Babban jigon waƙar shi ne Adalcin mulkin Musulunci da zaluncin mulkin kafirci. Dalilinda suka sa na tabbatar da haka su ne kamar yadda marubucin ya zayyana a cikin wassu baitoci da suka ratsa waƙar tun daga farko har ƙarshenta.


Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci
Ibrahim Mohammed
08060287141

1.     Mu gode Wanda yay yi mu musulimina,
Na Ahamadu Ƙadirawa masu Sunna.

2.     Salati nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu Shugabanmu zuwa ga dina.

3.     Da Allai nai Sahabbai nai Fiyayye,
Da Atbai da Tabi’i-Tabi’ina.

4.     Ku saurara gabatam muslimina,
Ku bi ta ku bar sarautak kafirina.

5.     Musulmi manya-manya da salihansu,
Ka zaɓen mai gabatat muslimina.

6.     Su taru su ɗauki alwashi na ɗa’a,
Ga foron nan na Alƙur’an da Sunna.

7.     Shari’a ko’ina tat tausa kowa,
Ta shuɗe ya ƙi ya so kowane na.

8.     Shi zan yarda da al’amarinsu ya zan,
A ba shi shi hanƙure nauyin abin nan.

9.     Shi ƙarfafa wajibi shi hana haramun,
Kamas salla masallaci shi gina.

10. Riyoji kasuwa hanya tafukka,
Kusheyi don shi sa matsaran abin nan.

11. Talakkawa marayu sa gwagware,
Abin matafa shi nura da alhakin nan.

12. Tsaron aumi tsaron matafa jihadi,
Shi kore masu aikin zalimina.

13. Shi sa matsara gari duka masu gyare,
Da alƙallai su zam masana na Sunna.

14. Shi aiki a tar da zakka kowace ta,
Shi sa a raba talakkawan garin nan.

15. Idan saura a kai ta a ba waɗansu,
Talakkawa a ba ta mujahiduna.

16. Shi aiki a tar da Baitul-mal gari duk,
A sa ta ga maslahatu kan garin nan.

17. Idan saura a kai ta a gyarta wansu,
Kamat gyaran birane don a zamna.

18. Masallatai ribaɗi don karatu,
Ibada don a samo addu’an nan.

19.  Makamayyen jihadi har dawaki,
Da nasu rabo akwai shi ga dukiyan nan.

20.  Da mallammai da alkalai da sauran,
Musulmi duk shi nura da maslahan nan.

21. Shi sa wani shugaban yaƙi shi zamna,
Iyakat muslimina da kafirina.

22. Shi zam shimgi shi daidai ganima,
Shi ɗau humusi shi nisanta amana.

23. Gululi duk shi bar shi shi tsorci Allah,
Ku saurara sarautak kafirina.

24. Saraki su ka ƙarfafa fada zaɓe,
Ga ‘yan sarkinsu wane a juye suna.

25. A ce sarki a ba shi abin sarauta,
Su zuzzuge gaisuwa da kiɗi na murna.

26. Ga al’adunsu kowaz zo shi duƙa,
Waɗansu suna afi ku ji wane dai na.

27. Su gangunma da algaitu kalangai,
Da tabburra abin wasa na sunna.

28. Da jan kaya da gwarje alharini,
Azurfa su abin girmansu ke nan.

29. Galadima magaji uban dawaki,
Yarima sayen kaza manyansu kenan.

30. Shi ɗauki wanda yas so kowane na,
Shi ba shi gari a ce sarkin gari na.

31. Su zage gaisuwa tare da ƙwace,
Su kai ma uban wuta nasu, duk su ƙuna,

32. Dawaki nai da sarki nai na yaƙi,
Su kai mai dukya shi ad da wannan.

33. Su ce doki tufan girma takobi,
Na manya na su amshe duk abin nan.

34. Su bar humusi su tausa sunka saba,
Su ce ko way yi kamu nas kenan.

35. Barori ag gare su da ‘yan barade,
Lifidda ba su tarac cin amana.

36. Gululi ba su istibra ga mata,
Su samu a nan su sa ɗaka, ha wutan nan.

37. Muna roƙonka kai Sarkin sarauta,
Ka sa mu cikin gabatar muslimina.

38. Mu zamna salihina mu sami tsiran,
Sarautak kafirina da fasiƙina.

39. Ka gafarta jama’aƙ Ƙadirawa,
Ka sa mu ciki ga hanayn nan ta Sunna.

40. Mu ƙara godiya mu zubo salati,
Ga Ahmadu mun cika bisa arba’ina.