Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 1: Cin Nasara


    Babban abin da ke damun mutane a yau shi ne rashin tabbacin wurin aiki. Ma'ana kullum mutum yana ƙoƙari ne ya kawo abin da zai tabbatar da shi a inda yake samu. Yana kuma tsoron kuskuren da zai yi a ce masa ya kama gabansa. To in ya sami damar...


    Hanyoyin Cin Nasara a Rayuwa 1: Cin Nasara

    Baban Manar Alƙasim
    Zauren Markazus Sunnah

    In aka ce nasara ana nufin isa ga biyan buƙata, ko samun abin da ake nema, in mutum ya ci nasara to ya iya rinjayar ƙalubalen dake gabansa kenan, kalmar nasara ba ta zuwa ba tare da mutum ya tsallake wani tarnaƙi dake gabansa ba, kenan maganar da Bahaushe yake cewa "Kowa ya ci zomo ya ci gudu" ta zama gaskiya, wani malamimmu Ustaz Ya'ƙub yake cewa ba abin da ake samunsa a bagas, in ka ga mutum ya ba ka abu ba tare da neman wani abu ba, kar ka yi zaton bagas ne ka ci baki bude, ka jira abin da zai biyo baya.
    .
    In ka ba Bature kyauta zai karba ya ajiye sannan ya tambaye ka "Me kake so na yi maka?" Hatta almajirai masu bara ba a jefa musu kudi haka arha, sai sun yi busa ko rawa da za su ja hankalin mutane, sannan a biya su, kenan samun nasara a rayuwa in muka dubi abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa yana nufin cikar burin mutum ne a kan abin da yake haƙilo tuntuni, kamar mallakar gida na kai, yin tafiye-tafiye, ko samun sabbin abubuwa na more rayuwa, kodai mutum ya wayi gari kuma ga kudi a banki bai da buƙatar sai ya fita kafin ya sami na rufin asiri.
    .
    Ko ya kasance yaransa suna karatu a manyan makarantun da ake buƙata, ko kuma a ce kowa na sha'awarsa yana fatar ya zama kamarsa, ko samun wani shugabanci na gwamnati ko na al'umma, ko ya riƙa ganin dandazon mutane suna zuwa wurin wata sana'a da ya fara, koda kuwa ƙarama ce wace ba ta taka kara ta karya ba, idan ya kalli jama'ar kuma ya ga don wannan abin da ya yi ne lallai zai san cewa ya ci nasara a ruwarsa.
    .
    Bai tsaya nan ba, mutum ya rabu da damuwa ma wani abu ne, to bare a ce ba ya tsoron wani abin da zai bijiro masa a rayuwa, kamar a ce ma'aikacin gwamnati ne amma yana da wata sana'a a gefe da take yi masa komai, in yau ya rabu da aikin gwamnatin ba abin da zai dame shi, shi kansa zai ga mutane na girmama shi, in ya yi magana ana sauraronsa ba don ya fi sauran 'yan unguwar ilimi ko girman shekaru ba, tabbas wannan ma zai iya zama cin nasara a rayuwarsa.
    .
    Babban abin da ke damun mutane a yau shi ne rashin tabbacin wurin aiki. Ma'ana kullum mutum yana ƙoƙari ne ya kawo abin da zai tabbatar da shi a inda yake samu. Yana kuma tsoron kuskuren da zai yi a ce masa ya kama gabansa. To in ya sami damar kawar tsoron ya yi nasara kenan, kawar da irin wannan ƙalubalen bai yuwuwa sai in ba wani a samanka wanda zai ce "Kama hanya", bare kuma a ce zai iya daukar nauyin wasu mutane waɗanda a ƙarƙashinsa suke, abincinsu na samuwa ne daga wani abu da ya ƙirƙira, kodai su dauka su je su sayar, ko kuma su taimake shi aiki, ya yanka musu albashi, wannan duk ci gaba ne ( Takbeerut Tafkeer na David p9).
    .
           NASARA CE ASALIN JIN DADI
    Da yawanmu ba su fahimtar nasara da irin wannan bayanin da muka yi domin tunaninsu kawai abin da za su ci ko su rufa asiransu su da iyalinsu, wani ma zai ce maka "In ka sami abida za ka ci ka sha ka yi zumunci ya ishe ka" ma'ana mutum bai da wani abu a rayuwa sai dai wannan, ya manta cewa maganar zumuncin da kudi ake yi, sannan zai yi tattalin abin da yake da shi a yanzu, ta yadda za a same shi a kullum, ko a ƙara yawansa tunda ana haihuwa iyali na ƙaruwa.
    .
    Da irin wannan ne za ka ga mutum ya rayu kullum cikin tsoron rasa abin da yake hannunsa na kudi ko na aiki ko muƙami, kullum hankalinsa yana kan dan kadan din da yake hannunsa, a zahiri duk wanda ya saka a ransa cewa ba zai iya zama wani abu ba da wahala ka ga ya zama din, don ba zai taba yin abin da zai kai shi wurin ba, ko mace da take ganin ita wata ce kar ka zaci tana da abin da wata ba ta da shi ne, ta dauki kanta ne ta kai wani matsayi shi ya sa take jin tabbas tana da matsayin.
    .
    Mutum ya tabbatar wa kansa cewa tabbas zai iya yin kaza, shi zai sa ya fara laluben hanyoyin da zai cimma burinsa, to ko bai sami abin da yake so duka ba za ka ga ya sami wani abin, misali saurayin da yake ganin zai iya riƙe mata, zai iya yin aure ka ga abokinsa da ya fi shi albashi ya cin abinci a gidansa, ga shi da ƙarancin albashin yana zaune da iyali, abokin kuma tsoron ciyarwa da riƙe matar ya hana, ba wani abu yake hana matasa isa wurin da suke so ba sai rashin motsawa tun farko, in ka ga abokinka ya fi ka.walwala da walawa yana aikatuwar da ba ka yi ka bincika, kowa ya ci zomo ya ci gudu.

    1 comment:

    1. Hakika abinda ya ke damun matasan mu kenan musamman graduate daga cikin mu, mukan dauki girman kai tahanyar raina Sana'a sannan kuma ba aikin government sai kaga mutum daga ya gama bautar kasa da wasu 'yan watanni na omo ma sai ya tambaya a gida wanda kuma hakan abin kunya ce a gare mu murungumi kana nan sana'oi kamar su sai da rake, shayi, leburanci da sauran su amma kuma bama jin kunyan tambayar kudin sabulun wanka a gida wannan wace irin rayuwa ce anya zamu iya cimma manufofin mu da irin wannan tinani da mutuwar zuciya, Allah ya sa mu fahinci dai dai mu rufawa kanmu asiri.

      ReplyDelete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.