Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin “Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci”


Ɗangambo, (2007) cewa ya yi abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai. Jigo na nufin saƙo ko manufar abin da mawaƙi yake so ya nuna ga jama’a cikin waƙarsa. Manazarci kan gane jigon waƙa ne bayan ya duba waƙar gaba ɗayanta, sannan kuma ya fahince ta sama da ƙasa daga nan kuma sai ya nutsu cikin kogin tunani domin fitar da jigon waƙar (Abba da Zilyadaini, 2000: 102).


Nazarin “Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci”

Abdul’aziz Sa’idu

07066557745

Gabatarwa
Al’ummar Hauswa kamar sauran al’umma suke wajen yin amfanid ahanyoyi wajen isar da saƙo. Daga cikin hanyoyin da suke bi wajen isar da saƙo akwai waƙa. Waƙa wani furuci ne (lafazi ko salo) cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙaida da kuma yin amfani da dabaru ko salo mai armashi (Ɗangambo, (1981). Waƙa ta ƙunshi ƙoƙluluwar hikima da tunanin ɗan’adam ta yin amfani da ƙwayoyi aunannu cikin kalmomi zaɓaɓɓu, wa ɗanda ake jerantawa cikin tsari fitacce, ta yadda za ta fa’idantar da abin nufi a taƙaice (Yahaya, (1985).
A ƙarƙashin wannan aiki za a yi nazarin rubutacciyar waƙa ne. kafin in shiga cikin aikin yana da kyau in bayyana ma’anar rubutacciyar waƙa da tarihin samuwar rubutacciyar waƙa da tarihin Abdullahi Fodiyo kamar yadda ya ba da gudummuwa a ɓangaren waƙa a ƙarni na sha tara, kuma waƙarsa na ɗauka ta Tsarin Mulki na Musulunci wajen aiwatar da nazari.
Ma’anar Rubutaciyar Waƙa
Sa’id, (1981) cewa ya yi: “Rubutacciyar waƙa ita ce wadda aka tsara aka rubuta ta a takarda don a karanta.” Muktar, (2006) cewa ya yi: “Rubutacciyar waƙa  wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomi da ake zaɓa waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci.
Tarihin Samuwar Rubutacciyar Waƙa
Rubutattun waƙoƙin Hausa sun samo asali daga rubutattun waƙoƙi na Larabci waɗanda malaman ƙasar Hausa suka nazarta dan ƙara fahimtar Alƙur’ani da sauran ilimin addinin Musulunci, tun cikin ƙarni na goma zuwa na sha shida ake tsammanin an fara rubuta waƙar Hausa inda aka binciko wata waƙa ta Wali ɗan Masani wanda ya yi zamaninsa a birnin Katsina ya rubuta waƙoa mai suna Waƙar Yaƙin Badar. Amma haɓaka da bazuwa ya samu ne a ƙarni na goma sha tara lokacin jihadin Shaihu Usmanu Danfodiyo masu jihadi sun wallafa waƙoƙi daga cikin wanda suka rubuta waƙoƙin a ƙarni na sha tara akwai Abdullahi Ɗan Fodiyo.
Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci ta Abdullahi Fodiyo wani ɓangare ne a fagen adabin Hausa mai zaman kansa wanda aka yi tsokaci a kansa wajen yin nazari. A fagen nazari ana buƙata a san abubuwa kamar haka:
1.     Tarihin marubuci
2.     Dalilin yin waƙar
3.     Shekarar da aka yi waƙar
4.     Sunan wanda ya yi waƙar
5.     Sunan waƙar
6.     Jigo
7.     Zubi da tsarin waƙa
8.     Salo
Tarihin Marubucin (Abdullahi Fodiyo)
Malam Abdullahi Ɗan Fodiyo an haife shi a wani gari da ake kira Marnona. A cikin ƙasar Wurno a cikinw atan Jumada Akhir hijirar Annabi Muhammad  (SAW) tana 1180 wanda ta yi daidai da 1766 miladiyya kuma shi Malam Abdullahi ƙani ne ga Shaihu Usmanu Bn Fodiyo. A hanun Shehu ya tashi ya yi tarbiyarsa ya karantar da shi alƙur’ani da fiƙihu da ilimin Larabci da tafsiri da sauransu tun tashinsa tare suke da Shehu, kuma shi ne ya fara yi wa Shehu mubayi’a lokacin da aka naɗa shi sarkin Musulmi kuma Abdullahi jarumi ne domin duk wani mai da martani shi ne ya ke yi kuma jarumi ne wajen faɗa da kuma kariya.
Malam Abdullahi ya haifi ‘ya’ya goma sha tara maza da kuma mata. Daga cikin su akwai: Mahmud, da Halliru da Aliyu da Abubakar da Kadija da A’isha da Maimuna da sauransu. Bayan an gama jihadi Shehu ya raba ƙasashen da aka ci yaƙi ya ba wa Abdullahi yankin yamma.
Malam Abdullahi ya rasu a garin Gwandu a cikin jihar Kebbi a zamanin sarki Muhammadu Bello a shekara ta 1244 hijirar Annabi Muhammadu (SAW), wanda ta yi daidai da shekarar 1828 miladiya, aka rufe shi a can. Malam Abdullahiya rasu yana da shekara 63 a duniya.
Sunan mawaƙin: Abdullahi Fodiyo
Sunan waƙar: Tsarin Mulki Na Musulunci
Dalilin Yin Waƙar
Waƙar na wayar da kan jama’a game da siyasa yadda tsarin mulki na Musulunci da kuma nuna wa jama’a illar mulki na kafirci da zalunci.
Jigon Waƙar Tsarin Mulki na Musulunci
Ɗangambo, (2007) cewa ya yi abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo manufa ko abin da waƙa ta ƙunsa, wato abin da take magana a kai. Jigo na nufin saƙo ko manufar abin da mawaƙi yake so ya nuna ga jama’a cikin waƙarsa. Manazarci kan gane jigon waƙa ne bayan ya duba waƙar gaba ɗayanta, sannan kuma ya fahince ta sama da ƙasa daga nan kuma sai ya nutsu cikin kogin tunani domin fitar da jigon waƙar (Abba da Zilyadaini, 2000: 102).
Saboda haka babban jigon waƙar shi ne Adalcin mulkin Musulunci da zaluncin mulkin kafirci. Dalilinda suka sa na tabbatar da haka su ne kamar yadda marubucin ya zayyana a cikin wassu baitoci da suka ratsa waƙar tun daga farko har ƙarshenta.
4.     Ku saurara gabatam muslimina,
Ku bi ta ku bar sarautak kafirina.
(Bt. 4 ɗango na 1-2)

5.     Musulmi manya-manya da salihansu,
Ka zaɓen mai gabatat muslimina.
(Bt. 5 ɗango na 1-2)


6.     Su taru su ɗauki alwashi na ɗa’a,
Ga foron nan na Alƙur’an da Sunna.
(Bt. 6 ɗango na 1-2)

9. Shi ƙarfafa wajibi shi hana haramun,
Kamas salla masallaci shi gina.
(Bt. 6 ɗango na 1-2)

21. Shi sa wani shugaban yaƙi shi zamna,
Iyakat muslimina da kafirina.
(Bt. 6 ɗango na 1-2)

Idan muka duba za mu ga cewa waɗannan baitoci na goma suna yin bayani ne kan Musulmai a kan mulki na Musulunci da bijire wa mulki na kafirci. Bayan wannan kuma a cikin waƙar ya yi bayani a kan yadda tsarin mulki na Kafirci yake. Ga misali daga cikin baitoci:
23. Gululi duk shi bar shi shi tsorci Allah,
Ku saurara sarautak kafirina.
(Bt. 23 ɗango na 1-2)

31. Su zage gaisuwa tare da ƙwace,
Su kai ma uban wuta nasu, duk su ƙuna.
(Bt. 31 ɗango na 1-2)

35. Barori ag gare su da ‘yan barade,
Lifidda ba su tarac cin amana.
(Bt. 35 ɗango na 1-2)

Idan muka duba za mu ga cewa waɗannan baitoci sun fito da bayani kan mulki na kafirci da kuma zalunci wajen yadda suke aiwatarwa.


Jigon Waƙar a Gajarce
Jigo a gajarce shi ne ƙananan saƙonni da mawaƙi ya yi amfani da su a cikin waƙarsa a lokacin da yake ƙoƙarin gina saƙonsa. Irin waɗannan saƙonni kan zamo wania bin dogara tamkar gwafanni da waɗanda mawaƙi yakan yi domin aza waƙarsa a kai Abba da Zulyadaini, 2000: 104). Wannan waƙar ta Tsarin Mulki na Musulunci ta hanyar baitoci ne za a bi domin fitar da ƙanann jigoginta:
Baiti na 1 – 3 Godiya ga Allah da salati ga annabi da sahabbansa
Baiti na 4 – 7 Biyayyar mabiya ga shugabanni
Baiti na 8 – 22 Ayyukan da suka rataya a kan shuwagabanni masu tafarkin Musulunci
Baiti na 23 – 28 Bayyana tsarin Musulunci da kafirci
Baiti na 2 – 36 Yadda zaluncin mulkin kafirci yake
Baiti na 37 – 40 Addua’ar rufewa da godiya
Warwarar Jigo
A nan za a yi sharhi ne kan jigon gaba ɗayansa. Za a duba shi dagangane da jawabin jigon da kuma abin da waƙar ta faɗa gaba ɗaya a taaƙaice (Ɗangambo, 2007). Sarɓi, (2007: 79) cewa ya yi, warwarar jigo sharhi ne da ya dogara da fahimtar da mai nazari ya yi wa waƙa da kuma irin ƙwarewarsa na sarrafa harshe.
Waƙar Tsarin Mulki na Musulunci waƙa ce da take bayani a kan mulki na Musulunci bisa ga sunan waƙar a cikin waƙar an bayyana yadda mulki na Musulunci yake da kuma yadda mulki na kafirci yake gudana. Bisa ga waƙar an fahintar da mutane game da haƙƙinsu da ya rataya a kan shuwagabanni ta fuskar muli/siyasa da kuma faɗakarwa wajen yadda za su zaɓi shuwagabanni na Musulunci da kuma illa ga akasin haka. Ga misalai daga cikin waƙar:
1.     Mu gode Wanda yay yi mu musulimina,
Na Ahamadu Ƙadirawa masu Sunna.

2.     Salati nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu Shugabanmu zuwa ga dina.

3.     Da Allai nai Sahabbai nai Fiyayye,
Da Atbai da Tabi’i-Tabi’ina.

A cikin waɗannan baitocin marubucin yana yin godiya ne ga Allah da ya yi su Musulmai kuma masu bin tafarkin manzon Allah (S.A.W.).
4.     Ku saurara gabatam muslimina,
Ku bi ta ku bar sarautak kafirina.

5.     Musulmi manya-manya da salihansu,
Ka zaɓen mai gabatat muslimina.

6.     Su taru su ɗauki alwashi na ɗa’a,
Ga foron nan na Alƙur’an da Sunna.

7.     Shari’a ko’ina tat tausa kowa,
Ta shuɗe ya ƙi ya so kowane na.

A baiti na huɗu wanda a nan ne babban jigon waƙar yake, ya bayyana Musulmai su yi koyi da magabatansu kada su bi sarautak kafirina. Sannan wajen zaɓen shuwagabanni su zaɓi salihai, sannan kuma su yi biyayya ga shuwagabannin nasu.
Idan muka lura za mu ga cewa a baiti na takwas zuwa na ashirin da biyu mawaƙin ya yi bayani ne a kan abin da shuwagabanni ke kansu. Ga misalan wasu baitoci nan kamar haka:
9. Shi ƙarfafa wajibi shi hana haramun,
Kamas salla masallaci shi gina.

10. Riyoji kasuwa hanya tafukka,
Kusheyi don shi sa matsaran abin nan.

19. Makamayyen jihadi har dawaki,
Da nasu rabo akwai shi ga dukiyan nan.

22. Shi zam shimgi shi daidai ganima,
Shi ɗau humusi shi nisanta amana.

Bayanan suna nuna ayyukan da suka rataya a kan shugabanni wajen fitowa da abin da ya shafi mulki. Haka kuma a cikin baitoci na shirin da uku zuwa baiti na ashirin da takwas mawaƙin ya bayyana yadda tsarin mulki na kafirai yake. Ga misali daga baitocin waƙar:
24. Saraki su ka ƙarfafa fada zaɓe,
Ga ‘yan sarkinsu wane a juye suna.

27. Su gangunma da algaitu kalangai,
Da tabburra abin wasa na sunna.

28. Da jan kaya da gwarje alharini,
Azurfa su abin girmansu ke nan.

Daga misalan nan na baitoci za mu ga cea ana gudanar da biki ne wajen zaɓar sarakuna da kuma naɗa su wajen yin shagali. Haka kuma abaiti na talatin zuwa baiti na talatin da shida mawaƙin ya fito ya bayyana yadda mulkin kafirci yake da kuma zaluncinsu. Ga wasu misalai daga cikin waƙar:
30. Shi ɗauki wanda yas so kowane na,
Shi ba shi gari a ce sarkin gari na.

31. Su zage gaisuwa tare da ƙwace,
Su kai ma uban wuta nasu, duk su ƙuna,

35. Barori ag gare su da ‘yan barade,
Lifidda ba su tarac cin amana.

36. Gululi ba su istibra ga mata,
Su samu a nan su sa ɗaka, ha wutan nan.

A waɗannan baitoci mawaƙin ya bayyana yadda mulkin zalinci yake a cikin mulkin kafirci, yadda suke mallakewar komai irin su ganima da kuma dukkan wani abu mai kyawu hatta mata ba su bari ba. A baiti na talatin da bakwai zuwa baiti na arba’in ya yi bayani ne wajen kammala waƙarsa aydda yake roƙon Allah ya tseratar da mu daga mulkin kafirai ya kuma gafarta wa jama’ar ƙadirawa ya yi kuma godiya da salati ga fiyayyen halitta annabin rahama sallallahu alaihi wa sallam. Ga misali daga baitocin waƙar:
37. Muna roƙonka kai Sarkin sarauta,
Ka sa mu cikin gabatar muslimina.

38. Mu zamna salihina mu sami tsiran,
Sarautak kafirina da fasiƙina.

39. Ka gafarta jama’aƙ Ƙadirawa,
Ka sa mu ciki ga hanayn nan ta Sunna.

40. Mu ƙara godiya mu zubo salati,
Ga Ahmadu mun cika bisa arba’ina.

A baitocin ƙarshe na waƙar ya yi addu’ar rufwa ta hanayr yin salati da godiya da roƙon Allah ya samu cikin tsari na sunna ya kuma kautar da mu daga mulki na kafirci.
Nazarin Salon Waƙar
Ɗangambo, (2007) cewa ya yi salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo. Za a iya fassara salo (ma’ana) kamar haka, salo wani yanayi ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci. Wannan yana nufin yin amfnai da wata kalma, lafazi yanayi, hanya ko tunani a maimakon wani.
Yahaya, (2002) cewa ya yi, salo a fagen nazarin waƙa wani muhimmin ɓangare ne kandami ne saboda kusan a ce kowane furuci a cikinw aƙa yana cikin wani nau’I na salo. Haka kuma kandami ne saobda a koyaushe mawaƙi yake ƙirƙirar waƙa mais auƙi ne ya zo da wani irin salo wanda da ba a taɓa lura da shi ba. Wannan waƙar ta zo da wasu salailai kamar haka:
a.      Salon zayyanawa
b.     Alamtawa
c.      Salon aron kalma
d.     Saɓi zarce
e.      Karin harshe
f.       Adon magana
Salon Alamtawa
Salon alamtawa shi ne wanda mawaƙi ke kiran wani abu da wani suna wanda a cikin harshen da aka yi waƙar suna ne ƙarɓaɓɓe da ke tsayawa a madadin wancan abu, ko kuma mawaƙin ya ba wani abu suna cikin waƙarsa bayan sunan da aka san abin da shi (Yahaya, 2001: 90). A waƙar an sami alamtawa kamar haka:
6. Su taru su ɗauki alwashi na ɗa’a,
Ga foron nan na Alƙur’an da Sunna.
Salon Saɓi-Zarce
Salon saɓi-zarce salon gangara ne babba. Salo ne wanda kan ɗauki magana daga wani baiti zuwa wani mai bi masa (Yahaya, 2001: 98-98). A cikin waƙar an amu irin waɗannan salo na saɓi-zarce misali:
19. Makamayyen jihadi har dawaki,
Da nasu rabo akwai shi ga dukiyan nan.

20.  Da mallammai da alkalai da sauran,
Musulmi duk shi nura da maslahan nan.
Salon Karin Harshe
Abba da Zulyadaini, (2000: 157) sun bayyana cewa, Hauswa na da akre-karen harshe da suka haɗa da Kananci da Katsinanci da Zazzaganci da Sakwkatanci da Bausanci da Dauranci da Guddiranci da Haɗejiyanci. Sakamakon mawaƙin Basakkwace ne, a cikin waƙarsa ta Tsarin Mulki na Musulunci ya yi amfani da karin ahrshen Sakwkatanci a wurare masu yawa. Ga misali a cikin waƙar:
10. Riyoji kasuwa hanya tafukka,
Kusheyi don shi sa matsaran abin nan.

11. Talakkawa marayu sa gwagware,
Abin matafa shi nura da alhakin nan.

Idan muka lura za mu ga cewa a cikin baitocin nan na sama mawaƙin ya yi amfani da karin harshe na Sakwkatanci.
Salon Zayyanawa
Salon zayyanawa yana nufin amfani da kalmomi a cikin waƙa waɗanda tattare da sauran maganar da suka fito cikinta za su ƙirƙiro siffar abu yanayi a cikin zuciyar mai karatu (Yahay, 2001: 89). A cikin waƙar ta mulki na Musulunci akwai irin wannan salon ga misali daga wasu baitoci:
26. Ga al’adunsu kowaz zo shi duƙa,
Waɗansu suna afi ku ji wane dai na.

27. Su gangunma da algaitu kalangai,
Da tabburra abin wasa na sunna.

A cikin waɗannan baitoci marubucin ya zayyana yadda kafirai suke yin bukinsu.
Salon Aron Kalmomi
Manazarci zai duba waƙar da ke gabansa domin ya tantance shin waƙar an yi amfani da da Hausawa ne ko kuma an yo aron wasu kalmomi daga wani harshe domin kuwa wasu lokutan mawaƙa sukan yo aron kalmomi daga Ingilishi, Filatanci, Larabci da sauransu (Abba da Zulyadaini, 2000: 153). Lallai mawaƙin ya yi aron kalmomin Larabci da ya yi amfani da su. Ga misali daga cikin waƙar:
2.     Salati nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu Shugabanmu zuwa ga dina.

5.     Musulmi manya-manya da salihansu,
Ka zaɓen mai gabatat muslimina.

20. Da mallammai da alkalai da sauran,
Musulmi duk shi nura da maslahan nan.
34. Su bar humusi su tausa sunka saba,
Su ce ko way yi kamu nas kenan.

A cikin waɗannan baitoci mawaƙin ya yi amfani da kalmomin Larabci irin su humusi da dina da sauransu.
Salon Adon Magana
Abbda da Zulyadaini, (2000: 141) cewa suka yi, salon adon magana wannan wata hikima ce da mawaƙa ke amfani da ita wajen ƙara wa waƙar su zaƙi da armashi a wasu lokutan. Adon magana kan zo da siga irin ta karin magana. A cikin waƙar an samu salon adon magana a ciki. Ga misali daga baitocin waƙar>
31. Su zage gaisuwa tare da ƙwace,
Su kai ma uban wuta nasu, duk su ƙuna.

Ya bayyana a baiti na na 31 cewa mai mulkin kafiri uban wuta.
Nazarin Zubi da Tsarin Waƙar Tsarin Mulki na Musulunci
Ɗangambo, (1981) ya bayyana kalmar zubi da tsari ta ɓangarori guda biyu. Zubi da tsari na gaba ɗaya da kuma zubi da tsari na cikin baitoci. Zubi da tsarin waƙa hanay ce ta shimfiɗa waƙa baki ɗayanta dangane da layuka da baitoci da amsa-amo da kuma jerantawar tunanin marubuci wajen kaiwa ga manufarsa Sarɓi, 2007: 80).
A ƙarƙashin zubi da tsari za mu duba waɗannan abubuwa ne:
a.      Mahaɗi
b.     Marufi
c.      Tsarin baitoci
d.     Amsa-amo
e.      Kari
Mabuɗin Waƙar Tsarin Mulki na Musulunci
A waƙar Tsarin Mulki na Musulunci mawaƙin ya buɗe waƙar da godiya ga Allah da salatin annabi (SAW) da sahabbansa ga misalai daga waƙar.
1.     Mu gode Wanda yay yi mu musulimina,
Na Ahamadu Ƙadirawa masu Sunna.

2.     Salati nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu Shugabanmu zuwa ga dina.

3.     Da Allai nai Sahabbai nai Fiyayye,
Da Atbai da Tabi’i-Tabi’ina.

Mabuɗin idan an lura ya fara daga baiti na 1-3.
Marufin waƙar – Ya rufe waƙar da roƙon Allah da neman gafara sannan daga ƙarshe ya yi godiya ga Allah. Misali a daga baitocin waƙar:
37. Muna roƙonka kai Sarkin sarauta,
Ka sa mu cikin gabatar muslimina.

38. Mu zamna salihina mu sami tsiran,
Sarautak kafirina da fasiƙina.

39. Ka gafarta jama’aƙ Ƙadirawa,
Ka sa mu ciki ga hanayn nan ta Sunna.

40. Mu ƙara godiya mu zubo salati,
Ga Ahmadu mun cika bisa arba’ina.

Tsarin Baitocin Waƙar Tsarin Mulki na Musulunci
Wannan waƙar ta Tsarin Mulki na Musulunci tana da yawan baitoci guda arba’in (40) kuma tana da yawan layuwa ko ɗango tamanin (80). Tsarin baitocin ‘yar ƙwar biyu ce.
Amsa-Amo
Ɗangambo, (2007) ya ce, amsa-amo shi ne sautin (gaɓar) ƙarshe na kowane ɗango. Shi wannan ya kasu kashi biyu, amsa-amon waje da kuma amsa-amon ciki ko kuma babban amsa-amo da kuma ƙaramin amsa-amo. Saboda haka, babban amsa-amon wƙar shi ne “na” da kuma “nan” domin kuwa akwai wurare da ake samun canji na babban amsa-amon waƙar.
Sannan ƙaramin amsa-amon waƙar yana canzawa daga baiti zuwa baiti. Wani ya zo da “na” wani kuma “wa” da sauransu. A taƙaice dai waƙar ba ta da takamaimai ƙaramin amsa-amo.
Karin waƙar Tsarin Mulki na Musulunci
Kari ko ma’aunin waƙa shi en tsari na daidaita ƙafafu ko gaɓoɓin layukan cikin baitocin waƙa, wato ya zama idan an yanka ta ta dangane da ƙafafu za a ga sun yi daidai idan kuma an auna ta dangane da nau’o’in gaɓoɓin, wato masu nauyi da marasa nauyi z aa gan su daidai (Sarɓi, 2007: 32).
Waƙar Tsarin Mulkin Musulunci tana da karin “Wafi” (Bawafira ce). A wannan karin ana maimaita ƙafa ta 3 ne ita kaɗai sau biyu ko uku ko ma sau huɗu, mufaa alatun.

Kammalawa
Lura da jawaban da suka gaba a kan nazarin waƙar Tsarin Mulki na Musulunci za a ga an kawo ma’anar rubutacciyar waƙa da tarihin samuwar rubutacciyar waƙa. Daga nan kuma aka ɗora ta bisa nazari inda aka fara da tarihin mawaƙi, sunansa dalilin yin waƙar bayanin jigo, jigo a gajarce da warwarar jigo da bayani a kan salo, sannan kuma aka kammala ta da zubi da tsari aka rufe ta.

Post a Comment

0 Comments