta.

 

Idan muka duba za mu ga dukkanin kundayen da aka yi bayani a sama sun kalli fuskoki daban-daban da nawa binciken. Ni kuma nawa binciken zai mai da hankali ne kacokan kan shaye-shaye a garin Gusau. To amma idan muka duba waɗannan ayukka da suka gabata kusan abubuwa ne da suka danganci junansu sai dai kowane aiki akwai inda ya dosa.

 

1.7 KAMMALAWA

Wannan babi ya yi magana a kan abubuwan da suka shafi gabatarwa da manufar bincike, dalilin bincike muhalin bincike, hanyoyin gudanar da bincike, hujjar cigaba da bincike da kuma bitar ayukkan da suka gabata, daga ƙarshe sai kammalawa.

Post a Comment

0 Comments