Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.
Karin Harshen
Zamfarci (Musamman A Garin Gusau) (5)
NA
BASHIRU HARUNA
BABI NA HUÆŠU
KARIN HARSHEN GARIN GUSAU DA DAIDAITACCIYAR HAUSA
4.0 SHIFIÆŠA
A babin da ya gabata an yi magana ne a kan ma’anar harshe da ma’anar karin
harshe da dalilin samuwar karin harshe. Bugu da ƙari, an yi tsokaci a kan rabe-raben
karin harshe da karin harshen gabas da karin harshen yamma. A wannan babin na
huÉ—u za a yi bayanin karin harshen
garin Gusau da Daidaitacciyar Hausa da tsarin sauti da Æ™irar kalma da ma’anar kalmomi da
ginin jumla.
4.1 KARIN HARSHEN GARIN GUSAU
Kamar yadda masana da manazarta suka yi bayanin cewa, karin harshe yana
faruwa ne daga wasu bambance-bambance a lafazi da kalmomi da jimloli ko a dukkansu
tsakanin sassan Æ™asa ko a rukunin al’umma. Don haka, idan muka yi la’akari da waÉ—annan bayanai za mu iya cewa karin harshen garin Gusau,
shi ne karin harshen da ya keɓanta ga Gusau da kewayenta. Wannan karin harshe da shi ne mutanen garin
Gusau suke amfani wajen gudanar da
rayuwarsu ta yau da kullum.
Karin harshen garin Gusau ya yi kama da karin harshen Katsina ta fuskoku da
dama, wata kila ma wannan shi ya sa da yawa manazarta kan kalle shi a matsayin
karin harshen yamma, amma a wani ƙauli, ko kusa ba su zama abu ɗaya ba. Saboda haka, idan muka dubi karin harshen garin
Gusau za mu ga cewa wani karin harshe ne, keÉ“aÉ“É“e wanda al’ummar garin Gusau ke amfani da shi ta fuskar kasuwanci da sauran
hulÉ—a irin ta sadarwa tsakaninsu da
sauran kare-karen harsunan Hausa, ba tare da wata maatsala ba. Don haka, idan
aka kwatanta Daidaitacciyar Hausa da karin harshen garin Gusau za a ga lalle
sun bambanta ta hanyoyi daban-daban kamar haka:
1.
Hanya ta farko da ta
bambanta Daidaitacciyar Hausa da karin harshen garin Gusau ita ce,
Daidaitacciyar Hausa wata tsararriyar hanya ce da hukuma ta gina tare da wasu É—a’idoji ko dokoki.
2.
Hanya ta biyu masana da
dama sun yi rubuce-rubuce, inda suka Æ™ara jaddada Æ™a’idojin rubutu don samar da Daidaitacciyar Hausa,
Daidaitacciyar Hausa ta ginu ne a kan kare-karen gabas tare da wasu gyare-gyare,
misali. Ginin kalmomi da nahawu da wakilin suna, yayin da karin harshen garin
Gusau ya ginu ne akan kare-karen yamma.
4.2 DAIDAITACCIYAR HAUSA
Daidaitacciyar Hausa, ita ce Hausa wadda aka tace ta kuma masana
ilimin harshe a tarurruka daban-daban
suka amince a yi amfani da ita. A shekara ta (1912) an kafa harshe na
Daidaitacciyar Hausa a ƙarƙashin Ɗan Hausa (Hans ɓischer) kuma an ci gaba da ƙarfafa shi har zuwa shekara ta (1988) lokcain da hukumar
harshen Hausa ta tabbatar da shi.
Daga ranar (28) ga watan Fabrairu zuwa (5) ga watan Maris na shekarar ta
(1966) an yi taron a Bamako na ƙasar Mali. An yi kuma taro na biyu a ranar (21) ga watan
Yuni shekarar (1970) a jama’ar Ahmadu Bello Zariya. Taro na uku kuwa, an yi shi
ne a cikin watan Satumba, shekarar (1972) a cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya
ta Jami’ar Bayaro Kano.
An yi dukan wabɗannan taruruka domin amincewa da kalmomin harshen Hausa waɗanda za a riƙa amfani da su da kumarubuta su. Haka kuma,
Daidaitacciyar Hausa ita ce Hausar da ake amfani da ita a wajen rubuta ƙasidu da littattafai,
sannan kuma a wajen sadarwa ta yau da kullum
ta zama ita ce ake amfani da ita.
“Daidaitacciyar Hausa ita ce nau’o’in Hausar da ake amfani da ita wajen
koyar da harshe wajen karaanta labarai a rediyo ko talabijin, ko wajen buga
littatafai ko jaridu da mujallu da sauran klamurarn da suka shafi aikin hukuma”.
Sani (1999).
“Daidaitacciyar Hausa
kasancewarta hanya ce ta baiÉ—aya da al’ummar Hausawa ke magana ko rubutu, to dole ne al’ummar ta kasance
tana magana baiÉ—aya wajen ayyana manufofinta da Æ™udororinta ga ‘yan baya
da ma sauran al’ummar Duniya wato tamkar fitila ce ga al’umma’. Zarruk (1990)
“Daidaitacciyar Hausa ita ce Hausa wadda aka tace ta kuma masana ilimin
harshe a tarurruka daban-daban suka amince da yin amfani da ita. Ya ƙara da cewa
Daidaitacciyar Hausa, harshe ne na wallafa wanda masana ke amfani da ita weajen
koyarwa da rubuta litattafai da Æ™asidu da kuma mujallu”. Wurma (2006:36).
“Daidaitacciyar Hausa samfuri ne na salon magana da dukkan Hausawa suka yi
tarayya a kan sa. Wannan samfuri kuwa kari ne da aka zaÉ“a aka daidaita masa Æ™a’idojin rubutu da na nahawu, kuma
aka adana su cikin litattafai da Æ™amusoshi”. Zarruk da wasu (1990:93)
4.3 TSARIN SAUTI
“Ilimin tsarin sauti ya shafi yadda harshen ke harhaÉ—a sautukansa bisa Æ™a’ida ya samar da ma’ana. Kwararre a wannan fage na ilimi
ana ce da shi masanin sauti n tsarin
sauti” (Sani 1999).
“Ƙwayar sau na iya kasancewa baÆ™i ne ko wasali mai ziza ko marar ziza” sannan akwai
hanyoyi uku da ake amfani da su wajen sifanta kowane irin baƙin sauti kamar haka:
i-
Yanayin furuci
ii-
Wurin furuci
iii-
Matsayin furuci (M.A.Z
Sani 2003:17)
Shima karin harshen garin Gusau ya kan yi amfani da waɗannan ƙwayoyin sautuka na Daidaitacciyar hausa sai dai wani
lokaci karin garin Gusau ya kan yi amfani da wasu keɓantattun ƙwayoyin sauti da suka bambanta da na Daidaitacciyar
Hausa.
D H K.H.G
arinjini Hwarinjini
arinciki Hwarinciki
D. H K. H. G
Kii i Kiihi
isga Hisga
Da i Dahi
Ta i Tahi
Sha i Shahi
Mar i Marhi
Sautin /ts/ marar ziza, ɗan bayan hanƙa zuzau na Daidaitacciyar Hausa ya kan sauya zuwa saytin /tc/ marar ziza, ɗan bayan hanƙa, ɗan atishawa, idan wasalin /i/ ya biyo /ts/ kaitsaye.
Tsinbirewa Ƙcnbirewa
Tsinuwa Ƙcintuwa
Tsinkaya Tcinkaya
Tsibi Tcibi
Tsiyaya Tciyaya
Sautimn /ts/ marar ziza, ɗan bayan hanƙa, zuzau na Daidaitacciyar Hausa ya kan sauya zuwa sautin /tc/ marar ziza, ɗan bayan hanƙa, ɗan atishawa, idan wasalin /e/ ya biyo shi.
D. H K.
H. G
Matsewa Matcewa
Tarwatsewa Tarwatcewa
Kitsewa Kitciwa
D. H K.
H. G
Leɓantattun ƙwayoyin sautuka a garin gusau sautin
/s/ marar ziza, bakanƙe, zuzau, na Daidaitacciyar Hausa a kan leɓantashi a karin harshen garin Gusau zuwa /sw/
D. H K.
H. G
Sacewa Swaacewa
Saaɓa Swaaɓa
Saaata Swaata
Sutin /ÆŠ/ mai ziza, naÉ—e-harshe, haÉ—iyau ya kan sauya zuw /ÆŠw/ mai ziza, doron
harshe, haÉ—iyaa a karin harshen garin Gusau.
ÆŠaaÉ—ii ÆŠwaaÉ—i
Sautin /z/ mai ziza, É—an dasashi, zuzau na Daidaitacciyar Hausa ya kan sanya zuwa /zw/ mai ziza
bahanƙe, zuzau,
Zaage Zwage
Zaarii Zwarii
NASO A KARIN HARSHEN GARIN GUSAU:
“Ya bayyana ma’anar naso de cewa lokacin da sautuka suka haÉ—u da juna a cikin ko jimla, É—ayansu na iya É—aukar kamannun É—aya yadda bambancin furucinsu zai ragu, wato su Æ™ara kama da juna, sautin na iaya É—aukar wata siafa ta wani sautin da ke kusa da shai”
(Bagari 1986)
“Naso shi ne tasirin
sauti a kan lafazin wani sauti daban
cikin kalma , a sakamakon haka kuma, sautukan biyu ko dai su yi É—ibi da juna ko su zamo iri É—aya. Ma’ana sauti guda kan nashe gudia a wannan lamari.
Baƙi kan nashe baƙi baƙi kan nashe wasali, wasali kan nashe baƙi, wasali kuma kan nashe wasali.
Shi ma haka karin harshen garin Gusau ya yi tasiri a kan wabni baƙi, wato baƙi kan nashe baƙi. Misali:
D. H K.
H. G
Barni Banni
Sarda Sadda
Yarda Yadda
Firda Hidda
Karian harshen garin Gusau ya kan ratge wasu baƙaƙe a maimakomn yadda suke a
daidaitacciyar Hausa, wannan yana faruwa ne da Æ™a’idojin rikiÉ—e-rikiÉ—en da ake samucikin ilimin furuci. Misali kamar haka:
D. H K.H.G
Sanar da Sanad da
Samar da Samad da
Kamar da Kamad da
Mayar da Mayad da
Shayar da Shayad da
Shiryar da Shiryad da
Komar da Komad da
Tayar da Tayad da
Karkatar da Karkatad da
Daga cikin kalmomin garin Gusau, akwai naso inda harafin /k/ ke nashe
harafin /r/ na Daidaitacciyar Hausa, ya yin nuna abin da aka mallaka. Misali:
D. H K.H.G
Gonarka Gonakka
Jikkarka Jikkakka
Hularka Hulakka
Muryarka Muryakka
Kujerarka Kujerakka
MALLAKA
Sigarsa ta fuskar ginin jimla. Nahawu fannin ilimi ne na kimiyar harshe
wanda ya danganci ginin jimla. Jima kuma magana ce cikakkiya mai ma’ana wadda
aka gina bisa wasu Æ™a’idojin harshe na musamman. Ginin jimla kuwa kalmomi ne daban-daban da ake
harhaÉ—awa wuri guda a samar hda jimla.
(Sani 1999).
Karin harshen garin Gusau kamar yadda sauran karuruwan
harsunan Hausa suke amfani da kalmomi dabn-daban su ba da jimla mai ma’ana.
Mallaka taa kasu gida biyu kamar haka:
1.
Doguwar mallaka
2.
Gajerar mallaka
Doguwar mallaka, a karin harshen garin Gusau a kan samu doguwar mallama
“nai” a jinsin namiji, da “tai’ a jinsin mace. A Daidaitaciyar Hausa kuwa,
akwai “nasa” dka “tasa”. Misali kamar haka:
“Nasa” ta Daidaitacciyar Hausa ya kan koma “nai” a karin harshen garin
Gusau.
D. H K.H.G
Shanu nasa Shanu nai
FaÉ—i nasa FaÉ—i nai
Hanci nasa Hanci nai
Baki nasa Baki nai
Haure naksa Haure nai
Madubi nasa Madubi
nai
Cokali nasa Cokali nai
Ruwa nasa Ruwa nai
Wando nasa Wando nai
Littafi nasa Littafi nai
Haka kuma a doguwar mallaka “tasa” ta jinsin mace ta Daidaitacciyar Hausa
“tai’ a karin harshen Gusau.
D. H K.H.G
Ƙafa tasa Ƙafa tai
Hanya tasa Hanya tai
Fanke tasa Fanke tai
Ana samun wani bambanci tsakanin Daidaitacciyar Hausa da karin harshen
garin Gusau, wannan kuwa shine, wajen da ake amfani da “wa” a Daidaitacciyar
Hausa, inda take komawa “ma” a karin harshen garin Gusau. Misali:
D. H
Ta yi wa É—iyar ta wanka
Ya yi wa motarsa gyara
Sun yi wa kansu aiki
Ya É—unka wa Musa riga
Ya saya wa yaro gilas
Ta sa wa Abu wando
A karin harshen garin Gusau, kuwa waÉ—annan kamlomi za su koma kamar haka:
K.H.G
Ta yi ma É—iyar ta wanka
Ya yi wa motarsa gyara
Sun yi ma kansu aiki
Ya É—unka ma Musa riga
Ya saya ma yaro gilas
Ta sa ma Abu wando
GAJERAR MALLAKA
A karin harshen garin Gusau babu wani bambanci tsakanin doguwar mallaka dia
gajeruwar mallaka, a gajeruwar mallaka a kwai “nai” da “tai’ na karin harshen
garin Gusau, a mai makon “nsa” da “rsa” Daidaitacciyar Hausa. Misali:
D. H K.H.G
Bakinsa Bakinai
Takalminsa Takalminai
Littafinsa Littafinai
Rediyonsa Rediyonai
Jakinsa Jakinai
Hancinsa Hancinai
Ruwansa Ruwanai
ÆŠakinsa ÆŠakinai
Haƙorinsa Haƙorinai
Batgonsa Bargonai
Kekensa Kekenai
Dokinsa Dokinai
D.H K.H.G
Amaryarsa Amaryatai
Wuƙarsa Wuƙatai
Wayarsa Wayatai
Kujerarsa Kujeratai
Matarsa Matatai
Takardarsa Takardatai
Hularsa Hulatai
4.4 GININ KALMA
“Nazari ne wanda ya shafi ginuwa ta kalma wato yadda kalma ke “kumbura” ta
bada wata ma’ana wato ta kumbura daga tilo zuwa jam’i ko kuma ta kumbura daga
jinsin namiji zuwa mace haka kuma nazarin ginin kalma nazari ne wanda ya shafi
“tsira” wato yadda kalma ke tsira daga aikatau zuwa suna ko daga suna zuwa
sifa”. Mamman (2006) .
“Idan aka ce ginin kalma, saboda ana rusa kalmomi nazari a Æ™wanÆ™wance da kuma daidaitasu” Alhassan
(2005).
“Ya bayyana tasarifi da Æ™irar kalma da ke nazarin Æ™wayoyin ma’ana a harshen da tushen
kalmomi da Æ™a’idojin kumburar akalmomi da na tsirar kalmomi da kuma li’irabin
kalmomi”Fagge (2013: 3)
A Daidaitacciyar Hausa da karin harshen garin Gusau babu wani bambanci
tsakani hanyoyin da ake amfani da su wajen samar da kalma sai da bambanci na É—afi da ake samu wajen samar da jam’in kalma. Misali:
Jam’in É—afi – aye
Tushe ÆŠafi Cikakkiyar kalma ta jam’i
Beb ... ...aye Bebaye
Bok ... ... aye Bokaye
Jaj ... ...aye
Jajaye
Dog ... ...aye Dogaye
Rag .... ..aye Ragaye
Jam’in ÆŠafin ukka
Tushe ÆŠafi Cikakkiyar kalma ta Jam’i
May .... Ukka Mayukka
Ray ... ukka Rayukka
Karn ... ukka Karnukka
Shaf.... ukka Shafukka
Mar .... ukka Shafukka
Tsar ... ukka Tsarukka
Jam’in ÆŠafin UNA
Tushe ÆŠafi Cikakkiyar kalma ta
Jam’i
Zak .... una Zakuna
Kaw... una kawuna
Rag ... una Raguna
Hul... una Huluna
Inj ... una Injuna
Kog.... una Koguna
4.5 MA’ANAR KALMOMI
Karin harshen garin Gusau da Daidaitacciyar Hausa na da kalmomi masu ma’ana
iri É—aya amma sun banbanta ta hanyar
furuci.
D.H K.H.G
Saƙo Satto
Tsami Yami
Masassara/Zazzaɓi Jamti
Cokali Cabi
Wari ÆŠwai
Dankali Kudaku
Nema BiÉ—a
Ɗauri Ƙunshi
Ganewa Lura
Sanyi ÆŠari
ÆŠimame Zahwahe
Zo Taho
ÆŠawainiya Takalihu
Koɓewa Yauɗi/guro
Tafiaya ÆŠar zazowa
Anguwa Shiya
Safe Sammako/Dongo-dungo
Anin/maɓalli Boti
Ido Ijiya
Shara/Bola Juji
FaÉ—a Hitina
Bashi Rance
Akwati Hontimoti
Ƙarya Zuƙi ta malle
Sama bisa
Riga Taggowa
Goshi Suma
Ƙofa/Ƙyaure Gambu
Rauni Jimuwa
Tasbi Tauzaha
Yamutsi Hargitsi
Ƙabaria Koshewa
Rediyo Radi’u
Wara/gala Ƙwai da ƙwai
Maganin sauro Igiyar
lehwa
Koko Kunu
Wari Zarni
4.6 GININ JUMLA
Jumla kamar yadda aka harhaÉ—a Æ™wayoyin ma’ana a samar da kalma haka ake harhaÉ—a kalmomi su ba da jimla mai ma’ana bisa ga tsarin
dokokin nahawu.
“Jumla ta Æ™unshi sauna da abinda aka faÉ—a game da suna. Saboda haka a kan sami wata jumla da ba ta É—auke da aikatau, sannan jimla tana iya zuwa sassauÆ™a ko harÉ—aÉ—É—iya ko sarÆ™aƙƙiya dangane da zubinta ko kuma tsarinta”. Amfani (2013).
“Jimla magana ce cikakkiya mai ma’ana wadda aka gina bisa wasu Æ™a’idojin harshe na
musamman”. sani (1999).
A karin harshen garin Gusau tsarin ginin jumla É—aya ne da na Daidaitacciyar Hausa, sai dai wani É—an bambance – bambance da ake samu na dokokin ginin
jumla. Misali kamar haka:
D. H
1.
Rigar Kande ce
2.
Matar Audu ce, ta zo
jiya
3.
Wata magana ce, Abu ya
yi
4.
Hassabn ya zauna cikin
damshin ruwa
5.
Musa ya fita da safe
6.
An sake buÉ—e makaranta sda yamma
7.
Amina ta kamu da zazzaɓi mai zafi jiya
8.
Sadiya ta yi wa É—anta wanka
9.
ÆŠalibai ba su yi wa kansu abin kirki ba
10. Butar Aude ce, Abu ya fashe
11. Aminu ya saya wa É—ansa kaya
K. H. G
1.
Rigar Hauwa ta
2.
Matar Audu ce, tat zo
jiya
3.
Wata magana ta Abu yayyi
4.
Hassan ya zamna cikin
damshin ruwa
5.
Musa ya hita ton da
sassafe
6.
An sake buÉ—e makaranta da marece
7.
Amina ta kamu da
masassara, mai zahi jiya
8.
Sadiya ta yima É—anta wanka
9.
ÆŠalibai ba su yi ma kansu abin kirki ba
10. Butar Aude ce, Abu ya hwashe
11. Aminu ya sa ya ma É—ansa kaya.
Idan aka dubi waÉ—annan kwatance da misalai da aka yi tsakanin Daidaitacciyar Hausa da karin
harshen Zamfarci musamman a garin Gusau, za a ga cewa ɗan bambancin kaɗan ne doa aka samu. Wannan ya ƙara nuna muna yadda masana da manazarta suka sa ido a kan
Daidauitacciyar Hausa, don samar da Daidaitaccen harshen a ƙasa.
Amma duk da haka, akwai kyakkawar fahimta tsakanin Daidaitacciyar Hausa da
karin harshen Zamfarci musmman a garin Gusau, domin ko wane na fahimtar wani ba
tare da wata matsala ba.
NAÆŠEWA
A wannan babi anyi magana a kan karin harshen garin Gusau da Daidaitacciyar
Hausa da tsarin sauti da ginin kalma da ma’anar kalmomi da ginin jumla. WaÉ—annan muhimman abubuwa su ne aka tattauna a wannan babi
na huÉ—u. A babin da zai biyo baya kuwa shi
ne na biyar taƙaitawa, hasashe da kammalawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.