Ticker

6/recent/ticker-posts

Adashen Mata A Garin Gusau (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu, Jami’ar Tarayya Gusau.

Adashen Mata A Garin Gusau (5)

NA

AMINA ABUBAKAR

Adashe

BABI NA HUƊU

YANDA AKE ADASHE A GARIN GUSAU

4.0 GABATARWA:

A wannan babi na huɗu za a yi bayani ne a kan yadda ake adashe a garin Gusau, bugu da ƙari, kuma za mu yi bayani a kan uwar adashe da kuma yadda ake zubin adashe a garin Gusau. Idan kuma aka nutsa a cikin babin za mu ga yadda ake kwasar adashe tare da duba muhimmancin adashe. Haka kuma za mu yi duba zuwa ga illolin da ke ƙunshe cikin adashe, daga ƙarshe kuma a rufe babin da kammalawa.

 

4.1 ADASHE A GARIN GUSAU

Tsarin adashe kan ƙunshi ƙungiyar mutane, waɗanda suka aminta da juna, kuma daga cikin su a ke samun shugaban adashe, ko mai tsarawa. A wani tsarin adashe kuwa ana samun shugaban adashe, da ma’aji, da mai kula da harkokin adashe a rubuce. Wasu kuma suna yin abin su da ka, ba tare da sun rubuta ba. Wasu ma kan tsara dokokin tafiyar da adashe a rubuce, wasu kuwa ba su rubuta dokokin tafiyar da shi.

 

A cikin garin Gusau, an samu tabbacin irin yadda tsarin gudanar da adashe yake a gargajiyance. A wannan tsarin mutane amintattu ga junansu suna shirya adashe tsakaninsu wanda sukan ƙunshi adadin daga mutum biyu zuwa adadin da ya samu na jama’a.

 

Daga cikin wannan adadi ne na masu yin adashe ake samun ɗaya wanda zai zama shugaban adashe, ko a ce uwar adashe ko uban adashe. A al’ada ana gudanar da adashe a ka ba tare da an rubuta ba.

 

Haka kuma dokokin da aka tsara wanda suka shafi zubi da kwasa, duk a ka ake amfani da su. Sai dai daga baya zamani ya yi tasiri wasu kan rubuta dokokin tsarin zubin adashe da na kwasa, kamar dokokin da suka shafi mutuwar wani bayan ya yi kwasa, wasu sukan rubuta cewa, sun aminta an yafe wa duk wanda ya rasu abin da ya kwasa saboda tausayawa ga magada. Haka kuma, kasawar ci gaba da zubi, tsarin dokar adashe ta tanadi duk sai kowa ya kwasa sannan a ƙarshe a mayar masa da adadin kuɗin da ya zuba. Wato mutanen da ya yi wa zubi, zasu mayar masa da kuɗin da ya zuba masu a lokacin kwasar su.

 

4.1 UWAR DUWATSU:

Uwar duwatsi, ita ce uwar adashe, uwar adashe ita ce wadda take zama jagoran masu gudanar da adashe. Haka kuma mace ce wacce take da riƙon amana, saboda ita ce wadda ta ke ajiyar kuɗaɗɗen da ake zubi. Uwar adashe ita ce wacce ake wa kirari da cewa “Gwaggon rikici”. Ana yi mata wannan kirari ne saboda dalilai kamar haka:

·         Dalili na ɗaya; uwar adashe kan cinye kuɗin da masu yin adashe suka zuba a yi ta yin rigima da ita.

·         Dalili na biyu kuma, idan sun haɗu da mayaudara daga cikin masu adashen suna gudu sai su yi ta yin rigima da su kafin su ba da cikon kuɗi.

 

Haka kuma, akwai wasu sharuɗɗa da ake son uwar adashe ta cika, ga su kamar haka:

1.      Ta kasance mai gaskiya da riƙon amana, yadda duk wanda ya yi zubi ba za ta ci kuɗinsa ba, haka kuma ta kasance mai gaskiya ce a cikin maganarta.

2.      Ta kasance ba mayaudariya ba ce.

3.      Ta kasance jajirtatta, saboda idan ta cika sanyi da yawa, duk wanda ya kwasa ba zai ci gaba da zubi ba.

 

4.3 ZUBIN ADASHE:

Kuɗin zubin adashe kan kasance bisa yarjejniyar masu yin adashe, saboda haka ya danganci yadda suka yi shawara a kan abin da kowa zai bada, to, sai a ci gaba da zubawa a kan lokacin da suka ƙayyade. Haka kuma, mutane biyu ko abin da ya fi haka kan haɗu su rinƙa zuba abin da kowane mutum ɗaya zai riƙa zubawa a duk bayan ƙayadadden lokaci. Wasu na zuba hannun ɗaya. Gwargwadon abin da mutum zai zuba shi ake kira hannu. Masu zubin adashe kan shawarci junansu domin abin da za su zuba ya zama mai yawa ne, don wannan zai ba kowa dammar kwasar kuɗi masu yawa don biyan buƙatarsu, kamar haɓɓaka harkokin kasuwanci ko sayen wani abu muhimmi 

 

4.3.1 LOKACIN ZUBIN ADASHE:

Lokacin zubin adashe, ya danganta ne ga yadda masu yi suka tsara uwar adashe ko uban adashe, wasu sukan ƙaranta lokacin zubi, wasu kuma suna tsawaitawa, ya danganta ne da adadin masu adashen da kuma kuɗin da suke zubawa. Sai dai ana iya cewa adashen mata na ƙungiya shi ne aka fi gajarta lokacin zubi dalili kuwa shi ne a yi kwasa da wuri don biyan buƙatu. Wasu na yin zubi duk rana, sai a yi kwasa a ƙarshen sati. Wasu kuwa suna yin zubi duk bayan kwana uku, kuma a yi kwasa a ranar da aka ƙare zubi ko bayan kwana biyar.

 

Wasu kuma suna zubi kullum har tsawon kwana goma ko sati biyu, sannan a yi kwasa. Wasu kuma a kwashe a lokacin. Kamar yadda wasu ma’aikatan Gwamnati kan shirya adashensu tsawon kwanan wata sannan su yi zubi, kuma a yi kwasa.

 

4.3.2 HANYOYIN ZUBIN KUƊIN ADASHE:

Ga al’ada, duk mai yin adashe, yakan bada kuɗin zubinsa ga hannu, wato zai bada tsabar kuɗi ga uwar adashe. Amman a yanzu a kan yi amfani da takardar izinin biyan kuɗi a banki wurin bada kuɗin zubi.

 

Kafin a fara zuba kuɗin adashe, uwar adashe ce kan ba da sanarwa cewa, tana son ta kafa adashe, zubi naira ashirin (20), amma kwasa duk bayan kwana biyar. To idan an samu masu yi a bisa wannan yarjejeniyar sun amince da haka sai a ci gaba da kawo zubi wurin uwar adashe. Wani lokaci kuma idan ta ga lokacin zubi ya yi wata ba ta aiko ba, to ita uwar adashen sai ta aika yaro ya je wajen wadda ba ta ba da kuɗin zubin ba, sai wannan yaron ya je ya amso kuɗin. Irin wannan hanya ta zubin kuɗin adashe ta daɗe ana gudanar da ita a gargajiyance a tsakanin masu yin adashe.

 

4.4 KWASAR ADASHE

Tsarin kwasar adashe ya danganta ne da yawan masu zubi, wa zai kwasa a farko, wa kuma zai kwasa a ƙarshe? Tsarin na da muhimmanci, domin duk wanda ya ba da zubinsa za a ba shi kwasa, ana zagayawa har a ba kowa. Wajen tsarin fitar da na farko zuwa na ƙarshe, wasu kan yi amfani da yawan shekarun masu adashen, ko kuma a yi la’akari da irin matsalolin da suka addabi kowa, yadda za a ba shi ya warware buƙatarsa. Wasu kuma kan yi la’akari da girman shuwagabanni wajen fitar da na farko.

 

Mafi yawanci, ƙungiyoyin adashe sun fi la’akari da tsarin kwasar adashe a kan yadda aka cimma yarjejeniya ga tsari na farko zuwa na ƙarshe.

 

Tsarin kwasar adashe, ya ba da dammar zagayawa har kowa a ba shi kwasa. Idan an kai ƙarshe kuma za a sake wani sabon adashe a karo na biyu. To a nan ma wasu na la’akari da cewa, wanda ya yi na ƙarshe to, sai kuma a ba shi kwasa ta farko, domin ya haɗa da kwasa ta ƙarshe, don ya ƙara bunƙasa da inganta rayuwarshi. Irin wannan tsari na kwasa an daɗe ana gudanar da shi a garin Gusau ga masu gudanar da adashe.

 

Wasu kuma na gudanar da tsarin kwasar adashe a rubuce. Kamar yadda ake yi a wannan lokaci, za a fitar da na farko har zuwa na ƙarshe, tare kuma da sa hannu don nuna yarda da amincewa da irin tsarin da aka yi, saboda gudun rigima. Bugu da ƙari, a kan gudanar da ƙuri’a ga masu yin adashe, musamman irin ma’aikata, domin a fitar da na farko har zuwa na ƙarshe, ga mutanen da ke yi ba tare da yin la’akari da wasu matsaloli ba, don kaucewa rigima da nuna rashin adalci ga wasu. Gudanar da ƙuri’a, ga masu yin adashe, wannan wani al’amari ne da aka fara yi daga baya, saboda ƙarin samuwar masu yin adashe, da bijirowar matsaloli, da son nuna biyan buƙata da sauri wannan ya haifar da gudanar da ƙuri’a tsakanin masu kwasar adashe.

 

Wani nau’i na kwasar adashe shi ne na kati ana gudanar da wannan adashe ne a rubuce, ba a ka ba, kamar yadda wasu ke gudanarwa. Ana yin wannan ne domin kaucewa wasu matsaloli da kan iya tasowa a kowane lokaci, da tasirin zamani da samuwar fahimtar juna. Uwar adashe dai na tafiyar da adashe a cikin irin wannan tsari mai ɗauke da sunayen masu yi, da adadin kuɗin zubi na kowa, da abin da ya kwasa ko ya amsa, kuma jerin ranakun kwanan wata har zuwa ƙarshensa.

 

4.4.1 KUƊIN GURBI/ GUIWA/KARIN ADASHE

Mafi akasari dai, al’umma na shiga adashe ne ba tare da sun biya kuɗin shiga ba, ko kuma kuɗin rajista. Ana shiga adashe ne haka nan ba tare da biyan wasu kuɗi ba, da sunan kuɗin shiga. Sai dai kuma wasu wurare ana karɓar kuɗin gurbin adashe a hannun kowane mai yi. Dalilin amsar waɗannan kuɗin na gurbi kuwa shi ne, lada ga shuwagabannin adashe.

 

Kuɗin gurbi dai, wasu kuɗi ne da duk wanda ya kwashi adashe daga hannun uwar adashe/ uban adashe zai bayar. Wannan kuɗi, an ɗauke su ne a matsayin ladar tari ne ga uwar adashe. Mutum zai cire abin da ya yi niyyar bayarwa ya bayar ga uwar adashe, a matsayin ladar tari. Uwar adashe ko uban adashe, ba su ƙayyade kuɗin gurbi, sai dai mutum ya ba da abin da ya yi niyyar bayarwa. Amman kuma wasu suna ƙayyade kuɗin gurbin da za a ba su, wato ladar tarin kuɗin adashen da za a ba su.

 

Kuɗin gurbi dai su ne ladar tari, mafiyawancin ƙungiyoyin adashe, suna kiran irin wannan kuɗi da sunan kuɗin gurbi. Wasu kuma kan kira shi da sunan “Guiwar Adashe” ko “Karan –Adashe”. Duk waɗannan sunaye ana amfani da su a garin Gusau da kewayenta. Wannan hanya dai a yanzu za a iya cewa ita ce hanyar da mafi yawancin masu gudanar da adashe suke amfani da ita. Domin irin waɗannan mutane ta nanne sukan ɗan sami abin biyan buƙatunsu na yau da kullum don kawar da talauci

 

4.5 MUHIMMANCIN ADASHE:

Dole ne ya kasance duk wani al’amari ko wani abu na rayuwar yau da kullum, to dole ne ya kasance yana da muhimmanci koda kaɗan ne. To haka shi ma adashe, kamar sauran al’amurra ne, yana da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma, musamman ma ga mutane masu ƙaramin ƙarfi.

 

Masana tattalin arziki sun ɗan yi tsokaci game da muhimmancin adashe ga kaɗan daga cikinsu:

 

Miracle da Cohen (1980), sun bayyana cewa “Al’umma na amfani da kuɗin adashe wanda suka tanada ta hanyoyi daban-daban domin biyan buƙatocin rayuwarsu.”

 

Aliero (2004) ya bayyana cewa “Mutane na gudanar da adashe ne don su bunƙasa rayuwarsu da kuma inganta ta don kawar da talauci.” Bugu da ƙari, ga wasu daga cikin muhimmancin adashe kamar haka:

1.      Sadar da Zumunci: Ta hanyar adashe, mutane kan ƙulla zumunci sosai a tsakanin su.

2.      Dogara da kai: Adashe yana taimaka wa mutum ya dogara da kan shi, ta hanyar ya tsaya ya nemi na sa na kan shi, don ya sami abin da zai gudanar da rayuwarsa.

3.      Bunƙasa Tattalin Arziki: ‘Yan kasuwa waanda jarinsu ya yi ƙasa, za su shiga adashe domin su tallata wa kasuwancinsu, saboda idan sun yi kwasa, to za a ba su kuɗi ne masu yawa, to da waɗannan kuɗaɗen sai su ƙara bunƙasa kasuwancinsu.

4.      Haɓɓaka Jari: Wannan ma wata muhimmiyar hanya ce, ta amfani da kuɗin adashe da al’ummar Hausawa ke yi. Kamar sayen motar sufiri, da babura, da injinin niƙa, keken ɗinki da sauran wasu hanyoyi na gudanar da kasuwanci.

 

5.      Sayen Abun hawa dan sauƙaƙa hidimomin rayuwar yau da kullum, kamar keke ko babur ko mota, da sauransu.

6.      Sayen wasu abubuwa na inganta rayuwa da suka haɗa da muhalli, abinci, sutura, biyan kuɗin makarantar yara, da wasu kayayyakin more rayuwar iyali, da sauran hidimar da ta jiɓinci al’ummar wuri na taimakon kai- da- kai da wasu hidimomi na dangi.

 

Haƙiƙa haka al’amarin amfanin kuɗin adashe yake tun can asali a gargajiyance, al’ummar Hausawa na gudanar da akasarin waɗannan hanyoyi. Kamar yadda masana suka riga suka bayyana, sai dai kaɗan daga cikinsu waɗanda suka samu bayan haɗuwar al’ummar Hausawa da baƙin al’ummu, wanda ya kawo ci gaban inganta rayuwar baki ɗaya. Kamar sayen galmar shanu ta huɗu, da tukunyar sanya ruwa don more rayuwa[1] 

 

3.6 ILLOLIN ADASHE:

Kamar yadda aka riga aka sani, komai na rayuwa yana da amfani, kuma a wasu ɓangaroran idan aka bincika yana da rashin amfani. To haka shi ma adashe kamar sauran al’umura yake, yana da amfani kuma yana da irin nasa matsaloli ko illoli. Illolin adashe sun haɗa da:

i.                    Cin Bashi: Yin adashe ko shiga adashe yana haifar da cin bashi, saboda idan mutum ya rasa kuɗin zubi, to zai fara tunanin ciwo bashi domin ya kai kuɗin zubi.

ii.                  Yaudara: Mayaudara, idan suka shiga adashe aka ba su kuɗin zubi, sai su fara wasan ɓuya da uwar adashe ko uban adashe, domin kuwa ba su son su biya kuɗin mutane da suka ci.

iii.                Rashin cika alƙawari: Ana samun wasu mutane waɗanda ba su da alkawari da riƙon amana, da sun cinye kuɗin zubi to za su saɓa alƙawari, ba za su ba da kuɗi ba sai an yi ta rigima da su.

iv.                Faɗa: Adashe yana haifar da faɗa, dalili kuwa shi ne, idan uwar adashe ta cinye ma ‘yan zubi kuɗi suna zubi to faɗa yana iya faruwa a tsakaninsu.

 

4.7 KAMMALAWA:

Wannan babi ya yi bayani dalla-dalla a kan dabarun da Hausawa suke amfani da su na karɓar kuɗi daga wani wurin da suka ba da ajiya don biyan buƙatun rayuwa. Daga cikin waɗannan dabaru, akwai mai nau’in taimako wanda wani zai tausaya ya baka kuɗinsa da sunan ka dawo ma shi da su zuwa wani lokaci. Wannan ɓangaren kuma kuɗi ne mutane za su tara su baka don ka biya buƙatar ka, kai kuma sai ka riƙa biyan su a hankali. Kazalika an tattauna yadda ake zuba adashen kwasa, da kuma wace ce uwar dutsi. Daga ƙarshe an yi tsokaci kan muhimmancin adashe, illolin adashe da dai sauransu.[1] Hira da Alhaji Umaru Suleiman mai Adashe 20/8/2019. Hira da Hajiya Ade Maiadashe, 24/8/2019

Post a Comment

0 Comments